← Book details Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 59

Sashe 14

Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna isowa bakin gate da wani irin sauri sojojin Marshal suka taso suka bude Mata kofa suna Mata gaisuwa cikin tsananin girmamawa dayasa Dadah sakin wata sabuwar hamdala cikin ranta abun na Mata Dadi sabanin Naj da "thank you" kawai ta iya bude Baki ahankali tace tana wucewarta kamar ba Amarya ba Kai tsaye gurin sashen hajjo suka nufa gidan tsit Suma duk baqi sun tafiyarsu.

Itace a gaba Dadah na bayanta da kallon ikon Allah da wannan Alamari saidai dayake lallabata sukeson Yi sai batace komaiba suka Isa babban palon gidan dazai isar da ita bangaren hajjo.

Kai tsaye ta shigo palon hajjo idonta dasuka kumbura suna kan kofar dakinta datakeda niyar shigewa ta rufe ta kwanta data shigo Dan Haka Bata lura da mutum dake zaune a palonba Yana cin abinci kan dining ta shige tabar Dadah dake shigowa da zama tana washe Baki ganin Jalal din zaune yanacin abinci tareda hajjo.

Cikin sakewa da farin cikin ganin Naj hajjo ta taso tana yiwa Dadahn barka da zuwa suka zauna suna sake gaisawa.
A 'dan taqaice ya taso yaxo suka gaisa da dadah yakoma dining din Dan baima faraba yanzune zai fara cin.

Hajjo na kallon kofar dakin da Naj tashige tasaki murmushi tana cewa"

Inshallah ahankali zata sake ai tamayi kokari da biyayya ko ahakan Dan Haka baza'a takirata ba zatai zamanta taredani har su daidaita da mijin.

Zare jallabiyar jikinta tayi tabar kayan baccinta har zata kwanta ta fasa ta fito Dan zuwa gurin hajjo Dan Bata Saba fushi da hajjon ba duk kuwa yanzu tanajin kaman antaru an Mata rashin kyautawa da adalci.

Tana fitowa dukkaninsu suka kalleta hajjo na murmushi tace"

Zo ki zauna Nan Najma Babu Mai takuraki akan auren Nan Inshallah,
Zaki zauna Dani har sai lokacinda kikaji da kanki kinason komawa gurin mijinki.... Da sauri Dadah tace"

Ba maganar saita buqata da kanta tunda ba itace me ikon kanta da yanda takeso ba,
Idan Kika biyeta tunda ba tunani cikakke akantaba da Haka zata qare rayuwar auren bare tana ganin cewan ta girmesa Wanda girmewar ta zama ta banza da wofi dankuwa yanzu a qasanshi kike.

Murmushi manya hajjo tayi tana kallon Najman dake gefenta zuru tace"

Bazata tareba saita buqata hakan da kanta inshallah,
Ina Kuma da tabbacin zata buqaci hakan Inshallah.

Kasa wata magana Dadah tayi sbd takaicin Najman datai shiru alamar hakan shine yayi Mata daidai ta miqe tana cewa"

To na tafi Ni Saida safenku Allah ya bamu alheri Dan dai Naga alamar a sashenki kila za'a haif....katseta hajjo tayi da cewa"

Amin ya Allah Dadah Saida safe" saboda sanin Dadah zata iya yanko zancenta tsakani da Allah.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

*_DM 14_*
Bayan tafiyar dadah hajjo ta kalli Najma da kallo daya zakai Mata kasan Kuka ta kwana ta yini tanayi duk da hakan fuskarta is so fresh sbd wankan da Bata Jima dayiba ga qamshinta tunda tafito ta zauna yake gauraye palon maida kallonta kan hanyar dining da jalal ke gurin har lokacin yanacin abinci Kamar wani sarki Wanda har lokacin Naj batasan da Yana palon ba ta miqe tana nufar hanyar dakinta tace"

Jeki ki kawomin ruwan dumi daki da Zuma zansha na kwanta 'yar gajiya nakeji.
Shigewa dakinta tayi tabar Naj na lumshe ido ahankali cikin sanyin jiki ta miqe ta nufi dining hanyar dining Dan dauko zuman tana tafiya a natse har saidata shiga dining area din da kyau taga Wanda ke tsaye agurin hannuwansa sanye cikin aljihun guntayen qananun kayan dake jikinsa zai bar gurin tana isowa.

