← Book details Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 59

Sashe 41

Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna Isa gida Sarah na parking suka fito Naj tayi gaba tashige gidansu tanajin bazata iya Shiga gidaba ta hada ido da hajjo da maganar cikin.
Bayanta anty Amina tabi Sarah Kuma da motar ta nufi gidan Alfa tashige tayi parking tafito itama jiki duk a mace da yunwa da damuwar halinda Naj take ciki.

Sashen hajjo ta nufa Kai tsaye cikin sa'a hajjon na Palo tana jiran Alfa dazasu asibiti tare,Sarah ta qaraso tana gaidata cikin girmamawa kafin ta miqa Mata key din motar Naj din tace"

Hajjo ga key din motar Naj zantafi gida Saida safe.

A asibitin Kika barotane?bazata dawoba ta huta tun safe.?

Shiru Sarah tayi tana Dan Jin nauyin fadawa hajjon saidai gwara ta fada Mata sbd a yau idan wani baijeba Dattijo zai iya yiwa Naj dukan fulawar biredi,ta daure tace"

Aa tare muka dawo tana Nan gidansu akwai matsala ne,tun asibiti ummanta tafara....shiru tayi tana kasa fada.

Da zallar mamaki hajjo ke kallonta tana cewa"

Meya samu Najman?
Matsala Kuma wace iri?

Miqewa dai tayi ganin yanda Sarah ke qaf qaf da ido tana qin fadar abinda Najma tayi ta nufi kofa tana cewa ruqayyat tashiga gidansu Najma.
Sarah Bata bita ba ta wuce gida tana fitowa.

Koda su anty Amina suka shiga gida Naj dakin ummansu take neman shigewa anty Amina ta jawota Bata tsaya koina ba sai gaban Dattijo dake zaune tareda Dadah suna maganar auren Asmau da za'a zo tambaya.

Dattijo ya dago yana kallon Naj din dake kuka har lokacin kafin ya kalli Anty Amina yace"

Ita Kuma wannan ya akai da itane?
Tasake gudowar ne batason auren?

Numfashin takaici anty Amina tasaki kafin tace"

Cikine da ita shine taje cirewa batareda sanin mijintaba yau dai harta Kai qarshen hakurinsa sai daya bayyanar.

Wani irin kallo Dattijo yayiwa Naj din Yana Dan gyara zama ya maida hankalinsa Kan Anty Aminar Yana sake tambaya cikin rashin gane bayaninta na farko yace"

ta samu cikine kokuwa?sake mun bayanin.

Dattijo cikine ajikin zata zubar bada sanin mijinba hakama bada sanin su hajjo ba......

Wani irin salati me qarfi Dadah tasaki tana kallon Naj da idanuwanta waje cikin daga murya da mamaki yagama suqeta tace"

'yar Nan ciki gareki?
dama Ashe kingama daidaitawa da mijin kike zuwa Nan Dan kin Gama rainamu kike zuba Mana hauka kullum bakyaso bakyaso to uban waye yayi Miki cikin?
Kokuwa shima mune mukai Miki Dole?yau ga 'yar banzar yarinya.

Hajjo data iso takuma ji abinda ake fada tayi saurin janye Naj tana kallon Dattijo daya Gama siqewa da wani irin mummunan baqin ciki da takaicin Naj din ta kallesu su dukan tace"

Haba Hana Dattijo wannan ba abun daza'aita tonawa bane Dan Allah abar maganar har asamu zuciyoyi su lafa Najma muje gida.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

*_DM 42_*
Kasa motsawa Naj tayi sbd tsananin nauyin da kunyar dasuka riqe qafafun nata,ta sake soke Kai hawayenta dake tsiyaya masu yawa suna qara gudu Akan fusakarta datai jajir tarasa ta Yaya zata dago ta kalli hajjo.
Miqewa tsaye Dadah tayi tana sake kallonta har lokacin da bayyananen mamakine a cikeda da ita Bata iyayin shiru da magana ta matso gaban Naj din tana Mata kallon kinci Amanata tace"

