← Book details Dr Zayyad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 36

Sashe 18

Dr Zayyad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama babba wadda tunda aka fara zancen abin duniya yashamata kai gabaki daya jitake kamar tashakesu musamman aunty maimuna datake jin tsanarta fiyeda ta kowwa tace cikin wayancewa da iya duniyanci, "Aini wllhy narasa wacce irin tsana zayyad yayiwa khadija, itakuma tanasane taringa shiga harkarsa bayan kuma tasan bayako bukatar yaganta agu muddin yana zaune,ninarasa meyake damunsu gabaki dayansu," Sosai maganar mama tasake Dakar zuciyar mutane dayawa sai dai kuma ita data fada tasan zata dakesu din kuma ko ajikinta bata damu da metafadaba, Aunty maimuna CE tayi carab ta amshe zancen dacewar, "Mama badai ki fahimci su bane gabaki daya su amma no saima nakeganin kamar fa kawai abinda suke boyewa shiyasa koyaya idan daya yayi badaidaiba saikiga daya yarunzura" Sosai itama maganar aunty maimuna tadaki zuciyar mama Wanda Har hakan ya bayyana akan fuskarta saikuma tayi saurin kawaddashi, Kasancewar bakowwa yafuskanci abinda aunty maimuna take nufiba Dan dama bataso su fuskanta tafiso sakon yaje inda ta bukata yakuma isa cikin sauki Dan Har result tagani, Shigowwar su hajjajune yasa ba Wanda yakuma magana, Aunty maimuna CE ta tashi tabawa hajjaju guri tazauna, "Sannu amaimuna allah yayimuku albarka" "Amn hajiya" Kafin akashiga yan gaishe gaishe tsakninta da umma tareda tambayar ya mejiki, Dasauki umma tace tareda sake cewa, "Ai da baban khadija take cewa koza'a sanarwa yan gidansu ammi rashin lafiyar tata ne,amma sainayi karambanin cewa tomu meye amfaninmu ai dadi shi akefada ba ciwoba" Sosai hajiya taji dadin hakan tareda karayiwa surukannata addu'ar cigaba da samun hadinkai, Tunda suma shigo mama babba ke baza idon Neman khadija da zayyad amma bata gansuba, Sosai tashiga sake2 aranta shin INA zayyad da khadija Muryar hajiyace ta katseta inda take cewa20 hajiyace takalli aminatu tace, "Waikekam lafiya tunda muka taho nake lura dake saikace wadda kwai yafashewa acikin ciki" Dan guntun murmushin yake aminatu tayi tareda buds Baki da nufin yin magana, Wata matace tayi sallama cikin nutsuwa,sanye take da dogon zumbulelen hijab dinta har kasa gakuma nikab din data rufemata gabaki dayan fuskarta babu abinda kake gani sai idanuwanta dataketa saddasu, Sosai yanayinta shigarta dakuma kamewarta yatafi da mutane dayawa musamman ma hajiya, Matsowwa matar tayi tareda dukawa har kasa ta gaisheda hajiya kagin tajuya tagaisheda mutan gurin, Sosai tashiga rayuwar hajiya lokaci daya, Cikin zumudi Dason gwaninta hajiya tacemata, "Yarinya ko akwai Wanda Kike nemane" Cikin jin kunya tasake rufe fuskarta tareda mikawa hajiya basket din tace, " Gashi agaida me jiki" "Aaaaaa lallai ba shakka yar nan sannu da kokari allah yasaka" "Oooo ni rabi,sannu da hidima yarinya saidai wllhy bamu wayekiba" Kamar munafuka haka tasake janyo hijabinta tana dan sake Kare idaninta daga karshe tamiketareda cewa, "Allah yakara sauki hajiya" Sai alokacin yan wajen da mamaki yakashesu suka fara yimata godiya cikin sakin fiska tareda sake tambayarta daga INA" Ahankali cikin sunnadda kai tace "in Dr yazo agaisheshi" "Aaaaaaaa iyyyyy lallai bashakka kace jikatace kai amma naji dadi nakuma gode to allah dai ubangiji yasa albarka Yakima sa ayi damu" Sai yanzu sauran yan gurin suka dauki haske da batun, Cikin sauri mama tadago tareda zubamata wani kallon tuhuma da baki isaba, Akaskance maman tacemata, "Yarinya ai kamata yayi kifito kifadamana abinda yakawoki bawai kizauna kina nuku2 ba" Murmushi tasakeyi tareda sake sunkuyarda kanta kasa tace, "Yi hakuri mama" Sosai zuciyar mama tabuga jin ta ambaci sunanta, Tabbas wannan yarinyar budurwar zayyad CE inkuwa bahakaba tayaya