Sashe 18
Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Tunda ba ni da hakuri ta fannin jima'i shiyasa kake zargina da zan iya neman namiji idan buk'ata ta motsa mini baka kusa."
"Ni ban fad'i haka ba Amina, wani abu ne nake ji game dake a can kasan zuciyata na rasa yadda zan cire shi kin san ranar da ki ka wayi gari a gidana ban rufe miki ba na gaya miki ni mutum ne mai kishi, a duk lokacin dana tuna wasu mazan sun sanki kafin ni wallahi ba na iya sarrafa kaina Ina shiga wani irin kunci da damuwa."
Ban yarda da maganarsa ba dalili nasan zai iya amfani da mayaudaran kalamai a wannan lokacin da ya ga ina nema na yi masa tutsu domin ya shaho kaina. Ai shi mai hankaline kuma mai shekaru ne sannan kuma kishi ba hauka ba ne, mata nawa manzon Allah s.a.w ya aura a matsayin zawarawa kuma ya rayu dasu cikin aminci bai zargesu ba.
"Kin ji ko, ki yi hakuri idan Allah Ya kaimu gobe zan shigo garin sai mu tafi jibi, hankalina sai ya fi kwanciya idan kuna kusa da ni."
A nutse na ce." Ba zai yiwu ba na gaya maka ba na so mu yi ta jayayya akan hakan yadda nake ha'kuri da dabi'unka a wannan ga'bar ni ma sai ka yi hakuri da abinda nake so."
Shiru ya yi bai ce mini komai ba, na dubi wayar na ga mun kai kimanin minti ashirin da wani abu muna magana ana ta janyewa Hamusu kudi. Na ce" Zan bashi wayarsa."
Bai ce mini komai naga ya datse kiran. Na ja tsaki a fili na furta shekarunka da iliminka sam ba su amfana maka komai ba. Wai kishi idan dashi din akwai hali da d'abi'a, tunda har yanzu ya'ki aminta da ni, yau ya bijiro da wannan fitina gobe ya bijiro da wata a wannan karon kuwa zan nuna masa ikona babu ruwana da kudi da shekarunsa dole na mutunta kaina.
Ban bashi wayar ba sai da na binciketa tsaf domin wata wayar takan ajiye recoding na goge komai sannan da ya shigo ya kar'ba tare da yi mini sallama ya tafi.
Sai da na yi wanka tukkuna na zauna a nutse na ci abinci hankalina a kwance yanzu na dan fara samun sasaauci a cikin raina.
Kiran anti Yagana ne ya shigo wayata a lokacin da muke magana da Sahura ta whasap tana ce mini gobe da wuri zata zo, na ce ta taho mini da Yusura ta d'an zauna mini tunda sun yi hutu.
Cikin fargaba na daga kiran na san dai fad'a ne zan sha shi akan abinda na yi wa Sukairaju ilai kuwa da abinda ta fara kenan yayin da kunnena yake jiyo mini sautin kukan Yusi.
"Ke da na ce miki daga zarar kin sauka ki kira ni shine don iskanci saboda kin san abinda ki ka yi baki kira ni ba, kin kyauta Amina, ke duk yadda aka yi dake sai kin b'atawa mutum rai, kin ce mutumin nan ya zo ya d'auki Yusi saboda tsabar rashin mutunci ashe yaudararsa ki ka yi yaro yana ta murna suka tafi tasha suka tarar bakya nan, to gashinan tun jiya yake kuka abincin kirki ya kasa ci.
[9/2, 5:52 PM] Aunty B: 72
Cikin ko'karin danne dariyar da take so ta kwace mini na ce." Anti Yagana ki yi hakuri don Allah wannan fad'a haka ko hadiyar yawu fa ba kya yi, ki yi hakuri ni kaina rashin kyakyawan network ne yasa ban kira ki ba amma na sauka tun kafin magriba. Zan kira Sukairajun a waya yanzu gobe sai ya kawo yaron. Amma Yusi ya cika shakiyi wallahi kawai ya sanyanki a gaba yana kuka kamar bai sanki ba."
Ta ja tsaki har yanzu da sauran b'acin ran a tare da ita ta ce." Ai duk ke ce ki ka janyo koma menene da farko ai da ki ka nuna ba za ki dashi ba ya ha'kura daga baya kuma ki ka ce a zo a d'aukeshi ya ba zai yi kuka ba."
Na ce" Anti Yagana kaina bisa wuyana ki yi hakuri."
'Kwafa ta yi bata ce komai.
Na ce." Alhaji Tajudden ya kira ki a waya ne?" Na tambayeta ne domin na san zai iya bi ta kanta wajan ganin ya tilastani."
"Bai kira ni ba wani abun ne ya sake faruwa?"