Da tuni da kike bori da yamutse yamutsen bakyason mijin da auren,qanin qawarki dama Ashe kingama daidaicewa da abinki Kika barni inata faman lallabaki Ina ranqwafar da duk masifata sai abinda kikaso nake Miki Dan kawai musamu ki hakura Ashe duk kallon Mai saman ruwa uwa kike Mana har kinsamu Dan rakiyarki a dakin hajjo¿

Kallon hajjo Dadahn tayi tana cewa"

Kinada labarin wannan salalar da akai Miki kokuwa kema bakida labarin Raina Miki wayon take?
Dattijo maza wanke fuskar Nan tata me Kama da wankakken karas da Marikanda saita nema hanyar asibitin makafi da kanta,
Dukan Yanda taci Amanar rarrashi da kwantar da Kan danake Mata zakamin Dan kuwa ta Jima tana zambatata,
Yarinya ido a kafe amma ta....

Cikin damuwa da Dan takaicin maganganun Dadah hajjo ta kalli Dattijo da baqin cikin duniya da takaicinsa yasashi qamewa gefe Yana kallon Naj din Dan kuwa dukan wankin bargo yakeson Mata Amma hajjo ta tareta shiyasa yakejin tafarfasar zuciya da kunyar yanda zai kalla su hajjon musamman Alhaji Alfa akan wannan mugun tunanin da niyar data shiga Naj din.

Har lokacin tana rakube Kai a soke takasa dagowa ta kalla kowa sai zuciyarta dake raunana da girman kunya da kukan kunyar Dan kuwa tonon asirin da Dadah ke Mata yasa kusan duk sauran jama'ar gidan suka fito tanaji Umma habiba data iso gurin da mamakin hayaniyar fadan Dadah daya dayake tashi cikin mamaki take kallon bakin Dadah dake fadar ciki ajikin Naj,ta Dan fito da idanuwa cikin kaduwa da mamakinta itama daya kasa bayyanuwa tace"

Najman ce da ciki?
To¿Lallai aure yayi albarka tunda har ansamu rabo kafin tarewa.

Da wani sabon takaici Dadah ta kalleta tana Mata mugun kallo tace"

Bar Nan tunda daman ke bakya fadar alkhairi.

Juyawa tayi ta tana barin gurin tana cewa"

ALLAH dai yasa a sauka lafiya tunda Naga kamar cikin ya kwana biyu da Samu.

Kamo hannun Naj hajjo tayi tareda kanta Kai tsaye suka wuce tana cewa"

Sai da safenku" suka wuce.

Tunda suka fito gidan hajjo ta saketa ahankali tana gaba Naj din na bayanta qafafunta na tafiyar da kyar sbd yanda takeji a zuciya da jikinta.

Suna fitowa waje motar Marshal na tsayawa da Umma aciki tafito fuskarta a matuqar daure hajjo na ganin hakan ta waiwayo ta kalli Naj da har lokacin kanta a qasa yake takasa dagosa a natse tace"

Najma wuce gidan Ina zuwa.

Daqyar ta daga kafafu ta taka ahankali ta wuce ta nufi gate din gidan securities na wangale Mata tashige.

Sai data Shiga harabar gate na biyu na gidan tasamu ta Dan dakata tareda Dan dagowa tana share hawayenta dasuka cika Mata ido ko gani Sosai batayi.
Wucewa zatayi ta qarasa ciki hancinta ya shaqo Mata qamshin turarensa ta dakata ahankali tareda Dan juyowa gabaki daya ta zuba Masa idanuwa Yana tahowa ya fito daga motarsa fuskarsa amatuqar kame Kuma da alama Baigada tsayuwarta agurinba Dan ko kallon gurin datake baiyiba ya wuceta kadan saiga Hannah ta fito tana ganinsa ta qarasa gurinsa da sauri tana wani irin karya jikinta da shape dinta yake bayyane cikin wata straight English gown data kwana jikinta sosai sai qamshi takeyi cikin kashe murya da kulawa tace"

Kasa hankalina ya tashi tun Rana nake kiranka baka dagawa asibiti ma ko danaje duba Hanifa bakacan duk sai ahankali na yasake tashi,Yaya kake?

