← Book details Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 59

Sashe 54

Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dare suka baro gidan bayan sunyi sallama da kowa umma ta hadota da tsaraba,suna dawowa gidan Kai tsaye a palon ta zauna tana fuskantar Sarah Dake jiranta ta zauna tana cewa"

Sorry Sarah nabarki jirana.

Karban files din hannunta tayi tana daukar pen tafara budewa tana kallon kayan drinks da aka kawowa Sarah da snacks tace"

Kici wani Abu Bari naduba nayi signing din sai driver ya maidaki gida tunda dare yayi.

Fira sukeyi sama sama tana duba takardun tana signing Sarah nafada Mata yanda abubuwan office din ke tafiya saita Dora da cewa"

Naj Abbas fa yanata yawon son adawo Masa da aikinsa anyi zama yafiso hudu Marshal ya tsaya akan hukuncinsa ya takura akan saina basa sabuwar number dinki Wai yanason magana dake Akan Marshal din kozaki Masa mgn dashi.

Bata dagoba abinda ke gabanta takeyi cikin rashin kulawa da zancen tace"

Duk indama zai samu Number na ki tabbatarda Baki Bari yasamuba
Maganar aikinsa Kuma bana tunanin ko hajjo zata sauya ra'ayin Wanda yake maganar akai bare Ni.

Qarasa signings din tayi tarufe file din qarshe tana hadawa ta miqawa Sarah tana cewa"

Thank you Sarah.

Naj zanyi kewarki gskia Amma Kuma hakan shine fatanmu ki kasance tareda mijinki kisamu hutawar gidan aure,Ina Miki fatan alkhairi a rayuwar aurenku.

Nagode Sarah,muje Naga Wanda zansa ya kaiki gida.

Miqewa sukai suka fara zuwa dakin hajjo sarah Tai Mata sallama suka fito suna kawowa harabar gidan Yana dawowa daga masallaci sallar ishai sanye cikin riga da wandon _Nike_ ash kala
Sarah ce ta gaidasa cikin mutuntawa da girmamawa matsayinsa name Companynsu.
Da kansa yasaka drivernsa yakai Sarah din gida da motarsa kafin suka nufo sashen hajjo tareda mutuniyar tasa tana gefensa Yana amsa wayar da aka kirasa lokacin har suka Isa ya wuce dakin hajjo Kai tsaye ita Kuma ta wuce dakinta.

Ya Jima sosai a sashen kafin ya tafi
Itama ta fito taje kicin ta dauko drink da snacks tadawo dakinta ta aje kafin ta Haye gado ta kwanta Dan tuni dama tayi Shirin bacci tana kwantawa bacci ya dauketa.

Washe gari qarfe Tara aka fito da kayanta aka Kai mota tafito sanye cikin doguwar English chiffon gown me Dan transparent sai blue skinny jeans daya lafe jikin cinyoyinta daga saman kuwa rigar ba transparent bace.
Handbag din _Calvin clein_ ce qarama a hannunta wadda wasu abubuwanta ke ciki qafarta kuwa loafers ne D&G.

Rungume hajjo tayi idanuwanta na Dan cikowa da hawaye ahankali ta furta" I will miss you hajjo.

Murmushi hajjo tayi tana shafa kanta tace"

Rayuwa mai albarka Najma,
Ki kula da kanki Kuma Kinga kinada ciki,munada buri da fata akan cikin Nan idan Allah yasa yazo lafiya yakuma Raya manashi.

Ahankali ta gyada Kai tana cewa"
Inshallah hajjo.

Fitowa sukai tareda Hanifa suka Isa sashensu Dad Alfa Wanda ke jiranta shima.
Yan bayanai da nasihu yai Mata kafin ya Dora da cewan yasaka Mata kudi a account din _CPB_ account na qasar da aka bude Mata kafin yayi Mata adduar fatan alkhairi suka fito jikinta duk a sanyaye.

Koda suka fito tareda Hanifa da Anty Amina data kalli Dad Alfa daya fito shima zai fita cikin girmamawa ta gaidasa tana matsawa daga hanyar dazai wuce din ya amsa tareda kallonta Yana cewa"

Aminah Yaya ummanku da Dadah Ina gaidasu.

