← Book details Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 59

Sashe 24

Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idan kafito ka rufe kofar.

Shan gabanta yayi tayi baya tana kallonsa cikin fara quluwa da dabiarsa ta kallesa cikin tsana da qyamar halayensa da Basu sauyaba tace"

Mr chairman behave yourself please kana neman wuce limits dinka
Hurumin wani kake neman shiga da wannan dabi'ar taka ka kiyaye.

Wani irin murmushin takaici yasaki Yana Mata kallon daya sake suqeta Yana tsananta Mata tsanarsa yace"

Wai kina maganar ke Matar aurece yanzu kokuwa kina nufin hurumin na waye akanki.

Sanin dama ba cikakkiyar hankaline dashiba yasata sake rabesa zata wuce yasake matsowa gurinta sosai zaiyi magana Wanda ke bakin kofar tun dazu yayi gyaran murya suka waiwayo gurinsa
tana ganinsa taji faduwar gaba akaro na biyu kenan data gansa gabanta na faduwa, dauke Kai tayi ganin yanda fuskarsa tayi ta rabashi zata wuce ya riqo hannunta tareda dawo da ita ya kalli Abbas dake kallon hannunsu a hade zuciyarsa na tafasa yanajin kamar ya Ari hauka yajuyewa Marshal din ita
Cikin muryarsa me kamewa ya kalli Abbas yace"

Zaka bamu guri ko" yaqarasa fada Yana nuna Masa kofa da idanuwansa dasuka saka Abbas din mufar kofa ya fice zuciyarsa na tiriri.

Bayan fitar abbas Dan rufe fararen idanuwansa dasuka sauya yayi kafin ya bude ya kalleta Kai tsaye yace"

Bayan wannan meeting din kafin kibar Nan ki tabbata kin rubuta resignation letter, daga yau na soke zuwanki aiki gabaki daya harda fita ma.
Yana Gama fadar hakan ya juya ya wuce sbd ita kanta tana iya jiyo tsantsar da gaske yake maganar Babu Wargi acikinta yabarta tsaye tana binsa da kallon mamaki Dan kuwa kasa dogon motsi tayi ganin yanda yau idanuwansa sukafi kullum nuna Isa da hadewa.

Daqyar ta iya tattara kanta takai gurin meeting din inda ita kadai ake jira
Tana shiga Abbas yabita da ido Yana satar kallon Marshal Wanda gabaki daya fuskar Nan tasa Babu wani sauqi ko rahama atareda ita Dan ko ita din Bata ishesa kallo ba.

Meeting din suka fara tsawon lokaci kafin aka kammala suka fito ko office Bata nufaba Sarah ta qaraso da sauri cikin sassauta murya tace"

Marshal na jiranki yanzu a mota.

Kallonta tayi tana dauke Kai ta qarasa office dinta tashige tana cewa"

Zankoma da kaina idan nagama.

Kasa juyawa Sarah tayi sbd tsoro da fargaban tunkarar Marshal da zancen Dan sanin ba Wasa ko reni bare sakin fuska.

Sake kallonta Naj din tayi tana cewa"

Me kike jirane?
Kije ki sanar Masa nasan hanyar komawa gidan da kaina.

Ganinsa bayan Naj din yasa Sarah Dan sauke Kai tana ficewa daga office din batareda tasake cewa komaiba.

Tana fita Naj dataji isowarsa ta hanyar Jin qamshin turarensa ta tamke fuske tana wucewa zuwa gurin handbag dinta zata fiddo wayarta.

Akaro na farko da bacin ransa yafara fita akan taurin kanta da rashin tunaninta Dan Haka Kai tsaye ya fizgo hannunta da handbag dinta a hannunsa yafice da ita.
Cikin Motar yasata kafin yashiga yaja motar sukabar gurin.

Itama Bata hakurin yakai maqura cikin bacin Rai ta juyo ta kallesa tace"

Ka tsayar da motar bana buqatan zuwa gidan ahaka sbd bana buqatan kowa nashiga rayuwata yayi abin dayaga dama aduk lokacinda yaga dama inaga hakan ya Isa so just stop the car Zan sauka.

