Sashe 14
Dr Zayyad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bisani ya maida yatsunsa saitin hancinta nanma yadanjima kafin yadanna kirjinta da karfi, Ko motsi ammi batayiba hakan yasa khadija kwala wata razananniyar kara aguje tayo kan yaya zayyad din tafada jikinsa tareda rukunkumeshi, Dakarfi take cewa yaya zayyad Dan allah karkace ammi ta mutu wllhy inasonta yaya zayyad kayi duk yadda zakayi ammi ta tashi pls da karfi take jijjigashi tana kukan Wanda duk Wanda me cikin falon saida ya tausaya mata amma banda mama babba da take fatan ammin ta mutu taga tsiyar khadija yanzu haka burinta bai wuce yadda khadijan ke jijjiga zayyad yatashi ya tsitssinka mata mariba yarinya said fitinar tsiya, Khadija kuwa dabatama San me mama babba ke sakawaba aguje tajuya kan amminta ta jijjigata da karfi tareda cewa "Ammi Dan allah kitashi karki mutu ki barni wllhy INA sonki ammina nasan bazaki taba jure ganinmu cikin wannan halinba pls ammi kitashi Dan allah" Sosai tausayin khadija yasake ahiga zuciyar mutane dayawa yaya munir kuwa sarkin karaya tashi yayai yana goge hawaye yayi hanyar fita yaya mamman ma binsa yayi, Jin ammi shiru yasa khadija Lamar mahaukaciya takara. Fadawa jikin zayyad din tareda sake rukun kumeshi yana cigaba da cewa, "Yaya zayyad pls karkacemin ammi ta mutu Dan allah inhar ta mutu to kacire nawa ran kamayar mata" Karon garko da yaya zayyad yaji tausayin yarinyar sosai acikin zuciyarsa hakan yasa yakara jawota jikinsa sosai tareda shafa mata bayanta, Matso da bakinsa yayi daidai kunnenta yaradamata cewar, Wayace miki ammi ta mutu ne kiyi hakuri bazata mutu tabarmuba kinji air tanasonmu sosai OK calm dow," Ahankali yaya zayyad take fadamata maganar tareda shafa mata bayanta, Shiru kuwa khadija tayi tana sauraron kalamansa, Sosai lamarin ya shamnaci mama babba yakuma kai kololuwa acikin zuciyarta muddin tanason cikar burinta Dana yarta to dolene zata dauki babban mataki akanlamarin, Wata muguwar tsawa manan tadakawa khadija tareda cemata, "Waike meyasa bakyajin maganane ke bakisan ma'anar haramcibane kamar bakya islamiya kinsani sarai in akwai abinda ke hadaki da zayyad bai wiuce yadda kike shisshigewa yarannan mazaba,sannan kuma ko kafin uwarkibtarasu allah yajikan ta da rahama ai babu abinda ke hadaki da ita saboda sannan sakarcinnaki da hsagwabe shagwaben shin ke bakisan me wannan shagwabar ke haifarwa mazaba..........afusace hajjaju tace "ya isa haka," Sosai maganar mama babba tadaki mutanen dake zaune Afalon musamman dr zayya Wanda tunda mama tafara maganganunta akan khadija zuciyarta tafara tafarfasa, Sosai maganganun maman suka yiwa zuciyarsa dabaibayinda yahanashi koda motsi bare kuma yayi yunkurin janye khadija daga jikinsa, "MARGANYA" Kalmar da take ta yawo akwakwalan mutane da dama acikin falon musamman Dr zayyad da yaji gabaki daya jikinsa ya mutu, Ganin yadda mutanen fake cikin falon sukebin mama da wani irin kallo hakan yasa jikinta yin sanyi, Sai yanzu take danasanin sakin layin datayi agaban mutane Wanda zai iya fallasa aspirin zuciyarta, Dabas zayyad yazauna daga tsugunniyar dayayi gabaki daya idanunsa sun canza zuwa launin ja tsabar tashin hankali kawai zaka fuakanta ayanayinsa dama fuskarsa baki daya, Kamar antsikareshi yamike tareda sunkutar ammi cikin Sauri yayi hanyar fita, Baba isuhune yabiyoshi cikin Saudi sukayi waje, akofar fita daga part din suka hadu da baba ummar,baba Iro,dakuma baba safiyanu suna shirin shigowwa kasancewar Koran gaggawa dasuka samu daga yaya minor cewar ammina batada lpy sosai, Zayyad kuwa ko ganin gabansa bayayi balle yakulada