← Book details Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 59

Sashe 38

Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana shiga hajjo na daki Babu kowa a palon bayan ruqayyat dake sake jere abincin Rana da aka fara gamawa.
Aje basket din hannunta tayi a dining ta juya ta nufi dakin Naj datake Jin shedan na ayyana Mata taje tunda Naj din Bata Nan zuwa yanzu tasan tana office.
Tana Isa jikin kofar ta Murda ta bude ahankali zata shiga taji Naj din na waya da Sarah cikin damuwa da rashin sukunin data tashi dashi akan cikin,gabaki daya hankalinta ya juye Tama rasa Ina zata saka ranta da tunaninta komai nata ya tsaya cak
A yanda ta yau din ta ringa Jin abubuwan da jalal yake Mata har cikin ranta ta tabbatarda aikin cikin jinintane sbd abinda yafaru a Daren yau din sosai jikinta ya karba hakan Wanda ta tabbatarda hakan yaci gaba tozarcin datake gudarwa kantane zai sameta sbd yanayi na cikin Wanda shima dakansa ya fahimci a Daren jikinta ya karba saqonsa tako Ina,
ta rintse ido tanajin wani irin kunya da takaicin kanta da ma na cikin Kai tsaye cikin damuwa tace"

Sarah ki shirya kizo yanzu Zaki daukeni muje wani asibitin ayi scanning Zan biya ko nawane a ciremun cikin Nan,
Kunyar zancen Nan ma yafita nakeji,kizo yanzu,gani Zan fara shiri.

Kashe wayar tayi tana kokarin saukowa daga gadon da gabaki daya qamshinsa yakeyi ta yamutsa fuska tareda miqewa tana gyara zaman towel din dake daure ajikinta Wanda Takoma bacci dashi bayan tayi sallah
Ta inda ta ajiye takardar jiyan ta dauko tasake budewa ta karanta zuciyarta na tsalle da quncin rashin sanin Yaya zatai da wanann qaddara ta cikin data sameta Kuma tsoron cirewar na Dan shigarta Dan Bata taba kwatanta hakan akantaba.
Shafa cikinta dake shafe ahankali tayi tana sauke numfashin dayake sake shigar da ita damuwa ta maida takardar cikin envelope dinta ta saka cikin handbag dinda zata fita da ita kafin ta daga qafafu ahankali ta nufi toilet yashige tareda rufo kofar.

Wani irin tsalle zuciyar Hannah keyi na shiga cikin wani razanannen yanayi na kaduwa da tsoro tsoro dakuma farin cikin Jin wannan muguwar tonuwar asirin dazai samu Naj Wanda zai taimaka Mata shikenan qarshen Naj da Marshal yazo,
Bama Marshal ba ko iyayenta saisun tsaneta bare familyn Alfa Dan kuwa ba tantama idan har yanda taji Naj nada ciki to cikin tsohon saurayinta dasuke aiki guri dayane Abaas lamido.

Da sauri ta bude kofar ahankali ta shige dakin ta isar jakar da Naj tasaka result din ta bude ahankali tana kallon kofar toilet din ta dauki envelope din tareda rufe jakar ta silale ta fice tareda rufe kofar ta bar sashen gabaki daya da sauri.

Sashensu ta qarasa hannuwanta na rawa da jikinta tun a Palo ta tsaya hannuwanta na rawa tafara kokarin Ciro takardar daga envelope din
Mum Malika dake zaune ta miqe itama ta matso cikin mamaki da son ganin menene take cewa"

Menene kiketa rawar jiki haka kina zare idanu.

Bude result din tayi dakyau tana karantawa zuciyarta na tsallen wasi wasi duk da shedan na saka Mata tabbacin cikin wani guri ta samosa
Saidai Kuma tunanin sanin wacece Naj da girman kamun kanta da sanin darajar kai nasata tunanin ba cikin kowa bane saina Marshal.
Cikin wani mummunan yanayi na fita hayyaci tace"

Uban waye yayi Mata ciki?Dan kuwa Babu wani kusanci a tsakaninta da Marshal bare ace cikinsa ne,
Wannan cikin bana Marshal dina bane,Sam Sam,
Zan nuna Masa wannan Dan yasan wacece Naj da irin rayuwar datake da wasu mazan...

