← Book details Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 59

Sashe 55

Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsaruwar palon da uban kayan kudin Dake cikinsa baya gabanta sbd yanayinda take ciki na gajiya da yunwa duk da komai na palon Dake milk da golden sun cika idonta Amma ba wannan time din yanzu
Kai tsaye hanyar dining room dinsa ya nufa da ita Yana Brian yakawo ruwa da black tea me zafi yanzu.

Zaunar da ita yafara Yi kafin yaja kujera shima ya zauna kusada ita Yana fara duba abincin dake Kan table din yaga chips ne dasu pasta salad sai qaton cake Wanda akai icing kadan.

Chips din yazuba Mata kadan da sai salad din dayaji red beef sausage kafin ya saka Mata fork aciki har Brian yakawo tea din a farin cup Kan trey Yana tiriri ya dauka tareda kaiwa bakinta Yana cewa Brian yaqara qarfin Aircon kadan sbd zataji zafi.

Ahankali take karban tea din daga hannunsa tanasha tana kallonsa yanda yakasa Bata cup din sbd karta kone sbd ganin Kamar batada qarfin riqewar.
Saidata shanye cup din tas ya aje cup din Yana kallonta da ido ya tambayeta ya Isa ko akaro?

Cikin Jin Dadi da samun nutsuwar kasancewarsu atare lokacin ta bude Baki ta furta"

Thank you.

Plate din gabanta ya nuna da ido Yana kokarin Kai hannu ta riqe hannun da nata ta kallesa kafin da ido ta kamar yanda taga dabi'arsace ta nuna Masa dayan cup din tea din tana cewa zataci da kanta.

Girgiza Mata Kai yayi Yana miqewa tsaye yace"

Zanje nafara watsa ruwa nayi salloli tukuna,Ki lura gurin cin abinci ok?
Kanta yayi kissing ya juya yabar gurin yana nufar hanyar dazata kaisa bedroom dinsa bayan ya Dan take steps biyar dasuka shiga cikin wata kofar wadda Nan ne hanyar dakinsa take bayan kayi Yar tafiya.

Tube kayan jikinsa yayi Kai tsaye bayan ya shigarda kwatinansu cikin qaton closet din kayansa daya cinye fiyeda Rabin bangon gefe daya na makeken dakin daya dauka sanyin Aircon da qamshin turarukansa masu tsada da qarfi dasuka Gama Kama dakin duk kuwa beddings din daza'a sauya dakin qamshinsa yake.

Toilet ya nufa yashiga yafara yin brush kafin yasakarwa kansa ruwan dumi Yana lumshe ido suna sauka jikinsa sbd nutsuwar dasuka fara basa ta warwarewar gajiyan zama.

Ya Jima sosai kafin yafito yabaro toilet din da qamshin shower gel dinsa Wanda jikinsa ma ke fitarwa.

Kai tsaye kofa ya nufa ya fito sbd sanin zuwa yanzu ta Isa Gama cin abincin Dan Haka Koda ya Isa palon a zaune yaganta Kan kujera tabaro dining din ya nufota ta zuba Masa idanuwa ganin dagashi sai towel iya qugu jikinsa da sauran ruwan wankan da yayo,
Yana qarasowa hannu ya miqa Mata Yana cewa"

Shall we¿

Cira hannunta tayi ta Kama nasa din ya miqar da ita Bai tsaya komaiba ya dauketa gaba daya suka nufa dakinsa.
Bai direta koinaba sai tsakiyar dakin Yana zare Mata Kaya ya dauko towel ya miqa Mata ta daura tana qarasa cire sauran kayanta ta nufa toilet dinda ya nuna Mata da ido tashige tareda rufowa.
Sabon brush tafasa cikin sabbin tarin brushes dasu shampoos masu tsada,dasu shaving cream da stick damasu kayan wanka dai duk masu kyau da tsada gasunan jere a makeken toilet din, tayi brush ta tattara gashinta ta daure tareda zaro wular wanka ta Leda ta Sanya tasakarwa kanta ruwan zafi itama tana lumshe ido nutsuwarta na qarasa dawowa taci abinci tayi wanka sallah kawai zata rage Mata.

