← Book details Dr Zayyad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 36

Sashe 15

Dr Zayyad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hanyar" Dasauri Dr zayyad yakawadda kansa tareda cigaba da ambaton innalillahi azuciyarsa "Dr yaya?" "Patient na bukatar taimako cikin sauri aganina kawai tunda yanzu nasan parent dinka sun iso zaifi kyau akai musu takadda sucike Dan cigaba bata taimako ta hanyar rai ko mutuwa" Sosai Kalmar mutuwa akan ammi take saka zuciyarsa daci hakan yasa ya furzarda wani mugun iska karon farko tunda yashigo asibitin yayi magana, "Kar abari kowwa yasan za'ayimata wannan taimakon gaggawar adaukko takardar incike" Dr binta CE tacire safarta tareda bude room din ta fito, Har rige2 ake wajen tambayar ya ake ciki, Kallon hajiya likitar tayi tareda kakaro murmushi ganin halin dasuke idan akafadamusu gaskiyar yanayin datake ciki to komaima zai iya faruwa yasa tace "alhamdulillah" Koda yanayinta ya tabbatar musu tana sone ta kwantar musu da hankali amma sunji Dan sanyi aransu hakan yasa suka koma suka zauna gabaki daya su suna nema mata sauki agurin ubangiji, To a can gidan ma hakan ne yakasance musamman ma bangaren samarin gidan kowwa yayi jugum kasancewar agurin kowwa ammi uwace, Bangaren baba Iro ma aunty maimuna CE tasaka su gaba sukayi alwalla suka dukufa nemawa ammin lapiya, Hakama mama karama da umma karama da su aunty zainab da aunty rukayya, Dr binta CE ta dawo dauke da takadda tamikawa Dr zayyad da Biro kawata kawata hannunsama kyarma yake dakyar yasamu yasaka hannu a inda ake bukata, Tabbas da ace Dr zayyad zai iya yin kuka today shine zai zamemasa Abu mafi a'ala acikin rayuwarsa danganeda yadda zuciyarsa gabadaya take abushe dankare da damuwa dakuma Bacin rai, Har sun fara Dora koriyar Riga da firsmask afisakar su sukaji ammi taja wani dogon numdashi Wanda yasa aguje suka fara rige rigen zuwa kanta, Gabaki daya kirjinta sai fat fat fat yake tareda sake wani wahalallen numfashi, Kankace me tuni sun maidamata oxygyn din tareda yimata duk taimakon daya dace kafin suka fito, Gabaki daya yan gurin ganin Dr zayyad yasasu tasowwa amma banda Baba isuhu Wanda yakaranta musu akan lamarin, Bayani yayi musu akan cewar ansamu ta farfado Dan haka yanzu zasu iya tafiya gidan abar mutum daya kawai agurinta, Abba ne yace to umma ta tsaya sukuma gabaki dayansu su tafi gida sai zuwa gobe idan allah yakaimu, Ahaka suka dawo gida karfe sha biyu da yan mintina gabaki dayansu har Dr zayyad kasancewar kawai manyan likitoci masu aikin dare kuma zasu kula da ita sosai kamar yana nan, Sadda suka isa gidan shiru gabaki daya yan gidan sunyi bacci hakan yasa kowa Yakama bangarensa, Su khadijama tuni sun shige day an dakin itada ummy da al'hussain kasancewar aunty maimuna fonitures dinta bibbiyu aka kawota dasu, Hakan yasa koda baba isuhu yadawo yashige dakinsa baimasan suna part dinsaba, Kasancewar khadija bata samu osasahen bacciba kuma ga kukanda tasha yasa tunda yayi sallar asuba bacci yasake dauketa akan daddumar, Ita kuma ummy ganin khadijar ta samu bacci yasa bata tasheta ba tabarta tavigaba da baccinta, Tanufi part din mamar, Abba kadai ta iske Avalon ahima har yashirya zashi asibitin suka gaisa, Agurguje ummy tashirya kasancewar zasu makaranta itada fateema tunda su suna da lectures kuma zasu biya asibitin su gaiaheda ammi, Koda aunty maimuna ta leko taga khadija bata farkaba ita ma kyaleta tayi tacigaba da baccinta, Karfe takwas da rabi gabaki daya mutanen gidan suka shirya zuwa asibitin, Umma karama dasu aunty rukayya da aunty zainab mama karama da ma ma