← Book details Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 59

Sashe 39

Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

No,yes I mean ta nuna bataso Amma ai na Mata mgn Kuma inaga tabar zancen.....

Miqewa yayi idanuwansa na sauyawa ya fice daga office din ya nufi motarsa Yana kokarin shiga idanuwansa a juye da wani irin mummunan yanayi saiga motar Isma'eel yashigo asibitin da gudu Yana Kiran nurses saiga dr sa'id yafito take sukai kansu sbd Hanifa da ake kokarin fitarwa motar jini ya balle Mata gabaki daya Bata hayyacinta.

Wayar Isma'eel dayaketa Kiran Marshal Bai dagaba itace tashigo wayarta daidai lokacinda zata saka hannu a takardar abortion din tana dauka cikin tsananin tashin hankali yafada Mata mugun labarin dayasata sakin takardar tana miqewa cikin tsananin tashin hankali ta fice da sauri Sarah tabita tana tambayar lafiya Amma Bata tsayaba ta karba keys din motar da kanta taja cikin tsananin gudu sukabar asibitin zuwa asibitin su Dr sa'id.

Suna parking taga motar marshal agurin Bata tsayaba sukai ciki da sauri tana Jin qafafuwanta na neman sagewa da tunanin halinda kowa zai Shiga idan Hanifa ta rasa cikinta.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

*_DM 40_*
Isarta bakin gurin yayi daidai da isowar anty Amina itama hankalinta tashe,
Idanuwanta na cikowa da hawayen tsananin damuwa da tsoron halinda Hanifa zata shiga ta juyo ahankali tana kallon Isma'eel da duk yagama ficewa hayyacinsa sbd damuwa saidai tawakkalinsa yasa yaketa kokarin natsar da kansa ya kalli Naj din kafin ya juya ya kalli Marshal dake magana da Dr sa'id cikin wani irin yanayi na tsananin zafi biyu daya hadu akansa fuskarsa amatuqar hade Babu rahama ko daya akai.

Shigewa Dr sa'id yayi da sauri yana cewa su Dan kwantar da hankalinsu Inshallah zasuyi iya kokarinsu.
Kasa zama tayi sbd tsananin tsalle da bugawar da zuciyarta keyi ta rintse ido cikin yanayi na sagewa Dan Bata fatan wani Abu ya samu Hanifa ko babyn,
Tana roqon Allah yasa Hanifa cikin Nan rabonta ne Dan tafi shaidar yanda take tsananin son haihuwa da samun baby Amma wannan ne karo na uku Wanda dagashi idan har ta rasa batajin za'a Kuma yimata wani dashen.
Matsowa Sarah tayi qafafunta a sanyaye ta kalli Naj cikin kulawa da Dan qaramin sauti tace"

Naj ki zauna Kuma ki Dan kwantar da hankalinki kema kinsan ba'a son kishiga damuwa sbd yanayinki please.

Satar kallon Marshal Sarah tayi taji gabanta yasake bugawa cikinta na Dan kadawa ta dauke Kai sbd ganin wani irin mummunan hadewar fuska da wani boyayyan fushi dayake cikin idanuwansa Yana zaune ya harde qafa Babu Wanda yacewa kala sai jiran tsammani dasukeyi.

Qin zama Naj tayi tana Dan kaida kawo ahankali idanuwanta na neman kuka Amma yaqi zuwa sbd tashin hankalinta biyu ya kasu tanajin tashin hankalin halinda Hanifa ke ciki ga nata tashin hankalin sbd sosai take sake jin tsoro da shakkar cire cikinta dayake neman mamayarta Wanda ke sake cusar Mata da kai gabaki daya ta rasa wane tunani zatai,ta rintse ido tana dafa bango sbd sarawar da kanta ke dauka Yana neman sakar Mata da jiri.

Anty Amina dake kallonta cikin kulawa tace"

Naj ki zauna Mana tunda kema zazzabin da kikai Ba gama sakinki duka yayiba karki qara Mana wata damuwa Anan idan Kika shiga cikin wani hali.

Sai alokacin ta kalli Anty Amina tanason fashewa da kuka yaqi zuwa ta Dan sake dafa bango Sarah na kamata ahankali ta qarasa kujerar kusada Marshal ta zauna tana sunkuyar da Kai har lokacin hankalinta duka baya jikinta.

Gabaki daya Babu wata alamar data nuna Marshal dake gurin yasan da wanzuwar dukkaninsu a gurin bayan anty Amina data Dan basa bakin komai zai daidaita inshallah Akan Hanifa itama bayan Kai daya gyada Mata ahankali bai samu cewa komaiba sbd a yanayinda yake ciki idan ya fitarda fushinsa da tsananin bacin ran dayake ciki kowa bazai iya tsayawa agurinba.

Ismail ma miqewa yayi yafara safa da marwa yana Dan bubbuga hannayensa dake nade a kirjinsa,
Yanason Kiran Yan gidansu ya sanar musu Amma bayason tayar musu da hankali tukuna sai ansamu Kan matsalar.
Hannuwan Naj rawa suke ta damqesu tana Dan rintse idonta daketa cikowa da hawaye Amma kuka da hawayen sun kasa saukowa tsoro ne fal aranta,
Hannu ta daga ahankali takai Kan cikinta ta dafe tana sake Shiga wani sabon yanayi,anty Amina dake lure da ita ta matso ta dafata Anatse tana kallon fuskarta da duk take bayyanarda damuwarta a natse tace"

Naj,kina Lafiya dai?

Kasa mgn tayi ta sauke Kai ahankali tana sake dafe cikin ta gyadawa anty Aminan Kai.

