← Book details Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 59

Sashe 36

Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Satar kallon hajjo dake duba sako a waya yayi Yana maida da kallonsa kanta Yana hadiye dariyarsa Dan kuwa ta shammacesa agaban hajjon yace"

Zan Rama ne kinci bashi Naj.

Murmushi tayi tana maida kallonta kan Hanifa data fito cikin Ado sai daukan ido takeyi sbd fatarta datai kyau Tasha gyaran umma dakuma cikin daya qara Mata kyau sbd ya fito sosai.

Zaunawa tayi tana Masa sannu da isowa daganan suka koma dayar palon hajjo kafin aka gama jere abinci Sukaci abincin dare kafin suka wuce Naj din ta rakasu har mota bayan Isma'eel yaje gurin Dad Alfa ya dade Kuma acan din suna mgna.

Bayan tafiyarsu a hanyarta takomawa sashensu ta hadu da mum Malika da Hannah zasu nufa part din zuwa gurin hajjo
Mum Malika na ganin Naj din ta zuba Mata ido tana Dan bude idanuwanta akanta sosai tana qare Mata kallo a sirrance,
Dan shiga tunani tayi tana sake kallon Naj har Naj din ta iso gabansu cikin nutsuwa tace"

Barka da maraice mum Malika.

Washe Baki mum din tayi tana Dan dawowa daga tunanin data shiga ta kalli Naj din suna qarasawa tace"

Naj Yaya kike?yaya jikin naki kinji sauki kuwa?
Ki daure kije asibiti,idanma bakyason zuwa akwai wani babban likita Dan uwan baban Hannah dake Nan ko Zan kirasa yazo ya dubaki harma da kayan dibar samples na awon idan ya Kama kokuma Hannah ma zata iya kaiki ki gansa.

Da Dan wani yanayi na kame fuska Naj din ta kalli mum din kadan kafin ta dauke Kai batareda ko inda Hannah take ta kallaba tace"

No thank you mum Malika ba buqatan hakan,Dr sa'id ma ya Isa.

Wucewa take kokarin Yi Hannah da tuni Naj din tagama isarta data bar gurin ta daga wayarta tana dorawa a kunne tace"

Hey sweetheart harka qara missing Dina yanzu fa muka Gama waya.

Ko dakatawa Naj bataiba ta wuce sbd Kota kanta zancen baibi ba Dan Haka ko data Isa palon Bata tsayaba ta wuce dakinta Kai tsaye Dan tasan fira suka kawowa hajjo Kamar yanda sukeyi akai akai.

Washe gari Haka ta shirya Takoma aikinta sbd rashin Hanifa ma agidan duk kadaici takeji sbd hajjo ko yaushe karatun littafantane a gabanta.

A office ko dataje kasa samun sukuni da nutsuwa tayi ta ringa zuba Amai Wanda yasa hankalin Sarah tashi Haka dai suka lallaba harta tashi Takoma gida,
Tana Isa gida abinci taci sosai tayi wanka tayi kokari ta zauna Palo sbd Kar hajjo tasan batajin Dadi.

Hakama washe gari a office Bata ganewa komaiba Haka ta jera kwanaki tana zuwa office Amma Babu wani sauki qarshe dai haka taji kamar qamshin office din ne yake sata wannan yanayin Haka tasa Sarah aka kusan sauya Mata komai na office din tasamu Dan saukin abinda take ji Amma duk da hakan gabaki daya tana cikin wani irin yanayi me wahala sbd yawan cin abinci akai akai ga yawan zazzabi da jiri dasuka sakota gaba uwa uba Amai dayafi komai wahalar da ita,
Takasa Kai kanta asibiti sbd tsoro da shakkar Jin wani ciwone ke damunta zuciyarta na cika da wani irin mummunan yanayi idanma tunanin hakan ya shigeta wato na zuwa asibitin.

Sarah duk tabi ta damu akan rashin lafiyan Naj din gashi tana boyewa hajjo sbd Karta damu Dan Haka ta takurata akan Dole suje asibiti kokuma ta sanarda hajjo rashin lafiyan.

