← Book details Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 59

Sashe 31

Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin wani irin dogon surutu da Hannah ke janyowa Wanda duk rabi na firar Marshal ce Dan nuna irin kusanci da soyayyar datake tsakaninta dashi,
Hanifa sai basar da zancen take sbd Hannah ta barshi Dan Naj dake zaune Amma sai sake jansa takeyi cikin salo da nuna isar matsayinta agurinsa.

Miqewa Naj tayi tabar gurin sbd surutun ya isheta musamman indai akansa ne Bata buqatan ji ta nufi hanyar dakinta tana musu Saida safe tashige.

Tana shigewa Hannah ta saki murmushi tana sauya zancen da cewa"

My in-law kinyi waya da Marshal ya Isa lafiya ko?sbd nakasa samunsa tun dazu,bazan iya kwanciyar hankali ba sainajisa,
Please idan kunyi waya ki sanar dashi inata neman wayarsa, please.

Ya Isa lafiya inshallah saidai Bai Isa qarasawa gidaba bare ya huta harya kunna wayar sai zuwa gobe Inshallah,idan ya Kira Zan sanar Masa Inshallah..Zanje na kwanta ko,Saida safe.
Miqewa tayi ta bar Hannah din a zaune ta nufi dakinta sbd tasan idan ba tashi tayiba Hannah Bata gajiya da magana.
Bin bayanta Hannah tayi da kallo tana Dan yamutsa fuska itama sbd tamafita Jin gundura dasu dukan dannewa kawai takeyi.
Miqewa tayi itama ta fice daga sashen.

Washe gari ba laifi ta tashi lafiya kalau sai Dan qananun abinda baza'a tasaba Dan hakama tana tashi wanka tayi ta shirya cikin riga da skirt na lace me tsada Mara nauyi ta fito sukai breakfast daga Nan sukai Shirin zuwa asibiti scanning din Hanifa da akeyi akai akai.
Koda suka Isa asibiti Dr sa'id na jiransu Dan Haka Basu wani Bata lokaci ba suka baro.
Driver ne yakaisu sbd Hanifa Isma'eel da Marshal sun hanata tuqi itama Naj din sbd Bata Gama warwarewaba hajjo tace itama Kar tayi tuqin.
Driver daga waje yayi parking daidai kofar shiga gidansu Naj din suka fito Kai tsaye suka shige gidansu Naj din kafin driver ya shige da motar can gida.

Tun a hanyar qarasawa cikin gidan suka hadu da Asmau zata fita ta qaraso tana cewa"

Anty Naj Ina wuni?gurinki fa zani yanzu,
Ta kalli Hanifa tana cewa"
Anty Hanifa Ina wuni?
Ya hajjo?

Lafiya kalau Asmau,ya karatu?Ina Umma habiba tana ciki?

Eh.

Wucewa Hanifa tayi Gama ta nufi sashen umma habiban suka gaisa kafin ta wuce sashen ummansu acan ta tadda Dadah zaune tsakar gida tana Shan radio da qatuwar sabuwar butarta a gefe sauraron Shirin hantsi.

Qarasowa tayi tana cewa"

Dadah hantsi akesha Bari nazo na tayaki Sha idan Zaki sanmun goronki.

Kallon Hanifan Dadah tayi tana washe Baki cikin farin cikin ganin cikinta daya fito tace"

Goro Kam Zan sanmiki kici Amma karki zauna Nan iska yayi yawa Zaki kwasa sanyi tafi gurin ummanku nasan dama can kikai gulmar na sanmiki goron ne yasa za'ai zaman Shan hantsi Dani.

Miqa Mata qaramin farin goro tayi tana cewa"

Allah ya nunamun NAJMA tazo tambayar goron Nan ranar nayi kwanan niyar azumin godiya ga Allah.

Najma dake qarasowa taji abinda Dadahn tace ta kame fuska matuqa rashin Jin dadin zancen da qyamarsa na bayyana fili a fuskarta tafasa zama gefen Dadahn ta gaidata kawai ta wuce dakin ummanta
Dadah tabita da fadin"

Duk mugun halinki sai Naga 'yayanki da yardar Allah,
Mara godiyar Allah.

