← Book details Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 59

Sashe 11

Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zo ki zauna kusa Dani mu Taya juna murna da Allah ya Sanya alkhairi sbd kema Zakiyi sirika a goben amatsayinki na yayar ango.

Hanifa Bata gane me hajjon ke nufiba ta qaraso ta aje kayan hannunta tana zama gefenta tace"

Naji dadin da auren Abbas da Naj Bai yiyuba Amma hajjo ai bazamuyi murna ba Kuma tunda Naj din na cikin damuwa duk da itama nasan Bata fasa auren bace ta abin daya faru ne.

Tunda safiyar ranar ta waye sai alokacin hajjo ta Dan saki guntun murmushi tana miqar da qafafunta kan qaramin sofa table dake gabanta tana cewa"

Gasamun qafafun ko da Dan sakemin gobe nasamu damar Dan zagayawa dasu cikin gidan kodan jama'a
Gobe Allah yayi damuwarmu akan rashin zuwan Marshal ta qare Dan kuwa yanzu tunda yanada Mata anan taredamu Dole zai ringa zuwa,
Mahaifinki ya nemawa Marshal auren Naj a Daren Nan Dan Haka ankai qarshen duk wata fitina gobe da Marsha za'a daurawa Najma aure Aminyarki ta zama sirikarki yanzu ita din tamuce halak malak.

Ruwan zafin da ba'a sirkaba ta tsunduma qafar hajjon aciki sbd rudewa cikin mamaki dason tabbatarwa tace"

Hajjo Aure tsakanin Naj da marshal??

Zare qafa hajjo tayi tana cewa"

Qonani kike Shirin yine kome?
Bari Naga auren nasu harma da 'yayansu idan Allah yace kafin ki qona qafafun na rasa na zuwa.

Da dai hajjo tayiwa Hanifan bayanin komai Jin tayi wani farin ciki da Bata tabajinsaba anan kusa ya dabaibata tako Ina duk da can qasan zuciyarta tanajin akwai qalubale a tsakanin yardarsu da auren su biyun Dan kuwa Babu me sauqin saukowa wani acikinsu ga maganar aurensa da Hannah gefe daya Amma Kuma tana danne hakan da farin cikin hadin Dan kuwa wannan shine perfect match agurinta ita da Marshal dinta da Naj dinta
Miqewa tayi tana cewa"

Alhamdulillah ya Allah mungode maka da wannan zabi naka.

Ficewa tayi da sauri ta nufa dakinsu da Naj din take kwance tayi sallah ta saka kayan bacci tayi kwanciyarta da gudunta taqarasa ta fada kanta tareda rungumeta tana cewa"

I love you Naj
I love you Naj

Da idanuwanta dasukai laushi ta Dan kalli Hanifan tana maidasu ta lumshe batareda tace komaiba sbd har tafara Jin bacci sai kawai ta maida idanuwan ta rufe da muryarta me taushi tace"

I love you too Amma bacci nakeji barni Dan Allah.

Dariya Hanifan ta Dan sake cikin tsananin farin ciki tace"

Yi baccinki Lafiya MRS DEEN MARSHAL ALFA.

Bataji abinda Hanifan taceba sbd baccin daya fizgeta.
Daganan Hanifa fita tayi dakin Takoma palo ta miqe a kujera ta Danna Kiran mijinta tafada Masa Nan take cikin Daren tafara Dora sabbin shirye shiryen komai danma kamar yanda hajjo tafada Mata a yanke auren kawai za'a daura baza'a daga maganar takurasu tarewaba yanzu sai kowannensu ya Dan nutsu Dan wannan alamari na gaggawar daya riskesu musamman sbd yanayi na yanda suke kallon junansu na tazarar shekarun.

Ta bangaren ummanta da anty Amina kuwa a Daren Basu rintsa ba sbd tsananin damuwa da rashin sanin mezai faru mezai biyo baya ga Dattijo har lokacin umman Bata sake sakashi a ido ba bare tasan da maganar auren a gobe ko babu ga anty Amina zuwanta biyu yinin tana dubo Naj Wanda tunda abun yafaru take daki kwance Bata buqatan ko tada maganar ayi.