su Abba yayi hanyar motarsa, Hakan dasuka ganine suka tabbatar da cewa lalli wannan karon ma ciwonnata yatashi da karfinsa Kamar yadda yasaba dasauri sika rufawa zayyad baya, amma INA kafin suje tuni zayyad yatada mota da wani masifaffen gudu yabar gurin, Tuni suka suka hau mortar baba ummaru suka rufamasa baya, Amma ina ko kurar mortar zayyad dai babu abinda suka gani hakan yasa suka nufi asibitin su zayyad din Dan kuwa sun tabbatar ba Inda zai kaita dama da can din, To shima abangaren zayyad ikon allah he kawai yakaisu asibitin lafiya yana zuwa kuwa ko daidaita parking baiyiba ya bude motar tareda sake sunkutar ammi yayi cikin asibitin da it's ko motarsa baitsaya rufewaba, Emergency ya wuce da ita yayinda nurses da likitoci suka rufo masa baya aguje kasancewarsa babban likita, Ko tsayawa kallon masu binsa da whilechair baiyiba sada yadanganada ita emergency, Dasauri wata likita mace tabude NASA wani special room yashiga da ita yadairata akan gadon cikin kankanin lokaci yafara acikin veto ran ammin, To koda su baba ummaru suka karaso sundaiga motarsa zayyad wani ma'aikacin asibitin yana gyara masa parking direct gun motarsa suka nufa lokacin yagama gyara parking din yana kulleta, Baba ummaru ne yayi masa sallama, Ma'aikacin ya amsa tareda basu hannu suka gaisa, Bayan sun gaisane suka tambayarsa Dan allah zayyad fa, Shi yay.musu jagora had zuwa emergency inda Dr zayyad din yashiga da ammi saidai kuma lokacinda sukaje tuni anrufe gurin mazaje sun Shiga bakin aiki, Saidai gurin zama mai kyau daya sama musu an an emergency din dacewar sun rigada sunshiga da ita bakin aiki saidai idan anfito, Zama suka duka su hudun kowa da abinda yake tinani aransa tareda addu'ar samun saukin ammin dama dukkan musulmi bakidaya, To a can kuma gida abangaren su hajjaju sosai abinda mama babba yayi yabata ran hajjaju Wanda har hakan yasa taja mama babba bangarenta kasancewar hajiya macece mai tunani yasa batayimata fada gaban ya'yansu da Matan gidanba tayimata fada sosai wannan kuma daga karshe tayimata nasiha akan lafazi, Daga bisani kuma hajjaju tace kasancewar darene kowwa yaje ya kwanta yaya munir ne zaikai umma babba da hajjaju asibitin inyaso dasafe kowwa Sai yaje yadubata, Hakan kuwa akayi Sai dai dakyar khadija ta yadda su hajjaju zasu tafi ita kuma gobe sazo gabaki dayansu, Ganin za'a bar ummy ita daya yasa hajjajun cewa su tafi bangaren aunty maimuna su zauna har su dawo inyaso saisukoma bangaren hajiyar lokacin su baba iron sun dawo, Hakan kuwa akayi su umma da hajjaju da yaya munir sika tafi asibitin ita ma umma karama naganin suntafi taja aunty zainab sukayi part din su, Aunty maimuna da ummy ma sukayiwa mama babba saidai safe sabanin khadija datakebin kowwa da ido saboda tsabagen tashin hankalin datake ciki, Sosai mama takejin haushin gabaki daya mutanen gidan harma da ummar data haifi zayyad din takumaci alwashin dole ko ta halin kaka zayyad mallakin aminatune,16 Haka mama tahada kan ya'yanta suka nufi part dinsu tareda train alwashi acikin ranta, Abangaren fareeda ma tunda suka bar asibitin take kuka bayadda merry batayiba amma fareeda takiyin shiru hakan yasa mery samun gefe guda parking din motarta takashe tareda fuskantar fareeda tace, "Wllhy kawata kin bani mamaki aiki me zayyad yayimiki baidace kikama kukaba haka sannan kuma nayi nayi dake kinsaka Samar dani abinda zayyad din yacemiki" "Shin fareeda idan har baki fadamin abinda zayyad yacemikiba ta INA kikeson infara taimakonki" Numfashi merry tasauke tareda yin shiru na yan mintina kafin daga bisani tacigaba da cewa, "Fareeda kisani cewar