← Book details Dr Zayyad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 36

Sashe 5

Dr Zayyad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zama tayi tafara cinnata abinci kasancewar su Abba sukan dauki abincinsune gabadaya su hadu abangaren hajjaju wani lokacinda kuma bangaren baba ummaru suci abincinsu, Ahankali sukecin abincin , Ummyce tafito daga dakinsu bayan tayi wanka , Ahankali ta karso gurin tareda Jan kujera tazauna, "Sannunku,yaya barka da rana" Kamar ba abinda yafaru dazu yace barkadai yakaratun ba yabo ba fallasa" "Alhmdulillah" ummy race daga nan tayi shiru da bakinta takama cin abincinta, Abangaren umma kuwa yunwace tafara tambayar khadija Sai alokacin ta tuna bataci abinciba, "Umma waime kika daga" Umma karamace tace "wllhy yau kwalelen mutum da abincinmu Dan tuwo mukayi" Arayuwar khadija ta tsani tuwo, hakan yasa tafara tartare yammatan kafafunta umma karama nayimata dariya, Yayinda itama umma hajara taketa matse tata dariyar gudun kar agani Bangaren ammi tanufa, Dasallama tashiga ganin suna dining yasa ta karasa batako damu da ganinsaba Wanda shima ko kulawama da wani yashigo baiyiba, Kamar yadda ammi tazata haka tagani badai mayafin data gama fadansa dazunnan, Flasks tadaga ganin bakomai aciki yasa takalli ammi tareda turo baki tace ammi INA abincina, Ammi da takaici yake Neman kumeta aranta kuma tunanin rashin wayo irinna khadija takeyi ace ummy hartafi khadija wayon gaishe da babba, "Ammi Wai INA abincina tafada ashagwabe" "Babu" Shine abinda kawai ammin tafada, Yarfa hannunta tafarayi tareda cewa "kayyy ammi yunwafa nakeji" Gaskiya rainin hankalin yarinyar nan yana nema yawuce gonada iri,to ko maryam zata tsaya yin wannan abunne tabe nakinsa yayi tareda fara hada kayansa zaibar gun, "Ammi Dan allah fa" tafada da wata iriyar sigar shegiyar shagwabar "Waito khadija banace miki kici Acan gurin hajiyaba no wllhy banzata zaki dawobama" Kuka tafara tareda bubbuga kafafunta ashagwabe , Gwalonda ummy tafaki ido tamata shiyasata wani irin dira kafau dayasa gabadaya jikinta saida yamotsa,by mistake Dr zayyad yakalleta da mamakin meye haka, Ai bashiri yakoma yazauna tareda matse kafafunsa jin wani irin zallo da hajiyarsa tayi sakamakon yadda gaba daya nonuwanta suka motsa, Kasa dauke idansa yayi akanta saboda yadda gabadaya shagwabar tata ta tafidashi da kuma salon yadda take dire diren gaba daya nonuwanta na wani irin motsawa, Lebenshi na kasa yakama yacije gam tareda kara matse cinyoyinsa sakamakon yadda hajiyartasa ke barazanar fitowwa, "Ya allah,yarinyar nan anya tanada hankali kuwa? Wai ita dole saita kasheni zataji dadine?6 Dire direnta tacigaba dayi batareda tadamu dawani abuna, Cikin shagwaba tacigabada cewa "Ammi kingafa ummy tanamin gwalo,wai yaza,'ayi mutum yayi girki sannan kuma ahanashi gsky nidai amasan yadda za'ayi dani" "To uwata baranatashi nashiga kitchen nadafamiki abinci kafin kisamin duka" "Amma dai ammi aiba batun hakabane saboda kawai ba'asona sainadafa abincin kuma ahanani adauka abawa wasu ......." *Shot up!!!" Dr zayyad yafada cikin tsawa tareda buga table din da karfi Wanda gabadaya empty plate din saida sukayi tsallae, "Ke wacce irin sakarar yarinyace wai?" "Kina abu kamar wata karamar yarinyar?,to ammin kikewa wannan haukan?," "Wllhy ammi duk laipinkune kundauki yarinya kun maidata gaban hajiya,itakuma hajiya bazata taba tsawatarmataba ganitake koma metayi daidaine..." "Ai wllhy dama batun yanzu ba nasan inada makiya kuma wllhy nidai kainuwace," khadija tafada cikin yanayintana shagwaba tareda cogaba da diddira kafafunta,Wanda kamar yana dirasune azuciyar zayyad tsabar sha'awa, Afusace yadauketa da wani gigitaccen mari,Wanda bawai tsabar tsana da haushibane yasaka Dr zayyad yiwa khadija wannan marimba,Sai tsabar azabarda matsanancin