Sashe 9
Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
************
Rungumeta Hanifa tayi idanuwanta zuciyarta na tafarfasa ta zare gyalen jikinta ta yafawa Naj din ajiki ta Jata ahankali zasu shiga cikin gida ummanta da idanuwanta sukai jajir zuciyarta na Mata wani irin tsananin nauyi Dan Bata buqatan tabbaci tasan auren Naj yasake rushewa kenan da nauyin murya tace"
Kuyi can gidan Hanifa kada kishiga Nan da ita akwai mutane zasu fahimci abin daya faru Kuma komai zai iya faruwa sbd wannan abun daya faru yanzu kuje can kawai tana buqatan kadaici Nima Ina buqatan nutsuwa.
Kallon umman Hanifa tayi cikeda damuwa tace"
Umma ke fa?
Ran Dattijo ya baci kada cikin mutane yayi Miki fada.
Bakomai kuje kawai kuje.
Juyawa tayi ta shige Dan ko kallon Naj takasa sbd tsananin baqin cikin halinda Naj din take ciki.
Sake rufeta Hanifa tayi tajata suka fice tana gani waje kowa ya rabe Yana kallo sojojin DM suka ja Abbas din daga cikin gate na biyu sukai Masa wani irin mugun duka sai gashi Yana ihun ceton Kai Dan azaba gashi me gidan nasu tuni yashige abinsa bare yace su barshi Haka Dan Haka sukai Masa iya Yinsu Saida akaje da gudu aka sanarda Dattijo ya fito cikin tsananin tashin hankali har Yana mugun tuntube zai kife ya ceci Abaas din Wanda baqar zuciyarsa batasa yayi nadamar abin dayayiba saima kallon kawu da yayi da bakinsa fal jini cikin tsananin baqin ciki yace"
Naj ce tasa amun wannan" daga Haka Bai qaraba ya juya ya fada motarsa Yana dafe gefen cikinsa dake Masa mugun ciwo yakasa Jan motar sbd ko gani bayayi sosai Dan take fuskarsa tayi wani irin tashi Kamar burodi Dole jiki na rawa kawu yakirawo jamilu dansa dake cikin gida yazo ya Kama mishi Abbas din suka maida baya jamilu yaja motar kawu na gaba suka nufi asibiti da Abaas din Dan kuwa tuni ya kumbure musamman bakinsa daya baje.
Tunda suka Iso palon hajja Kai tsaye Naj daki ta wuce idanuwanta jajir Bata buqatan komai da kowa a yanzu tunani kawai takeso abarta Dan hakan yasa Hanifa Bata bita dakinba ta zauna Palo tareda sauke wata nannauyan ajiyar zuciya ranta amatuqar jagule itama.
Kallonta hajjo tayi tace"
Meya farune naganku haka? lafiya kuwa?
Kai tsaye Hanifa ta fada Mata abindaya faru tana qarawa da cewa"
Dattijo shi laifin umma yagani
Ummanma tanacan cikin tsananin damuwa ko wannan karon dai anfasa auren Naj.
Hajjo sosai itama zancen ya mummunan Bata ranta tace"
Ina yiwa Najma adduar alkhairi akan aurenta aduk sallata Dan Haka inaga hakan shine mafi alkhairi gareta Allah yakawo Mata mijin daya fisa.
Amin"Hanifa tace jikinta amatuqar sanyaye idanuwanta sai cikowa sukeyi da hawaye tana maidawa sbd Allah yasani batason Abaas da Naj to Amma Kuma da aka fara hidimar bikin nan bazataji dadin wargajewar auren Naj dinta akaro na maimaci.
Har dare Naj na kwance a daki idanuwanta rufe kaman me bacci saidai ba baccin takeba Dan Babu ta yanda zata iya bacci duk cikin aure aurenta da ake fasawa Babu Wanda ya dasu ta Hanya mafi Muni Kamar wannan.
