← Book details Dr Zayyad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 36

Sashe 11

Dr Zayyad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gate yafice abinsa me gadin nadaga masa hannu amma ko kallonsa baiyiba Shi kuwa yaya baffa tunda Dr zayyad ya tasheshi sukayi ido biyu dashi tabbas yaga wani Abu a idon Dr zayyad din Wanda koda baisan komaiba aduniya zai iya fassara wannan a in da (WUTAR KAISHI book dina na gaba)tabbas guguwar kishi yagani a idon Dr zayyad Sai dai abin yake daure masa kai shin Dr zayyad son khadija yakeyine kokuwa kiahin yan uwantakane amatsayinta na kanwarsa?" To amma kuma in hakane ai baidace yadakar masa kafa sosai har haka ba sannan kuma bai kamata yaganshi cikin wannan fishinba, Ganin duk wannan bazai kaishiba yasa yaja kafarsa da yake da tabbacin yasamu targade yafita daga gidan ma gabaki daya, Abangaren khadija kuwa gaggo na falo tayi da sallama gabaki daya jikinta asanyaye, "Assalamu alaykum" "Amn alaykissalam" Goggo ta amsawa khadija tareda mikewa tsaye tayo gurinta tana tambayarta, "Lpy kuwa khadija yanaga jikinki sukuku ko bakoso zuwan bane" "Aa wllhy goggo mekikagani" khadija tafada tareda fadawa kan kujera tasaki wata nannauyar ajiyar zuciya, "Goggo INA wuni ygd" "Lpy kalau khadija ya mutant gidan inasu hajiya" "Sunan lpy kowwa yanatacewa agaisheki " Khadija tafada da Dan murmushi akan fuskartata, "Ina munir din banga yashigoba ko yamakarane" Shiru khadijar tadanyi tareda sake sauke wata ajiyar zuciyar tace, "Aa goggo bashine yakawoniba yaya zayyad ne," tafada cikin sanyi murya, "Hmmmm nifa ince aikuwa ko da naji dama ni araina saidana ayyana zayyad ne" "Wai meyasa zayyad yake hakane?,kekuma meyasa kikafiya yimasa laifine nariga nafadamuku zayyad yanada saukin kai sannan uwa uba kuma India zakayi yadda yakeso to bazaku taba sabawaba, kema kinada naki laipin koma ince kinfishi,aibake kadai bace agidan meyasa bayayiwa sauran yan uwanki hakan", Zumburo baki khadija tayi tareda fara yayyarfa hannuwa, " to waini goggo menayimasa ne ,ai wllhy dama nadade dasanin keda ammi bakwa taba ganin laipin yaya zayyad komai yayi Sai kuce bashida laipi,kenan kullum nice nakeda laipi" "Nidai bacewa nayi kiyimin kukaba kitashi kishige ki ajiye kayanki kizo kike dining kick abinci" "Nina koshi" Khadija tafada lokacin da take hawa matattakalar benen, Yayi auki, Cewar goggo halima tana murmushi, Khadija kuwa tana zuwa daki tafada kan gado tareda sakin ajiyar zuciya, A can kasan zuciyarta kuwa tunanin abinda yafaru acikin motar taketa faman yi gsky yaya zayyad bakaramin Dan iska bane mugu kawai ai wllhy saita fadawa hajiya abinda yafaru, "Dana koma gida zanfadawa Abba abinda kike da bukata tun kafin kijawo mana abin kunyarda bazamu iyaba,ai gwamma aringa yimiki abinda kike da bukata tun kafin kijawo mana magana" Magan ganin yaya zayyad suka ringa yimata yawo akunne,kenan hakan yana nufin yaya zayyad zai fadawa Abba hakanne ayimata aure, Cab wllhy bazata taba yaddaba, "Tokiyi shiru da maganar abinda yayimiki amota kasancewar inhar kika fada yaya zayyad zaice ai abinda kike da bukata kenan" Cewar wani bangare na zuciyar khadija, Ahaka dai taita tunane2 har bacci barawo yayi a won gaba da ita, ********* Abangaren zayyad kuwa tunda yatafi zuciyarsa take tafarfasa ko da yaje office ma bawani aikin kirki yayiba, Tunaninsa gabaki daya yana gidan goggo halima shin meye tsakanin khadija da baffa, Shifa yasan kwata kwata baffa bashida hali mai kyau anya kuwa babu wata banzar alaka tsakanin baffan da kanwarsa, Wani zazzzafan numfashi ya furzas tareda Cuba agogo, Yakagu karfe ukku da rabi tayi yatafi gidan goggo halima kasancewar zuciyarsa kwata kwata bata