← Book details Dr Zayyad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 36

Sashe 1

Dr Zayyad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry WordDocument 0Table Data Normal Default Paragraph Font Table Normal No List PAGE 1 Gidan alhaji babangida wapa gidane babba Wanda za,a iya kirada family house. Gidane daya tsaru sosai kasancewar gidane daya hada yan uwa. Alhaji babangida wapa shine sunana asalin tsohon gidan Wanda allah yatimasa rasuwa tun a shekaru goma baya dasuka wuce. Tsohon Dan canjine Wanda kuma shahararrene tafannin kasuwanci dakuma dukiya. Matarsa daya aduniya wato hajiya rabi,hajiya rabi takasance mace mai kirki da kuma son mutane dason zumunci, Sunada yara bakwai Wanda acikinsu hudu mazane inda ukku suke mata, Kasancewar alhaji babangida wapa mai ilimin addini yasa yatsayawa ya,yansa sukayi ilimi sosai aduka bangarorin biyu watau boko da Arabic Hakan yabasu damar Gina rayuwar ya'yansu visa soyayyar junansu da kuma son zumunci Sannan uwa uba kuma kowwa zaune yake da kafafunsa. Baba ummaru shine babba sai baba safiyanu sai goggo halima itace ta ukku daga ita kuma Sai baba Yusuf Wanda ake kirada baba isuhu sai goggo shatu goggo safiya da kuma auta wato baba Ibrahim Kasancewar alhj babangida mutum be dayakeson yaya yayansa sun hada Kansu yasa yasiyi katon tankamemen fili inda yayiwa kowwa part dinshi kuma dukansu iri daya tun kafin ma suyi aure sannan kuma shima yagina nashi acikin Gidane daya hadu iya haduwa,katon gate ne Wanda idan kashigo zaka iske harabar filin ajiye abin hawa agefen dama, agefen hagunka kuwa wani filine shima daban Wanda yafi wancanna ajiye motocin,inkadan yi gaba kasan kuwa zaka iske part hudune manya iri daya sai wani babban part dayake gefe shima daban. Akowanne part yana daukeda babban falo sai kofofi guda ukku ,kowacce guda inkashiga zaka iske falone mai Dan girma sai bedroom da kuma bathroom sannan akowanne part akwai babban kitchen Baba ummaru shiyafara yin aure Wanda abikinsanema sukadawo gidan Ayanzu baba ummaru yanada mata biyu umma hajara itace babba inda takeda yara biyar YAYA ZAYYAD shine babba sai yaya munir sai kuma aunty zainab yaya al'amin da kuma Yusuf karami wato baba karami Sai kuma umma zulaihat da takeda yara biyu rukayya da Ahmed sakamakon haihuwa datake suna mutuwa Masha allahu suna zaman lafiya sosai sai dai sha,anin arayuwa kuma Shima baba safiyanu yanada mata biyune da yara biyar mama babba wato hajiya safiya tanada yara ukku aminatu Fatima dakuma aliyu,sai mama karama datakeda yara biyu sultan da hamida Baba isuhu yanada mata daya da yara hudu Muhammad SANI Wanda ake kirada mamman sai khadija da sa,adatu wadda suke kira ummy sai kuma maryam Sai kuma matar baba iroro wadda ita yanzu takeda shekara ta biyar da aure inda kuma ta haifi yara biyu dayan yarasu yanzu daura daya wato al Hussain Googo halima tana nan itama cikin garin kano tana aure kasancewar ita bata taba haihuwaba yasa yanzu haka akabata maryam yar gidan baba isuhu tunda ada tarike hafsa yar gidan googo shatu Goggo shatun ita tana aure a danbatta tanada yara biyar itama hafsa itace babba wadda take gurin goggo halima har tayi mata aure sai shams shamsiyya faisal dakuma noor Goggo safiya intake aure abuja inda mijinta yake rikakken Dan boko ma,aikacin bankine arayuwa suke ta yan boko hakan yasa takeda yara biyu sudais dakuma intisar Wannan kenan Yanzu gaba daya agidan baba ummaru ne kamar uba inda yakasance shine babba sannan kuma yan uwansa najin maganarshi sosai da sosai Haka. Shima baba isuhu yakasance mutum mai zafi hakan yasa gabaki daya yadan gidan suke tsoronshi Akaf gaba daya oyayen gidan sunfi Nina soyayyar