Ko data fito yagama sallolinsa baya dakin ya fice zuwa dining inda yashawo tea me zafi da abinci yadawo dakin daidai Gama sallolinta da addua ta miqe tsaye ya qaraso Yana kallon yanda cikinta ya Dan taso kadan cikin doguwar rigar robar dake jikinta Mara nauyi ko kadan ya janyota jikinsa Yana tayata qarasa zare hijab dinda Tai sallah Yana miqa Mata cup din ruwan daya shigo Mata dasu ta karba Tasha kadan ta miqa Masa ya aje Kan table din Dake tareda kujeran dakin Yajata suka qarasa bakin gado ya yaye Mata tattausan duvet din dake Kan gadon Yana cewa ta kwanta da ido.

Hayewa tsakiyar gadon tayi kafin shima ya hawo Yana rufe musu Rabin jikinsu tareda Kai hannu gefen gadon ya kashe musu hasken dakin bai jimaba Yana shafa cikinta bacci yayi awon gaba da ita kafin shima yadaukesa.

Bacci me nauyi sukai sai yamma suka farka lokacin har qarfe biyar din yamman can ta Dan gota shine yafara tashi ya nufi toilet yasakeyin wanka jikinsa yasake sakewa dakyau kafin yafito ya shirya cikin riga da wando three quarter na _Catier_ farare tas dasuka matuqar qarawa farar fatarsa kyau da fitarta hutunta.

Wayarsa ya dauko ya maida layukansa na qasar tareda kunnawa lokacin ta tashi harta Shiga toilet wanka itama.
Bayan fitowarta daga bayin kallonta yayi daga qasanta zuwa sama fararen cinyoyinta Dake bayyane sbd qarancin towel din dake jikinta yaji tana neman kunce Masa notikan saiti ya kirata da hannunsa daya Yana sake kallon cinyoyin nata da tana tahowa,
Ko data iso gurinsa janyota yayi Kan cinyarsa cikin kunnenta ya rada mata"

Ki saka kayanda zaki barmun wainnan a bude"" yaqarasa fada Yana shafa cinyiyin.

Kallonsa tayi ya kashe Mata ido daya Yana cewa" yes" da ido.

Miqewa tayi fuskarta na bayyanarda murmushin data kasa riqewa ta nufi gaban mirror ta shafa Neutrogena oil cikin oils din data gani a gaban mirror din ta fitarda turaren khumrah me sanyi da tsananin qamshi ta shafa tareda tsayawa gaban closet din tana tunanin maganarsa akan abinda zata saka Masa din.

Duba kayanta tayi kaf taga babu ma wani abun kirki da Hanifa tasaka Mata a kayan sai jallabiyas guda biyar sauran duk jeans ne da blouse sai skirts sune kawai abun arziki bayansu gabaki daya kayan baccine na rashin mutunci dasu bumshort wainda batamasan a Ina Hanifan ta siyosuba harta sako Mata batareda tasaniba.

Jin tayi Bata wani damuba ta dauki wata free silk short gown purple tasaka bayan tasaka condom bra me taushi data lafe jikinta rigar iyakacinta Rabin cinyoyinta,take taji kunyar kanta na neman kamata Amma ta daure tabar rigar ta nufi inda ya aje Mata tata wayar bayan yasaka Mata wani layin ta dauka tana sake kallon kanta a mirror tanajin shakkar fita ahakan Dan tuni ya fice daga dakin Amma yunwar datakeji Dole zata fita dakin.

Da wayarta a hannu ta fito palon qamshin khumrahnta me tsananin qamshi na _*AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902*_ Wanda ummanta ta karbo Mata sbd hadin na musamman ne umma batada kayan hadin irin humran shiyasa ta siyo Mata agurin _*Amaryar kb global enterprise*_ na tashi daga jikinta Ahankali.

Waya yakeyi da hajjo Amma fitowarta yasa yayi shiru Yana sauraron hajjo kawai sbd hankalinsa yabar gurin hajjon Kuma,
Rigar jikinta yakewa wani irin kallo yana cewa"

Qawar Hanifa zata kasheni.

Qarasowa tayi gane da hajjo yake wayar ta karba wayar cikin farin cikinta daya bayyana kan fuskarta dake sakin murmushi cikin kewan hajjon tace"

Hajjo Ina wuni¿

Lafiya kalau Najma,Yaya kike?
Ya gajiyar hanya?
Ya jikinki Kuma?