Zasuji" tace kafin suka wuce mum Malika na Bin su ukun da muguwar harara tana cewa" tsofin munafukai acikin ranta.

Suna Isa mota Yana zaune cikin bayan motar Yana waya a natse fuskarsa sanyeda _American optical_ goggles dayayi Masa wani irin kyau Dan gabaki daya tun anan din yakoma shigarsa ta can turai.

Hango Hannah sukai tafe a shirye cikin riga da wandon jeans na _Valentino_ tayi kyau sosai itama fuskarta sanyeda _Bulgari flora_ glasses dinta dama tuni aka saka akwatinta a mota.,
Baki sake Hanifa ke kallonta Anty Amina ma kusan kasa riqe mamakinta tayi Banda Naj dataji wani Abu yataso Mata ta juyo ta kallesa ta cikin glass din motar taga ko gefenda Hannah din ke tahowa Bai kallaba sbd hankalinsa nakan wayar dayake Yana Dan Yi Yana dagowa ya kalleta cikin kasa gajiya da kallonta.

Maida kallon nata takuma Yi Kan Hannah da kayan jikinta dasuka bayyanarda rayuwar turai gabaki daya atareda ita Allah yasama dad ya fice da kila shi zai iya Mata mgna Amma mum Malika Kam rungumeta tayi tana washe Baki tace"

My baby I will miss you, please ki kula da kanki karki wahalarda kanki akan program dinnan Amma kiyi kokari ki dawo min ta abinda zanyi alfahari dake, Allah yasamu abinda kikaje yi,
Dan qasa qasa tayi da muryarta yanda bazasujiba tace"

Idan kungama kwanakin program din kibar masaukinki kikoma gidan Marshal din kema kafin kidawo.

Gyadawa mum din Kai tayi tana murmushi tace"

I love you mum, muntafi saimun dawo.

Baya gefen Marshal su Anty Amina suka saka Naj dataji Kamar tafiyar tafita ranta Amma Kuma ayanda takeji ko cewa akai anfasa da ita ta zauna bazata zauna din ba matuqar da Hannah za'ai tafiyar.
Tana zama ya Kama hannunta ya sarqe da nasa Yana Dan kashe Mata ido daya har lokacin Yana waya.

Gaba Hannah tashiga badan tasoba aka tada motar suka fice daga gidan su anty Amina na bin motar da ido.
Ciki suka dawo bayan tafiyansu Naj din suka zauna palon jiki a mace sbd sunsan sai wani ikon Allah ne zai Hana qura tabiyo bayan wannan tafiyar tasu da Hannah tunda sunsan Naj din ita Kuma kayan haushinta sunfi na kirkin yawa zata tsaya fushi da basarwa har Hannah ta ringa Mata shishiginda zai iya kawo damuwa.

A airport suna Isa Babu Bata lokaci sbd time yayi akai duk abinda za'ai suka wuce.
Ticket din Economy class aka siyawa Hannah sabanin shida Naj dake first-class sbd Daman yanason sakewa da Naj din yanda zata sake Masa hannunta kuwa dama Yana cikin nata tunda suka zo airport din har suka Shiga jirgin suka zauna Wanda Hannah tayi zagi,tayi Allah ya tsine yafi so a qirga.
##MAMUH#

************************

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

*_DM 51_*

*_AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE_*
08067558902
Manyan Mata,manyan yara dasukasan sunsan kansu afagen zagewa suyi gyara me kyau na musamman suzo ga gwanarmu wadda muka tabbatarda aikinta da kyawun kayanta,
*_AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE_* nada kayan gyaran Amare da masu haihuwa,gyaran jiki Dana cikin jiki harma dana fata Wanda take aikawa koina a fadin Nigeria.
Ta bangaren kayan Mata ma kuwa dukkanin kayan gyaran dakike buqata tanadasu kala kala masu kyau da tsafta tareda inganci da qarfi,
Mun tabbatarda aikinta shiyasa muka kawo muku tallarta.
*_AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE_*
08067558902
******************************