Dr sa'id ne ya bude kofa yafito ahankali tareda wani Dr Adebayo
Dukkaninsu suka kallesa suna kallon idonsa da bakinsa jiran Jin abinda zai fada Dr Adebayo kuwa wucewa yayi zuwa office dinsa.

Kallon Marshal Dr Sa'id yayi Yana sauke numfashi tareda ajiyar zuciya ahankali kafin ya maida kallonsa kan Isma'eel a natse yace"

Hanifa ta rasa cikin sbd ta haifi babyn da Bai Isa haihuwaba kwata kwata hakan ne yasa babyn baizo da raiba sbd baima Gama zama cikakkiyar halittaba,
Jinin ya tsaya duk da ta zubarda jini sosai Amma bama buqatan qara Mata wani jinin sbd munduba pcv dinta is normal,
ayi hakuri Haka Allah ya nufa,wannan jarabawa ce idan anyi tawakkali za'a cinyeta Kuma za'a ga ribar hakan, Allah yabata lafiya,an bi kofar baya anfita da ita zuwa dakin hutawa zaku iya samunta acan.

Sake kallon Isma'eel yayi Yana cewa"

Zaka jira mu hado maka babyn sai aje a rufe ko.

Kallon Marshal da idanuwansa suka qarasa sauyawa gabaki yayi cikin kulawa yace"

Sorry Marshal,Allah yabada hakuri yabada rayayye,
Ita Hanifan kwata kwata Babu wata matsala atareda ita yanzu saidai damuwa Dan Haka tana buqatan ku dukan.

Juyawa yayi ciki yakoma Dan hado gawar 'dan babyn yakawo.

Kowa agurin kasa kuka yayi sai Naj dakejin kukan nason taso Mata Amma yaqi fitowa ta dago jajayen idanuwanta ta kalli Isma'eel da qarfin imaninsa yasa ya daurewa zancen sosai Yana jiran fitowar Dr sa'id
Kasa kallon gefen Marshal tayi tanajin nauyin zuciyarta na qaruwa ta miqe Kai tsaye ta bar gurin ta nufi hanyar dakin datasan can za'a Kai Hanifan a  Amenity Sarah na bayanta anty Amina kuwa matsowa tayi cikin kulawa da tsananin tausayawa tana sake bawa Marshal hakurin wannan rashin shida Isma'eel dake gyada Kai cikin wani yanayi Yana cewa"

Bakomai anty Amina nagode.

Marshal kuwa Kai kawai ya gyada Mata har lokacin Yana zaune a inda yake idanuwan Nan tamkar zasuyi Aman wuta sbd baqin ciki,bacin Rai dakuma damuwar Hanifa.
Tsayawa tayi itama har akawo babyn.

Da tsananin sanyin qafa Naj ta tura dakin tashiga fuskarta na narkewa da ganin hanifar wadda tana ganin Naj din ta sauke Kai wani irin gigitaccen  kuka na zuwar Mata da sauri Naj din ta qaraso ta zauna tana rungumeta itama Bata hawayen na gangarowa alokacin.

Kuka Hanifa keyi Sosai Wanda yake fitowa daga tsakiyar ranta tareda dibbin 'daci da ciwon rashi na cikinta,
Sosai takejin wani irin radadi da zafi dama ciwo Wanda takeson kokesa idan zai fito shiyasa take kukan sosai zafin zuciyar Amma yakasa raguwa saima tsananta da quncin keyi.

Kukan Hanifan har cikin zuciyarta Naj ke jinsa sbd kukane da Bata taba irinsaba,kukane me cin Rai na Shiga zuciya,tanason Bata hakuri Amma takasa bude Baki sbd tanajin ciwon da Hanifan keji,tasake rungumeta nata hawayen na sake gudu.

Kukan datakeyi tuni yafara daga hankalin Naj din ta dago tana kallonta ta bude Baki murya a yamutse taka cewa"

Hanifa Dan Allah kiyi hkr ki daina kuka Haka Inshallah Zaki samu wani babyn,
Dan Allah ki daina kuka Haka Kinga Baki Gama warwarewa kada wata damuwar ta shigeki.......

Wani kukan me qaramin sauti yakuma zuwar Mata tana girgiza Kai cikin dasashiyar murya tace"

Naj Ina tsananin son babyna Amma Allah baiyi Zan zama uwaba.

Hanifa karki cire Rai daga rahamar ubangiji Dan Allah..."Naj tafada hawaye na gangarowa idanuwanta dasukai jajir.

Naj bakowane yakeda rabo da Sa'ar zamowa uwa ba kila Ina cikinsu duk da na dandana zamowa uwa me renon ciki ko ahakan na godewa Allah
Amma zafi nakeji da qunci cikin zuciyata sosai......kakane yaci qarfinta ta sunkuyar da Kai tanayi.

Gabaki daya jikin Naj mutuwa yayi da Tsananin tausayin Hanifan Dan kuwa ko Hanifan Bata fadaba kowa yasan zatai qunci sbd tsananin soyayyarta da son haihuwa Amma Allah ya qaddara hakan,
Sake mutuwa jikinta yayi da wannan yanayin na Hanifa ta dafa cikinta tanajin shin idan ta cire cikinta zata iya Shiga irin wannan halin na Hanifa na kuka da baqin cikin rasa nata babyn¿
Dafata Sarah tayi ahankali,Bata dagoba ta rufe idanuwanta hawayenta na gangarowa akaro na farko taji kamar qaunar cikinta ta motsa aranta tasake kallon yanayin quncin dake Kan fuskar Hanifa ta rufe ido tanajin qaunar cikinta amatsayinta na uwa,
Uwa mahaifiya zata zama,idan ta cire cikin tazo kukanta yafi na Hanifa.
Chapter 39 · 0% Book details