Daka tawa tayi ahankali ta waiwayo zatai magana gabaki daya ranta ba Dadi Anty Amina data fito daga dakinta ta riqo hannunta tana girgiza Mata alamar kada tafada koma menene tayi niyar fada.

Juyawa sukai suka nufa dakin ummansu dake zaune dakinta tana hada khumras masu shegen qamshi da kame jiki Kamar na _*YERWA INCENSE*_ tana jinsu takuma San da Amina Bata Hana Naj din mgn ba zata iya fadar abinda Dadah yau zata Hana uban kowa bacci a gidan sbd zaunarda Dattijo zatayi ta hada masu gurminda zai fatattaki kowa da bacin Rai.
Naj tareda Aminar ne suka shigo kafin Hanifa dake bayansu suka zauna Naj na cewa"

Umma barka da aiki,
Ina wuni?ya gidan?

Amsawa umman tayi batareda ta kalletaba sbd A qule take da ita akan wannan taurin Kan da muguwar zuciyar sbd Hanifa kawai ta kyaleta Dan batason tayi Mata fadan rashin son datake nunawa auren jalal a gaban Hanifa Dan kuwa tasan ko Dadah sbd Hanifan na gidan ta taqaita tata masifar.

Kusada umman Hanifa ta zauna tana daukar kwalban khumrah daya tana shinshinawa tace"

Umma wannan khumrahn wankane ko?
Eh Hanifa,Yaya jiki jikin?
Ankai Miki wainarki Kan lokaci kuwa?

Eh umma naci kafin mufita anjima alalan manja nakeso umma ko gobe da safe ruqayyat Basu iyaba idan sunyi qarfi yake.

Anjima Inshallah Zainab zata kawo Miki yanda kikesonta.

Yawwa Ngd ummana.

Ganin yanda umman fuskarta ba asakeba da alama ranta bace yake akan Naj hakama anty Amina ma Babu wani dogon magana ita kanta Naj din duk tayi wani iri ranta ba Dadi itama kowa sai kame kamen yaqen Dole yake Kuma duk tasan sbd itane ba'ason tada maganar Dan kada asa taji ba Dadi saidai ita Bata damu sosai da duk qin auren da Naj keyina sbd tasan Dole bazata iya karban aure irin wannan lokaci daya ba tunda har bata fitina ko fada akan auren ko ahakan ai ba laifi tasan wata Rana zata Aminta da auren.
Kallon umma da anty Amina tayi cikin nutsuwa da sanyin murya tace"

Umma kuyi hakuri ku sake bawa Naj lokaci Inshallah komai zai daidaita tunda na tabbatarda itama kasa amsar abin ne Kai tsaye yasa takejin bazata iyaba Amma ai komai lokaci yakeso.

Da kallon takaici umma tabi Naj din hakurinta na qarewa tace"

Kinji abin datake fada ko?
Fahimtarki takeso ayi abaki lokaci akan abinda kece aka rufawa asiri da kuwa da Bai aurekinba da yanzu kinanan kina zaman wulaqanci da matsuwa agidan wani,
Shine namiji shine yakeda damar cewa bayaso sbd shine me riqe auren Amma kece kike rainin wayon da kikaga dama sbd sun nuna suna sonki.

Dagowa Naj tayi da idanuwanta dasukai jajir suna neman cikowa da hawaye tace"

Umma.....

Katseta anty Amina tayi da cewa"

Naj bakida gskia ko kadan
Kuma wallahi kunya kike bani da wannan dabi'ar Taki sbd banyi tunanin ko Dan su hajjo ba ki nunawa wannan auren tsana haka,
Menene matsalarki?

Kukan baqin cikin datake dannewane tsawon lokaci ya kufce Mata tana cewa"

Wallahi bazan iyaba,
Nakasa,
Shin meyasa da aka tashi taimakon nawaba Amin taimakon da akasan Zan iya dauka,
Zuciyata zafi take,
Ciwo take,radadin hakan nakeji Dan Allah Araba wannan auren koba komai Ni bazan iya da Wanda yakeda wadda yakeso ba.....

Au bayan girman da kike ganin kinmasa yanzu Kuma hadda wadda yakeso tazama dalili kenan?