Da sauri mum Malika ta qwace takardar tana karanta cikeda mamaki da firgici itama,
Ta dago tana jinjina Kai cikin Shiga tunani tace"

Tun kwanaki Naga alamar ciki ajikin yarinyar Nan Amma ban kawo hakanba araina sbd sanin Babu wani kusanci ko mu'amalar kusa dake Shiga tsakaninta da Marshal Kuma banajinma kowa yasan sunada kusanci kowa yasan Babu wata mu'amalar kusa tsakaninsu to Ina wannan cikin ya fito???

Qwace takardar Hannah tayi idanuwanta na sauyawa da tsananin baqin ciki da tashin hankalin rashin sanin taqamaimai cikin Ina ya fita cikin tsananin baqin ciki da zafin Zuciya tace"

Koma Ina ya fito nasan bana Marshal bane,
Ko Ni Marshal Bai taba yiwa kallon sha'awa ba nida nake Masa shigar daukan hankali kala kala tareda bayyanar Masa da duk wasu sigar daukan hankalin maza Amma Bai taba Bina da kallon sha'awa ko so dayaba bare ita da Bai taba ganin wani kayan daukan hankaliba ko jikinta a bayyane bare har ya iya kusantarta Dan Haka Marshal bayada alaqa da wannan cikin shiyasa Dole Zan nuna Masa Dan yasan waye Naj da halinta ko zai sawwaqe Mata taqara gaba.

Zama mum Malika tayi tana janyota ta zauna itama cikin nata baqin cikin tace"

Ba kince tace abortion zataiba?
Kibari saimun samun tabbacin abortion din saimu samu hanyar sanar dashi ta yanda idan yaji tayi wannan abun qyamar Kuma tana kokarin zubarwa Dan Kar wani yasani zaifi daukan zafi mukuma mu samu abinda mukeso,
Amma dai yanzu ki Adana takardar Nan ba yanzu zamuyi amfani da itaba karki Bari zafin Zuciya da rashin hakurinki ya Bata Mana aiki nasan halinki bakida dangana ko kadan.

Zafin da zuciyar Hannah ke Mata yasata miqewa tana maida takardar cikin envelope ta nufi daki ta dauko mukullin motarta ta fito ta fice zuciyarta na wani irin nauyi Dan dai ita tarasa yadda da zancen inda zata saka cikin.

Motarta ta nufa ta bude tashiga tana kokarin tayarwa Naj ta fito Sarah na tareda ita tana sanyeda doguwar rigar jallabiya ash da gyale black datai rolling Jakarta na hannunta Sarah ta karba key suka Shiga motar suna kokarin tadawa ta fito Tata motar zuciyarta na sake tafasa ta nufi sashen Marshal da tashinsa bacci kenan yayo wanka Yana sanyeda qananun Kaya ash da sukai Masa kyau ya dauki wayarsa zai saka Kira Hannah Tai knocking kofar.

Kallon kofar yayi tareda Dan dauke Kai sbd baya buqatan damuwar kowa yau shiyasama yau zai tafi gidansa dake anguwarsu ta sojoji zai Kira Dr sa'id can ya samesu ya duba Masa Naj din acan yanason sanin menene matsalarta Dan ko yau da asuba tayi Amai kafin yafita sallah.

Bude kofar yayi tareda zuba Mata idanuwansa fuskarsa a kame ta kallesa tanajin zuciyarta na qara mamayuwa koina da sonsa,
Bazata rasashiba Kota halin Yaya, Marshal natane Dan bazata iya rayuwa babusaba.

Juyawa yayi yakoma ciki ganin irin kallon datake Masa da dukkanin idanuwanta abinda yafi tsana kenen agurin Mata yawan kallo.

Idanuwanta rufewa sukai da takaici da baqin ciki da tsananin kishinsa ta fitarda envelope din hannunta ta qaraso ta ajiye Masa a gabansa ta juya zata fice saikuma ta dakata tareda juyowa ta dawo cikin marairaice fuska hawayen data Dade tana dannewa tun dazu na radadin da zuciyarta keyi zuciyarta na zafi tace"

Marshal ina maka son da bazan iya cin Amanarka ba Kamar Naj sbd Haka nakasa boyewa abinda naji nakuma ga tana kokarin Yi,
Abortion take kokarin........

