Sashe 30
Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 10 min read
Da ya zo bai shigo ba ya kira ni a waya ya ce na fito na same shi. Hijabi nasa har kasa na rufe fuskata da nikab da zan fita na ce Yusura ta kulle gidan ta ciki idan na dawo sai na buga.
Can tsallake na hangi motar wata kala ce daban domin bata nuna alamun tasa ba ce wata'kila ya yi hakan ne domin kada jama'a su gane wanene tunda duk motacin da yake tu'ammalli suna da alama wannan babu wata alama sai ta lamba. Sukairaju na jingine a jikin motar shi ma fuskarsa rufe da fece mark.
Ina karasawa ya risina mini muka gaisa kafin da sauri ya bud'e mini motar na fara ko'karin shiga yana hakimce cikin k'ananun kaya da rigar sanyi mai kauri a sama. Kansa sunfuke da hula irin ta sanyi har kunne ya rufe idanuwansa sakaye da gilashinsa na ka'ida.
Na zauna sosai kafin Sukairajun ya shiga ya ja mota.
A hankali na furta." Barka da dare, ya jikin?"
Yana kallona ya amsa "Barkanmu dai ya gajiya?"
Shiru na yi ban bashi amsa ba, shi ma bai sake magana ba wata'kila ya yi hakan ne saboda kusantuwar Sukairaju tunda kallon da ya yi mini da farko shi ya tabbatar mini da cewa akwai magana a bakinsa.
[9/11, 6:25 PM] Aunty B: 79
Gidansa na unguwar sharada kwanar ganduje wajan gidan Hajiya Mariya shi ya fi kwanta mini a raina dalili akwai alkarya a wuraran kuma daf da titi ne, bayan haka kuma ya yi kusa da wajan gidan Sahura dukda akwai 'yar tazara amma dai ba sosai ba za mu dinga samun sau'kin ganin ganin juna mussaman daga bangaranta.
Gidane iya gida wanda aka narka dukiya wurin gina shi, gini mai k'wari da nagarta da kuma ababen more rayuwa sabo ne ga dukkanin alamu ba a jima da gama aikinsa ba. A gyare yake ko'ina sai da ba a shirya shi da furnitures ba da sauran kyale-kyalen zamani gidan ya yi mini sosai domin bai kai girman na legos ba ya yi daidai da zama babu tsoro da fargaba.
Ya ce tunda shi na zaba to shi ma ya yi masa gobe kuma zai sanya a shirya mini komai na ce to shikkenan. Muka shishiga ko'ina muka duba muka hau saman benan ya bud'e wani d'aki a saman wanda shi kadai ne a dan shirye shi ma ba komai ba ne sai babban kafet da tuntu manya manya irin na sarauta uku, da manyan labuleye da suka kewaye d'akin.
Muka shiga d'akin yana gaya mini watani shida da suka gabata ya yi wani bako daga kasar senegal shine ya sauke shi a d'akin a dalilin tsaro da rashin yardar mutumin wai ya ji labarin najeriyar ta lalace da 'barayi masu satar mutane shine yake jin tsoron zuwa ya kwana a hotel. Anan ya sauka tsayin sati hud'u har ya kammala abinda ya kawo shi ya tafi.
Dariya kawai na yi domin nasan mutumin yana da gaskiya najeriya ta lalace sai da ta katsan-tsanan.
Ganin ya nemi wuri ya zauna har da kishingida a jikin tuntu na ce masa yana da kyau ya tashi mu tafi saboda dare ya fara yi goma har da minti biyar ga gari na damuna, ga kuma yarinyar mutane na bari a gida ita kadai.
Bud'ar bakinsa sai kawai ya ce." Ai kin zo kenan Hajiya kayanki kawai zan tura Sukairaju yanzu ya d'auko miki." Ya fad'a babu alamun wasa.
Da mamaki mai yawa a tare da ni na ce." Kai ma kasan hakan ba mai yiwuwa ba ne, ko ka manta da cewa na bar yarinyar mutane a gida, kuma me yasa Sukairaju zai je ya d'auko mini kaya ba ni da sirri ne, ai ba haka muka yi da kai ba.
Ya tashi zaune sosai yana kallona ya ce." Ba mu yi haka ba, amma yanzu na yanke hukuncin yin hakan domin ban ga amfanin komawarki wannan gidan ba tunda babu wanda za ki yi wa sallama."