Koda akai sallar asuba kusan daga Dadah har Dattijo da Hanifa Basu rintsaba sbd zumudin safiya tayi ta waye a daura auren Nan kada wani abun ya gitta afasa Dan Haka daqyar kowannensu yaga anyi sallar asuba gari ya waye aka hau sabuwar hidima gadan gadan.

***********
Tsaye yake daga bakin qatoton window na cikin geam room dinsa dake cikin flat dinsa Wanda Babu kalar tsadadden lafiyayyan geaming machine dinda Babu aciki Wanda duk inda yake yasaba amfani dasu shiyasa jikinsa kallo daya macen datasan asalin jikin namiji me kyau qaqqarfa bazataji ta mutu a sonsaba take musamman idan tsautsayi yasa kasamu ganinsa ba riga.

Tsaye yake Yana amsa waya sanyeda black three quarter da black armless riga Wanda suka fidda hasken fatarsa sosai dama Kuma black shine kalar kayan dayafi so kila Kiran kalar tana Masa tsananin kyau ne.

Gama wayar yayi daidai knocking kofarsa da akai Wanda hanifa ce kawai yasan tana zuwa ta buga kofarsa Kai tsaye saidai akirasa a waya sbd sanin shi ba mutum bane Mai son hayaniya.

Kashe wayar yayi ya fito daga geam room din ya nufi Palo ya ajiye wayarsa akan kujera ya nufi kofar cikin nutsuwa ya saka hannu ya bude tareda juyawa Yana cewa"

Menene Kuma tunda safe Nan?kinsan bana ganin kowa fa tunda safe is too early now Hanifa.

Muryar Dad Alfa yaji yace"

Munsani Marshal Deen Dan hakan before anything ma we are really sorry to disturb.

Waiwayowa yayi tareda kallon Hanifa dake gefen dad din kafin ya maida kallonsa kan dad din ya na Nuna Masa kujera Yana cewa"

Sorry Dad banyi tunanin ganinkaba Ina tunanin haniface sbd itace tafi iya damuwa musamman da safe.

Zama yayi bayan dad din ya zauna Yana cewa"

Good morning Dad antashi lfy?

Lfy Alhmdlh.

Hanifa ya kalla ahankali yace mata"
Gud morning madam.

Murmushi tayi tana ajiye kayan data riqowa dad tana miqewa tsaye da farin ciki shimfide kan fuskarta ta kalli qafafunsa dake sanye da slippers na Gucci farare tas kaman baya tafiya dasu sai qafafun Naj dake tsaf fes fes Kamar hakan suka fado mata tace"

Inada aikin Yi Zan tafi Anjima dai nasan zamuyi magana idan kayi lokacina." Ta juya ta fice.

Baibita da kalloba sbd yawan kallo ba dabi'arsa bace ya Dan kalli dad da fararen idanuwansa shima dad din shi ya kalla kafin ya nuna Masa kayan dake ajen da hannu Yana cewa"

As you know yau akwai taron daurin aure So ansamu matsala anfasa daurawa da wancan din saidai za'a daura da Wanda na Isa dashi ga Kaya Nan su babban rigane kayi amfani dashi anjiman sbd mutane zasu taro akwai kuma media you'll more comfortable in it tunda daurin aure ne na hausawa.

Kallon kayan yayi kafin ya kalli dad din Kai tsaye yace"

Thank you.

Gingina masa Kai Dad din yayi Yana cewa"

Ok then see you.

Tashi dad din yayi ya nufi kofa marshal din na bayansa har harabar gidan kafin ya juya zai wuce saiga Hannah Wanda ta fito daga sashensu hajjo data sakawa ranta zuwa gaishesu kowace safiya da Rana da yamma sbd sake samun damar kame zuciyar Marshal tana ganinsa ta qaraso gurinsa tana sake wani irin qayataccen murmushi jikinta sanye da wata doguwar straight English gown ta roba data Dan lafe a jikinta kyakkwan shape dinta a bayyane.