babba da ameenatu duk sun fito kasan cewar baba Iro yace tabar khadijan idan tatashi sa taho tareda su, Duk sun hallara a farfakiyar gidan baba ummarune yace mazan su hau motar yaya munir yayinda yace hajiya da mama babba da umma karama su hau motar sa, Yaya mamman akace yaje yacewa yaya zayyad inya shirya yazo yadauki sauran amotarsa, Abangaren yaya zayyad kuwa tunda suka dawo daga asibiti yakasa samun sukuni abubuwa dayawane duke yawo akansa yama NASA tunanin me zaiyi, Ba abinda yafiyimasa yawo a kwakwalwa sama da maganganun mama musamman ma akan waccan izzatun yarinyar, Shin shi yaishema yataba magana da mamar akan cewar khadija tana likewa maza? Sosai yaringa tunani akan abubuwa dayawa Wanda sanadin hakan ya haifar masa da ciwon kai hakannema yasa baiyi bacciba sai wajajen karfe biyu ahima bayan yayi alwalla tafara nafila daga bisani baccin ya kwasheshi Wanda yasa shi dakyar yatashi da wani masifaffen ciwon kai yayi sallar asuba kafin yakoma baccinda baitashiba har yanzu, Ganin kofar dakinnasa arufe yasa yaya mamman bugawa Wanda hakan yatashi Dr zayyad daga bacci, Cikin magagin bacci yace, "Waye" Daga waje yaya mamman yace, "Yaya zayyad nine mamman dama Abba ne yace inka shirya kafito kadauki sauran mutanen muje asibiti" "OK mamman kace masa wllhy na makarane yanzuma zantashi " Yafada cikin muryar bacci17 "OK " Yaya mamman have tareda komawa yasanarda abban sakon yaya zayyad, Dole baba safiyanune yadauki motar sa shima tareda cewa sauran yaran su shiga, Har kowwa yashiga amma mama babba tana hanga idanu kota hango khadija amma batagantaba kuma bataga alamun zata fitoba, Lallai kuwa yarannan watakam sun hada meeting ne akan sai kowwa yatafi sannan su taho,itadama ba tun yanzuba take tunanin duk rashin jituwar munafurcine tsakanin khadija da zayyad din amma aboye akwai wani abin, "Wai ina ita khadijan ne ko ita bazataba" Mama babba tafada kamar bawani Abu azuciyarta, Baba ummarune yacewa amima taje takirata abangaren hajiya, Harzata tafi aunty maimuna tacewa baba ummarun ai khadijan tana part dinta tana bacci kasancewar jiya bata samu isasahen bacci ba yasa abban alhusaain yace abarta sa taho dashi da ita da hajiya, Baba ummarunne yace "badamuwa Ku kushiga muje" Sosai wani mugun bakin ciki yatasowwa mama babba aranta tace, "Lallai itama matar Iro ganinakefa kamar tafara wuce gona da iri tayi wata kwafa acikin ranta" Azahiri kuwa sai ta wayance dacewa, "Allah sarki ai khadija akwai sawa rai damuwa,totunda hakane ke aminatu kifito kije gurinta tunda dai taku tafi zuwa daya ki lallabata ta tashi taci abinci tayi wanka inyaso saiku taho tare" Tafada tareda kallon aminatun takashe mata ido gamida cije lebe batareda kowwa yaganiba, Sosai aminatu tadauki haske da maganganun mahaifiyar tata,hakan yasa tayi azamar fitowwa, Sosai kowwa agirin ya yadda da maganar mama babba batareda sakawa ransa komaiba kasancewar babu Wanda ke kawo wani Abu aransa, Saidai kuma aunty maimuna taga sum abinda mama babba tayi sannan kuma ranta yadarsa mata wani Abu amma kuma bata fahimci komaiba haka suka dauki hanya yayinda aminatu kuwa tawuce part din aunty maimuna, To abangaren merry kuwa yau tunda sassafe ta tashi tadafa ingantaccen ruwan shayi tareda soyayyen dankalin turawa da kwai dakuma lafiyayyen bread, Bayan yayi wanka tasaka wata wadatacciyar doguwar riga tareda daukar wani kyakkyawan zumbudeden hijab tasaka tadaura nikab afuskarta, Bakaramin kyau shigar tayimataba kasancewar bata saba dayintaba hakan kuma bakaramin takurata yayiba, Agsky badan soyayyar Dr zayyad data takurawa rayuwartaba da babu