aurenki da zayyad dolene muddin zayyad yabijirewa bukatarki kawata wllhy Sai yayi kuka da idanunsa" Tabbas zayyad Sai yasan cewar shi karamin Dan duniyane kuma Sai yasan cewar ke fareeda ba kanwar lasawa bace" Cikin shasshekar kuka fareeda tafara magana, "Hmmm merry kenan bazaki taba gane waye zayyad ba saboda duk ta inda kike tunani zayyad yawuce nan" "Merry ina me tabbatar miki dacewar zayyad bazai taba yadda da bukatataba saboda no kaina naga alamun hakan" "Kawata ki kwantar da hankalinki nayimiki alkawarin cewar tabbas Dr zayyad Sai yazama naki, shin kokin manta dacewar munada makamin yakara zayyad ahannunmu," "Hmmmm merry kenan zayyad wayayyen mutum ne kuma cikakken Dan duniya maiji da baiwar da allah yayimasa Dan haka barazanarmu bazata taba tsoratashiba" "Hhhhm" merry tayi wata dariyar bariki tareda wurga idanunta takuma saukesu akan fareedar tareda jefamata kallon bakida wayau, "In banda abinki kawata mezamu tsaya bata lokacinmu akan zayyad ai planned dinmu tafi karfin yatsaya akan zayyad, Fareeda nahada kullin da zai tashi da zayyad matsawar yaki yadda da batun aurenki sannan kuma akarshe bom dina yafada har gidansu kuma gaban mahaifansa Wanda duk runtsi dolensu koda zayyad zai mutu su aura mishi ke" Tunda merry tafara magana fareeda ke kallonta ta yadda da kawartata sannan kuma tasan halinta akan dukkan abinda tasaka agaba, amma kuma lamarin zayyad Nada wuyar fassarawa, Sosai tafara sake2 akan maganganun merry saidai koma meye tana da tabbacin kawar tata zata fiddata kuny, Hakan yasa ta share hawayenta tareda yiwa merry alkawarin daina kuka akan lamarin zayyad din, Wani shu'umin murmushi merry tasaki Wanda har kasan zuciyarta yaji dadin hakan acikin ranta kuma tacewa fareeda sha sha sha (tofa anya kuwa merry allah dai yakyauta) Kiran wayar merry da akayine yamaido da ita daga duniyar tunanin dubawa tayi tareda satar kallon fareeda takasan ido kafin ta daga, Tana dagawa kuwa daga dayan bangaren akacemata, "Yanzu haka Dr na asibiti ankawo ammi batada lpy sosai" "OK nagode" kawai merry tafada tareda kashe wayar, Aranta ta ayyana daga yau duk wani bincikenta akan Dr zayyad yakare yazama dole daga gobe tafara bayyana gabansa da iyayensa amatsayin kamila Kamar yadda ta tsara shirinta na mallakar Dr zayyad, Dama kuma matsalarta bats wuce kawata ba kuma ita dakanta zata tirata ta tura manta rijiya da kanta, Tabatan da fareeda tayine yasa ta dawo hayyacinta tsabar iya duniyancinta yasa ta wayance da cewa, Kawata bari in saukeki agida saboda wani Koran gaggawa dana samu, Kasancewar dare yafarayi sosai kuma wannan lokacin fareeda na bukatar hutu kodan kukan datasha hakan yasa bata wani damuba, Merry nasauketa agida kuwa ta wuce gida Dan cigaba da shirshiryen kudurinta na alwashin karbe Dr zayyad daga hannun fareeda Wanda tafara tun farkon ganin hoton zayyad, Hakan yasa aduk lokacinda kawartata tace zata hadata da zayyad su gaisa saitasan yadda tayi tazille Wanda duk hakan yana cikin shirinta saboda bataso zayyad yasan zahirin ko iylta wacece bare kuma yaganta tareda kawartata fareeda, Abangaren Dr zayyad kuwa tunda suka shiga emergency da ammi suketa kokowa da numfashinta Wanda yazuwa yanzu oxygyn din dasuka sakamatama nema yake yagagari numfashin tunda yayi low sosai, Lura da numbers din jikinsa oxygen din yasa hankalin Dr Sam abokin acikin zayyad dakuma Dr binta hankalinsu yakai makura atashi, Dr binta CE ta cewa su Dr zayyad, "Dr kuyi hakuri yanzu hanya daya taragemana wadda inhar bamuyi nasara akantaba saidai kuma mubarwa allah lamarinsa kuma kunsan tanada hatsari kasancewar kuma kunsan