← Book details Dr Zayyad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 36

Sashe 9

Dr Zayyad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kawai takeyi shigowwa fateeman ne yasa tayi saurin rarumar hannunta suka zauna abakin gado, "Mama meyafaru ne?" "Hmmm fateema kenan ai infadamiki tsinanniyar matar can kinga kuwa yadda take bawa zayyad abinci abaki kamar wani karamin yaro" "Hmmm aini abinma daure min kai yayi, nan mama ta labarta mata abinda yafaru" Cikin yanayin damuwa da zubar da hawaye fateema take fadamata cewa, "Mama dama ai nafadamiki cewar naji umma tana cewa ita da abinda zai yiwuma aida yar gida za'ayi da ya zayyad da khadija" "Amma ai run awancan lokacin kincemin babanku Ummaru yace tabar maganar ma kar wani yaji ko?" "Eh hakan yace wai bazai taba yiwuwaba" "To ki kwantar da hankalinki fateema nayi mini alkwarin saikin mallaki zayyad ahannunki" Murmushine yasubucewa fateema tareda cewa, "Allah shi yadda mamanah" "Amn yar kirki yanzu kije ki wanke fuskarki ,Sannan kuma kamar yadda nafadamiki karki yadda ko yar uwarki Amina tasan kinason zayyad" "Insha allahu mama babu Wanda zai SANI" Washe gari da safe kuwa yakasance ranar alhamis zayyad ya tashi da shirinsa na zuwa gurin aiki, Bangaren su umma yafara shiga atsakar gidan ya isketa tana aikace aikacen gida kasancewar zainab tayi safiyar tafiya school, Dasallama yashigo tareda gaisheda umman tasa, Ko kallonsa batayiba Yakima maimaita gaisuwar tasa nan ma ba amsa , Daya daga bakinsa zai sake maimaitawa tsam yaga tabar gurin tashige falo, Ko ba'a fara masaba tasan tabbas ta tsuniyar gizo bata wuce ta koki, Kada kansa kawai yayi tareda sauke nannauyar ajiyar zuciya, Aransa yaketa sake saken wai yanzu ita wannan yarinyar badama wani ya ta bata sai su kama sababi saboda antabo yar gwal, Tabe bakinsa yayi tareda yin sallama afalon bakowwa,hakan yasa yanufi bedroom din umman tareda yin sallama, Aciki ciki ta amsa yashiga tareda dukawa agabnta ya sunkuyar da kansa kasa tareda fara cewa, "Umma Dan allah kiyi hakuri" "Ashe kama San kayi laipi kenan,Dan zayyad wai meyake damunkane?" "Ai ni ban taba sanin bakada kunya ba,shin zayyad wai bakajin kunyar ammi ne?" "Zayyad koni Dana haifeka bana dawainiyar da ammi takeyi akanka,yanzu haka inka bincika bataci abinciba saboda bakajeba" "Zayyad ina guje maka hakkin wannan baiwar allah,ace bakada abin tsana aduniya sai jinin matar da tafi kowwa kainarka," "Ni bance maka idan khadija tayi laifi karka hukun ta taba kayimata kamar yadda kake yiwa kowwa,amma meyasa ita zaka dinga yimata abubuwa har asamu wasu su rings ganin tsanar dakakeyimata tafara yawa" Ko ba'a fada masa ba yasan yarinyar nan itace Munafukar data fadawa ummansa abinda yafaru,amma wllhy zai canza salo akan ta munafuka kawai, "Shi kenan umma kiyi hakuri insha allahu hakan bazai sake daruwaba" "Da dai ka kyautatawa kanka zayyad nidai nafadamaka gsky" "Insha allahu" "To allah yatsare" "Amn" yafada gamida mikewa yayi waje abinsa, Yana ganin bangaren baba safiyanu yadauke kansa kasancewar abinda mama tayimasa jiya, Aguguje yashiga part din baba Iro abakin kofar falo ya iskesu aunty maimuna tarako amininin NASA kuma uba agareshi zai tafi gurin aiki, Kasancewar baba Iro bawai yagirmi yaya zayyad sosai bane, "Gsky auntynmu kin rike wuta,watam har yanzu oga bai tafi kasuwarba ko?" "Cikin raha baba Iro yace, " gwauro ma bai tafi gurin aiki ba bare kuma mai iyali" Haka dai suka Dan taba raha tareda gaisawa suka fito, Adaidai part din ammi suka rabu inda baba Iro yawuce zai hau abin hawansa yatafi, Dr zayyad kuwa bangaren ammi yashiga, Akan