← Book details Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 59

Sashe 44

Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

*_DM 44_*
Bayan fitarsa Hanifa kasa nutsuwa tayi da yanayin Naj saidai batace komaiba sbd ta fahimci dalilin hajjo na hakan sbd wannan rayuwar dasuke tsaf dadin bakin mum Malika da ikonta na zama Mata agurin Dad Alfa zai iya sawa aure tsakanin marshal da Hannah ya yiyuwa Wanda bawai suna qiyayya da hakan bane har cikin ransu itada hajjo basa kaunar Marshal yayiwa Naj kishiya sbd ko auren Mata Gama tantacewaba da dadinsa da komai ayi Mata kishiya yanzu bazai yiyuwa ga ciki ajikinta wata damuwar zata iya kamata Dan Haka itama Bata bayan auren Marshal ko wane iri bama na Hannah kawaiba da koma waye.

Tana Gama cin abincin ta miqe zata wuce hajjoma data rigata miqewar cikin kulawa tace"

Je kidubo Mana ita tana Lafiya kuwa¿

Hanyar dakin Naj Hanifa ta nufa ta bude Kai tsaye ta tura tashige tareda rufowa tana kallon dakin ganin Naj din Bata ciki taji motsin ruwa a toilet tasan tana toilet ta nema guri Kan gadonta tana kokarin hawa ta dakata tunanin ranarda Naj din ta hanata hawa Kan gadon na dawo Mata,
Ta dan ja baya tana sake kallon gadon abun daya faru ranar Yana dawo Mata,ranar da gskiyar ruqayyat kenan anan dakin Marshal din yakwana???
Kenan....
Girgiza Kai tayi tana Hana kanta cigaba da tunanin sbd Bai kamata ba tafasa hawa gadon tareda koma Kan sofa ta zauna tana sakin boyayyan murmushi sbd mamakin cikin Naj daya shigi kowa sbd abune da ko a mafarkin lulaye Babu Wanda yataba hasko hakan zata taba faruwa a yanzun,
Ki ita datasan wasu abubuwan na kebewansu da lokacinda ya dauketa daga office sukai tafiya Bata taba tunanin wani Abu zai Gama haduwaba a lokacin yanzu iya tunaninta laifi Naj din Tai Masa ya dauketa sbd ya hanata zuwa office amatsayin hukuncinsa Ashe babban aikine yasamu Naj dinta.

Jin Abu yayi yawa shiru Shiru yasata aje tunaninta ta juya tana kallon kofa cikin mamaki kafin ta miqe tsaye ta Isa jikin kofar tace"

Naj, Naj wankan da yawa fa baiyiba kinsan yanzu sanyi ba Wasa ya kamaki sbd cikin jikinki,
Idan sanyi ya kamaki zai illata babyn please kibar wankan Haka ki fito kokuma nashigo na kashe ruwan.

Komawa tayi tana kokarin zama taji Naj din Bata kashe shower ba ta fasa zaman ta nufi toilet din Kai tsaye tana budewa daidai Naj din na Gama daura towel da qyar sbd rawar sanyin da dukkanin jikinta keyi Dan ruwan sanyine ta sakarwa kanta.

Da wani irin kallo Hanifa ke binta cikeda mamaki ganin har kanta tayi wankan sai tsiyayan ruwa Kan keyi ta janyo wani towel da sauri tana Dora Mata akai ta jawota kamar wata qaramar yarinya suka fito toilet din dukkanin jikin Naj rawar sanyi yakeyi sosai zaunar da ita tayi bakin gado tana goge Mata kanta cikin kulawa da damuwa take cewa"

Naj menene hakan kikaiwa kanki?
Kinsan hakan zai iya saki ciwo
At least yanzu ki ringa tunanin abindake jikinki kafin kiyi wani abun hi sanyi gashinan a fili ya kamaki
I have to call Marshal sbd yakira Dr sa'id bakida Lfy gskia.

Aje towel din hannunta tayi ta nufi waje Dan dauko wayarta sbd rawar sanyinda Naj din keyi yayi yawa ko mgn takasa yi sai idanuwanta dake cikowa da hawaye suna komawa.