Ciki tsananin bacin Rai yayi wani mugun parking da motar ya juyo ya kalleta da idanuwansa dasuka sakat gabanta muguwar faduwa da muryarsa data sake kayar Mata da gaba yace"

Zan banbanta Miki tsakanin iko da dama dakuma ganin dama Wanda Duke suke a hannuna na rayuwarki gabaki daya ta yanda gaba Zaki San waye mijinki waye tsohon saurayinki
And Kika sake magana agurin zakisan waye Wanda igiyar aurenki yake a hannunsa.

Fasa nufar gidan yayi ya juyarda motar da wani irin speed yakama hanyar qaton gidansa dake cikin anguwarsu ta sojoji wadda duka manyan sojojine acikin anguwar shiyasa tsaronta yafi kowace anguwa a garin.
Tun a checking point din farko da sojoji ke gadin anguwar taji gabanta yafara faduwa sbd tasan yanada sabon gida a anguwar wanda zai zauna da Hannah bayan aurensu
Idan tashiga anguwar Nan tasan Babu me fitar da ita idan bashiba Dan tsananinta taji hankalinta na neman tashi Amma sbd taurin zuciya taqi cewa komai bare kallonsa.

Suna Isa gaban makeken gate din gidan aka wangale Masa sbd kurtun sojan dake gadin gidan Yana zaune kofar gate din Kan kujera Yana waya.

Parking yayi gefen wata Mercedes Benz beymach dinsa wadda take gidan tunda ya siyeta take gidan ko hawanta Bai tabayiba.

Fitowa yayi batareda yabi takantaba ya nufi kofar shiga wadda keda code tana ganin hakan tasan ko zatai shekarun duniya agurin bazai dawoba Dan Haka ta fito tabiyosa Dan Jin dalilinsa na zuwa Nan din da ita Dan tanada abin Yi idan shi batadashi.

Tana Shiga palon ta kallesa lokacinda yake shigewa hanyar bedrooms ta dauke Kai tana Jin zuciyarta na zafi da kalar nasa cin ran ta nufi kujera ta zauna Dan kuwa kozasu shekara anan itama bazata bisa ta rokesaba akan ya maidata gida tunda taga a sama yake.

Agogo tafara kalla ganin lokaci na tafiya Dan kuwa tunda yashiga Bai fitoba taga magriba tayi har lokacin Babu motsinsa
Ta fiddo wayarta daga cikin jaka tana dubawa saigashi taji qamshinsa Yana dosowa ta dauke Kai daga kallon inda zai fito din ya qaraso ta gabanta sanye da farar jallabiyar data qara Masa kyau sai qamshi yake zubawa ya kalleta da idanuwansa datakejinsu suna yawo akanta ya wuce ya nufi kofa ya fice zuwa masallaci sallar magriba.

Wayarta ta duba Dan Kiran hajjo sai taci Karo da saqon Hanifa data rubuto Mata"

_Sarah tace tafiyar office ta gaggawa ta kamaku Allah ya tsare adawo lafiya sirikita karki damu nariga nafadawa hajjo_

Da alama da wata manufa hanifar Tai Mata text din Dan Haka sai kawai ta aje wayar tana miqewa dan yin alwala a toilet din dake palon farkon kafin yadawo.

Da dubara da kame kame tayi sallar magriba da ishai da kayan jikinta Takoma kujera ta zauna tana jiran dawowarsa.
Bai dawoba sai qarfe goma na Daren lokacin wani wahalallen bacci ya dauketa Amma sbd tariga tasawa ranta rashin yadda dashi da sukuni tanajin motsi ta farka tareda bude idanuwanta ahankali dasuke cikeda baccin bacin Rai da gajiya tagansa gabanta tsaye Yana kallonta cikin yanayi na Dan tausayawa sbd ganin taurin kanta yasa ko ruwa batashaba duk da yaga alamar tayi salloli sbd ganin toilet din daya gani tayi amfani dashi na palon.