Wucewa yayi tana binsa a gefensa ahankali ya furta" Hannah kaina na ciwo bana buqatan abin dazai qaramin ciwon kan ok???

Ahankali Naj data dauke idanuwanta daga kansu ta daga qafafunta tafara tafiyarta ta wucesu batareda taji abinda suke fada ba Kai tsaye sashen hajjo ta nufa ta shige,

Shima hanyar nasa sashen ya nufi yabar Hannah tsaye agurin tana binsa da kallo zuciyarta fal farin ciki ahankali tace"

Koma dai menene Kai nawane tunda nasan yanzu kowa yasan da maganar cikin zanjira gobe naji sakamakon inda cikin yafito.
Juyawa Tai itama ta wucewarta.

Naj na Isa palo Bata tsayaba Kai tsaye dakinta ta wuce tareda rufowa ta qarasa Kan kujera ta zauna sai alokacin yasake sakin sabon kuka Mara sauti tana dafe zuciyarta dake tsananin zafi da bugawa.
Sai datai kukan hartaji sauran qarfinta ya qare ta share hawayenta tareda miqewa ahankali ta nufa toilet ta shige bayan ta cire kayanta.
Wanka tayo sosai tasamu jikinta ya Dan sake taji qarfi qarfi Bata shafa komaiba ta saka riga da wandon bacci masu kauri da hula tana sallame sallar ishai ruqayyat na shigowa daukeda abinci ajere harda orange juice da kwanakin akaga ta maqalewa Sha sai yanzu da zancen cikin ya fita suka fahimci dalilin Shansa kenan.
Ajiyewa ruqayyat tayi tana gaidata kafin ta juya ta fice.

Tsananin yunwar datakeji tasata cin abincin sosai bawai Dan tanada appetite na comes din ba Tasha orange juice din ta miqe ta nufi gado ta Haye ta kwanta tanason fita Amma bazata iya kallon hajjo ba ta kwanta tareda rufe idanuwanta bayan ta rufa.
Tanaji ruqayyat tayi Knocking kafin tashigo ta tattara kayan abincin ta gyare gurin ta fice bayan ta kashe Mata wuta.

Washe gari tun da wuri ta tashi tayi sallah Takoma bakin gado ta zauna tana tunanin yanda zata iya fitowa Palo ta nufa kicin neman abinda zataci sbd cikinta dake wani irin kukan yunwa,batasan da wane ido zata kalla su hajjo ba.

Daurewa tayi takoma ta kwanta bayan taci wani short bread biscuit dake cikin handbag dinta wani sabon baccin wuya yakuma dauketa.
Bata Farkaba sai qarfe Tara shima yunwarce takuma tada ita ta sauko gado nufi toilet takuma yin brush ta fito Kai tsaye ta nufi kofa ta bude ta fito palon sbd tunanin zuwa lokacin hajjo tana asibiti taje.

Dining ta nufa Kai tsaye ta zauna babu kowa a palon da dining din duk saitaji jikinta yaqarayin sanyi ta zuba abincin ahankali tafara ci wayarta na hannunta tanason Kiran Hanifa taji Yaya jikin nata Amma takasa sbd Jin nauyi da kunyar,
Ita yanzu shikenan abin daya sameta kenan na kayan kunya da to Nan asiri.

Kofar dakin hajjo aka bude gabanta ya buga da qarfi jikinta na mutuwa ta dago ahankali tareda waiwayowa idanuwanta suka sauka Kan kyakkyawar fuskarsa dakeda cika ido yafito dakin hajjon ta dauke Kai ahankali daga kansa ganin Babu alamar zai nuna yaganta kokuma yasan da ita a palon ya nufa kofa ya fice yabar palon da qamshinsa daya sanyata Dan rufe ido tanajin cikintama yacika da abincin ta miqe tabaro dining din takawo tsakiyar palon saiga hajjo ta fito fuskarta ba wani alama na bacin Rai ko fushi ta kalli Naj din cikin kulawa tace"

Najma kinci abinci kuwa?

Batareda ta dagoba ta bude Baki bayan ta sauke Yar ajiyar zuciya tace"

Eh.
Chapter 41 · 0% Book details