← Book details Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 59

Sashe 12

Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A waje Babu kowa maza tsit duk an tafi gurin daurin auren da za'ayi dama a babban masallacin juma'ar da Alhaji Alfan ya Gina acan farkon layinsu jami'an tsaro da securities kuwa koina cikin layin akwaisu
Sojojin Marshal ne a kofar gida tsatsaye jikin motarsu da alama jiran fitowarta sukeyi ta wuce Kai tsaye ta shige gate suna bude Mata da sauri
Ahankali tace" thank you" tana wucewa hankalinta a waya.
Tana saka Kai a palon hajjo Yana fitowa sanye cikin wata navyblue hilton filtex da rawar da yakeyi kawai zai bayyana kudi me yawa ya lashe
Sai hular daya saka wadda ke nuna Bai Saba sakawaba Dan yanda ya sakatan ta Dan Yi gefe Amma sai hakan yayi wani irin yiwa kyakkyawar fuskarsa dake fidda wani irin qyalli na kwarjini da cika ido ta dauke idanuwanta akansa tana rabewa ya kalli Dan qaramin siririn gyalen dake kanta Wanda iyakacinsa kafadunta ya dauke kai Yana wucewa sbd lokacin daurin auren yayi saura mintuna basufi goma sha uku ba ita Kuma tana shigowa tsakiyar palon hajjo da wasu baqinta da Basu Dade da isowaba sukabi Naj din da idanuwa gabaki dayansu.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

*_DM 12_*
Ganin duka idanuwansu akanta yasa ta sauke idanuwanta tareda qarasowa a natsenta cikin taushin murya da rashin karauniya tace"

Ina wuninku Baabah barka da zuwa.

Sake Mata kyallon qiri qiri su baabar keyi wato yanne da qannen mahaifiyarsu Jalal dinne suka qaraso yau sbd tun a Daren jiyan hajjo da Alhaji Alfa suka sanar dasu auren jalal din daya Kama na gaggawa saidai Ba'a sanar dasu yanda akai auren ya yiyuba dakuma girmarsa datai sbd idan ba'a fadaba zakacema ta girmenta sosai Sosai sbd yanayin jikinta datake me kyau da burgewa da nasa jikin daya bude sosai sbd exercise dakuma tsayi daya fita sosai Dan Haka cikeda yabawa suke kallonta fatarta na daukan musu ido sbd zallan gyalan dilka da wasu abubuwan da akaita Bata tana Sha Dana mulkawa.
Baabah tace"

Lafiya kalau alhmdlh,ya hidimar kike 'yar Nan? Ya hidimar jama'a?
Allah ya Sanya alkhairi kinji,
Allah yayiwa wannan auren naku albarka.

Da sauke Kai tayi shiru batareda tace Amin din ba tunda tasan abinda yake Nan ba aure.

Hanifa dake daki tagama shiryawa cikin Ado na shigar alfarma tana qamshi sbd mijinta da tuni ya iso suna gurin daurin auren
Fitowa tayi takama hannun Naj sukai dakin tana cewa"

Naj zo ki sauya shirinki inasa ran yanzu kowane lokaci za'a daura auren
Zo kiyi ado A ranar farko mijinki ya ganki da ado na musamman.

Zama kan sofa dake dakin Naj tayi tana aje wayarta da kallon Hanifa cikin Dan basarwa tace"

Nasan kinsan anfasa auren Nan just drop your drama.

Murmushi me girma Hanifa tasaki tana cirowa Naj din wani tsadadden navyblue lace me tsananin taushi da rashin ado na hayaniya Wanda yaja kudi sosai gurin siya tareda wani transparent emboidery veil ta aje gabanta tana cewa"

Dan Allah ki shirya kadaki Bari asan abinda yake faruwa musamu Mana a watse lafiya basai kin nuna musu Abbas yafasa aurenki ba ki nuna ko babushi Zaki iya rayuwarki ta walwala da farinki.

Da gangan ta fada hakan Dan Naj din ta shirya da farko qin yadda tayi sai daga baya ta saka kayan ta zauna bakin gado sbd zuciyarta data fara harbawa da sauri da sauri Kamar zata Fado ta Dan dafe kirjinta tana sauraron bugun zuciyarta daya sanyata lumshe fararen idanuwanta ta rufe tanajin kamarma hadda faduwar gaba.