Raina a b'ace na tsaya kawai ina dubansa gabad'aya ma bakina ya mutu da masifar takaicinsa na rasa ma wane nazari zan yi.
ya yun'kura ya tashi yana ce wa. " Tunda ba ki aminta da Sukairaju ya d'auko miki kayanki ba ni ne ba kya so ba huta to zan koma tare dashi zan had'o miki kayan tare da yarinyar shikkenan ko ."
Shiru na yi ban iya cewa dashi komai ba. Ya d'auki gilashinsa da ya ajiye ya sanya ya tashi yana sa takalminsa hanyar fita ya nufa na bi shi da ido ina jin wani bala'in takaicinsa, da gaske dai yake na zo kenan amma mutumin mugun dan rainin wayo ne, shiyasa wasu lokotan baya ba ni tausayi.
Zamana na yi gabad'aya jikina babu k'wari na fito da wayata daga cikin jaka ina dubawa goma da minti ashirin a ganina yanzu kafin su dawo har sha daya na dare ta yi. Ni hankalina ma ya fi tashi akan yarinyar mutane da take amana a hannun
Ina nan zaune tsit babu motsin komai sai uban hasken fitilu a ko'ina, tsoro ya dan shige ni na zame na kwanta a hankali ina kiran sunan Allah kad'aici ko kad'an bashi da dad'i
Wajejen goma da minti arba'in kira ya shigo wayata na duba sai na ga lambar Sukairaju ban kawo komai ba na d'aga na ji shi cikin tashin hankali .
A tsorace da kidima na tashi zaune." Hatsari Sukairaju Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! na tashi tsaye da wayar a kunnane yana fad'in." Ki d'an samu nutsuwa duk muna lafiya babu wanda ya samu mugun rauni Yallabai ne ma ya samu targad'e a 'kafa. Hawaye ya fara sauka a saman fuskata na ce.'' Ita yarinyar fa ina fatan lafiyarta lau, kuma ya aka yi hakan ta faru? kuuna Ina yanzu."
Ya ce." Ga mu nan bakin titin rijiyar zaki wajan Musa iliyasu.
Na ce." Garin Yaya haka ta faru Sukairaju ina Yallabai din bashi wayar ina so mu yi magana."
Shiru na ji sai tashin iska gabana yana ta bugawa na ji gyaran muryarsa kafin ya ce." Babu wani ciwo mai muni fa ki kwantar da hankalinki."
Na ce." Yanzu kuna Ina ku dawo gida don Allah dare ya yi ina Yusura tana nan lafiya ko."
A nutse ya ce." Gata nan kusa da ni tana lafiya babu abinda ya sameta, ni ne ma na yi gocewar
'kashi a k'afata za mu zo yanzu."
Ya kashe wayar bai jjra jin abinda zan sake fadi ba.
A tsaye na wanzu har Allah Ya sa suka shigo gabad'aya Sukairaju da akwatin kayanmu ni da Yusura shi kuma yana dan jan kafarsa amma jikinsa kalau daidai da gilashinsa yana idonsa.
Zuciyata ta dan yi sanyi na dubi Yusura sai zare Ido take yi kamar ma a tsorace take idonta da alamun kuka.
Na kama hannunta muka shiga d'akin ta zauna jikinta a sanyaye. Shi kuma yana can nesa saman kafet tunda d'akin da girma sosai yana tattare kafar wadonsa da ya ji ciwo. Na tsaya kawai Ina dubansa ina jin wani iri a a jikina, na san akaina duk wannan abin ya same shi, ina ganin idan ban yi hakuri na zauna dashi cikin ko wane irin yanayi ba Allah zai iya saka masa.
Sukairaju ne ya shigo ya ajiye kayan a gefe, shine kuma ya gyara masa targadan tunda ba yadda bai yi dashi ba tunda lamarin ya faru su wuce asibiti a duba shi wurin da ya goce asa magani ya ce a a baya son haniyar jama'a, za su dame shi da zuwa dubiya harda masu neman labari tunda abin ya faru cikin dare wajan da babu idananun jama'a sosai kuma ba a fahimci wanene ba kawai magana ta mutu motar ma a can suka barta bakin wajan da abun ya faru suka shigo babur din adaidaita sahu. Mamaki mai yawa ya kama ni. Lallai na yarda soyayya babu abinda bata sanyawa, tana k'askantar da mai mulki mai saurata attajiri mai ilimi da sauransu.
A wannan ga'bar na jinjina masa sosai kuma na yaba masa har cikin raina.
To shi dai Sukairaju ya san mota lafiyarta lau tunda sabuwa ce bata da wata matsalar komai amma bai san ya akayi har 'kososhin tayar baya suka kwance ba sai da lamarin ya faru wanda Allah ne kadai ya auna arziki da sai da a ji mummunan labari tunda sitiyarin motar da ya k'wace daga hannunsa kifawa motar ta yi da kyar suka fito.