dining ya isketa tazuba abinci ta ijiye agabanta tanata juya cokalin, Bata ma San zayyad yashigoba kasancewar ammi akwai saka Abu arai Dan run jiya take wannan tunanin gaba daya ma Rabin kanta ciwo yakeyimata sosai ma kuwa, Cokalin yazare daga hannunta hakan yasatayi firgigit gamida sakin wata boyayyar ajiyar zuciya, Murmushi ta kakalo tayimasa tareda cewa, "Gsky zayyad bakada dama to Dana tsorata da na zura da gufu fa" "Hmmm ammi kenan ainasan ammita jarumace shiyasa Nana wani dar akanki" Zayyad yafada lokacin da take zama akan dining daukeda murmushi afuskarsa yana kokarin kwantarwa da ammi hankali kasancewar yahango damuwa karara akan idanunta, Amma dayake ammi macece mai kokari yasa bats bukatar wani yasan halin da take ciki musamman ma zayyad din, Doya da kwai taxuba masa a plate tareda zuba NASA hadadden kunun gyadar dayaji madara acikin Kofi ta turamasa gabansa, Ahankali yafara kai hannunsa yadauki doyar tareda kaiwa bakinsa ya gutsura, Lumshe idonsa yayi tareda bude su ahankali aranshi yake ayyana baiwar tsafta dakuma iya girki irinna ammi, Kara dauka yayi yakaiwa ammin bakinta, "Zayyad kaci abincinka karka makara lokacin aiki banaso kazamto daya saga cikin masu cin haram," "Zayyad karka manta cewar koda da minti daya ka makara agurin aiki da gangan sannan kuma kacimusu kudin albashi complete to kaci haram" "Hakan yasa kaga kullum nake karfafa maka gwiwa akan karinga tafiya aiki da wuri hakanne zai bamu kwarin gwiwar ragargazar albaahinmu cikin kwanciyar hankali kasancewar halal din danane" ammi tafada tana murmushi, "To shikenan ammi zan tafi amma sai kinyimin alkawarin zakici abinci ki koshi" "Zanci zayyad dina amma kaimafa saikayi min alkawarin zakaje kagaisheda hajiya" Badan ran zayyad yaso ba ya amsawa ammi saidan yakara kwantar mata da hankali, Ya amsamata da confidence tareda daukar brief case dinshi dakuma mukullin motarshi ammi tayomasa rakiya kamar yadda tasaba tatimasa addu'a yafita yadauki hangar part din hajiya11 to abangaren khadija kuwa kasancewar yau batada lectures yasa tunda safe ta tashi take shirin tafiya zoo road gidan gidan goggo halima kasancewar kullum goggo halimar tana korafi akan rashin zuwan khadija gdn ganin kowwa yakanje amma ita khadija bata fiya zuwaba, Gashi allah yadorawa goggo haliman kaunar khadija danma hajiya tahanata rikon khadija ne yasa yanzu khadijar bata hannunta, Tunda tafadawa goggo halima zatazo yaya baffa Dan mijin goggo halimar yaketa faman kiranta, Kasancewar tasu tazo daya sosai da yaya baffa yasa mutane dayawa suke tunanin ko soyayya sukeyi, Abangaren yaya baffa ma y ana matukar son khadijar aransa saidai ganin kamar it's khadija kwata kwata bata ra'ayin hakan yasa ya kyaleta ganin kamar Idan yatakuramata Dan zumuncin dake tsakaninsu, Aduk sadda yaya baffa da khadija suka zauna suna hira takan nunamasa itafa kwata kwata bata da ra'ayin wata soyayya, Hakan yasa yabar a in azuciyarsa har said lokacin da ta yarda dashi dakanta amatsayin masoyi, Yanzu hakama yaya munir take jira kasancewar shi zai sauketa agidan goggo haliman kafin yawuce gurin aikinsa, Tana zaune afalo tayi shirin tafiya, Sanye take cikin doguwar rigar abaya kirar Dubai, kasancewar ta fara sosai yasa rigar mai ruwan maroon dakuma afon golden din duwatsu tayimata kyau matuka, Wani kalar rolling head yayi da Dan karamin mayafin bawata kwalliya yayi sosai ba amma yayi masifar kayu, Rike take da wayar ta kirar Samsung yana game kasancewar khadija ma'abociyar son yin game, Hajiya CE agefe azaune tana lazimi da casbaha ahannunta, Baba ummaru ne yayi sallama "Assalamu