Tana fita dakinta ta Isa da sauri ta dauko wayarta tadawo palon inda hajjo ke kokarin shigewa dakinta ta saka Kiran JALAL din kamar bazai daukaba sbd gabaki daya bayajin mgn da kowa a yanzu tunanin halinda cikinsa yake ciki yakeson samun nutsuwar Yi,
Daukar wayar yayi batareda yace komaiba ita Bata tsaya Jin miskilancinsaba Kai tsaye cikin damuwa tace"

Naj nata rawar sanyi kamar ma dai sanyin yariga yashigeta ta sakarwa kanta ruwan tsayi ta tsaya cikinsu,
Bansan yayama zance ba ko zanyi ka Kira Dr sa'id ka......

Kashe wayar tayi lokacinda tayi ido biyu dashi Yana shigowa palon cikin kamewa Yana sanyeda shirt ash kala da farin three quarter sai slippers din Gucci dake qafarsa ya qaraso tsakiyar palon fuska a kame kamar Babu damuwar komai aransa na Kiran da Hanifan Tai Masa ya kalli Hanifa dake kallonsa Kai tsaye yace"

Tana Ina?

Ha hannu ta nuna Masa dakin Naj din tana cewa"

Tana dakinta" kafin tai wata maganar ya juya ya nufa dakin yabi ta gaban hajjo data tsaya Jiran Hanifa tagama wayar tafada Mata 'dumi zai ragewa Naj din sanyi da tea me zafi basai Ankira Dr sa'id ba.
Hajjo na ganin ya nufa dakin ta juya ta shige dakinta bayan tacewa"

Hanifa kisa ruqayyat ta dafa Mata tea me zafi takai abata Tasha.

Shigewa Tai dakinta sbd ita yanzu al'amarin nasu su keyi itace me Jin nauyi tunda cikin Nan ya bayyana takasa yadda da a sashenta duka wannan hidimar ke wakana Dan Haka gwara tana basar dasu sbd Kar taga abinda yafi qarfin tsufanta tunda Marshal shi ko ajikinsa
Cikinma Naj kawai ke dawainiya da kunyarsa shikuwa saima ikonsa na uban cikin dayake nunawa.

Kicin Hanifa ta juya ta nufa da kanta tahau dafawa Naj tea din Wanda zata saka Masa ginger kadan.

Zaune take bakin gadon har lokacin daureda towel din tana rawar sanyi idanuwanta a rintse sosai takejin sanyin har cikin qamshinta,
Ana zuba sanyi a garin sosai ga ruwan da matuqar sanyi Kuma ta saukesu tun daga kanta takuma Jima aciki.

Bude kofar dakin akai aka turo tareda rufewa ya tsaya a gurin tareda zuba idanuwansa akanta Yana Mata kallon dayayi kwanaki Bai mataba.

Ahankali taji qamshin turarensa na gauraya dakin yana shiga hancinta,
Dan motsawa tayi ahankali tareda bude idanuwanta dasukai ja ahankali ta kalli bakin kofar zuciyarta na narkewa da wani irin Jin tanason yin kuka idanuwansu suna Shiga cikin na juna batareda kowannensu ya dauke nasa idonba.

Cikowa idanuwanta keyi da hawaye suna neman gangarowa ta lumshe idanu jikinta na sake daukan rawar sanyin.

Dan dauke Kai yayi tareda sauke numfashi ahankali kafin ya zare hannuwansa daga aljihun three quarter wandon dake jikinsa ya tako ahankali ya qaraso inda take zaune Yana isowa gabanta baice komaiba ya sunkuya zai dauketa ta dago a Dan hawalce ta kallesa daidai fuskarsa datake daf da tata fuskar numfashinsu na haduwa sosai zuciyarta taqara tsananta bugu har kirjinta dake daure da towel Yana yin sama Yana komawa qasa.

