← Book details Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 59

Sashe 32

Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka Dadah ta ringa Bata rarrashi da maganganu sbd ganin fadan ba inda zai kaisu saiga tone tone har Azo abata goma biyar Bata gyaru Dan ita da wannan aure ya mutu gwara aje ahakan tana zaune gurin hajjo indai da auren yafi musu zasui jira har Allah yasa auren yazama Kamar kowanne auren.

A dakin Dadah tayi zamanta saidata nutsu kafin Dadahn da kanta ta rakasu har palon hajjo suka Kuma taruwa suka rarrasheta kafin Dadah ta tafi
Har dare hajjo da hanifa na tarairayarta Dan tasake Haka suka Kwana
Ko Dad Alfa da kansa Saida yakirata suka sake zama da hajjo suka ringa rarrashinta cikin kulawa hartazo tanajin kunyar abin qarshe Dole ta sake Dan ganin yanda duk suketa sake lallabata shiyasa ta sake sosai ta koma bakin aikinta,

Hannah da mum Malika Koda sukaji abindaya faru Dadi Kamar me musamman suka sake maida himma gurin ganin auren Hannah da MARSHAL din ya tabbata,
Duk yanda Hannah taso fadawa marshal din rigimar Bata samu damaba sbd baida lokacinta busy yake sosai gashi yanata tafiye tafiye acan din Dole ta hakura harta samu lokacinda zata fada Masa.

Umma da Dattijo Basu duk da zancen yayi kwanaki sosai Basu daina fushi da itaba sama sama suke amsa gaisuwarta idan tashigo gidan Dadah ce dai take lallabata dataga fushin ba yayi sai anty Amina daketa aikin dawainiya da duk abinda Hanifa keso sbd cikinta daya fito sosai yanzu.

Takoma aikinta gadan gadan sai yamma take dawowa musamman da ayyuka sukai Mata yawa na 'yar rigimar da ake wadda ta tarar Marshal ya fige Abbas daga ALFAs Amma sauran shareholders din Basu yardaba shikuma sbd yafi kowa hannun jari aciki yace hukuncinsa kenan.
Rigimar tasa ayyuka sun Mata yawa sbd dukkanin ayyukan office din president na companyn yadawo office dinta tunda Abbas an dakatar dashi say angama rikicin gashi Marshal din yatafiyarsa saiya dawo Kuma.

Da mamakin wannan qarfin halin nasa take aikin office din kullum sbd ayyukan sun Mata yawa ko yawon meetings yasa har wata Yar rama ta taso mata.
Saidatai wata daya da sati biyu tana fama da ayyuka kafin ayyukan suka Dan daidaita tafara samun kanta har tana dawowa gida da wuri.

Yau tunda tazo office din batai komaiba sbd jiri datake gani tun jiyan tafara jinsa yanayi Yana tafiya.

Dafe kanta tayi tana Dan rufe ido ta bude ahankali ta dago tana kallon Sarah data shigo office din ta bude Baki ahankali tace"

Sarah please bani ruwa me sanyi nasha.

Kallonta Sarah tayi da mamaki tace"

Me sanyi ko me Dan sanyi kadan?

Batareda ta dagoba tace"

Me sanyi sosai.

Da mamakin Sarah takuma kallonta sanin Bata Shan ruwan sanyi zatai mgn saikuma ta fasa ta nufa fridge ta bude ta dauko Mata ruwan roba masu sanyi sosai ta kawo Mata ta miqa Mata.

Karba tayi ta bude Kai tsaye takai bakinta tana Sha Sarah na kallonta da mamaki.

Ajiyar zuciya kadan ta sauke bayan tagama sha ta ajiye sauran ruwan tana cewa"

Sarah zanje gida yanzu kaina na ciwo Ina buqatan hutawa ko zai sake.

Tare suka fito da Sarah din itace take tuqin takaita gida suka nufa cikin gidan tare.

A Palo suka tararda Hanifa zaune tareda anty Amina data kawo Mata sabuwar Awarar da Umma ta Aiko Mata wadda akaiwa sauce din kayan miya dasu carrots da kwai.