alaykum" Khadija ta amsa tareda mikewa Dan girmamawa tac, "Abba sannu da zuwa" "Yawwa khadijana sannunki da gidan" Har kasa taduka bayan abban yazauna ta kuma gaishe shi, Cikin fara'a da Nina tsan tsar soyayyarsa ga yar tasa ya amsa, Dan Baba Ummaru yana daya saga cikin spotters din khadija agidan, Komawa tayi kusadashi tazauna tajingina da kafafunsa kasancewar khadija ma'abociyar son jiki, Shaka suketa Dan taba hira har hajiya ta shafa addu'ar tareda mikewa taba cewa, "Sannu da ahigowwa yaro",kasancewar sunan da take kiranshi kenan, " kashigo inata lazimi itakuma wannan magen harta rabo jikinka,aini bansan irin Hadiza ba wllhy" Dariya Abba yadanyi tareda zamowwa yarankwafa yana gaisheda hajiya, Amsawa hajiyar tayi daga nan kuma suka fara Dan taba fira, Yaya zayyad ne yayi sallama tareda shigowwa falon Ganin Abba A falon yasa shi Dan sakin fuskarshi daga murtuketan dayayi, Akan daya daga cikin kujerun falon yazauna tareda tareda gaisheda hajiya, Ayadda yagaishe da ita itama haka ta amsa Adan fisge, Har ga allah lamarin hajiya da yaya zayyad zai baka mamaki Yakuma baka dariya musamman idan dayan su yana fishi, Abba ma Dan murmusawa yayi aransa take ayyana fadan hajiyar da zayyad yanzu da ace abban zaiyiwa zayyad fada to da tasa sai tafi zafi akan ta zayyad din, Aciki ciki khadija tace, "Yaya zayyad INA kwana" Ko kallonta zayyad baiyiba yamaida hankalinsa akan abbansa dayakeyi masa magana akan matsalar yaron daya yi karaya amakotansu, "Eh Abba amma ai no dakaina nacemusu wannan kafar tasa dama bai kamata atsaya ana jagulata agidaba,sannan nakuma cemusu su kaishi nan dala orthopedic har takadda nabasu dakuma nmb wayana amma basu yi komai ba", Yacigaba dacewa, " ni INA ganin abarsu kawai Abba may be sunfi bukatar aci gaba da jagwalgwala kafar ne agidan" "Aa kaje dai gurin aikinnaka kadawo inyaso sai.mu shiga gabaki dayanmu daga nan maga yadda za'ayi" "Badamuwa Abba sai na dawo" yamike gamida daukar mukullin shi, "Adawo lpy" cewar hajjaju, "Amn" yafada tareda nufar kofar falon, Har yakusa fita Abba yadakatar dashi, " ammm zayyad yawwa damage cewa nayi katafi da kanwar taka mana wai gidan goggonku zataje tun dazu take jiran munir shiru,wata kila kuma makara yayi shiyasa yawuce kadai San yanayin aikinsu," Abban nagama fadar hakan yadauke kansa yamaidashi kan TV sabodama kar zayyad din yakawo masa wani raini, Agsky daba Abba bane yafadi wannan maganar to ba shakka zai iya jayayya dakoma waye, Amma kashhh! Saidai kuma bazai taba sabawa mahaifinsaba saboda waccan makirar yarinyar saboda ya tabbatar wannan yana cikin ahalin munafurcinta, Watakam shi zatayiwa shune da Abba saboda tsabar ta rainashima shine zai kaita unguwa, Hmmm lallai kuwa ta dakko ruwan dafa manta, Amma bkomai cikin ruwan sanyi zaiyi maganinta,yafada aransa , Khadija kuwa wani iron faduwar gaba CE ta ziyarceta wllhy bazata taba bin wannan mugun ba cabbbb, Ai wllhy ta gwammace tafasa ma ta hakura, Kashetama ake so yayi kenan kafinma suje Inda zasu, Jin shirun yayi yawa yasa Abba cewa, "Zayyad are u OK" Dasauri zayyad yace , "Yes Abba tasameni a mota" "Nidai Abba wllhy nafasa zan jira yaya munir din gobe sai muje inyaso sai in fasa kwanan" Khadija tafada aahagwabe tana rirrike hannun abban, Wani mugun bakin ciki ne yatasowa zayyad, Wani ysushe yarinyar nan tayi mugun rainashine har haka,.... Tunaninsa yakatsene lokacin da yaji hajjaju nacewa khadija, "Gsky Hadiza bakida halin kirki kwata kwata wllhy,yo INA amfanin mutuminda baza'a tana bashi uamarniba sai yayi gardama," Shi yanzu zaidun da aka likamasa ke yatafi
Chapter 9 · 0% Book details