Miqewa tayi ahankali takoma Palo inda hayaniyar baqin gidan take Anata fira
Tana fitowa dukkanin idanuwansu suka sake dawowa Kanta suna Yana baiwar kyawu da Allah yayiwa Naj din qamshin wani irin fitinannan turaren da ummanta ke Mata gyara dashi daya Gama Kama jikinta Dana kayanta tareda kayanta da aka turara ya gauraya palon cikin nutsuwa da farin ciki a fili hajjo tace"

Masha Allah, Allah na gode maka da ganin wannan Rana Allah kasawa aurensu albarka da farin ciki me dorewa.

Amin Hanifa ta amsa idanuwanta akan Naj da ko itama dasuka taso tun yarinta tare sukai rayuwa tare koyaushe tana yabawa.

Qarasowa tayi gefen Hanifan ta zauna tana duba wayarta hankali kwance ba damuwar komai su Kuma suka cigaba da sha'anin gabansu.

*****
An daura Auren JALALUDDEEN MARSHAL ALFA da NAJMA ABDULLAHI BELA akan sadaki naira dubu dari cif Wanda duban jama'a suka shaidar cikin mamakin sauyi da aka samu ciki harda jama'ar su Abbas da yawa sun halarta sbd basusan cewan an fasaba duk da hakan dai kowa tanata fatan Allah yasanya alkhairi Wanda aketa bawa Marshal hannu Ana tayasa murna shidai bin kowa yake da mayun idanuwansa sai hannu dayake bawa manyan mutanen dasuke miqa Masa hannu Dan tayasa murnar aurenda Saida ya iso gurin yasan nasane.
Isowarsa gurin yasa mahaifinsa daketa dakon jiran isowarsa ya qaraso gabansa Yana kallonsa Kai tsaye yace"

Za'a daura auren Najma dakaine Ina roqon alfarman ka amince da hakan sbd wancan ya fasa adaidai lokacinda Babu wani mafita shiyasa a matsayinsa na mahaifinka Kuma itama Ina matsayin uba gareta na hadaku ta hanyar nema maka aurenta Ina fatan zakamin biyayya.

Fararen mayun idanuwansa ya zubawa Dad din kafin ya Dan sauke Kai cikin miskilar murya yace"

Ok Dad.

Hakan dayace yasa Dad din Jin wani irin sanyi da nutsuwa sbd yanata nazarin yanda zai fahimtar da jalal din hukuncin dasuka yanke Kai tsaye akansa batareda Jin shawararsa ko raayinsaba tunda ba yaro bane yanada iko da yancin zabarwa rayuwarsa abokiyar rayuwarsa da kansa duk da yasan karba Masa Marshal din yayi sbd yariga yazo gurin bazai iya komawaba yasa Dad din kunya Amma yanayinsa kawai ko Bai fadaba Dad yasan anyi Masa shigar sauri Dan kuwa Babu tsarin aure agabansa yanxu musamman da wannan din da za'a daura da ita Dan kuwa a yanda suke dinnan ba lallaiba ta kwantar Masa da Kai shikuma bayasa ran macen dake qarqashin ikonsa zatana Masa kallon qani ko wani Abu Dan kuwa shi mijin macen dazata bisa ne Amma tunda su dad din suka zaba auren dama agurinsu zata zauna so ba damuwarsa bane sosai aciki tunda shi bataredasu zai zaunaba a taqaice ma yaji bazai iya dogon zamaba komawa zaiyi.

Dan Haka Ana gama daurin aure akai gagarumin reception da akai liyafar alfarma shidai ko ruwa Bai Sha ba aka fara watsewa ya zame yayo gida kansa na 'dan sarawa Dan Haka Koda ya iso gida Kai tsaye flat dinsa ya wuce ya zare babbar rigar jikinsa da hula da komaima ya cire ya fada toilet ya sakarwa kansa ruwan dumi ta shower Yana sauke ajiyar zuciya.