Kallo daya Naj tayiwa Awarar taji tana son ci abinda Bata taba yiba shine ko dakinta Bata shigaba ta qaraso gefen Hanifan ta zauna ahankali tana cewa"

Yunwa nakeji sosai har kaina Yana ciwo.
Ta dauka plate tana miqawa Hanifan tana cewa"

Samun zanci.

Zuba Mata Hanifa tayi tana cewa"

Lallai yau 'yar gaban goshin hajjo yunwa takeji tunda ko daki bazaki iya qarasawaba.

Batace kalaba saidataci Awarar a bakinta taji kanta dake sarawa ya daina ta dago ta kalli Hanifan ahankali tace"

Thanks.

Sai alokacin ta kalla anty Amina tana cigaba daci suna gaisawa anty Amina na kallonta dakyau cikin nazari tace"

Naj bakida lafiyane Naga kamar kin fada.

Kallonta Hanifa tayi tana cewa"

Ramar aikice Amma duk da hakan Ni Banga ramarba haske dai Naga tayi sosai kodai bakida jini ne Naj?" Taqarasa fada tana Dan zare ido.

Batareda ta dagoba tace"

Lafiyata kalau stress ne kawai amma zanshiga hutu sbd komai yakoma yanda yake a office din Inshallah.

Saidata qoshi kafin ta qarasa dakinta tabarsu a palon ta tube ta shiga toilet wanka.
Sai datai wankan taji jikinta ya sake sosai ta fito daureda towel ta nufa jikin mirror kenan taji wayarta na ringing ta juyo ta nufa wayar dake Kan gado ta dauka sai kawai taga No din qasar waje destination id dinta ya nuna Mata United States of America.

Kai tsaye ta dauka batareda ta tsaye tantance kiranba Wanda yake Vidcall sai ganin mutum tayi ya bayyana kan screen din wayarta Yana zaune cikin lafiyayyan palonsa sanyeda uniform dinsa na sojojin America dasukai Masa wani irin kyau uwa uba hutu da nutsuwar daya samu ta bayyana ataredashi Ya zuba Mata fararen idanuwansa har zuwa kirjinta dake daureda towel Tsananin hasken data qara yasashi sake zuba Mata idanuwansa,
wannan ne Karo na farko data gansa cikin uniform ta dauke kainta ganin irin kallon dayake Mata sai alokacin ta tuna da towel ne jikinta ta kashe wayar tana jefarwa Kan gado ta tafi tahau shirinta.

Baccin maraice yayi sai magriba ta tashi ta fito bayan tayi sallar magriba sbd yunwa me tsanani datake ji.
Kicin ta nufa sbd sanin lokacin cin abincin Daren baiyiba tasan Hanifa na kicin sbd Bata jimawa bataci ba shiyasa take zuwa kicin taci ta koshi Kuma ahau dining aci da ita.

Tana Shiga kicin din ba kowa sai ruqayyat dake qarasa aikin abincin Daren ta nufa fridge ta bude ta dauko milk drink tasha sosai ta dauko cake guda hudu ta cinye ta qara da apple biyu kafin taji ta dan samu nutsuwa ta fito suna hadewa da Hanifa dazata Shiga kicin din neman abinda zataci itama tace"

Naj yunwa nakeji cake zanci da Madara tunda kin cunyemun awarar da Umma takawo min dazu.

Batace komaiba Takoma Palo ta zauna tana duba wayarta tana jiran agama abincin akawo dining.

Sallar ishai taje tayi tana fitowa hajjo na fitowa suka dunguma dining Hanifa tuni ta riga kowa Isa.

Naj din ita tazubawa hajjo abinci takawo Mata ruwa da komai ta kalli Hanifa da Bata harta zuba abincinta tafara kaiwa Baki.