yadda da baffa ba Dan yasan halinsa sosai... Wayarsace ta katseshi daga tunanin daya tsunduma, Ahankali yajawo wayar tareda dubawa ganin sunan faredda ne yasa yakyale Koran har yakatse, Saidatayi masa kira biyar bai dagaba daga karshema yakashe wayar, Ayanayin da yake ciki baya tunanin daya wata wayarda batada muhimmanci agaresa musamman ma dayasan zatayimasa tuni ne akan haduwar tasu, Tsaki yaja tareda ciza kan boron da yake hannunsa da karfi Wanda tuni dama yagama shan azabar cizo agurin Dr zayyad din, Yana zaune ahaka akayi nocking din kofar office din NASA, "Yes come in" Turo kofar tayi cikin isa da takama kana ganinta kaga cikakkiyar year bariki kasancewar tsinannun Riga da sket dasuke jikinta Wanda ilkahirin jikinta awaje yake fawani urban attachment data saka akanta yatsun hannunta gabaki dayansu dauke suke da farcen dashi Wanda yasha lalle,sanye take da wani urban gilashi a idonta, Gaba daya dai iein shigar Sai addu'a dinnan,babu batun mayafi ajikinta Sai kafarta da take cikin wani hill mai azababben kyau, Fareeda CE tashigo ba ko sallama tana taunar cingam,13 cikin takun isa takaraso tareda Jan kujerar dake kallonsa ta zauna, Tunda tashigo ko kallon inda take zayyad baiyiba,bawai Dan bayason ganintaba, Aa kodaya sai Dan wani yanayi dayakeji aransa Wanda yakasa fassara shi da komai karshema yake Neman rikita masa kwakwalwa, Duk iyayin da take da tura bres gaba daya Dr zayyad bai luraba saboda kwata2 hankalinsa baya jikinsa, Ahankali tasaka tattausan hannunta ta riko hannun Dr zayyad, Ko uffan bata CE ba tacigaba da murza masa hannun NASA ahankali tareda tsaresa da idanunta dasuka sha eyelashes, Sun dauki dogon lokaci ahaka kafin daga bisani yasaki wata nannauyar ajiyar zuciya, Ahankali ta zare hannunta daga NASA tareda mikewa tanufi fridge din, Ruwa mai sanyi tadauko tareda cup ta koma tazauna tareda tsiyaya masa ruwan acikin kofin takan bakinsa, Baiyi gardama ba kuwa yashanye ruwan Tass, tareda kara sauke ajiyar zuciyar, Tashi takarayi tanufi hanyar fita, Da idanu Dr zayyad yabita yadda take karya jikinta tsabar kwarewa da bariki kai zaka rantse babu kashi ajikinta, Wata shu'umar mika Dr zayyad dinyayi tareda laso lebensa na kasa yadan kamashi yaciza, Key ta murzawa kofar tareda juyawa tajingina da kofar gamida bankaro kirjinta tankalli sama tayi wata shu'umar mik, Dasauri Dr zayyad yakama babban birninsa yarike gam tareda rumtse idonsa da karfi yabudesu akan fareedar, Wani shu'umin murmushi tasakar masa tareda kara rangwadowwa tadawo gabansa, Har yanzu idanun zayyad nakanta kuma had yanzu din babu Wanda yafurta wani Abu acikinsu, Kujerar data tashi ta koma ta zauna tareda sake zuba masa idanunta, Tuni tafara gano lagonsa akanta hakan yasa ta kara kaimi akan jawo hankalinsa, "Nakira wayarka baka dagawa karshe kuma ka kashe wayarka,hakanne yasa nataso da kafata zuwa wajenka Dan ganin meyake damun mijina ne" Sosai Kalmar ta ta karshe ta daki dodon kunnenshi,amma dayake zayyad cikakken Dan duniyane hakan yasa tagagara samun amsarta akan fuskarshi, Wani shu'umin murmushi yasakarmata tareda kashe mata ido daya, Itama murmushin tayi tareda makemasa kafada dacewa, "Naki wagon" "To meyasa zakizo kisakamin rai bayan kinsan kuma baki shirya kula daniba," "Zayyad kenan aini takace kuma koda yaushe banida wani burin data wuce nafarantamaka nakumayi abinda kakeso," "Nagode" yafada tareda lumshe idanunsa, "Meyasa kaki daga kirana zayyad" "Mtsss wllhy rainane adan bace hakan yasa nakasa daga kowanne kira bama naki kadai ba" Zayyad yafada tareda jawo wayarsa ya kunna, Tasowwa fareeda tayi tadawo kan bencin dayake gabansa tazauna tareda sakalo hannuwanta duka biyu ta jikin