← Book details Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 59

Sashe 28

Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta Jima sosai acikin toilet din kafin tafito bayan tayi hadda wanka Wanda yasa jikinta sakewa sosai saidai fuskarta da zuciyarta cike suke da zallar damuwa da baqin ciki
Ta shafa Mai kadan ta shirya cikin riga da skirt na atampa dark purple dataiwa farar fatarta kyau sosai musamman yau din da fuskarta tayi fresh duk da kumburin idanuwanta datasha kuka Yana nunawa ta fesa turare ta fito kanta ba dankwali sai qaramar hular da Bata rufe gashinta duka ba hakan Kuma ya qara Mata kyau ta nufa dakin hajjo tana kokarin nutsar da kanta Dan kada agano halinda take ciki.

Saida takai tsakiyar dakin ta tsaya cak ganinsa zaune gefen hajjo gabaki daya dakin yadauki qamshinsa yayi wanka yana sanyeda riga da wando na farin yadin filtex me laushi da tsada
Yaji shigowarta da dakatawarta Bai juyoba hankalinsa na Kan hajjo dasuke mgn Amma ganin Naj din itama saita tsaya kallonta cikin mamaki tace"

Najma kindawo ne?
Yanzu kuka dawo kokuwa cikin dare?
Qaraso mana,
Sai tafiya Kuma takamaki daga office Baki dawoba,
Anya wannan aikin yakamaceki kuwa yanzu Najma?
Shi wannan na tambayesa tun ranar da kukai tafiyar yace da saninsa Kika tafi,ga wayarki akashe haniface kawai tace tana samunki Kuna mgn.

Daqyar ta iya qaqalo wani munafukin murmushi tana kallon hajjon a natse tace"

Da safen nan nadawo duk Kuna bacci Bari naje gurin Hanifa kafin ki Gama.

Juyawa tayi ta fice batareda tajira wani zancenba Dan
Batareda ya waiwayoba yasaki wani irin murmushin dayasa hajjo kallonsa da dukkanin nutsuwarta cikin mamaki dan ba abune daya fiya yiba ta maido hankalinta kansa yace"

Yaushe ka shirya tafiya da matarka?

Bai kalletaba hankalinsa nakan waya yace"

Saita shirya Bina da kanta.

Bana tunanin zatai hakan sbd haryanxu Bata amintaba da auren
Kuma Sam banason a takurata Akan komai.

Wani shegen guntun murmushin yakuma saki Yana cewa"

Kar a takurata abarta harta Aminta dan kanta.

Tsoki hajjo tasaki cikin quluwa dashi tace"

Tashi ka ficemun sbd kedai haryau zance dakai bayada Dadi
Mutum saiya zage yamaka mgn me tsayi ko mahimmanci ka jeho Masa kalma daya amsa,banason kayan takaici tashi kaje kafin na qarasa quluwa da wannan muguwar dabi'ar taka mara Dadi.

Bai tashiba saima kallonta da yayi yanaci gaba da duba wayarsa Yana cewa"

Ahaka fa kike damuna yaushe Zan dawo idan bana nan.

Murmushi tasaki tana cewa"

Ta Nan ka bullo Kuma.

Naj Kuma tana fitowa dakin ta nufa dakin Hanifa ta tura kofar Kai tsaye ta Shiga saiga Hannah zaune a kejarar dakin tana Taya Hanifa yanka qatuwar guava data tashi tunda safen da marmarin ci
Da mamaki Hanifan ke kallon Naj fuskarta na yalwatuwa da farin cikin ganinta ta ware Hannu tana cewa"

Hey sweetheart sannu da dawowa nayi kewarki sosai sirikata.

Tsuke fuska Naj din tayi tana Mata kallon daya sanyata rufe Baki tana cewa"

Sorry sorry.

Qarasowa tayi tana zama bakin gadon kusada Hanifan ta bude Baki cikin kulawa tace"

Ya ya?ya babyn?

Lafiya kalau muke,ya Hanya? Da gajiyan tafiya?

Alhmdlh" kawai ta furta tana basar da zancen ta hanyar Dan kallon Hannah datace"

Naj sannu da Hanya?
Inane kukaje aikin ne hala?