halinda yake ciki Wanda yazuwa yanzu gabadaya mararsa tafara rikewa, Jin saukar gigitaccen marin yasa zainab kwalla wani matsiyacin ihu tareda juyawa cikin masifaffen gudu tayi part din hajjaju, Dr zayyad ma afusace yajuya gamida komawa busa kujerar falon 3seater yakwanta ruf da ciki gamida damke mararsa tsabar wata iriyar fitinanniyar sha,awa datake azalzalarsa, Shin me hakan yake nufi,wai meye ajikin waccan sakarar yarinyarne, Mtsssssssss yaja wani mugun tsaki tareda kara damke mararsa, Tsakinsane yamaido ammi cikin hankalina tareda sauke ajiyar zuciya, Tama rasa abinda zatace akan lamarin khadija saidai addu,a, Ummi ma hajiyar zuciya tasauke tareda Jan kafafunta tanufi daki, Da gudu khadija tashiga bangaren hajjaju, Hajjajun tana falo azaune kan kujera saijin khadija tayi tafadomata tareda sakin wani matsiyacin kuka, Tuni hankalin hajjaju yakai kokulawar tashi, "Hadiza meyafaru?" "Me akayimikine?" "Wai Hadiza bakyajinane" Cigaba khadija tayi da kukanta, Hajjaju na lallashinta da rokonta akan tafdamata abinda yafaru, Saida tagaji Dan kanta sannan cikin shasshekar kika tafar cewa, "Wai ammi CE daga naje inajin yunwa natambayi abincina tacemin babu shinefa nace meyasa zan girka abinci ahanani," To daga nafadi haka yaya zayyad yaringa dukana da marina," Aikafin takai karshen zancen tuni hajiya tafara tafa hannuwa tareda rafka salatittika kantakai wannan tadauki wani, "Yanzu Hadiza duk babartaku tana gani zayyadu ya gwaje kwanjinsa akanki?", " wllhy tana gani hajiya ko tari batayiba" Khadija ta fada tana cigaba da kukanta, "Wllhy bazai yiwuba Hadiza dole inkwatomiki uancinki, yo ko kato zaydu ya gwajewa kwanji ai yayi laushi bare kumake," "Keji duka Dan girman allah jikinta yarinya duk yayi laushi" Hajjaju ta fada gamida mikewa tayi waje, Kara mikewa khadija tayi kan kujera tareda cewa mugu kawai, Tunda hajjaju tafita take mita hartaje bangaren ammi , Ko sallamar batajira an amsamata ba tacigaba da mitarta, "Wllhy kunji kunya,kuma ni munafuntata akayi aidanasan Dan azalinci Hadiza aka kirawota wllhy dabazan bari tazoba, Ammi CE tamike daga kan kujerar datake tareda cewa "sannu da zuwa hajiya ga guri ki zauna," "Hmmm aidama mana kyace inzauna yanzu ke Dan allah ko kunyama bakyaji agabanki wai garsakeken kato kamar zaidu Yakama Hadiza yayita duka hada su mammarinta?" "Wllhy hajiya ba haka akayiba kekanki hajiya kin rigada kinsan cewar kwata kwata khadija batasan kunya, Yo dama mana aidole kice haka,hadizar metake cewa wani agidannan,yarinyar da bata fiyama shiga sabgar kowaba" "Kiyi hakuri hajiya,niganinayi baikamat ace mutum kamar zayyad khadija ta tsaya tana yimasa hayaniya akansaba kuma Dan yadaketa ai tarbiyya yayimata amma kiyi hakuri" Tafi hajiya tafarayi tana salati "Yanzu garsakwken kato kamar zaidune za,ace Dan yadaki Hadiza yayi saidai." Duk surutunnan da hajiya ke zubawa bataga zayyad daya ke kan kujerar kwanceba, Wanda yazuwa yanzu tafara Neman fita daga hayyacinsa saboda tsabar azabar da marar sa takemasa, Jin surutun hajjaju na Neman FASA masa kai yasa cikin karfin hali da jarumta tareda kokarin boye yanayin dayake ciki yasamu tamike zaune, Kara cije lips dinshi yayi da karfi saboda azabar karuwa dayake jin sha'awar tasa nayi, Cikin karfin hali yayi azamar mikewa, Dasauri Yakoma yazauna tareda kara dafe mararsa saboda yadda hajiyarsa ke Neman tona asirin yanayinsa, Juyowa hajiya tayi jin motsin mutum abayanta..... "Au ashema kana jina isasshe amma bazako tankaminba ko" Ko kallonta baiyiba saima sake damke kansa dayayi saboda saramasa dayafarayi, "Oni rabi watakam zaidu INA magana kana daga kai saboda gani mahaukaciya,watakam ciwon kai ma zansakamaka ko, Afusace cikin yanayi na kaiwa matuka adauriya zayyad yamike tareda fara Jan kafafunsa yanufi kofa, " lallai zaidu ka