Har dare Babu me dadin Rai acikinsu anan gidansu Hanifa Abu komawa yayi Kamar na zaman makoki Dan kuwa murna da farin ciki sunkoma damuwa da baqin ciki amma dai lokacin basusan menene zai farun gobe ba yiyuwar auren kokuwa¿
Hajjo data Kira Umma ta Dan Mata maganganun kwantar da hankali tareda sake tunatar da ita daukan qaddara me kyau da sabaninta Yana daga cikin zaman cikakken me mumini me Imani Dan Haka kada ta damu sosai tayi addua kafin safen Allah yasa suji alkhairi idan fasawarce alkhairi idan Kuma yin auren.
Cikin rauni da tsananin damuwa Umma tace"
Na yarda da qaddara hajjo Amma tayaya Dattijo zai lalata rayuwarta ta hanyar aura Mata wani cikin fushi idan ikirarinsa yazama gaskia rayuwarta zata iya lalacewa a qarshe dai auren da aka dage da sai tayin baiyi Rana ba kenan.
Inshallah rayuwar Najma bazata lalace Alfa bazai Bari a lalata rayuwar Najma ba zanyi magana dashi idan har sun fasa auren a hakura Allah zai kawo Mata wani.
Sai alokacin Anty Amina dake dakin Naj da Babu mutane tareda umman taji abin daya faru hankalinta yayi mummunan tashi cikin damuwa da Dan tsoro ta kalla idanuwan umman dake son cikowa da hawaye a raunane tace"
Umma Dan Allah kada kiyi kuka wannan jarabawace Allah kewa Naj Inshallah zata cinye.
Sauke Kai umma tayi tana girgizawa ahankali cikin tsananin baqin ciki da damuwa tace"
Wannan jarabawatace Nima sbd Ina cikin wani hali na tsananin baqin ciki da damuwar rashin auren Naj
Dadah bazata qara Bari nasha ruwa gidan Nan ba cikin kwanciyar hankali
Ga Dattijo Yana rantsuwar aurar da ita ko duk Wanda yasamu wannan karon tayaya Zan iya kwantar da hankalina da hakan?.
Zama Anty Amina tayi itama tana rafka tagumi cikin tashin hankali da tsoro ta bangare daya tana adduar Allah yasa kada Abbas din yafasa sbd duk halinsa gwarashi an sanshi idan yafasa ba'a San wa dattijo zai aurawa Naj din ba tunda yayi rantsuwa to tabbas kowa yasamu zai iya daura mata Dan Haka ita dai anata gwara Abbas din dai ko yayane.
Ta bangaren Dad Alfa hajjo takirasa yazo tayi Masa bayanin komai ta dora da cewa"
Auren wannan yaro ga yarinya Mara hayaniya da nutsuwa Kamar Naj Sam baiyiba Kuma hakan ya nuna Babu da'ar sanin darajar mace data aure atare dashi Dan Haka idanma su Basu fasa din ba kayi magana da Dattijo a hakura afasa bashi auren.
Shiru Dad Alfa yayi Yana nazarin maganar wadda ta Sosa ransa matuqa shima sbd yanajin Najma tamkar Hanifa Dan Haka Aure Kam kosu Abbas Basu janyeba babushi Dan idan har zai iya yaga Mata rigar mutunci Haka acikin gidan iyayenta tun kafin aure bayan aure al'amarin bazaiyi kyau da dadin ji ba Dan Haka take ya yanke shawarar neman Dattijon tun Daren suyi magana hajjo ma tace"
Idan ka aika kiransa zakuyi magana ka kirani Nima zanyi Masa mgn Dan kada ya qarfafa abin sbd hankalin Fatima umman Najma din ya tashi matuqa da hukuncin dazai yanke.
A asibiti su kawu sai kame kamen zancen ban haquri yakeyiwa mahaifiyar Abbas da qanin babansa Dan mahaifinsa ya rasu Yana Basu hakuri da Basu tabbacin bayan daurin auren gobe za'a zauna ayi magana.
Hajiyar Abbas da ranta yagama mummunan baci ganin yanda kamannin danta ya sauya lokaci guda take ta rufe ido tace wallahi tallahi ko 'yar gwal ce Naj danta bazai auretaba Kuma bazasu yarda ba saisunyi shari'a dasu dattijon akan wannan dukan da akaiwa Abbas dan kuwa zata saki dukiya iya dukiya sai an hukunsu.