Sai dayayi wanka yafito yaji ya Dan samu nutsuwa da saukin ciwon kan ya saka guntayen qananun Kaya yaje fridge yasha ruwa kadan yadawo yashige daki ya kwanta Yana kashe wayarsa cikin nutsuwa bacci ya daukesa.

Saida 'yan daurin aure suka dawo kowa yaji da Wanda aka daura auren zallan mamakin al'amarin yasake yayata gidansu Naj da hayaniya saidai Kuma tunda dai ansamu andaura Mata auren ba'a fasaba gabaki dayaba a watse a banza yasa aketa sabuwar murna Allah yayi lokaci yayi tayi aure duk da wasu da yawa sun manta da banbancin shekarun sbd matsayinsa da yanayinsa yasama har wainda suka kusan haihuwarsa suna basa tsananin girma sbd matsayi da kamewa shiyasama ake mantawa da wani banbancin shekaru sai murna sukewa umma Allah yabasu Wanda yafi abundama suke buri tako Ina.

Dadah kuwa Banda sadaka da godiyar Allah tana washe bakin babu abinda takeyi yau Jin takeyi wani irin sakat daga ita har Dattijo da sai baza babbar riga yakeyi Yana gaisawa da manyan mutanenda yasan Albarkacin auren Naj da jalal ne yakeci Dan kuwa ganinsu Koda appointment ne shi bazai samuba Dan Haka sai farin ciki yakeyi Yana baje babbar rigarsa ta tsadaddiyar shaddar da Alhaji Alfan ne yake dinka Masa daman.

Yana dawowa gidan yakira Naj a waya yace maza tadawo gida yanzu.

Da mamaki ta fito zuciyarta ba Dadi sbd dai ga dukkan alamun data gani agun mutane andaura auren kenan
Ta hadiye wani Abu me daci da nauyi daga maqogoranta Dan kuwa auren Abbas shine mafi mumman al'amari daya sameta a wannan rayuwar.

Ko data shiga gidansu sama sama takejin Ana mata adduar Allah yawa aure albarka Saikuma tafarajin Ana Kiran sunan Jalal da cewan mijinta
Kanta ne taji ya dauka ciwo sbd komaima ita yanzu a duhu yake Mata Kai tsaye dakin Dadah ta Isa sbd tasan Dattijo daya aika kiranta Yana can tana Isa tashiga da siriryar sallama ta nufi gefen Dadah daketa washe Baki cikin farin ciki ta zauna ahankali tareda bude Baki cikin taushin muryarta tace"

Barka da jumaa Dattijo.

Gaida Dadah tayi itama duk da dazun sun gaisa data shigo.

Kallonta Dattijo yayi dakyau yana Dan kame fuska yace"

To Najma Kamar dai yanda Kika sani yau ne ranar daurin aurenki da Abbas
Amma sbd rubutowa ta ubangiji Allah baiyi shine mijin ba Dan kuwa a jiya suka sanarda sun janye sbd abindaya faru a jiyan da safe.

'dan shiru yayi kafin yacigaba da cewa"
Sakamakon hakan yasa Babanki Alhaji Alfa da hajjo suka bayyanarda buqatarsu tason nemawa JALAL aurenki muka amince atake sbd Babu wani zabin kokuma mafita Daman cigaban dayafi hakan Dan Haka dai a taqaice andaura Miki aure da JALAL yanzu ke matarsace halak malak saidai Hajjo ta nema alfarmar kada a takuraki da maganar tarewa gurinsa kokuma wani abun yanzu duba da yanda akai auren Dan Haka Zaki zauna gurinta kafin daga baya idan an natsa Kya koma sashen mijinki kokuma ki bisa can qasar dayake.

Akaro na farko a rayuwarta data kafe Dattijon da ido idanuwan nayi jajir ko qyaftawa batayi zuciyarta ta tsananta dokawa har batasan lokacinda ta bude bakiba tace"

JALAL qanin Hanifa?
An daura auren kokuwa dai za'a daurane yanzu??

Gano inda ta dosa da Aniyar bijirewa auren yasa ya tsuke fuska cikin bori yace"
Chapter 12 · 0% Book details