Sunkuyawa yayi ya dauketa gabaki dayanta ya nufa dining da ita ya zaunar tareda nuna Mata kayan tarkacen abinci da drinks daya shigo dasu da ido ta miqe tsaye tana kallonsa da cikin masifa zatai magana Amma batama da qarfin yin masifar
Yana ganin Haka ya dauka yoghurt me sanyi kadan ya bude ya zaunar da ita yabata abaki ba musu ta bude bakin ta Sha sosai sai alokacin tasamu damar kallonsa tana qwacewa daga jikinsa.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

*_DM 25_*
Miqewa take kokarin Yi ya ajiye cup din dake hannunsa ya kalleta da mamaki akan fuskarsa datake sata dauke idonta daga kallonsa ya mayarda ita zaune kan qafafun NASA tareda zura hannayensa ya rungumota ta baya Ya zuro kansa ta wuyanta daidai kunnenta ya bude Baki ahankali ya furta"

Me kike yiwa gaggawa na guduwa bayan kin shanyemun yoghurt¿
Kinsan me hakan ke nufi kuwa?""" Ya qarasa maganar Yana shafa fuskarta da tasa.

Yi tayi kamar bataji abin daya fadan ba taci gaba da kokarin kwacewa daga jikin nasa yasake shigewa da ita jikinsa Yana kallon wuyanta dayake shaqo qamshi daga gurin ya lumshe fararen idanuwansa ahankali kafin ya saketa ahankali Yana Dan dauke kallonsa daga kanta ta miqe tsaye fuskarta a daure sosai duk da tanajin takaici da kunyar kanta data Sha yoghurt din gashi Yana kawo Mata wani zancen kunya da takaici Dan kuwa tasan fassarar kalmar daya fada ta cewan" tasan me Shan yoghurt dinsa yake nufi"

Miqewa yayi shima ya Dan kalli fuskarta dake daure ba sassauci ko kadan,
Juyawa yayi ya nufi kujera ya zauna Yana kunna tv tareda daukan remote yakai _Aljazeera_ Yana maida hankalin shi 4 akai.
Yana kallonta tagajinda tsayuwa batace ko kalma daya ba sbd qin yadda ta saukar da Kai tace ya maidata gida fuskarta har lokacin a daure Takoma Kan kejeran dining din ta zauna tana jiran yagama yabar palon.

Baibi takanta ba sbd shima bawai rigimar ya iyaba dakuma daure daurenta shiyasa yashareta yaci gaba da kallon labaransa Yana duba agogo akai akai har Sha daya(11:00) tayi ya miqe tareda kashe switch na komai ya nufi hanyar bedroom dinsa batareda yabi takanta ba sbd yaga har lokacin tana zaune daram ga idanuwanta dasuke nuna tsantsan baccin dake cinsu Dan Haka Yana shigewa ta taso a galabaice ta kwanta kan kujera tana rufe ido Dan kuwa tasan baccin wahala ne zatayi gabaki daya batajin zata iya bacci a sofa sbd uban gajiya da takurar datakeji na rashin wankan dare na kafin kwanciya data Saba uwa uba kayan jikinta Suma batajin zasu barta ta iya bacci Amma Haka ta kwanta tana rufe ido.

Wanka yafito ya saka riga da wandon bacci masu Dan kauri na rugby ya zura slippers ya fito palon Yana duba agogon dake bangon tsakanin Master bedroom dinsa da bedroom dinda zai zama na Matar gidan yaga 11:37.

Bacci wuyane yayi gaba da ita me Dan nauyi Dan kuwa harda yunwa na tareda ita,
Idanuwansa ya zuba Mata ya kalleta da kyau yanajin tausayinta dakuma mamakin taurin zuciyarta tareda bakinta dayake zaro ko wace irin magana ya fada.
Chapter 24 · 0% Book details