su ga zayyad kasancewarsa da na farko dasukafara samu Zayyad shine babba agidan inda yayi karatu mai tsayi Wanda yakai matakin Dr afannin acikin likitanci yanzu haka cikakken likitane dake aiki a asibitin malam aminu kano Zayyad yakasance gwarzo kuma cikakken namiji Wanda yakeji da kuruciyarsa dakuma takama da kudinsa Zayyad kyakkyawan namijine akin karshe iron mazannan first class,ingarman namijine sosai yanada tsayi sannan kuma yanada murjajjen jiki,farine sosai yanada saje sannan sannan yanda baking gashi mai kyau kamar na larabawa . Kasancewarsa cikakken namiji mai lafiya hakan yasa yakeda ha'awa sosai rikakkene kuma kwarrarren nmb daya a iya duniyaci,amma hkan bai hanashi shan kanshi da Jan aji ba sannan duk iya duniyancin Dr zayyad baitaba sex da wata yarinyaba koda yamotso jarabarsa aguri yan matansa baya bari takaishi ga sex dasu yakai basar dasu yasha magani,yakandaiyi soyayyar nan tazamani Kasanceqarsa Dan boko tasa had yanzu dayake cikin shekara ta talatin da biyu bashida niyyar aure mahaifinsa da dangin mahaifinsa suna iya kokarinsu akan su tursasa masa amma da anfara maganar sai hajjaju wato kalarsu tanuna adaina takuramsa shi aure mukaddarine takance "kumama zaidu yanada niyya (dayake it'a hakan take kiransa tun bayaso had yahakura)mutuminda har ginin gida naban mamaki yayi" Ahakan dai suke takurawa to tun wata rana da babannashi yaji abinda yake aikatawa ashahararren gidannasa dake rukunin unguwar yan gayu ta tudun yola,Inda wani mai samaasa ido aharkar dannasa yake fadamasa amafiya yawan lokuta dannasa yakanzo da yammata iri daban daban gdn ,hakan yasa yacemasa yadaina kwana can din yadawo tsohon dakinsa dayabari na boys quarters cikin yan uwansa yazauna,sannan dolene kuma yayi aure acikin kankanin lokaci. Hakan dayajine yatashi hankalinsa acewarsa shi bai shirya tsufaba, to nanfa akaitayi Inda data karshe dai hajajju hardasu hawan jini antakurawa jikanta, to daga karshedai maganar yayi aure ta lalace, su hajjaju hardacewa"nidaqyarma inba aljanace ta auri zaiduba namiji har namiji amma ba sha'awar aure"lol Abangaren sauran yaran gidan kuwa yaya munir mutum ne dabaruwanshi shi kowwa nashine yanason wasa dakuma raha Inda yanzu shima cikakken manager bank ne Yanada saukin kai sosai inda yanzu haka magana tayi nisa tsakaninsa da aunty shamsiyya ta danbatta so ake tagama hada n.c.e dinta asha biki Yaya al'amin ma bashida fada amma bayason raini ko kadan shibama mazauni bane yana aikin s.s be inda yanzu haka yana jihar jigawa Aunty zainab ma tana karatu inda yanzu haka take hada degree dinta afannin jarida itama danata masoyin Dan yamaso ayi bikinta tun baya akabari sai ahada Dana yaya munir , Aunty rukayya tana aji ukku itada yaya Ahmed da baba karami inda suke kokarin ganin sun samu kwalin degree Sai aminatu da Fatima ya'yan baba safiyanu dakuma maryam ummy da maryam aliyu mamman dasuke shekara ta farko amakarantar gaba da secondry kasancewar ba Nisan shekaru sosai atsakani Sauran yaran gidan kuma duka suna matakin secondary me banda al Hussain dayake nursery WANNAN KENAN KHADIJA da fateema da aminatu da ummy sun kasance kawayene tun suna primary Sai dai halin khadija yafita daban shiyasa hajjaju take ganin kamar hajiya safiya mahaifiyar khadija wato mamee bata sonta Wanda kwata kwata ba hakabane halin khadijarne baizo daidai da yadda mamin takesoba shiyasa, Arayiwar khadija ita kaifi dayace sannan kuma batacika tsoron abinda kowwa yake tsoroba Tanada rashin kunya dakuma Nuna hakan yasa duk yadda Dr zayyad yake dasawa da mahaifiyar khadija amma kwata kwata shi yarinyar bata ranshi kamar yadda ahima bata ranta Dan tanada wata kawarta wadda