abinda zaisaka ta kunshe jikinta cikin wannan urban lafta laftan kayan, To saidai kuma soyayya daban take musamman ma kaunar datakeyiwa Dr zayyad din wadda take junta har cikin bargonta, Haka ta fito daga gidannata da basket din Mayan break din tahau motarta rayi hangar asibitin malam aminu kano, Ahanya takira wata nmb bugu biyu aka daga ko sallama babu tafara dacewar, "Kamal kudifa nake biyan ka Dan kayimin aiki amma bazaka taba kiranaba saidai ni nakiraka natambayeka Abu" Daga dayan bangaren kuma akace, Hajiya merry kiyi hakuri naso kiranki wayannawanefa ba kati sannan kuma kinga INA bakin aiki kamar yadda nafadamiki cewar adokar aikinmu bawanda ke sauka daga bakin aiki sai lokacin saukarsa yayi" Tabe bakinta tayi tareda rausayar da murya tace, "Naji,ya aka tsaya" "Eh to har yanzu dai mutunen naki baizoba amma naga yanzu yan gidansu sun shigo" "OK badamuwa" Takashe wayarta tareda yin wani katsssss da cingam din bakinta days zamar mata kamar wata doka, Koda aminatu tashiga part din aunty maimuna ta Tatarar da khadija na bacci, Tsayawa tayi akan khadijar tana karemata kallo, Anya kuwa hasashen mama gskyne akan cewar akwai wani Abu tsakanin yaya zayyad da khadijar, Tabe baki tayi tareda samun gefen gadon ya zauna aranta tana saka cewar komaidai menen to yaya zayyad natane ita daya kuma tafi wannan alwashin, Sosai ta tsare khadija da kallo batun yauba take tunanin wai me khadija ta fitane datake da nasarar da ita ba tada ita, Hakadai tacigaba da yan sake2 da tunanin abubuwa daban2 Khadija CE tajuya da addu'a abakinta tareda mikewa tana salati, Ahankali tafara murza manyan idanunta harta budesu tangaram akan aminatu datake zaune akan gado da wayarta ahannunta, Ziro sambala2 kafafunta tayi kasa tareda saka silifas din daauke gefen gadon, Da kasan ido aminatu Kebin kjafijar da kallo batareda ta San tanayiba ta Dan Tabe bakinta ahankali tareda dauke kanta kamar ma bata lura da khadijanba, Duk abinda takeyi khadijan batama San tanayiba tunda ba ganinta tayiba, Bandaki tanufa tayi wanka tareda daukar sabon brush din datagani tabare tazuba toothpaste ta wanke bakinta tareda dauro towel tafito, Har yanzu aminatun na nan India tabatta, Gaban madubi ta nufa direct ganin babu iron mandatake shafawa agurin yasa takoma India tavire hijabin datayi sallah ta daukr tasaka tareda kallon maryam tace, "Nizan wuce part din hajiya" Adan kufule maryam takalleta tareda cemata, "Aikedama bakisan abin arzikiba,inba hakaba taya za'ace inzo gurinki inkintashi mutafi tare kuma kintashi amma kikasayimin magana sabosa tsabar ji da izza" Tunda tafara maganar khadija take kallonta harsaida takai karshe sannan khadijar ta Tabe baki tareda sakar mata wani sakaran murmushi mai ciwo tayi gaba abinta, Sosai ran aminatu yabaci kasancewar dama da akwai wani abin azuciyarta afusace ta taso tabiyo bayanta, Afalo ta isketa tsaye ita da baba Iro yanacemata shima ankirashine kasuwa zai fara zuwa amma hajjaju tace taje, Aminatu CE tagaisheda baba Iro ya amsa tareda cemata, "Au dama kema baki tafiba," " eh dama Abba be yace inzo in khadija ta tashi ma tafi tare" "OK badamuwa yanzu kuje bangaren hajiya in zayyad yagam shiryawa kwa tafi tare" Sosai gaban khadija yafadi tunawa da abinda yafaru amotarsa tuni yanayinta yakara canzawa, Aminatu kuwa wani dadine yafara lullubeta koba komai yanzu zata fara nunawa yaya zayyad soyayyarta agaban kowwa tunda ko baisotaba idan iyayensu sukaga yadda take sonshi dole su auramata shi sannan kuma ga mama datasan zata kara zuzuzta abin,hakan yasa taji wani sassanyan
Chapter 15 · 0% Book details