← Book details Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 59

Sashe 52

Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hanifa Kika Kuma tada maganar Nan Zan Saba Miki kokuma ayau basai kin shiryaba ki tattara kibi mijinki.

Najma tashi kije ki dan gyara kizo ki kaiwa mijinki abinci yanacan yauma da ciwon Kai yadawo.

Sunkuyar da Kai Naj din tayi tana kasa amsawa hakama tana kasa tashi Saida hajjon takuma maimaita zancen  kafin ta miqe ta nufi dining zata dauka takai tadawo
Hajjo tace"

Aa kindawo a gajiye ahakan Zaki?
Kije ki Dan gyara duk qamshin kwakwa ma kukeyi
Tashi kema,kuje kuyi wanka kafin taje takai Masa.

Tashi tayi ta wuce dakinta bayan tagama fadan sbd Naj tasamu sakewar wucewa wankan dakinta.

Saida hajjo ta shige kafin ta juyo ta nufa hanyar dakinta tanajin Hanifa na cewa"

Saida safe Naj.

Bata kulataba ta shige dakinta dama Kuma wankan takeson Yi har cikin ranta.
Wanka tayi tana fitowa ta saka kayan bacci riga da wado dogo har qasa kafin ta saka doguwar hijab Nayan ta shafa khumrah me sanyin qamshi ko wayarta Bata daukaba ta fito ta dauka abincin ta wuce zuciyarta na ingizata ga son sanin halinda yake ciki na ciwon Kan.

Tana isowa kofar palon sashen nasa ta tararda Hannah tsaye tana Shirin buga kofar.
Tsayawa tayi sukaiwa juna kallon mintuna biyu kafin Naj ta dauke nata idon tana juyar da kanta zuwa ga kallon kofar Shiga zuciyarta data sauya tana ingiza kanta ga juyawa ta komawarta Amma zuciyar ta hanata hakan sbd rashin sukunin ta tafi tabar Hannah din agurin,
Hannah ta juyar da fararen idanuwanta tana yiwa Naj din kallon mamaki tace"

Lafiya dai kuwa??

Dan qaramin numfashi ta sauke a boye kafin ta sake kallon Hannah da itama tsoron Allah daya kasheta da mamakin Naj din a natse cikin sanyinta batareda tabi takan abinda Hannah din ta tambayaba tace"

Bayajin Dadi ko kinyi knocking ba lallai yabudeba.

Sake kallon kayan dake jikin Hannah din tayi sbd wata doguwar straight gown ce data lafe jikinta dakyau ta fidda da shape dinta ba laifi  kanta babu komai sai wata qaramar hula data saka wadda kusan Rabin gashinta ya fito itama qamshin take fitarwa Sosai.,dauke kanta tayi Anatse kafin ta qarasa jikin kofar takai hannu ahankali ta bude kofar Kai tsaye tashige tareda rufowa tasaka lock.
Jingina tayi jikin kofar tareda rufe ido tana Dan sauke numfashin dazai rage Mata nauyin da zuciyarta tayi.

Hannah kuwa kasa motsawa tayi agurin sbd al'amarin yafara Mata yawa, zuciyarta gap take da bugawa da halinda Marshal dama wannan Naj din suke sakata,
Cikin baqin ciki da takaici dama bacin ran daya qulleta tace"

Ubanwa ya tambayeki idan baida lafiya ko lafiyarsa kalau¿
Juyawa tayi Rai baqi qirin ta wuce tanajin Kamar tatashi kowa daga bacci gidan yafito sbd masifa.

Barin jikin kofar tayi ahankali tana Dan kallon palon da wutarsa take kashe saita gurin dining ce kawai a kunne Wai AC Dake aiki ta nufa hanyar kicin tana tafiya jiki amace
Takai Kan dining ta aje tareda sauke qaramin numfashi tana Dan rintse ido kafin ta waiwaya ta kalli hanyar bedroom dinsa tana juya yanda zata Kai kanta da kanta bedroom din.

Bama kanta qwarin gwiwa tayi tareda Dan taqaita Jin nauyinta da kunyarta ta nufi dakin zuciyarta na tsalle sbd haryanxu takasa sabarwa da kanta sakewa akan duk wani al'amarin daya shafesa ko yashigo dashi ciki.