wuyansa, " Meya bata maka rai zayyad" "Wllhy wani family issue ne" kawai yacemata tareda kokarin kawadda zancen, "Jiya kince kinason ganina yau allah dai yasa lpy...." Wayarsa CE takatsesa daga maganarsa yajawo wayar tareda dubawa, Sunan ammi dayagani yasashi yin murmushi tareda janye hannuwan fareeda daga jikinsa gamida daga wayar yasakata akunnensa, "Assalamu alaykum"aka fada daga can bangaren " Amn alaykassalam ammi an wuni lpy" "Lpy kalau zayyad ya aikin," "Masha allahu ammi na yajikinnaki?" "Alhmd nama warware dama ciwon kaine,naga Baka kiranibane kuma naji ance kunfita da yar kwayar kanwar taka,tonadaisan duk yadda akayi ta batamin ran da" Ammin yafada Adan sake da alamun raha, "Aa wllhy ammi na aikinne yadan cakudemin amma inata so inga nagama nakiraki" "Masha allahu yarona,gsky INA alfahari da kwazonka,hakan yasa akoda yaushe nakeyimaka addu'ar allah yarabaka da haram komai kankantarshi yahadaka da halak," Har cikin zuviyar Dr zayyad yakanji dadin addu'ar ammin sannan kuma yakanji kunyar kansa da kansa idan har takirashi yana cikin wani yanayi dabashineba, Yanzu haka jiyake Kamar tana ganin fareeda takuma San me take faruwa tsakaninshi da fareedar, "Zayyad" Are u ok" Ammi ta katse masa tunaninsa, "Yes ammi" Dr zayyad din yafada "OK bara nabarka kayi aikinka ngd kakularmin da kanka, Dan allah zayyad kadaina sakaci da azkar dinka kaji," "Badamuwa ammi na ngd bye" Ya kashe wayar tareda ajiyewa gefe, Nannauyar ajiyar zuciya yasauke tareda fara azkar din acikin zuciyarsa, Gabaki daya jikin farreda tayi sanyi, Tarasa kome yasa idan matar nan takira zayyad yake canzawa, Duk runtsi da dadin romance din da zayyad yashiga muddin matar nan takirashi tofa gabaki daya takan rasa kansa, Yanzuma hakance zata faru saboda tarigada tasan duk wani plan dinta akan zayyad yarigada ya rushe, Gaba daya zuciyarta ta dagule Wanda Har hakan yafara bayyana akan fuskarta , Tunawa da maganaganun Merry kawarta yasa ta dake tareda kokarin kawadda fushin dayake kan fuskarta , Takoma kan kujerar tazauna tafuskanceshi sosai, Shima zayyad gyara zamansa tareda duba agogaon dayake hannunsa,karfe hudu saura minti biyu, Gyaran murya yayi cikin sanyi dakuma mutuwar jiki yace, "Ammm fareeda dubada lokaci yafara ja make ganin kamar zamu iyayin komai wacce maganace anan,kasancewar nandinma da wadataccen sirrin yin magana koda takunshi sirrin" Sai da tadan sha kanshi na yan seconni kafin tafara maganarta cikin salonta, "Yawwa nagode da bani lokacinka dakayi ,duk da sai wannan shine karo na ba adadi da nabukaci hakan Dan tattauna maganganun dana tabbatar zasu kawo ci gaba sosai atarayyarmu," "Zayyad! Agaskiya nafara gajiya da kallon da mutane suke mana,hakan yana nufin inason ka kawo karshen sa icon da mutane suke mana nida kai," Takai karshen maganarta tareda kureshi da ido, Cikin halin ko inkula da nunamata shi cikakken Dan duniya ne yace , "Fine sai mu canza taku" Sosai maganar zayyad tadaki kunne da zuciyar fareeda, "Zayyad sai mucanza taku kamar ya" "Kamar yadda kikasani fareeda,kinsan INA zuwane na daukeki Wanda nima sai yanzu nake ganin rashin dacewar hakan,musamman ma kinga gsky ni daga gidan manyan mutane nafito,so mutuncin iyayena zai iya zubewa in yakasance kullum ana ganina INA zuwa daukarki," zuciyartaosai maganar zayyad takai kololuwar zuciyar fareeda amma dayake ahawarar merry nayimata kuwwa a kwakwalwa hakan yasa tasake danne zuciyarta tareda sake marairaice murya tace, "Zayyad" Sosai yasake kankance idanunsa akanta,scan cikin zuciyarsa kuwa yana ayyana shashanci irinna fareeda, Shin ko aure zaiyi zai auri mace kamar fareeda ne?, Wai ko tanaso ta nuna masa baisan
Chapter 11 · 0% Book details