*_51_*
Saida asuba jirginsu ya sauka lokacin Naj tayi matuqar gajiya sbd yanayi na ciki ga Kuma yunwar datake damunta duk da snacks din dataita ci Basu Mata maganin yunwartaba abincin gske take buqata shiyasa duk jikin yake a sanyaye bawani qwari Koda suka fito zuwa gurin motar dazata daukesu zuwa gida sai sake lagwabewa takeyi Yana riqeda ita cikin jikinsa duk Rabin hankalinsa nakan Naj din harsuka Shiga mota ko yanzu Hannah dince agaba suna baya dukkanin farin cikin tafiyar data taho dashi ya bace ya maye da zallar baqin ciki da takaicin yanayinda idanuwanta keta game Mata suna ciki musamman yanda Naj din duk tayi wani laushi da sunan gajiya shikuma sai tarairayarta yakeyi Yana damuwa kamar wadda zatai nakudar cikin ta haife Masashi yanzu.
Tsoki taja me qarfi Wanda ya tunatarda Marshal tana cikin Motar ya Dan dago daga shafa fuskar matarsa dayakeyi ya kalleta Yana Dan kallon hanyar dasuka biyo kafin yace"

Kifadawa drivern inda za'a kaiki saimu ajeki mu wuce.

Ajiyar zuciya tayi tana kokarin danne baqin cikin datake ciki da bacin Rai ta bude Baki tareda waiwayowa ta kallesa kafin ta kalla Naj dake jikinsa idanuwanta a 'dan rufe hannunta na riqe cikin nasa ta saki yaqen takaici tace"

Tunda Naj batajin Dadi da gajiya atareda ita hakama ga ciki tariga ta galabaita afara kaiku gida asamu akula da ita Ni sai a kaini daga baya.

Baice komaiba Dan shima isarsu gidance agabansa sbd halinda Mrs din take ciki.
Dan matsa hannunta yayi ahankali yana cewa"

Sorry wifey munkusa isa gida da kaina zanyi feeding babyna da mummynshi abinci.

Bude idanuwanta tayi ahankali ta zuba Masa idanuwanta dasukai laushi ta kallesa, take tsikar jikinsa ta tashi ya Dan bude idanuwansa akanta Yana rage murya Sosai yace"

Zaki kasheni ne?idan Kika sakemin wannan kallon bansan abinda Zan iyayiba acikin motar nan,ki ajemin kallon Nan zuwa gobe idan kin huta saikimun shi nikuma Zan nuna Miki qarfin tasirin dayakedashi akaina.

Duk da jikinta amace yake saidata Dan so barin jikin nasa sbd maganar dayake Yana sake Dan matsa hannunta da wata sigar.

Maida yayi takoma ta lafe ajikinsa din Yana cewa"

Shikenan bazan sake cewa komaiba.

Hannah tsabar hankalinta nakansu duk yanda yayi qasa da murya Saida kunnuwanta suka jiyo Mata abinda yake cewa,ta rintse idanuwanta tana damqe handbag dinta datakejin kamar ta rufe drivern dake tuqin da ita duk da kuwa baisan ma meke faruwaba a motar.

_North Beretania street,_
_Honolulu Hawaii_
_US._
Parking motar drivern yayi batareda yashigo da itaba har bakin kofar shigewarsu sbd Marshal din daya bada umarnin hakan Dan a tafi akai Hannah Dan ganin yake itama bazata rasa gajiyaba.

Kayansu aka fitar Mai aikinsa namiji Wanda Kuma Kuma shine cook shine me kula da komai na gidan bayan securities guda biyu na office da aka basa shine yadauki kayan Yana Masa sannu da dawowa tareda kallon Naj dake riqeda hannun mijinta har lokacin cikin girmamawa yace"

Welcome ma'am.

Thank you" ta furta ahankali kamar Mara lafiya.

Password din kofar yasaka kofar palon ta bude yafara shigewa ciki da ita brian na bayansu janyeda luggages dinsu,
Brian yayi saurin nufar switch na wuta ya kunna take koina haske ya kawo ya qarasa ya rage Aircon Dake aiki Wanda ya kunna dazu bayan yagama gyaran koina.
Chapter 54 · 0% Book details