Saidata Kuma sauke numfashi da ajiyar zuciya kafin takai hannu ta Murda kofar dakin a natse ta bude tana kallon Dan duhun daya gauraya dakin sbd wutan a kashe sai hasken bedside lamp na gefe daya dake kunne Wanda yabata Daman ganin fuskarsa Dake bacci cikin nutsuwa da alama baccin yasa ciwon Kan tafiya.

Kasa dauke idanuwanta tayi daga kan fuskarsa zuciyarta na gauraya da dukkanin nutsuwa da wata irin alkunya duk da bacci yake.

Bakin gadon ta tsaya saiti da kansa tareda durqusawa takai hannunta kan goshinsa ahankali ta Dan dafa saikuma ta dauke da sauri tana miqewa tsaye zata juya taji anriqo hannunta.

Kasa waiwayo tayi saima idanuwanta data rufe Jin kunya da mamakin ba baccin yakeba kenan.
Batareda ta waiwayoba ta bude Baki a natse cikin qaramin sauti tace"

Hajjo tasa akawo maka Abin......

Cikin muryar bacci da 'yar kasala ya katse da cewa"

Kullum komai hajjo ke sakaki Yi,yanxu kiyi Wanda hajjon Bata sakakiba ki hadamun ruwan zafi zanshiga cikinsu nayi wanka tunda nayi bacci yanzu jikina zai sake.

Sakinta yayi Yana tashi zaune ya jingina jikin gadon Yana kallon qatuwar hijabin dake jikinta.

Kasa juyowa ta kallesa tayi ta bude Baki ahankali tace"

Hajjo zataga na Dade.

Batareda ya kalletaba ya zuro qafafunsa daga kan gadon yana zare qaramar shirt din Dake jikinsa dukkanin jikinsa ya bayyana ya nufi toilet din Yana cewa"

Ki koma gurin hajjon idan nagama zanzo da kaina gabanta na daukoki da hannuwa.
Shigewa toilet yayi yabarta tsaye tana bin kofar daya shige din da kallo
Ta kujera ta zauna tana tunanin tsaf zai aikata abinda yafada din Dan Haka zata jira yafito taji me zatai masa ta koma.
##MAMUH#

********************
*_MG's skin care_*
Hi team no makeup
Ina kanawa mutanena🗣️
Shin Ina masoyan mg's ina ma'abota ado da kwalliya kusaurara kuji dame nazomuku 💃
Nasan dayawa kunsiya kayanmu Kuma kunshaida yadda suke gyaranjiki cikin lokaci kalilan Koda iyasabulun kikayi anfani dashi sekinyaba balle kankat wato beauty kit dinmu toh inamaitabbatar muku cewa ynx kayanmu ankaramasu kayayyaki Wanda zasu Kara gyara fata fiye da tsammanin Mai tunani within 2weeks zakicanza kiga duk inda kikayi se anbiki d👀 domin ynd fatanki zaikoma Shar kamar madara bawanda zemiki kallo daya yadauke idanunshi😃😍
Hajiyata shin menene matsalanki, pimples ne?
Spot? sunburn,acne, stretch marks, knuckle, wrinkles, Black head,ko kinshafa Maine yabatamiki jiki
Inamai shaidamiki cewa ynx ne lokacin dayakamata kiyake dukkan wadannan kema kidinga fita sakayau abunki baruwanki da kunshe fuska ko kice sekinyi makeup hjy fita zar abunki kinuna ainihin natural beauty dinki😍domin kayanmu gbdynsu organic ne babuna bleaching zssu sa ki haskaka fatarki tayi ta kyalli kamar madubi ze fiddomiki d ainihin natural beauty dinki ne😘kunaji barin fadamuku wani Abu billah wannan prdcts damuke dashi ynx Koda kudinki seda rabanki domin duk sunzarce nabaya ankaramasu abubuwa dayawa masu matukar anfani agyaran fata🤗Ina Wanda basasan shafa Mai koda sabulun kawai kike anfani dashi inamai tabbatar Miki zkg ynd jikinki zekoma luwai luwai😘
Soap:3k
Beauty kit:12k
Chat:08062991549
07066210195
Call :07046881166
08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare
amare inakara shaidamuku duk wacce tayi anfani d kayanmu Bata bukatar gyaranjiki sedai ra'ayi🥰
Masoya kunanan kauna yanda nakwashe aljihu domin nafarantamuku kuyi achieving goal dinku pls Nima kunanan kauna kufarantamin😪🤠aljihuna yafarfado hilis karnakoma kauyenmu🥲
Yar shawarmannan duk nasaba😤 hilis kugarzayo arabani da kaya🤝
Nd guest what🤩
Duk Wanda yy siya 10k zuwa sama zesamu Karin gift😃
Pamper your skin🧖‍♀️
Shine like a bride👰🏻
Glow🧚🏻‍♀️