rainani saboda banina haifekaba,duniya kenan," "To wllhy bari ubannaka zaizo yasameni" "Adaiyi hakuri hajiya," ammi ta fada gamida rissinar dakai, Ko kallonta hajiya batayiba tayi gaba fuuuuuuu, Tanufi part din ta, Zayyad ma dakyar yasamu yakai kansa dakinsu tareda fadawa bakin gado yakwanta yana juyi hannunsa rikeda mararsa, Yafi awa daya akwance kafin wani wahalallen bacci yakwasheshi, Abangaren hajjaju kuwa kafin takoma tuni baccin wahala yadauke khadija, Tunda takoma babu abinda takeyi Sai mita, Saida aka kwala kiran sallar magarub zayyad yatashi da wani azababben ciwon kai, Zuwa lokacin kuma akaso Dari na feeling din dayakeji babu kaso hamsi, Adaddafe yayi wanka tareda dauro alwalla yagabatarda sallah, Akan daddumar yazauna yajingina bayansa da bango tareda jawo wayarsa, Train missed calls ne barkatai ,Wanda yawanci duk na abokansane Sai ammi da abbanshi saikuma fareeda, Abbana yafara kira bugu biyu aka daga tareda sallama "Wa alaykassalam Abba anwuni lfy" Daga dayan bangaren aka amsa da, "Lpy kalau,allahbdai yasa lpy Dan naji muryarka wani kala sannan kuma nakiraka baka dagaba bayan ancemin kana gida," "Wllhy Abba banajin dadine kuma bacci yadaukeni sakamakon magani danasha" "Assha to allah yakara sauki, Indai kaji da dama to inason ganinka kamar yadda nafadamaka dazu,Iran allah yakaimu bayan issha abangaren hajiya," Gabansane yadan fadi danshi har ga allah kwata kwata bayason abinda zai kara hadashi da yarinyar nan,Dan wllhy matukar hankalinsa yana tashi haka to komaima zai iya faruwa,.... "Zayyad ko bakajinane" Abba yafada jin zayyad din yayi shiru, Ahankali yasauke ajiyar zuciya tareda cewa, "Badamuwa Abba insha allahu zanzo" "Allah yakara dauki" abban yafada tareda kashe wayar, Bayan kashewar yakira ammi sukayi magana tabashi hakuri akan fadan hajiya tareda tambayarsa akawo masa abincinsa dakin ko zaizo nan? Cemata yayi zaizo yaci tareda kashe wayar Abokinsa yakira Wanda amininsane sosai kuma gurin aikinsu daya wato Habib, Habib shima kamar zayyad yake kasancewar Sai hali yazo daya ake abota, Saidai sabanin zayyad shi Habib yakanyi sex,bashida akida irinta zayyad, "Hellow guy son ya kk" "Lpy kalau" aka fada daga dayan bangaren "So ya yau yakuma aiki" "Lpy kalau,saidai lpy yau bakazo office ba?, Kuma true out yau baka kiraniba?,nikuma nakiraka dazu naji ba,a dagaba shine nace ko ansamu harka," Tsaki zayyad yayi tareda cewa, "Malam ciwon kai nakeyi sannan kuma nakiraka zaka karamin Sai shouting kakemin", Cikin raha Habib yace , " to oga ayi hkr" Mtsssss. Zayyad yaja tsaki tareda kashe wayar yamike har yanzu jikinsa ba kwari yayi gaba abinda, Sanin halin zayyad da Habib yayi yasa shima baikuma kirana saboda yasan kozai kwana yana kira bazai dagaba, Bangaren ammi yakoma yaci abinci yasha magani sannan yadan kishingida akan kujera, Kiran sallar osshane yasa yamike tareda ficewa zuwa masallacin dayake jikin gidan, Acan ya iske gaba daya kannensa maza da kuma uyayensa, Bayan idar da sallar ne baba ummaru yace yanaso su hadu abangaren hajiya, Kamar kullum yauma taron dai akan maganar Dr zayyad ne da yan uwansa, Saidai ayau zayyad din baisamu goyon bayan hajjajunba sakamakon taba mata yar jikallen tata dayayi Wanda sanadiyyar hakan ko sallamrsa bata amsa ba, Haka dai akayi taron aka gama Wanda sum rabinsa akan zayyad ne saikuma maganar saurayin aunty zainab Wanda yazo da maganar cewa amaido aurensa da aunty zainab din nanda wata biyu sakamakon seminer dazai tafi Wanda yakeso yatafi da mararsa can ta gama karatunta akasar america, Akarshedai an yanke shawarar hadawa Dana yaya munir da aunty shamsiyya acewar baba ummaru itama Sai ta karasa karatunta anan, Sannan kuma al'amin ma Iran yadawo shima yace datashi maganar auren saidai shi bazamu Yankees masa hukunci
Chapter 5 · 0% Book details