Wani kallon daya dago Yana Mata yasa maganarta maqalewa tana kallonsa zuciyarta na harbawa da fatan yayi mummunar fusatar dazata tashi kowama ayi duk abinda za'ai.

Idanuwansa ya maida Kan takardar data aje yakai hannu Kai tsaye ya dauka ya bude.
Sunan asibitin yafara kalla yaga asibitinsu Dr sa'id ne ya gangaro da idanuwansa zuwa cikin takardar Yana karantawa.

Shiru yayi idanuwansa zube akan takardar wani irin yanayi na rashin tabbaci da Kuma abinda Hannah tafada yasashi aje takardar tareda miqewa ya nufi dakinsa ya dauko key din motarsa ya fito lokacin Hannah tuni ta fice ta nufi motarta itama ta fice Suma su Naj tuni suka fice daga gidan suka nufi wata private hospital dinda wata yayar Sarah ke aiki.

Scanning aka fara yimata bayan sister farida Tai Mata dogon bayanin illar abinda takeson ayi din na cire Mata cikin tana sake cewa"

Ki koma gida kiyi tunani wannan abune me girma ba'ason gaggawa.

Sarah da duk hankalinta yake atashe tanajin zuciyarta na turata data Kira Marshal ko Hanifa ta sanar musu tunda takasa Hana Naj din da idanuwanta suka rufe da kunyar aji zancen cikin bayan itama din tana iya ganin hankalinta ba akwance yakeba da al'amarin.

Ahankali tace"

Naj Dan Allah mukoma gida ki sake zaunawa kiyi shawara akan hakan.

Cikowa idanuwanta sukai da hawayen dake bayyanarda tsananin damuwar da zuciyarta ke ciki ta girgiza Kai ahankali tana kallon takardar scanning din dake nuni da cikin watansa biyu da sati biyu harda kwana uku ahankali tace"

Sister nagama yanke shawaran Yi din kawai.

Da kansa yake tuqa motar zuwa asibitin Dr sa'id sbd Yana buqatan mgn dashi bazai iya jiran saiya tashi aikiba yazo gidan Dan Haka Kai tsaye can ya nufa.
Kirane yashigo wayarsa ya Dan kalli wayar Yana ganin sunan Hanifa ya share Kiran Dan baya cikin mood na magana da kowa yanzu sai zuwa anjima.

Ko daya Isa asibitin sai alokacin ya nema wayar Dr sa'id cikin sa'a Yana office zaune Dan Haka koda yashigo cikin mutuntawa Dr sa'id ya nuna Masa kujera Yana cewa"

Barka da zuwa Marshal,
Hope lafiya Naga kazo da kanka asibitin Kai tsaye?
Badai jikin Naj ko Hanifa bane ko?

Dan rufe fararen idanuwansa yayi ya bude Yana kallon Dr sa'id fuksarsa a kame kamar koyaushe Kai tsaye yace"

Dr ka duba Najma akan ciwon dake damunta inason sanin taqamaimai menene matsalar,Ina nufin akwai abin daya kamata nasani?

Kallonsa Dr sa'id yayi Yana sauke ajiyar zuciya a fili tareda gyara zama cikin nutsuwa yace"

Ciwonta ba komai bane face laulayi na ciki datake dauke dashi Wanda dama Dole zata ringa irin wainnan qananun ciwon kafin cikin yafara qwari.

Rufe idanuwa yasake Yi ya bude ahankali yanajin wani irin yanayi na shigarsa ya sake kallon Dr sa'id zaiyi mgna text din Sarah yashigo wayarsa Kamar hakan"

_please kana buqatan zuwa wannan address din Naj tanason aikata abinda yake hadari ga rayuwarta._

Sake karanta saqon yayi zuciyarsa na kasa fahimtar zancenta duka ya dago ya kalli Dr sa'id cikin yanayi na ransa dake neman baci yace"

Tasan cewa tana daukeda ciki ne?

Eh munyi mganar da ita saidai gskia zancen cikin kamar Bai kwanta Mata.

Ta maka maganar cire cikin kenan????"" Yafada Yana kafe kallonsa kan Dr sa'id din daya fara kame kamen boye zancen da yayi.
Chapter 38 · 0% Book details