← Book details Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 33

Sashe 31

Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Jin ya yi shiru kansa a kasa shi ya tabbatar mini da cewa maganganun Sukairaju sun kar'bu a wurinsa. Na ce." Kada ka yanke hukunci cikin fushi, ka yi bincike dukda abin akwai rikitarwa amma ba na tsammanin za a had'a ba ki da Sukairaju a cuce ka."
Ya dube ni kafin ya ce." Za a had'a ba ki da Hamusu kenan?"
Da tsananin faduwar gaba na ce." Hamusu kuma?"
"Kwarai kuwa bayan shi wanene makusancinki?wanene ya kawo ni gidanki ta yaya za a kwance k'ososhin dake jikin tayar motata babu sanin Hamusu."
Na gyad'a da zullumi mai yawa a tare da ni na furta." Ba na tsammanin haka ranka ya dad'e, dukda dai ba a shedar mutan amma Hamusu ba zai aikata hakan ba."

"Me yasa kai tsaye ki ka fad'i haka umm?" Ya fad'a idonsa a tsaye akaina cike da zallar tuhuma da mugun zarginsa da ya motsa.
Shiru na yi domin kuwa ba na so mu jayayya agaban Sukairaju.
Ganin haka ya dube shi tare da ba shi umarnin fita.
Ya tashi yana fad'in." Na gode Yallabai, amma ya kafar taka Ina fatan bata yi maka ciwo ko?"
A takaice ya ce." Ta warke Sukairaju na gode, kada ka yi nisa zan iya nemanka a kowane lokaci."
Ya d'an risina yana godiya kafin ya kama hanyar fita.
D'akin ya yi shiru ni fargaba da damuwa sun ishe ni, zuciyata nata tsalle da k'in rashin amincewa Hamusu zai aikata mini haka. Wata zuciyar tana ce mini Amina makashinka fa yana gindinka, ba ki san menene a zuciyarsa ba zahirinsa kawai ki ka sani.
Hawaye masu zafi suka fara kasa tsere a kumatuna idan kuwa hakan ya tabbata lallai Hamusu ya cutar da ni ya zalinci kansa ya zalince ni, ya 'bata mini nasabar yarana."
Ya nisa kafin ya ce." Har yanzu ba ki yarda da maganata ba ko?"
Girgiza kaina na yi a raunane na ce." Ba wai ban yarda ba ne, abun ne kawai yake ba ni mamaki da al'ajabi."
Sai ya girgiza kansa yana fad'in." Ni ma zargi na ce Ina yi ba wai na ce shi din ba ne, amma dai kin san shine mafi kusa dake da ni, kuma shine ya yi mini jagora gidanki, kafin Sukairaju ya san inda nake wanene zai je ya kwance 'kososhin mota?"
Ina kuka na ce." Yanzu ka gama fad'a zargi kawai kake yi baka tabbatar ba, to me zai sanya ka tsaye ba tare da ka tsananta bincike ba ka nuna shine, kenan zargin da kace ka na yi bashi da amfani kawai ka fito fili ka ce Hamusu ne yake yun'kurin raba ka da duniya shikkenan sai zambu da gugar zana su 'kare."
[9/13, 10:30 AM] Aunty B: 80
Ganin yadda hankalina ya tashi da maganar da ya yi akan Hamusu ya sanya bai sake tashin maganar ba, amma nasan ba wai ya ha'kura ba ne ya yi shiru ne saboda bashi da tabbas akan abinda yake zargi. Ni kaina ba wai na ce Hamusu ba zai iya aikata hakan ba ne, ai da adam ne wanda yake tattare da ajizanci amma amincewa kai tsaye bashi ne adalci ba. Muna nan dai zaune ni dashi cikin rashin sukuni ya kira personal doctor dinshi a waya ya yi masa bayanin yadda yake ji a jikinsa gabad'aya ko'ina ciwo yake yi masa ga rashin test a bakinsa da zazzabi kad'an. Doctor din ya ce zai yi masa text na magunguñan da zai sa a sayo masa domin yanayin bayanin da ya yi masa yana tunanin zazzabin maleria ne ke so ya kama shi.
Ban yi mamaki ba da farko kukan ciwon jikin da yake yi na d'auka tsautsayin da suka samu ne ya ce shi babu wani waje da ya bugu a jikinsa bayan 'kasan giwarsa da targad'an da ya yi. Tabbas zazza'bin kuwa zai iya kama shi sakamakon sauron da ya cije shi a gidana. Ya kira Sukairaju domin ya zuwa wajan sayar da magani ya sayo masa. Kafin shigowarsa na ce." Ni da za ka d'auki shawarata da ka je asibiti ba fa a wasa da lafiya."
"Ba ina da ni ." Amsar da ya ba ni kenan babu walwala a fuskarsa. Sai na yi shiru kawai na zuba masa ido yana da wani irin hali muddin bai so yin abu ba to babu wanda ya isa ya tursashi, ni kuma a tunani na zuwa asibitin kamar zai fi muhimmanci ko da yake wannan din ma ga dukkanin alamu babban likita ne tunda ba zai d'auki likitan da bai san aikinsa ba domin duba lafiyarsa ba.
Zuwa la'asar gidan ya shiryu ta ko'ina har kicin komai ya ji, da alama masu aikin sun jima suna murza zaransu domin ni na d'auka za su iya kaiwa dare basu gama ba.
Suka tattara kayan aikinsu suka tafi lokacin ma shi maigidan yana bacci saboda ya sha magani. Ni da Yusura muka zagaye ko'ina dakuna ukun da suke falon dukkunnsu a shirye kowane da set din gado kewaye da labuleye masu kyau falon set din kujeru biyu ya ci masu kyau da tsada da labuleye wad'anda suka dace wurin tibi ma yasha ado mai d'aukar hankali ko'ina hasken fitilu irin na zamani sun shirya mini kicin dina tsaf duk abin buk'ata babu wanda babu da alama kamfanin sun jima suna yi masa aiki.
Sukajiru ya dinga shigo da kayan abinci yana jibgewa a store din dake cikin kicin din da yake da yalwar gaske.
Gidan ya ba ni sha'awa sosai kuma daidai misali domin bai cika girma na d'aukar hankali ba sai dai an tsara shi sosai daidai zaman da babu tsoro kuma babu takura.
Chapter 31 · 0% Book details