Itama al'amarin ya isheta tana buqatan ganin Dr Dan Haka ta yanke shawaran zuwa asibitin,
Daga office batareda sanin kowaba suka nufa asibitin itada Sarah wadda itama tata zuciyar ke harbawa da abinda zasu jiyo sbd zuwa yanzun tagama tabbatarwa kanta cikine da Naj din Wanda tasan akwai tashin hankali idan har hakan ta tabbata agurin Naj,qarin mamakinta Kuma yaushe har hakan yafaru duk da dai ba abin mamaki bane tunda tanada aure Amma auren da mijin Kuma.....

Isowarsu asibitin yasa ta dakatarda tunaninta suka fito Kai tsaye office din Dr sa'id Wanda takira a waya suka nufa.

Tana buga kofar yasan itace Dan Haka ya taso ya bude Yana kallonta yace"

Kafin mu zauna muje a dauka sample dinki ko?

Gyada Masa Kai kawai tayi ahankali suna juyawa zuwa Lab yana sake Mata tambayoyi akan yanayin datakeji tana basa amsa ahankali sbd jikinta dake amace.

Bayan an dibi jininta a lab din suna fitowa daqyar suka Isa office dinsa ta ringa Amai a toilet dinsa daqyar ya tsaya Mata ta dawo ta zauna Sarah na shafa bayanta tana Mata sannu cikin kulawa da tausayawa.

Ruwan roba Dr Sa'id ya dauko daga fridge ya kawo ya miqa Mata Yana Mata sannu cikin kulawa saiga result din ankawo.

Karba yayi Yana budewa ya nufi kujerarsa ya zauna Yana fara karantawa.

Ajiyar zuciya ya sauke ahankali bayan yagama dubawa ya dauki biro yayi signing ahankali ya miqa Mata Yana cewa"

Well kamar dai yanda nayi tunanin ciwon shine kina daukeda juna, You're pregnant Naj.
Yanxu zanmiki scanning sai muga ko wata nawa ne.

Daukewa numfashinta yayi cak sbd wutar jikinta tako Ina data dauke ta zubawa bakinsa dake bayanin ido tana daina fahimtar abinda yake fada.

Da sauri Sarah ta dafata tana shafa bayanta tareda bude Mata ruwan tana kaiwa bakinta cikin kulawa da tsoron yanayinda Naj din tashiga tafara Kiran sunanta tana cewa"

Naj, Naj, Naj are you okay?
Please ki saki numfashinki Mana,
Say something Naj.

Buga bayanta tayi da Dan qarfi sai alokacin numfashinta yadawo da qarfi ta dago ta kalli fuskar Dr sa'id din da idanuwanta dasukai jajir Nan take sbd firgici da tashin hankali Babu tunanin komai sbd kanta da tunaninta dasuka cushe Kai tsaye tace"

Banason sanin ko wata nawa ne ka ciremun cikin.

Wani kallon tsananin mamaki da Dan qaramin firgici Dr sa'id dama Sarah sukai Mata atare yasake kallonta Yana cewa"

Ciki fa nace Miki kinadashi Naj.

Rintse ido tayi wasu irin hawaye na balle Mata tace"

Ka ciremun kawai Dan Allah bana buqatan kowama yasan da cikin Nan.

Ajiyar zuciya ya sauke sbd abinda yakeson fada Mata ba lallai ta fahimtaba ya kalli Sarah da itama shi take kallo tana fatar karya amince din ya maida kallonsa kan Naj din cikin nutsuwa yace"

Kije gida yanzu kina buqatan hutawa tukuna zuwa gobe ko jibi zamu sake mgna sbd Dole saina Miki scanning dinnan kafin wani maganar Amma dai cire cikin shine abinda bazai faruba.

Miqewa tayi Sarah na riqeta ta zame ta fice ahankali result din awon na hannunta ta share hawayenta ta Isa mota ta bude ta shige sai alokacin tasaki wani irin kukan daya daga hankalin Sarah takasa tada motar Kuma batace kalaba sbd karata damu Naj din Dan kuwa ko ita Jin wannan Batu yasa taji hankalinta ya tashi da yanda cikin zai bayyana ga maganar cirewa da Naj din keyi Wanda bazata bartaba gskia saidai suyi fada kowama yaji abinda yake faruwa.