Mayun fararen idanuwansa ya 'dan zuba Mata sbd yaji maganar Dadah ta banbancin shekarunsu data kawo Wanda yasashima 'dan kallon nata Dan ganin abinda ake ikirarin ya girmesa a jikin nata Wanda a iya ganinsa baiga komaiba sai kayan baccin dake jikinta riga da wando ba bra ajikinta sai idanuwanta dasukai nuni da kukan datai ya kalli iya tsayinta da shafaffen cikinta ya dauke Kai ahankali Yana barin gurin yabarta tsaye tanajin wani irin damuwa da 'dacin zuciya me qarfi duba da kallon tsaf sama sama da yayi Mata ya dauke Kai ya wuce yabar gurin da qamshinsa na _Tom Ford, Tobacco vanille_ daya zama Kamar maita tasan qamshim kamar me sbd shikadai tasani me amfani da turaren Dan tsadarsa.

Numfashi me zafi ta sauke tareda shaqaqqen tsokin dabai fitoba taji duk komai ya fice Mata a sukwane ta hadowa hajjo ruwan takai Mata ta fito ta wuce daki ta kwanta tanajin wani Abu toshe a maqogoranta da qyar tasamu bacci ya dauketa.

Qarfe Tara na safe ta fito Palo sanyeda doguwar straight gown ta atampar super exclusive maroon dataiwa farar fatarta kyau fuskarta fayau ko kwalli Bata sakaba saidai qamshinta daya zama na koyaushe dayake tashi jikinta idan ta kusantoka.
Da slippers a qafarta ta nufi kicin ta hado tea me zafi sosai tadawo Palo ta nufi dakin hajjo tana sha ta zauna kujerar dakin tana cewa"

Ina kwana hajjo.

Amsawa hajjon tayi tana cewa"

Kinyi waya da Hanifa kuwa?
Tun jiya Isma'eel yakira batajin Dadi Wai hannunta na dama ya riqe Yana ciwo kamarma yakira wayarki a kashe yace.

Miqewa tayi tana cewa"

Bari na dauko wayar tun jiya na kunna inaga Banda caji ne Bari nasaka nasamu ko kadan ne saina kirasu kafin na Isa.

Kallonta hajjo tayi tana cewa"

Ki Isa Ina da sabon aurenki akai Najma¿
Kinga hakuri Zakiyi tunda Isma'eel din na Nan Kuma Dr sa'id ma yaje tun jiyan Dan Haka basai kinjeba yanxu Bari a kwana biyu tukuna.

Shiru tayi yanayinta ba Dadi idanuwanta na sauyawa da ciko hawaye kafin Tai magana Hannah tashigo dakin da sallama muryarta a shaqe,hajjo na ganin fuskarta tasan itama kwana tayi kukan Dan kuwa a kumbure idanuwanta suke jajir.

Naj ta qurawa ido zuciyarta na wani irin harbawa da zafin radadin kishinta me qarfi saidai kamar yanda mum Malika ta hudubar da ita akan danne fushi da boye bacin Rai shine matakin nasarar komai tunda dai kowa yasan daga Naj din har marshal ba son juna sukeba aurene kawai na Hadi na huce takaici da fita kunya Dan Haka fushi da qunci ba nasu bane samun zama Matar JALAL da rabuwarsa da Naj ba wani Abune dazai Basu wuyaba ko daga musu hankali Dan Haka dole zasu danne 'dacin zuciyarsu.

Dan yaqen dole tayi tana qarasowa ciki ta zauna kusada Naj tana cewa"

Hajjo Ina kwana?
Ya gajiyan taro?
Allah yasanya alkhairi.