Kirjin nata ya kalla da fararen idanuwansa sbd towel din Bai wani dauru sosaiba juyi daya zai iya sawa ya zame ya dauke idonsa akai tareda kallon fuskarta dashi take kallo itama
Ya dauketa Kai tsaye tareda nufar gaban mirror da ita ya zaunar Kan kujeran gaban madubin tareda janyo hand dryer saiga Hanifa tayi Knocking kofar dakin tana cewa" ga tea din takawowa Naj.

Aje dryer din yayi tareda komawa sofa ya zauna sai alokacin yace Hanifa ta shigo.

Shigowa tayi tana kallon Marshal din batareda ta kalli inda Naj takeba sbd Karta qara Mata jin nauyi ta aje Trey din da cup na tea din ke Kai tana cewa"

Ga tea zai taimaka tasamu dumin ciki dakuma rage sanyin.

Lokacin ta juya tana cewa"

Zanje nayi waya Allah ya sauwaqa." Ta fice tareda rufe kofar dakin.

Daukan tea din yayi ya dawo inda take ya miqa Mata sai alokacin ya bude Baki yace"

Kisha.

Ahankali ta dago hannunta dake rawa ba musu ta karba takai bakinta tabude ta Dan kurba taji zuciyarta bataso zata iya Amai ta aje tana Dan rufe ido
Baice komaiba ya dauka dryer din Yana duddubawa sbd baisan ta Yaya zai iya busar Mata kanba tunda ba aikin maza bane.
Ajewa yayi dayaga zata Bata Masa lokacine kawai ga sanyin yana sake shigarta,
Wayarsa ya fidda ya saka Kiran Hanifa tana dauka yace"

Kizo ki Mata wannan drying din
Sanyin na sake shiganta banason nayi nayi nasata Jin zafi bansan ya akeba.

Dawowa Hanifa tayi dakin tana waya da mijinta har lokacin Dan Haka sama sama ta Dan busarwa da Naj din Kai sbd zuwa lokacin zazzabi me qarfi da zafi ya kamata daqyar take zaune a agaban madubin, Hanifa na gamawa ta fice ya taso yadawo ya Kama hannunta ya miqar yaga ko tsayuwar Bata iyayi sosai yakuma daukanta ya nufi Kan gadon dakin da ita ya kwantar tareda gyara Mata towel din jikinta ya nufa wardrobe dinta ya dauko Mata wata shirt me Dan kauri ya dawo bakin gadon ya tayarda ita zaune yana zare towel din jikinta zai saka Mata.
##MAMUH#

*KUYI MANAGE YAU UZURI YA DAN KAMANI ZAMU KAMA GOBE INSHALLAH.*

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

*_DM 45_*
Rintse idanuwanta tayi ahankali tana Dan juyar da kanta gefe kadan ta riqe hannunsa da hannunta da babu qarfin jiki tana Dan girgiza Masa alamar zata iya sawan da kanta.
Ba musu ya miqa Mata rigar tareda sakinta Yana komawa Kan kujera ya zauna tareda folding hannayensa Yana Dan dauke Kai daga kallonta zuwa Kan wayarsa dake vibrating na shigowar Kiran Hannah da sunanta Yafito Kan screen din wayar.

Idanuwan Naj sun sauka akan wayar takuma ga sunan me Kiran tadauke Kai tana qarasa zura rigar ajikinta ta zame ta kwanta tana rufe ido cikin tsananin azabar zazzabi me qarfi.

Tasowa yayi bayan ta kwanta yaja bargo ya rufe Mata jikinta bayan yasakawa dakin key yadawo ya zauna bakin gadon Yana Dan dafe kansa sbd sarawan dayake Dan masa.

Bai kwanta ba Sai dayaji zafin jikinta na qaruwa gashi dare yayi bayason Kiran Dr sa'id Dan Haka ya zare takalman qafarsa tareda kwanciya gefenta Yana jawota jikinsa ya shigar ya rungumeta sosai bayan ya zare rigar jikinsa itama ya zare Mata tata sbd su samu body contact din dakyau zafin jikinta ya rage.
Chapter 44 · 0% Book details