zatasan su sannan kuma takama sunanta, Kenan zayyad dinne dakansa yafadamata sunansu kilama harda matsayinsu, Lallai yazama dole tasan abinyi, Tunda aka fara wannan abin kan umma take asadde, Saidai tarasa komeyasaka takasa jin yarinyar azuciyarta kama daga maganarta har kallon yarinyar datayi bata ji wani abuba, Kodan dai ita har cikin zuciyarta tayiwa zayyad mata saidai kuma bazata taba iya fitowwa tace ga wadda takeso zayyad din ya auraba kasancewar tana kara da lamarinsa, Misamman yadda taga ammi tafita Nuna kulawa akan zayyad din hakan yasa takasa furta abinda ke zuciyarta, Saidai kuma ita batada wani dalili nakin yarinyar dayakeso tunda daga ganinta yarinyar kirkice allah ubangiji yadaidaita lamarin allah yasa hakan shine mafi alkairi, Mikewa tayi tareda cewa sai anjimanmu tayi gaba, Godiya suka shiga yimata, Zumbur aunty maimuna ta mike tareda kama hannun zainab tace zomurakata mana, Badan zuciyarta zainab tasoba haka suka tafi hajiya nasakamusu albarka da yaba hankalinsu yayinda mama babba da aminatu sukabisu da harara, Sosai aunty maimuna tasawa zuciyarta shakku akan kasancewar yarinyar datazo budurwar zayyad, Saboda aunty maimuna tanada baiwar saurin fahimtar lamari musamman ma idan akace narashin gskyne, Har tadanyi nisa suka isketa aunty maimunace tayi saurin karasa tadafata, Adan razane tajuyo kasancewar tana duniyar tunani, Ido cikin ido sukayi da aunty maimuna, Aikuwa cikin sauri tadauke idonta tareda saddasu kanta, Murmushi aunty maimuna tayi tareda cewa, "Mun gode da ziyara sosai,agsky Dr zayyad ya iya zabe,in wllhy dayacemin ustaziya CE zai aura nayi matukar mamaki musamman yadda take zuzutaki," Anazarce aunty maimuna tafahimci yadda maganarta tadirar mata sannan kuma tayi nasarar fahimtar sakon data aika, Cikin hikima wayau dakuma dubara tacigaba dacewa, "Amma kuma sai dai kunyimana baaki bitu kedashi shiyace mana ne gone zakizo kekuma gashi kinzo yau,shiyasaka ma kikaga kamar ba'a ganekiba" Awannan karonma maganar ba iya kunnen merry tadiraba hard a cikin zuciyarta tayimata wani mummunan dira Wanda har saidai miyau ya sarketa, Tari tadan farayi kadan, aunty maimuna tacemat, "Sorry fa natsayadda amaryarmu da surutu gashima naga kamar alamun Dana ciwon kai nadamunki ko" Cikin azarbabin samun mafita merry tace, "Eh wllhy aunty" "Ai naga alama sosai ma musamman kwayar idonki data canza launi kamar wadda kikasha maganin mura" Akidime merry tadago tadubi aunty maimuna, Fuskewa aunty maimunan tayi kamar ma batasan tafadi wani abuba tareda kawadda zancen tacemata, "Muje natsayaddake mutakamiki ko" Ahanzarce merry tadan fara tafiya yayinda aunty maimuna ta tabo aunty zee wadda tayi mutuwar tsaye,tareda cemata, "Muje status" Ajiyar zuciya aunty zainab tasaki tareda bin abayan su da mamakin halin aunty maimuna saikace jami'ar tsato, Har mota suka rakata tayimusu godiya kafin aunty maimuna tace, Gsky mungode da ziyara kwanannan zancemasa yahadamana zugar dangi mujemiki ziyara duk da madai ke kadai kikazomana ko kanwarki baki tahomana da itaba Dan rowwa kada kannen zayyad sugani suyaba ko," Sosai zuciyar merry ke bugawa,murmuahin yake tayi tareda bude motar tashiga, Aunty maimuna ta rufemata, Ko saurarar daga mata hannunsa dasukeyi batayiba taja motar ta kamar anayimata tsere azuciya, Ko titi bata hauba motarsu zayyad tashigo asibitin, Taga shigarsu hakan yasa takarawa motar gudu tareda tarin tambayoyi acikin zuciyarta, Su aunty maimuna natsaye da aunty zainab motar zayyad tafi parking a parking space din da merry tadauke motar ta, Ko gama parking baiyiba khadija ta kama murfin motar lock yadanna tareda tsayawa yadaidaita parking yagama shan kanshinsa kafin cikin halin ko inkula yafara magana batareda ya kalletaba, Wllhy salon inji kinsake yimin rashin kunya