Kwana muka yi ba mu rintsa ba muna tattauna maganar ni da shi yana zargin dai akwai masu bibiyarsa tun bayan zuwansa zai dai tsananta bincike.
Da gari ya waye muka tashi da gyara masu aiki suka zo domin su kintsa gidan.
Sukairaju ya fita ya samo mana abinda za mu ci. Da muka yi waya da Hamusu na gaya masa yadda akayi amma ban fad'a masa tsautsayin da maigidan ya samu ba ya ce zai zo da yamma.
Yusura kam yarinyar na da nutsuwa kasa zama ta yi tare damu a d'aki daya bacci ma jiya dan barawo ne ya sace ta kuma don ba yadda za ta yi ne ta kwana a d'akin wai sai ta fita sai da na yi mata jan ido tukkuna na nuna mata gidan sabo ne ko ta fita babu d'akin da za ta samu a kintse balle ta kwanta shine ta takure a wata kusurwa ta rufa da hijabinta. Da safe kuwa ta fice wai zata duba gidan .
Jiya dai da abin ya faru jikinsa lafiya lau banda targadan da ya yi sai kujewa a daf da gwiwarsa bayan wannan kam babu wata matsala sai da garin ya waye kuma ya fara kuka da ciwon ga'bo'bi na ce masa asibiti ya kamata ya je a duba shi sosai ko da daddare ne tunda yana gudun idonanun mutane wata'kila akwai abinda ya bugu a jikinsa ya ce ba zai je ba na kyale shi kawai. Gabad'aya na rasa yadda zan yi da sha'aninsa jikinsa ya nuna alama yana buk'atar ganin likita. Ya d'auki wayarsa Ina zaune ya kira Sukairaju wallahi na zaci ya d'auki shawarata ne ashe ba haka ba ne, koda Sukairaju ya shigo sai ya rufe shi da fad'a irin wanda ban ta'ba ganin ya yi masa irinsa ba domin kuwa a cikin yaransa na tabbatar da cewa yana sonsa kuma tasu ta zo daya. Fadi yake yi da kai za a had'a ba ki a kashe ni ko Sukairaju me ya sa na d'auki amana ragamar kula da rayuwata shige da fice na da duk wani motsina amma za ka bada goyan bayan cutar da ni, ban aminta da kai ba a wannan ga'bar jiya na yi maka shiru ne domin ban gama nazari akan faruwar wannan lamarin ba, yanzu zuciyata ta amince mini da hadin bakinka wajan ganin kun kai ni kasa in banda kai babu wanda ya san na shigo garin nan ya aka yi har k'ososhin jikin sabuwar motata za su zube baka sani ba, ina kake ina ka ajiye motar ? Kai ne ka cire k'ososhin ko kuwa wani ka biya ya cire domin biyan buk'atarku wannan amsar nake so ka ba ni tun muna biyu ni dakai ka fito ka gaya mini asalin abinda ya faru.
Ya zube a gabansa cikin tsananin damuwa da tashin hankali yana cewa." Wallahi Yallabai ban san yadda aka yi ba, kuma zargin da kake yi mini ba haka ba ne, ba ni da niyyar cutar dakai Yallabai shekara nawa muna tare menene ban samu ba ta dalilinka, babu abinda ba ka yi mini ba na rayuwa idan ma na cutar da kai nasan Allah ba zai barni ba, a ko'ina ne zan iya sadaukar da rayuwata akan taka rayuwar ni dai nasan lokacin da muka koma unguwar domin d'aukar kaya daka bar ni a bakin mota ka shiga gidan na dan zaga baya domin yin fitsari da na yi sai na fito sai na tsaya sayan lemon fata anan bakin titin dai shikkenan abinda na sani, ina kuma tunanin wannan damar aka samu har ka cire k'ososhin motar ni kaina ranka ya dad'e na fara zargin akwai hannun Alhaji Sammani a ciki dalili nasan tunda ka rubuta masa takardar sallama ba zai ta'ba ha'kura ba mutum ne ma'ketaci wata'kila yana bibiye da kai har ya gano kaine ake d'auka a motar dukda boyewar da ka yi, kuma ranka ya dad'e jama'a da yawa sun san kana garin nan tunda shekaran jiya mun shiga asibitin Malam Aminu cikin motocinka wanda kowa ya sanka dasu, to ka ga bibiyarka ba zai yi wa wanda yake burin cutar dakai wahala ba.