Kawu najin Haka wani irin dunqulallen baqin ciki ya tsaya Masa a zuciya ba Dan qarar datace ba sai fasa auren da akai Wanda dama jikinsa yabasa za'ai hakan.
Danne baqin cikinsa yayi yaso qanin mahaifin Abbas din yabashi dama suyi magana ta maza a fahimci juna idan yaso bayan an daura auren ayi maganar wannan Amma Sam shima abin Bai Masa ba ace anyiwa ango duka a gidansu amarya wannan al'amarin babbane.
Kallon Dattijo alhajin yayi a natse yace"
Alhaji Ibrahim katafi kawai maganar Nan bazata yuyuba yanzu sbd halinda shi Abbas din yake ciki maganar auren Kuma a goben dai gskia bazai yiyuba saidai ko kila gaba.
Shiru Dattijo yayi zuciyarsa na quna da tarin baqin ciki,
Shi shikenan kullum cikin gayyata yake Yana Tara mutane Ana fasa aure har sai yakai ya gayyata ba'a zuwa.
To anyi na qarshe da yardar Allah.
Juyowa sukai suka fice daga asibitin suka tari adaidaita sahu suka shiga Babu me cewa qala dagashi har jamilu Wanda shima fasa auren Bai Masa Dadi ba sbd baiga abin fasa aurenba idan an zauna anyi magana Amma sun dauka zafi har suna maganar qara da shari'a Wanda zaice Dan basusan a Ina akai dukan bane da bazasuma fara kawo maganar qara da shari'ar ba Dan kuwa yanasa ran sojojin Marsha ne sukai dukan bama na Alhaji Alfan ba bare ace da sauki.
Koda suka iso gida Saida Dattijo sukai sallar ishai a masallaci kafin yashiga gida dake danqam da hayaniyar Yan biki dasuka zozzo cikinma da yawa zuriar wasu Basu zoba sbd sunsha zuwa bikin Naj din Ana fasawa shiyasa ba kowane yasamu zuwaba.
Gurin Dadah ya aika jamilu yace yakirata sbd zancen bazai yiyu acikin gidanba dayake da mutane ko Ina.
Dadah dake zaune tana Shan radionta cikin kwanciyar hankali ta kalli jamilun daya fada Mata Dattijo na son mgna da ita ta kalli fuskarsa tsaf taga ba wata annushuwa jikinta yabata ba lafiya Allah yasa ba abinda yasaba faruwa bane,ta kashe radiyon tareda miqewa da hijabinta dake jikinta ta nufi kofa tana tafiya ahankali irin ta tsofin da qafafunsu Basu cika wata isashiyar lafiya ba ta nufi waje batareda kowa yasan ta fitar ba.
Dattijo dake tsaye Yana jiran isowarta Kiran alhaji Alfa yashigo wayarsa dama shima gurin nashi suka nufa ayi maganar gabaki dama Dan Haka Dadah na qarasowa yace"
Dadah muje can gurin Alhaji Alfa ayi maganar sbd Nan akwai mutane yanacan Yana jiranmu.
Dadah najin Haka tun Basu qarasaba take cewa"
Ibrahim maganar auren Naj din ce Babu ko?
Shiru yayi zuciyarsa a jagule Bai amsaba har Saida suka Isa cikin babban palon gidan na baqi suka zauna dama Alfa na palon shida hajjo suna Kiran isowarsu.
##MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
*_DM 10_*
*_MG's SKINCARE_*
*_Ina manyan Mata da manyan yara masu buqatan gyaran jiki da fata akan tabbaci da ingancin kyawu da aikin me kyau kuzo ga mg's skincare inda sukeda nagartattun sabulai da creams masu kyau da aiki,_*
*_mg's skincare nada black soap dasu molato soap hakama akwai gangariyar sabulu na musamman Mixed na Molato/black soap Wanda hadinsa da aikinsa karshene sbd mun gwada mun tabbatar 💯_*
*_Akwai Kuma herbal whitening black soap Wanda shima aikinsa na musamman ne,_*
*_Saikuma beauty kit gbdy nagyaranjiki su cream dakomai ne acikin shi,_*