Hawayen datake dannewa suka gangaro ta qarasa gaban hajjo ta durqusa tana sake siririn kuka ahankali tace"

Dan Allah karkiga laifin kukana hajjo zuciyatace ke zafi bansan yazanyiba naji sauki bayan kukan sbd abin yazomin a bazatane.

'dan tausayinta hajjo taji Kuma tasan Kam Dole hannah zataji damuwar abin musamman datasan ayanzu Kam babu ranar auren Hannah din da jalal sai taga Najmanta tasamu zama dakyau tukuna Dan Hakan takejin tausayin Hannah ta dafa kanta tana cewa"

Kiyi hkr shi aure muqaddarine Kuma Allah yayi itace zata zama Matar ayanzu Amma kadaki daga hankalinki Matar mutum kabarinsace kema lokacin ne baiyiba ki kwantar da hankalinki kinji.

Shiru tayi tanajin wani qaton takaicin tsohuwar Yana tsaya Mata a maqoshi datake Mata zancen wani lokaci bayan ba Haka takeson ji ba.

Share hawayenta tayi tana miqewa a sanyaye ta juyo gurin Naj datake Shan tea dinta batareda ta maida hankalinta kan zancensuba ta Dan saki yaqen murmushi tace"

Naj Allah ya Sanya alkhairi da fatan bazaki ringa Jin damuwar alaqata da Marshal ba.

'dan kallonta Naj tayi kafin Kai tsaye tace"

Thank you" kawai taci gaba da Shan tea dinta Dan ita abundama zai ringa alaqantata da Marshal din Bata buqata Dan Haka Hannah ma na cikin abinda zata nesa kanta dasu.

Kallon tsaf Hannah taqare Mata tana ayyana wannan shariyar ta Naj datake Kamar wulaqantawa gareta kafin ta juya ta fice idanuwanta na sake kadawa da Jan baqin ciki da takaicin hajjo da Naj din.

Cajin wayarta Takoma daki tayi takira Hanifa sukahau wayarsu duk da taqi Bari Hanifan tayi Mata maganar auren itama Hanifan data fahimci Haka saita bar yimata maganar suka hau zantukansu.

Saida tayi sallar azahar ta 'dan ci abinci kafin taje gurin gaida Dad Alfa datun jiya Basu haduba tafara zuwa gurin mum Malika ta gaidata Kamar yanda suka Saba Babu komai a fuska mum din ta tarbeta suka gaisa Tai Mata addua da fatan alkhairi Hannah na daki tanajinsu taqi fitowa sbd ayanzu kyakkyawan fuskar Naj tafasa zuciyarta yake itakuwa Naj Kai tsaye palon Dad din ta nufa tana duba wayarta ahankali tashiga da sallama ta tura kofar palon tana kashe wayarta Yana zaune kuwa a palon suna magana da jalal dake gefensa sanye cikin farar jallabiyar datasa takasa ganesa sosai Dan kuwa hardasu qaramar farar hular tabani kaji hadisi datai Masa wani irin kyau sbd kayane dabai cika sawaba sai yazo Nan Dan acan kayansa idan ba suit ba sai uniform din aikinsa sai kuwa qananun kayan Shan iska dayafi sakawa idan baya aiki komai Wanda suna cikin kayan dasuke Masa kyau sbd kyan fatar jikinsa.

Dauke Kai tayi daga gefensa tanajin idanuwansa na yawo a jikinta ta qaraso ta zauna a qasa tana gaida Dad din cikin nutsuwa.

Amsawa yayi Yana Mata barka da gajiyar biki cikin farin ciki kafin ya Dora da yimusu nasiha musamman ita akan dole tabi umarni da hukunci JALAL kowane irine cikin biyayya.

Shiru kawai tayi batareda ta dagoba har yagama ta Dan dago tace"

Nagode Dad" ta miqe ta fice batareda Tama nuna tasan da akwai wanzuwar wani a palonba bayan su.

Bayan fitarta waiwayowa dad yayi ya kallesa batareda yace komaiba ya Dan saki gajeran murmushi Yana mamakin qarfin girman Kai irin nasu su duka biyun Wanda bazai taimakesuba.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
Chapter 14 · 0% Book details