Na ce." A a, magana ce dai muke yi ni dashi, ya ce ya mayar da ni, to ba ni da yadda zan yi dole nayi hakurin cigaba da zama dashi kodan farincikinki amma fa ba zan koma legos ba anti na gaji da zaman can wallahi, na amince duk lokacin da ya ga dama ya zo ya same ni anan din sai ya ajiyeni a wani gidan.''
"Wannan kuma tsakaninku ne ke za ki janyo hankalinsa har ya amince da bukatarki, ni menene nawa a ciki."
Na ce." Anti Yagana na san zai iya kiranki ya gaya miki ne, ni kuma ga abinda na yanke."
"Ni dai hudubata ki bi mijinki Amina wannan ce a tsakaninmu, aure kuma ba inda ba ya kai mutum, da farko ni ma ban so zamanki a can ba amma daga baya dana je na ga wurin da kike zaune cike da tsaro sai hankalina ya kwanta, maslaha ce tsakaninku ni ban ga abin ja'in ja ba, tunda yana da wata matar a can ba lefi ba ne don ya bar ki anan din."
"Ni ma abinda na gani kenan, kuma kin ga harkokina sun yi karfi sosai, zamana anan din zai sake kawo cigaba."
"Kada dai ki gaya masa haka zai ga kamar da niyyar hakan a cikin ranki yasa ki ka ce za ki zauna, ina ce Hamusu yana tsaya miki akan komai Amina har yanzu zuciyarki tana yi miki sha'awar rayuwarki ta baya ko."
"Wallahi ko daya anti Yagana kawai dai zuciyar ce a haka, ko kad'an ba na son zama ina so naga ina juya kudi suna shiga suna fita, kuma ba na so komai na rayuwa ya gagareni."
Ta sauke ajiyar zuciya tana cewa.'' Abu ne mai kyau hakan, amma ke za ki yi kokarin shawo kansa ya aminta da buk'atarki don wallahi ni dai ko ya kira ni ya gaya mini ban san abinda zan ce masa ba."
Na ce." Zan jajurce akan hakan anti in sha Allahu kuma zai kyaleni. Sallama muka yi, ban bukaci ta ba ni Yusin ba domin zuciyata tana iya karyewa kukan da yake yana ta'ba ni daurewa kawai nake yi.
To koda na kira Sukairaju a waya akan maganar yadda za a yi ya kawo mini yaron gobe ya ce mini ai tuni ma sun yi magana da ogansa gobe da wuri za su taso. Na ce masa shikkenan idan sun sauka ya kira ni a waya Hamusu ya je ya d'aukosu tunda ba sanin inda nake ya yi ba.
Bacci na yi sosai babu wata fargaba da tsoro tunda gidan ba bak'ona ba ne, bayan haka kuma yaran shago sukan kai karfe daya na dare suna aiki kafin su rufe shagon kuma a bakin titi muke duk dare idan ka farka ba zaka rasa jin motsi ba.
Wajan shida da rabi Babanmu ya kira waya dan kiran ne ma ya tashe ni daga baccin da ya kwashe ni bayan sallar da na gabatar. Na daga da dan faduwar gaba domin wayar safe haka take da sanya fargaba ko alheri za a gaya maka idan kaga kira irin wannan dole ka ji wani iri.
Sai da naga mun gaisa a tsanake babu tashin hankali a muryarsa sannan hankalina ya kwanta na saki ajiyar zuciya.
Nutsuwa na yi ina sauraran maganar da yake gaya mini cikin rarrashi da ko'karin nuna mini cewa na bi mijina ga dukkan abinda ya umarce ni, sannan kuma na yi koyi da Mamanmu wadda ta har ta rasu bata ta'ba yi masa jayayya ba, ya kuma kawo mini misali da ita kan cewa itama haka ta ha'kura da iyayenta da 'yan uwanta ta biyo shi saboda samun ladan aure."
Zuciyata ta d'an karye kad'an amma ban saduda ba, yana fara maganar na fahimci inda ya dosa mutumin nan ya kira shi ya gaya masa akan matsayar da na tsaya, saboda ba na son yin jayayya dashi ya sanya na ce masa shikkenan zan bi umarinsa idan hakan zai faranta masa rai. Aikuwa ya dinga yi mini addu'a da fatan alheri wadda har na fara nadamar hakan da na yi masa domin ba har zuciyata na aminta ba.
Cikin damuwar hakan Sahura ta zo ta same ni domin goma na safe ma anan ta yi mata tunda ba aiki a ranar. Zuwanta da minti ashirin Hamusu ya zo da kayan abinci da duk abinda zan buk'ata kafin ya wuce asibiti wurin Gwaggwo na ce ya gaya mata da yamma za mu zo ni da Sahura in sha Allahu.