Lafiya kalau hajjo,Yayasu Dad Alfa?
Ina Hanifa?

Karban wayar Hanifa Dake kusada hajjo tayi suna breakfast ta miqe tabar gurin hajjon tana fada Mata wata maganar data sanyata satar kallonsa itama tana Dan barin inda yake din sbd Hanifa zata iya zancen dazaiji tasata Jin kunya kokuma janyo Mata aiki.

Sun Jima Suna wayar harya gaji ya matso inda take ya kwantar da kansa Kan cinyoyinta Yana shaqar qamshin humrarta data shafa koina (08067558902) me sake kashe Masa jiki.

Ko data Gama wayar sallar magriba yajasu sukai tare kafin suka fito Sukaci abincin da Brian yagama dafawa suka koma sallar ishai tukuna yasata Tai brush ta kwanta shikuma ya janyo laptop Dan akwai aikin dazai duba.

Sai dare sosai kafin yagama ya kashe komai ya nufa toilet yayi brush da alwala yazo ya saka night suit ya Haye gadon tareda shigewa bargon ya shige jikinta.

Washe gari qarfe Tara na safe yayi Shirin fita cikin uniform dinsa na aiki dasukai Masa kyau matuqa qaqqarfan jikinsa ya bayyana acikinsu Banda cika Mata ido da kwarjini babu abinda yakeyi harsaida yagane irin kallon datake Masa ya janyota jikinsa lokacinda zai fita yakama bakinta ya tsotsa da kyau kafin yasaketa ahankali ya furta"

_I love you Najma_

Dagowa tayi da sauri ta kallesa kalmar na samun tarbon farin ciki a Zuciyarta har batasan lokacinda hannunta dake cikin nasaba tasake qanqamesa.
Ya kalli hannun Yana sakar Mata murmushi yace"

Ki kula kinji¿

Kai ta gyada Masa tana zare hannunta ya nufi kofa ya fice Yana sake sako Mata kiss ta bakinsa.

Tanajin tashin lafiayyar motarsa dako kukan engine bakaji ta sauke ajiyar zuciya tareda juyawa ta koma bedroom din tafara gyarawa ta dauko sweeper taqarasa gyaran Tai mopping ta kunna Aircon dasuka kashe da safen ta sauran dakunan gidan guda biyu da Palo da sauran duk Brian tunda safe yashigo yayi aikinsu yayi musu breakfast kafin ya wuce,
Dan Haka qaramar rigar baccin Dake jikinta ta zare kafin ta shige toilet tayo wanka tana fitowa ta shafa abinda zata shafa na kayan qamshi dasu Mai ta saka jeans blue da farar _Fendi_ sleeves tayi sallah yadawo Palo ta zauna tana waya dasu anty Amina da ummanta harda Dadah Saida aka Bata Tai Mata tsiyar saidai kawai tayi murmushi sbd yanzu kewarsu take bazataji haushin maganganun na Dadah ba qarshe anty Amina aka barwa wayar ta zauna Tai Mata bayanin daketa cin zuciyarta akan zuwan Hannah Dan Haka ta dorata akan hanyoyin da dama danta hanawa Hannah da kowama dama akan mijinta tunda Babu abinda ya saura kashi ya Dame da duwawu.

Bayansu da Hanifa takuma waya sunjima sunayi kafin takira Sarah itama daga qarshe takira Dattijo da dadin duniya ya ishesa yau Naj na gidan mijinta zaune.

Har bayan magriba Bai dawoba Dan Haka duk saitaji kadaici da kewa Kuma takasa cin abincin Daren ma sbd wata vegetable rice da egg aciki brian yayi ita Kuma taji batasonta Dan Haka cake da milk kawai Tasha tayi wanka tasaka rigar baccinta qarama tana idar da sallar ishai Yana dawowa dayake tayi locking kofar daga ciki bayan tafiyan Brian Yana Danna doorbell ta taso tafito bayan ta aje hijab dinta.
Tana budewa ya kalleta Yana yaba kayan jikinta yashigo ta tura kofar ta rufe Yana rungumota ta baya kafin yayi magana ahankali ta furta"
Chapter 55 · 0% Book details