Tada motar tayi suka nufi hanyar gida Naj din ta dauka tissue ta goge fuskarta datai ja sbd kukan datai din
Saikuma zuciyarta dake doka wani irin tsalle.
Suna shigowa layin gida Sarah ta hango sojojin dasuka saka gabanta faduwa itama Dan kuwa da yiyuwar Marshal ne yadawo.

Naj Bata lura dasuba Saida suka Shiga harabar gidan taga motarsa dake quryar rumfar motoci a fili sai sheqi takeyi ta dauke ido sbd gabaki halinda take ciki baya barinta bi takan tunanin komai ta fito ta nufi ciki bayan Sarah ta wuce batareda ta Shiga cikiba itama.

Kai tsaye ta shigo palon ahankali cikin yanayi na son boye halinda take ciki ta qaraso cikin palon ba kowa sai hajjo dake waya hankalinta Kuma duka Yana Kan wayat ta nufi hanyar dakinta takai hannu zata bude taji an rungumota ta bayanta ahankali hannuwansa na sauka Kan takardar dake hannunta har lokacin
Ya sako fuskarsa wuyanta ahankali tareda sakar Mata wani irin numfashin daya sakata juyowa da sauri bugun zuciyarta na tsananta
Idanuwanta suka sauka cikin nasa Ya qaro wani irin haske da fresh na hutun gske da rayuwarsa take ciki ahankali yakai bakinsa kunnenta ganin irin kallon datake Masa zaiyi mgn hawayen idonta suka balle tana sake damqe result din a hannunta.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

*_DM 38_*
Dagowa yayi ahankali daga jikinta Yana kallonta a natse ganin hawayen dake gangarowa daga idonta fuskarta na sakewa kamar wadda dama take nemansa ta saka Masa kukan.
Fuskarta yakai hannuwansa Yana kallonta sosai da idanuwansa dake cikeda Tsananin qaunarta data kasa boyuwa daga cikin idanuwan ya shafo hawayen ahankali Yana janyota jikinsa cikin taushin murya da girman kulawar da baya fitarwa yace"

Lafiya?
Zo Nan,inace kukan na kewata ne ba gani ba¿

Maganarsa tasa hawayenta tsananta gudu tana sake damqe result din a hannunta sbd yariga yakaita ya barota batasan ta Yaya zata iya kallon kowa na duniyarba da cikin Wanda Bata karba ba amatsayin miji Wanda Kuma ko tarewa bataiba amatsayin Matar aurensa to ta Yaya kowa zaiyi kallon ta samu cikin¿
Bazata iya wannan kunyarba Tai Mata girma me tsananinda bazata iya daukaba Dan Haka tunda Babu Wanda yasan da cikin zata ciresa batareda kowa yasaniba arufe zancen.

Kama hannunta yayi ya bude kofar dakinta yayi ciki da ita ya qarasa bakin gado ya Isa ya zauna tareda zaunar da ita Kan qafafunsa ahankali Yana kallonta kafin ya maida kallonsa kan takardar dake hannunta datake sake riqewa da kyau.

Cikin nutsuwa yace"

Ok ok,ok hawayen ya Isa Haka Zakiyi ciwon kai,"
Handkerchief dinsa me qamshi ya fitar daga aljihunsa ya Kai Kan fuskar tata yafara share Mata hawayen dasuka kasa tsayuwa har lokacin saima sake ballewa dasuke Mata kuka me qarfi takeson Yi ta fitarda tsananin quncin da zuciyarta ke ciki Amma takasa.
Miqewa tayi daga jikinsa tareda nufar tashige ahankali tareda rufowa.

Lumshe fararen idanuwansa yayi tareda miqewa tsaye ya fice daga dakin a palon har lokacin hajjo na zaune tana abin Dake gabanta yafito ya fice zuwa sashensa Kai tsaye.
Chapter 36 · 0% Book details