takan bata labarin zayyad din takan ganshi a unguwarsu dakuma abinda takeji agari,hakan yasa khadija takara tsanar zayyad dakuma miyagun halinsa, Khadija tanada cutar aljannu Wanda basu fiya tashiba Dan tunda take sai biyu suna taba tashi amma insuka tashi sukan bata wahala sosai Wanda komai sai anyimata Dalilin karbo mata magani da'akeyine yasa takoma gurin hajjaju gaba days dazama Khadija takasance irin matannan ne dakoke mace kika kalli jikinsu saikin yaba bare kuma namiji bawai tanada jikibane kokadan, Sai dai tanada mazaunai masu daukar hankali Wanda duk abinda zatasaka sukan bayyana tanada dukiyar Fulani wayanda auka cicciko kuma suke atsaye ba alamar zasu lankwasa doguwace amma ba sosaiba tanada murjewar jiki sannan farace sosai kyakkyawar gaske WANNAN KENAN BARI MUSHIGA ASALIN LABARIPAGE 2 Da sauri2 yaketa shirin fita kasancewar lokaci yafara ja gashi har karfe takwas saura Monti biyar, Tsaf yagama shiryawa cikin suite bakake masu bala'in kyau dakuma daukar hamkali, Mukullin motarsa yadauka da agogo yafito cikin sassarfa yanufi part din mahaifansa, Da sallama yakarasa yashiga inda yataradda part din ahiru hakanne yatabbatar masa da yaran sun tafi makaranta Sakin ummy zulaihat yafara lekawacikin sallama da taushin murya, Atsaitsaye suka gaisa yafito yaleka dakin ummansa nanma kozama baiyiba masa cewarma ba fuskaryin hakan, Ahaka gaba daya yashiga kowanne part kamar yadda al'adar gidan take Bangaren hajiya safiya wato ammi shine karshe Dan haka yana fitowwa daga gurin baba Iro can yanufa, Da sallama yashiga part din cikin xazzakar muryarsa "Assalamu alaykum" "Amn wa'alaykassalam" ammin tafada daga cikin babban falon, "Ammi kinaciki" "Wllhy INA daga nan tundazu nake jiranka naji shiru da yanzu make cewa zan leka in gano ko lfy" Murmushi yayi tareda zama akusada ita sosai yace "wllhy lafiya kalau ammina baccine yayi dadi har nama kusa latti" "To ai tunda lafiya da dadi sai katashi kaje ga abin karinka can kan dining kayi maza kaci karkayi latti" "Tom ammina yafada yana murmushi tareda mikewa yayi dining". " anya kuwa Hadiza rayuw zata yiwu ahaka ace mace sai shegen lalacin tsiya tundazu yan uwanki suke jiranki harsun gaji suntafi sunbarki" Hajjajuce atsaye akan khadija wadda takoma bacci bayan tayi sallah,tundazu suke tashinta amma tayimusu banza Har sungaji suntafiyarsu abinsu sun barta, Yazuwa yanzu hajjaju takai Bango da rashin mutuncin hadizar,afusace tayi waje , Sanin madoki tatafi nemowwa yasa khadija najin tafita tamike yana harare harare tareda nufar kofa tana kunkuni"ai wllhy indai baki dainacemin hadiza ba to wllhy Nina bazan FASA miki duk abinda nagadmaba fitinanniyar tsohuwa kawai" Kofar ta rufe tadawo tashiga bandaki,kasancewar tasan tamakara sosai yasa bata wani dadeba ta Tito daureda towel akugunta, taja stool tazauna tana shafa mai. Ahankali yake cin abincin sunadan taba hira da ammi har yagama ya wanke bakinsa gamida daukar mukullin motarsa,tarakoshi har baking part dinnata kamar yadda tasaba addu'a ta yimasa yayi gaba yana daga mata hannu yanufi part din hajjaju Hajjaju kuwa data fita dakko madoki tanajin rufe kofar khadija" tace ja'ira Aida kintsaya year banza" Dakinta tashiga tadauki mayafinta tafito Dan dama tanason lekawa makotane tadubo Dan makocinsu dayasamu karaya. Batafi minti biyu da fitaba ahikuma Dr zayyad yashigo yanata sauri2, Ganin baiga hajjaju afaloba yasa yatura kofar bedroom dinta yaleka bakowwa aciki hakan yasa yanufi kofar day an bedroom din yatura junta kulle kuma yasan yaran suntafi makaranta bare yayi tunanin wannan izzatun yarinyarce takulle dakin acewarsa wai tafi kamada izzatun
Chapter 1 · 0% Book details