Sashe 32
Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Da fargaba na tashe shi domin yin sallar la'asar ganin hud'u har da rabi ta yi nasan ba a yi masa gwaninta wani lokacin to amma ai babu biyewa son rai wurin take umarnin Ubangiji ina ganin idan har na bar shi ya cigaba da barcin lokacin sallar ya kure ina da lefi, bayan haka kuma shi kansa baccin gabanin la'asar ko bayanta Annabi ya yi hani dashi.
Ya tashi kuwa da d'an sau'ki jikin nasa don har gumi yake yi yana gabatar da sallar ya nemi abinci don da alama cikin magunguñan akwai wanda ya ke bud'a ciki kuma wai towon dawa irin wanda na yi masa a gidana.
Ban yi masa jayayya ba na fita na duba cikin store din duk kayan masarufin da Sukairaju ya zube babu na towo babu dawa balle alkama sai samovita sai shinkafar towo.
Na fita na sanar masa Ina dasu a gidana zan kira Hamusu yanzu sai ya je ya kawo mini. Da yake yana buk'ata bai ce a a ba.
Na kira Hamusu na yi masa bayani sosai yadda zai fahimta na kuma bashi kwatancen gidan, da yake dan halak ne awa daya da yan mintoci sai gashi a babur dinsa ya kawo mini komai.
Sosai ya ba ni tausayi saboda hidimar da yake yi a kaina ko ciki daya muka fito iyakacin abinda zai yi mini kenan. Ya kuma ki tafiya wai lallai yana so ya gaisa da magidan kafin ya tafi. Sai na nufin saman zuciyata na dan bugawa na same shi yana waya da wani mutum na dan tsaya kimanin minti goma ya kammala kafin ya dube ni kadaran kadahan na ce." Hamusu ne yake so ku gaisa yana kasa na ce bari na nema masa izini."
Ya d'anyi jim kafin daga bisani ya ce." Ya shigo mana."
Na juya babu k'wari a jikinsa. Na same shi a falo suna dan hira da Yusura na ce .'Ka hau saman d'akin da yake kallonka yana ciki.."
Ya tashi da sauri yana fadin." Bari na sauko yarinya sai kin gaya mini sunan saurayinki tunda ni ba kya sona."
Na dube shi da mamaki yana hawa benan na dawo da kallona kanta sai sinne kanta take yi na ce." Cewa ya yi yana sonki ne?"
Ta daga kanta tana dariya kafin ta ce." E, mana, ni kuwa na ce masa ai ina da saurayina."
Murmushi na yi da cewa." A Ina saurayin naki yake ko shine dan gidan Yayar babanku wanda Sahura take gaya mini."
Ta daga kanta da kunya mai yawa a tare da ita. Na ce." Hamusu kenan shi ma ai da alkawarin auran wata a wuyansa ko ta biyu zai yi dake ne?"
Da sauri ta ce.'' A a mama ni fa ba na son kishiya." Ta fad'a har muryarta tana rawa nasa dariya ina fadin." To shi wanda kike so din kina da tabbacin ba zai yi miki kishiya ba."
Shiru ta yi bata ce komai ba. Sai kawai na girgiza kaina na wuce kicin da tunanin halin kuruciya yarinyar.
Cikin nutsuwa na fara gudanar da aikina gefe guda kuma ina cigaba da nazarin yanayin rayuwar nan ta duniya wato dai muddin kana raye ka dinga ganin abubuwan al'ajabi da ban mamaki kala kala.
Muryar Hamusu na ji a kicin din yana fad'in." Anti ni zan tafi?''
Na juyo Ina dubansa yanayinsa ya nuna mini ba a nutse yake ba domin damuwa muraran ta bayyana a tattare dashi.
Cikin nutsuwa na ce." Shigo ciki mu yi magana."
Ya shigo yana sunkuyar da kansa kasa, tausayinsa ne ya kama ni har na ji kwalla ta cika idona tabbas mutumin nan akwai maganar da ya gaya masa wadda ta sosa masa rai da wahala ka ga Hamusu cikin irin wannan yanayin mutum ne mai ha'kuri da yawan fara'a ba ka taba gane yana cikin damuwa koda kuwa akwaita a tare dashi.
Na ajiye rariyar da take hannuna na ce." Ko ba ka gaya mini ba nasan abinda yake da akwai amma ina so ka sani ban goyi da bayan wannan zargin da ake yi maka ba, kuma duk inda za mu je ina nan akan bakana ban goyi da bayan a tozartaka ba a shirye nake da barin auran akan a wulakantaka Hamusu na zauna dakai nasan halinka kiyashi ba zaka kashe da gangan ba balle har ka yi yun'kurin kashe mutum. Bincike dai ban hana shi ya yi ba, amma rashin sanin wanda ya aikata ba zai sanya a gazgata cewa kaine ba, ai alheri ba ya zama sharri Hamsu ka samu nutsuwa kuma kada kada damu gaskiya zata bayyana.
"Wallahi anti gabad'aya a cikin fargaba nake ya za a yi na aikata wannan mummunan aikin me ya yi mini da zan yi yun'kurin kashe shi a yake gaya mini fa wai lallai da sanya hannuna wurin faruwar hakan, wallahi tallahi anti ban aikata ba, ai mutumin nan alheri ya kamata mu yi masa duba da abubuwan da yayi mana na sadaukarwa da taimaka ko k'aunar jininmu da yake yi ya cancanci sadaukarwa ta kowane fanni, shiyasa hidima idan tasa ce wallahi ba na gajiya koda kuwa zan kwana a tsaye. Na yi mamakin jin wannan furucin daga bakinsa anti duk da duniya ta lalace akan samu irin hakan amma wallahi ni ba na daya daga cikin butulayen mutane."
Na ce." Kada da ka damu Hamusu ka shige ka je ka cigaba da sabogiginka hankalinka kuma ya kwanta barazana yake yi maka domin akan bincike yake har yanzu shi ma bai gama tabbatarwa ba."
Ya girgiza kansa a sanyaye ya ce." Shikkenan anti ni ma kuwa ba zan bari ba wallahi zan tsananta bincike na kuma sanya ido domin tonuwar asirin wad'anda suka aikata hakan."
Na ce." Shikkenan hakan ya yi amma don Allah kada ka gayawa kowa maganar nan Hamusu ka barta cikin ranka." Ya ce." Na yi alkawarin yin hakan in sha Allahu rabbi anti.