Sake fashewa tayi da wani kukan tana cewa"

Ni koma menene Dan Allah Araba auren Nan.....

Wani irin salatin Dadah sukaji data shigo tana kallon Najman bakinta na rawa gurin magana saikuma kawai ta fashe da kuka tana cewa"

Innalillahi-wainna ilaihirrajiun
Wace masifar ce zata kunno Kai rayuwarki Najma,
Wace tsanace kikewa wannan auren dako shekara daya baiyiba za'a kidawo zawarci,
Najma Dan Allah ki duba tsufana da mutuncin Dattijo ki hakura ki cirewa ranki masifa ki runguma aurenki....

Irin kukan da Najma da Dadah keyi yasa umman sake Shiga wata mummunar damuwa da baqin ciki ta tashi cikin tsananin fushi tayi Kan Naj din Hanifa da duk hankalinta itama ya tashi ta tashi da sauri ta janye Naj din tana kasa mgna sbd ganin cikin qanqanin lokaci Abu yazama tashin hankali.

Ba shiri Dadah tasa aka Kira Mata Dattijo tun kafin ya qaraso sashen yake jiyo fadan umma da ranta yayi mummunan baci qololuwa dakuma kukan dadah daya Gama daga hankalin kowa.

Anty Amina ce tayi Masa bayanin abin Dake faruwa tana dasa Aya ya kalli Naj cikin tsananin bacin Rai da baqin cikin daya rasa abin dazai Mata
Tana durqushe gefe har lokacin kuka takeyi me qarfi na rashin sanin mafitar abindayake cin ranta.

Kallon umma yayi cikin fushi da bacin Rai me tsanani yace"

Najma dai takai matakinda tafi qarfin umarnina Dan Haka ke dakika haifeta bakifi qarfin umarnin nawaba saiki shirya kayanki dan wallahi tallahi tana dawowa gidan Nan da sunan aurenta ya mutu bazata zaunaba tare zaku bar gidan nan.

Kallonsa umman tayi cikin baqin cikin koyaushe yayanta sukai laifi aurentane yake barazanar rawa,
Ta maida kallonta kan Najma tace"

Kinji ai saikije ki hado kayan naki mubi duniya tunda shine sakamakon dazaki bani.

Dadah cikin kula tace"

Najma Dan Allah ki dubi girman Allah kiyi hkr ki dangana wlh na zubarda makaman yaqina na yarda anmiki ba daidaiba ki dangana ki runguma aurenki wlh gaba Zakiyi farin ciki da yardar Allah.

Cikin fushi Dattijo yace"
Ki daina rarrashinta Dadah wlh ko ta tashi ta fice Kona nema mugun ice nai Mata dukan da bazata iya komawa da qafafuwantaba.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

*_DM 33_*
Janyeta anty Amina da Hanifa sukayi ta suna sake bawa su dattijon da Umma hakuri Dadah kuwa kamata tayi tayi dakinta da ita ta zaunar tana kallonta tace"

Ki dauka dangana 'yar Nan kibi umarnin mahaifinki da mahaifiyarki tunda dai kinsan bazamu zabar Miki mugun abu ba,
Banda abinki Najma kinyi aurenki kina cikin kwanciyar hankali da nutsuwa meyafi hakan,
Dan shekarun da Kika basa waye yasani tunda idan aka kalleku ma sai adauka sa'an babban yayanki ne,
Shin menene illar auren qaninka tunda?
Shin kin manta Nana Khadija ko data aura Manzon Allah ya girmesa da shekarun dasukafi Wanda kikaiwa naki mijin ita datafi daraja ma ko farin ciki da wannan koyin bazakiyiba ki faranta Mana?
Mu idan bakya Yi danmu munada fada da takura to kiyi Dan hajjo da Alfa Mana,ga Hanifa Nan haryanxu Bata ganin laifinki tana bayanki sbd irin qaunar datake miki
Dan Allah kiyi hkr kiyi zamanki gidan aurenki tunda har daga mijin harsu hajjon sun amincew zamanki ba takura sai kinji kin samu nutsuwa da auren.
Chapter 31 · 0% Book details