Yi tayi kamar bataji Hannan ba ta miqe tana nufar kofa tace"

Zanci abinci a dining.

Miqewa Hanifa tayi tana cewa"

Nima yunwar nakeji,
Hannah ko Zakiyi breakfast damu?muke ko.

No nariga naci abinci bana buqatansa qarawa Zan fitanema nace Bari nashigo na dubaki tun shekaran jiya banshigoba.

Dining suka nufa ita Kuma ta fice daga sashen batareda tasan Marshal na sashenba Dan da Babu inda zata.

Tea kawai ta iya Sha sai doya kadan da aka soya da egg sauce ta miqe tana kallon Hanifa dakecin doyar sosai tace"

Inajin Dan ciwon Kai da gajiya zanje na kwanta ko zansamu bacci kafin lokacin sallah.

Ok ki kula, Allah ya hutarda gajiya.

Daki Takoma ta Isa gadon ta kwanta tareda qarawa AC qarfi sbd zufi takeji na zazzabi dake hawa Yana sauka ajikinta ta rufe cikin bargo tareda rufe idanu ahankali bacci me qarfi ya dauketa.

Bacci Sosai tayi Bata Farkaba sai guraren la'asar ta tashi zaune ahankali tanajin tasamu sauki Sosai ko Ina nata ya sake ba laifi ta sauko gadon tareda cire kayan jikinta ta nufi toilet tadake wankan ruwan zafi sosai ta fito da walwalarta tafarayin sallar azahar da la'asar kafin ta Dan shafa Mai ta Sanya doguwar rigar atampa ta fito.

Daga hajjo har Hanifa na zaune palon Hanifa na kallo hajjo na karantunta data Saba da medical glass dinta a fuskarta,
Naj din na fitowa duk suka bita da ido hajjo Kai tsaye tana cewa"

Najma lafiyarki kalau kuwa?Naga duk kinyi wani iri kamar bakyajin Dadi?
Anya Baki debo sanyi a tafiyar Nan ba fuskarki duk ta kumbura,kodai bakyajin Dadi ne?

Hanifan ma zuba Mata idanuwa tayi tana jiran amsar da Naj din zata Bata Dan itama dai taga alamar Kamar batada lafiyar duk fuskarta a kumbure Dan ko yanzu data shiga wanka saidatasha kukan qaqa nikayi kafin tafito.

Dan murmushin Dole tasaki tana qarasawa dining tace"

Lafiyata kalau hajjo kawai dai garin akwai sanyi ne sosai shine yake damuna matuqa Amma zankira Dr sa'id saiya kawomin maganin sanyin Inshallah Kuma ma zuwa gobe Inshallah Zan warware tunda nadawo gida.

Zama tayi ta diba abinci tafara ci bayan Tasha ruwan zafi Dan tafijin dadinsu fiyeda abincin,
Saidata koshi ta taso tadawo gurinsu palon ta zauna Hanifa na janta da Hira sosai tana Dan qoqarin sakewa da amsawa
Hajjo kuwa saiyi takeyi tana kallonta sbd hankalinta kamar Bai kwanta da lafiyar ba ganin take Najma din batada lafiya boyewa takeyi sbd kada ta daga musu hankali idan taga ankwana biyu Bata warware ba zata Kira Dr sa'id da kanta yazo ya duba musu ita.

Ba laifi ta Dan sake sunata hirarsu akan babyn Hanifa da duk suka qwallafa Masa Rai har akai magriba suka shige sallah
A dakin Hanifa sukai sallar acan tayi zamanta har ishai Hanifa nata Koro Mata bayanin scanning dasukai shekaran jiya da Kuma dawowar da Isma'eel zaiyi qarshen wata.
Saida sukai sallar ishai suka Gama zantukansu da Naj daurewa kawai takeyi tana danne damuwar halinda take ciki kafin suka fito cin abincin dare.

Dukkaninsu suna zama Kan dining din ko fara cin abincin basuiba saiga qamshinsa ya fara tunkaro dining din tanajin hakan tasan waye ke zuwa Dan Haka ta Dan hade fuska tana daurewa Dan Hana kanta miqewa tabar gurin sbd hajjo dake gurin gashi tariga tana zaune ne da a tsaye take saitabar gurin..