Good morning Marshal" tafada tana tsayuwa agabansa.

Dan kallonta yayi tareda dauke Kai Yana kallon hanyar sashen hajjo da Hanifa ta fito ta koma cikin sauri tana waya da alama dai gabaki daya tama manta da ita din ba wata lafiyayya bace take irin wannan kaida kawon sbd hidiman bikin Naj din.

Juyawa yayi ya wuce Yana cewa Hannah din"

I will talk to you later zankoma bacci yanzu.

Daukeda murmushi a fuskarta tace"

Ok love" tana bin bayansa da kallo Kamar zuciyarta zata narke gabaki daya akansa,
Tana yiwa marshal so me tsanani Dan ita ba Shirin aure gabanta a da Amma yanzu sbd shi aure takeso Kai tsaye ba Jan lokaci shiyasa zata dage da Binsu hajjo ko zata samu a saka ranar bikin nasu tunda ansan da maganar auren nasu.

Alhmdlh Koda Naj ta tashi safiyar lafiya kalau ta tashi kamar koyaushe data Saba tanada qarfin zuciya Kuma tasaba da hakan tunda ba yanzu ne hakan ta taba faruwa da itaba Dan Haka dataga Suma su Hanifa da hajjo dasuke damuwa koyaushe maganar aurenta ta fasu taga wannan karon Suma Basu nuna damuwaba saima farin ciki dasuke da hakan yasa ta qara cire abin a ranta tayi wankanta ta fito sanye da riga da skirt na atampa Maroon data yiwa kalar fatarta kyau tazo palo ta zauna gefen hajjo daketa faman waya tasha ruwan dumi da Zuma da Madara ta koshi ta tashi taje ta dauko qaramin gyale ta yafa kanta ta fito tareda wayarta a hannu tana kunnawa ta nufi gidansu bayan ta biya gurin mum Malika ta gaidata Dad baya Nan jama'arsa nata isowa so baya gida.

Ko data Shiga gidansu Haka ta ringa Dan gaggaisawa da mutane harta Isa dakin Dadah da yau farin cikin duniya tana cikinsa bakinta Sam baya rufuwa sbd farin ciki danma Dattijo ya kwabeta akan kada ta fadawa kowa komai sai sunsamu an daura auren lafiya sunga aure ya dauru tukuna Dan Haka Babu Wanda yasan da maganar bayan ummanta da Dattijon yafadawa yau bayan sallar asuba aikuwa gari na wayewa sadaka me yawa umman ta Tara almajirai tayi tareda duqufa da adduar auren ya dauru taga ya dauru itama Dan har lokacin daga ita har Dattijo gabansu Bai daina faduwaba sai sunga anshafa fatiha aure ya dauru.

Kodata Isa can cikin gida gurin ummanta dasu anty Amina sai hidima akeyi sai hakan yaso Bata mamakinsu saidai Tai musu uzurin basusan Babu maganar aurenba sai anjima idan lokacin daurawan yayi sunji ansanar anfasa Dan Haka batai wani yunqurin maganar da kowannensuba Dan dama ba halinta bane yawan maganganu musamman irin wannan Dan Haka dakinta ta shige tana hada sauran kayayyakin lefen Abbas dake dakin Dan tasan maida Masa za'ayi Allah yasa ko takarmi daya Bata sakaba a kayansa duk aurenta idan za'ayi hajjo ke hada Mata lefe na musamman sbd gudun irin Hakan.

Har qarfe daya da rabi tana gidan inda tana gamawa Kai tsaye ta fice Takoma bayan tabar musu kayan shirye tsaf a tsakar dakin ta fito tana waya da Sarah Dake sanar da ita gatanan a Hanya tana zuwa.
Chapter 11 · 0% Book details