*********************************
*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

*_DM 50_*
Tunani tashiga na son tafiya Amma tana shakkar maganarsa datafi kowa sanin zai iya aikata abinda yafada din Wanda ba hajjo kawai ba kila ko Dad Alfa zai iya ganinsu ta samansa idan suka fito harabar gidan ahakan Dan Haka ta daure tasake bawa kanta danganar zaunawa jiran nasa..
Bude kofar toilet din yayi yafito daureda towel a qugu,ta dan dauke kanta tana kallon wani qaramin farin frame me kyau Dake gefen kujeran datake hotonsane tareda Hanifa aciki suna wata qasar turawan Wanda kayan jikinsu ne ya tabbar Mata da hakan ta qurawa fuskarsa ido tana sake qare Masa kallon da bazata iya yimasaba a fili dukkanin zuciyarta da gangar jikinta na tsayuwa akan Abu daya data kasa yadda yasameta wato shine SO,
Son JALALUDDEEN,qanin qawarta dasuka taso tare,
Tayaya?
Yaushe?
Kuma garin Yaya duk hakan ya shammaceta yashige......

Zama yayi kusada ita Yana zuro fuskarta kusada tata Yana kallon hoton data zubawa idon fuskarta na tona asirin zuciyarta ya bude Baki zai magana qamshin mouthwash dinsa na mint ya daki hancin Yana shigewa ta zuciyarta tasake raunana a hankali yace"

Ni din daine qanin qawarki aminiyarki Kuma mijinki uban babyn Dake cikinki,
Yaya??kin bada garine kokuwa inada sauran aikin daban qarasa?" Yafada Yana zura hannunsa cikin hijabinta ya Dora kan cikinta dayayi tauri ya Dan taso Yana shafawa fararen idanuwansa masu kwarjini Kan fuskarta Yana Jin qaunarta da Sonta daya riga yayiwa jarumtarsa da kemewarsa illar da Babu gyara.

Yanda yake shafa cikin cikeda kulawa yasata kasa jurewa ta dago ta kalli fuskarsa da har lokacin ita yake kallo cikin yanayi kulawa da so me girma.

Babyna yafara motsi?" Ya tambaya yaba kallon cikin.

Ahankali ta girgiza Masa Kai jikinta na mutuwa da yanda yake binta da wasu kallon kasalan da Bata Gama sakinsaba shima.

Amma Yana lafiya ba right?

Da mamakinsa take sake kallonsa Dan tarasa ta Yaya babu ruwansa Kai tsaye yake maganarsa duk yanda tazo Masa arai Kuma ko agaban waye.

Kama lips dinta yayi da hannunsa ya shafa Yana Dan daga mata ido alamar ta amsa Masa tambayarsa.
Dole ta bude Baki ahankali tace"

Lafiya kalau.

Kissing hannunta yayi Yana cewa"

Hakan nada kyau,yanzu muje kiban abinci inajin yunwa.

Miqewa sukai ya zare Mata hijabin ya aje a kujeran dasuka tashi suka fito Palo tana gaba Yana bayanta hannunsa riqeda Nata Yana biyewa tafiyar saibinta datakeyi a natse da sanyi Wanda ke sake shigarda ita ransa sbd a ra'ayinsa Yana qaunar mace me sanyi da nutsuwa shiyasa tayiwa zuciyarsa kamunda ba fili tako Ina.

Zama yayi Yana duba agogon yaga qarfe goma Sha daya takusa Dan Haka yace kadan zata saka Masa bayason nauyin abincin tunda dare yayi har Haka.
Kadan din tasaka Masa takawo Masa drink tana kokarin komawa ta zauna ya janyota ya zaunar a Kan cinyarsa Yana cin abincin da ita ahaka ta ringa binsa da idanuwa tako Ina Yana sake cikata da mamakinsa da girman abubuwan dayake Wanda basa boyuwa.
Chapter 52 · 0% Book details