Muryar Hannah taji cikin wani irin salon nemawa Kai gurbi tana cewa"

Hajjo anan zanci abinci Nima yau can masu aikin mum Malika abincin dasukai yayi Mai sosai zaisani zafin Zuciya.

Da Yar kulawa hajjo tace"

Eh gskia karki ci idan zai saki damuwa zoki zauna kici anan din.

Da sauri ta qaraso taja kujerar dake kusa data Marshal din ta zauna tana jifansa da wani irin kallo
Shikuma hankalinsa gabaki daya baya kanta Yana Kan abincin da Naj ta zubawa kanta taqi ko dagowa ta kalla inda suke Dan Jin take cikinta yagama cika da wani irin takaici.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

*_DM 29_*
Hannah da kanta ta miqe tariga kowa zuba Masa abincin duk da tana iya kokarinta na riqewa da kiyaye duk wani abin dayake so dakuma ya shafesa Dan Haka abincin iya daidai Wanda tasan yanaci ta zuba masa tareda lemon juice me zuma datasan bayan _RED BULL Blue edition Energy drink_ shikadai yakesha.

Zama tayi tana zuba nata abincin kadan sbd Babu wata yunwar datakeji taci abincinta tun dazu sbd Marshal din yasa tace zataci anan din duk da zuwa yanzu da Naj ke sake zamar Mata abin takaici da baqin ciki Sam said Dole take iya zama guri daya da Naj din Dan dai kawai tana mum Malika nasata dannewane tana boyewa.

Naj cin abincin takeyi a hankali duk da yariga ya gundureta cin kawai takeyi a natse batareda ta kalla kowaba sai hajjo data kalleta cikin kulawa ganin yanda takecin abincin cikin nutsuwa ahankali duk da tasan sanyi da komai a natse hali da dabi'ar Najman ne Amma ita dai tafiyar Nan duk tasake sakurkuce Najman,
Cikin kulawa tana kallonta tace"

Najma jikin ne haryanxu?
Nace ruqayyat ta dafa Miki Ginger tea da Zuma sbd da alamar wannan sanyi ya kamaki sosai a wannan tafiyar,
Gobe Dr sa'id zaizo ya dubaki.

Dagowa tayi ta kalla hajjon tana aje spoon din hannunta cikin nutsuwa tace"

Naji sauki fa Kuma bawani ciwo bane sanyi ne kawai basai Dr sa'id din yazo ba zansha Ginger tea din zuwa gobe Zan qarasa warwarewa.

Zanfi samun nutsuwa idan Dr sa'id yazo yadubaki" hajjo tafada Kai tsaye tana kallon Najman kafin taci gaba da cin abincinta.

Shiru Naj din tayi tana daukan spoon taci gaba da cin abincin tana ganin irin kallon da Hanifa ke binta dashi tayi Mata banza Bata bi ta kantaba.
Hannah ta karba zancen da cewa"

Naj inane kukaje da Sanya zai kamaki Haka?

Sai alokacin ya dago ya 'dan zubawa Naj din ido wadda tun dazu dasuke zancen Bai dagoba Yana jinsu tambayar hannah tasa ya dago yana kallon Naj din.

Ahankali taji idanuwansa akanta Dan Haka ta sake kame fuska tanacin abinci tana share tambayar hannah da shirun yasake habbaqa tsanar Naj din aranta ta dauke Kai daga kanta ta juyo gurin Marshal din zatai mgn ya aje tissue dinda ya goge Baki Yana miqewa tsaye ahankali alamar yagama ya zuba hannayensa ahankali ya tako zuwa inda take zaune ya sunkuya ya saukar Mata da wani irin lafiyayyan kiss a kumatunta na hannun dama ya Kai Bakinsa kan kunnenta ahankali qasan maqoshi da wata irin murya me tsananin taushi ya furta"

Ki tabbata kinsha ginger tea dinnan sbd wani sanyin dazai iya kamaki.

Dagowa yayi ya kalli su hajjo Kai tsaye cikin attitude yace"

Goodnight,Mu kwana lafiya." Ya juya ya wuce yabar gurin.
Chapter 28 · 0% Book details