narantse da allah abinda zanyimiki saiyafi Wanda nayimiki tunda ke bakyaji ba abinda kika ajiye sai fitsara dayiwa nagaba gunguni marar da'a kawai, Sannan kuma da alamun zazzabi ajikinki kisameni a office ki karbi magani salon kuma ki ki zuwa kiga yadda zanyi dake kazama kawai" "Hmmmmuymnn babban kazami yawuce meshan bakin wani" Ita kanta khadijan batasan sadda maganar ta subuce tafitoba, Aikuwa zayyad yafincikota tareda sake Jade bakinsu, Ganin motar zayyad yasa su aunty maimuna tsayawa amma da taayuwar motar sun kusa minti ukku ba'a bude anfitoba hakan yasa aunty maimuna kwankwasa bakin gilashin motar batareda tana ganin nacikin motarba, Dr zayyad kuwa tunda Yakama bakin khadija yake tsotseshi,jin bugs window din motar yasashu sakarmata baki tareda kallon ta da shanyayyun idanunsa, Kallon gobema kya sake kafin yacire lock din, Numfashi khadija ta zauna maidawa kamar yadda yamaida Kansas jikin kujera, Kara kwan kawso kofar da akayine yasa khadija bude bangarenta ta fito tanata kumbure2. Da fishi, Ko kallon su aunty zainab dasuke jikinta motar batayiba tayi gaba abinta, Shima fitowwa yayi tareda kallon su kamar baiyi komaiba ya wani basar shi adole babban yaya, Aunty maimuna ma dariyarta ta guntse tareda kallonsa tace sannu da zuwa, "Yawwa yace yame jiki kuma" Badai mugantaba tunda mukazo amma ai nasan dasauki sosai" "Yaya zayyad INA kwana" Aunty zainab tafada tareda kama hannunsa tarike kasancewar sosai Duke shiri, Shima hannun NATA yadamke sosai tareda kallon ta da Dan murmushi yace, "Morning dear" Shaka suka karasa cikin asibitin, Tuni khadija ta karasa rai abace ko sallama babu tana shiga tanufi cinyar umma tadora kanta tareda fashewa da kuka, "Subahanallahi khadija meyafaru" Umma duk ta rikice tambayar meyafaru, Sosai zuciyar mama yayi sanyi ganin zayyad yasaka khadija kuka aranta takecewa, Ai maganinki kenan makwakwaciya nasan dukanta yayi allah yakara, Shigowwar Dr zayyad CE tamaida hankalin Umma kansa koma karasowwa baiyiba tamike tana huci tace, "Zayyad wai meyasa bakada tausayine Dan allah uyhm,yanzu yarinyar bawani lafiya tacika ga maraicin uwa tana gadon asibitin shine zaka kamata kadaka,zayyad menafadamaka gameda dukan khadijane" Ganin ran umma yabaci sosaine yasa hajiya cewa, "Wai kekam kamar bakisan halin khadija da munafurcin tsiyaba,shin in dai ba'a yabawa zayyad ba aibaza'a kuahemasaba,kuma batareda kin bincika kinjiba zaki kamasa da fada haka kawai," "To amma hajiya keda kanki fa kinsan halin zayyad akan yarinyar nan shi kwata2 bata hakuri da ita bayama ko jin kunya yaringa dukan karamar kanwarsa" "To ba abinda kike tunanin bane,yarinyar nan gabana zaidu yatsareta saitaci abinci amma takiya hakan yasa nabarosu agidan kuma nasan tsaretan dayayi taci abincinne zaisakata wannan tukuburin fitinanniya kawai" Wani shocking mama babba taji, Waimezaisa tunaninta yayita rabuwa gida biyu itafa tafi bukatar kulawar zayyad ta ta allaka ga amintu kawai21 Shidaibzayyad gaba yayi abinsa yawuce cikin dakin da ammi take, Tana Dan zaune jikin gadon andan daga gaban dajingina bayanta, Dasallama yatura kofar yashiga idonsa nakan ammi, Ahankali ta amsa masa sallamarsa saboda jikinta ba kwari ko kadan, Matsawa Dr zayyad yayi kusada ita Yakama hannunta tareda kallon fuskarta , Nurse din datake zaune ta tashi tamikomasa kujera kafin tafice daga dakin, "Sannu ammina yajikin" "Dasauki sosai zayyad ya aikii" Ammi tafada ahankali cikin sanyin murya sosai, "Aiki alhmd, yanzu me kikeji ajikinki" Ahankali tadan dafa da niyyar tazauna sosai, Mikewa Dr zayyad yayi yakamata ya gyaramata zamanta sosai tareda kara mata follow abayanta, "Nagode sosai zayyad allah yakara lafiya da Nisan kwana" "Ammi kefa uwace Dan haka d'a baya bukatar godiya daga iyayensa"
Chapter 18 · 0% Book details