Zama tayi itama tareda zubawa ta zauna suna binta da ido ta dago ta kallesu ganin irin kallon dasukewa abincinta yasata kallon abincin sai alokacin taga ta zuba da yawa ba kamar yanda ta Saba ba dama kwanakin gabaki daya cin abincinta ya sauya ta Dan fuske tana cewa"

Yunwa nakeji sosai duk yau banci wani abincin kirkiba.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

*_DM 34_*
Hajjo kallon abincin takuma Yi kafin ta kalli Naj din cikin kulawa da nutsuwa tace"

Najma ki daina zama da yunwa Haka sbd zata iya Miki illa yanzu wannan abincin zai iya qulle Miki ciki,Kisha tea kafin ki ci abincin cikinki ya sake tukuna.
Kallon Hanifa tayi tana cewa"

Miqa Mata tea din ta zuba ta Sha.

Qaramin flask din dake cikeda black tea dinda yaji kayan qamshi da hadinsu lemon da Zuma wanda koyaushe dashi ake jere abincin safe Rana da dare Wanda qaidar hajjo ne wadda ta Saba da Shansa Kuma al'ada da dabi'ar Shan nasa ya Kama duk Wanda yake gidan ko baqi akai idan za'a kawo musu ruwa sai an tambayesa ko akawo Masa tea din.

Miqawa Naj Hanifa tayi tana cewa"

Kin riga kinfara cin abincin kinsha tea din daga baya" ta aje tana daukan spoon tafara cin nata abincin.

Kamar yanda tasaba cin abinci a natse ta cinye abincin tas tasha ruwa kadan ta zuba tea din Wanda kurba daya Tai Masa ta ajiye tana cewa Alhmdlh ahankali.

Kallonta hajjo tayi tana sake cewa"

Idan Zaki ringa zama da yunwa irin Haka Zaki sa ciwofa ya kamaki karki sake hakan daga yau.

Guntun murmushi tasaki ahankali tana kallon Hanifa da har lokacin abincin takeci tace"

Yaune kawai hakan bazai Kara faruwa Inshallah hajjo.

Barin gurin tayi ahankali tanajin nutsuwarta ta dawo ta dawo palo ta zauna sai alokacin ta dauka wayarta tana dubawa har Hanifa da hajjon suka Gama suka baro dining din hajjo tayi dakinta sbd qafafunta da ruqayyat zata gasa Mata da ruwan dumi.
Hanifa Kuma gefenta ta zauna tana daukan tata wayar itama tace"

Naj gobe umma zata faramun sabon gyara Isma'eel zai dawo next week fa.

Juyowa Naj din tayi ta kalleta tana sake maida hankali kan abinda take dubawa a wayar tace"

Shine kike Zillo Haka?
Cemasa zanyi yayi zamansa sai zaki haihu yadawo muga qarshen gyaran.

Dariya Hanifan tasake tana cewa"

Zillo ma ai kadan ne zille zille zanyi ma idan ya dawo tunda bansan kalar zille zillen da matan duniya ke can suna Masa ba tunda bana kusa Dana Haka idan yazo nawa lokacin ne nayi haukama idan Zan iya,
Hannah kina ganin duk ranarda tasamu auren Marshal wannan rawar kan datake ai uwar ubansa zamu gani akan wannan datakeyi Yan.......

Hade sauran maganar tayi tana rufe bakinta Jin Naj din tayi shiru sbd gabaki daya ta manta da Naj take maganar,ta Dan kalli fuskar Naj din data juyo itama ta kalleta tareda sake wani irin guntun murmushi tana basarwa da cewa"

Ashe kinada qarfin yiwa miji zille zillen Kike makure Mana fuska ki nade muna dawainiya da matarsa.

Haba sirikita idan bakiyi hidima daniba waye zaiyi....

Dan kame fuska Naj din tayi Hanifan tasaki dariya tana cewa"

Sorry my Naj.

Wayar Hanifan ce tayi ringing ta waiwayo tana kallon wayar ta maida kallonta kan Naj da kallo daya tayiwa wayar taga sunan me Kira ta dauke tana maida hankali akan tata wayar.

Dauka Hanifa tayi cikin murmushin ganin video call ne ta dauka Kai tsaye tana cewa"
Chapter 32 · 0% Book details