← Book details Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 59

Sashe 6

Deen Marshall Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

No din Dr sa'id Naj takira saidai Bai daga ba Dan Haka tayi tunanin Yana aikine kokuma yashiga CS Dan yawanci hakan kesashi barin waya office Dan Haka Bata Bata lokaciba tasake hada ruwan dumi ta gasawa Hanifan jikinta tareda sake Bata magani gashi duk yanda taso Hanifan taci abinci takasaci qrshe dai da kanta ta hado Mata ruwan dumi da Madara da Zuma tasamu ta iya Sha tayi bacci.

Saida Hanifan tayi baccin tasamu ta tube tafada toilet tayi wanka tayi sallah tafito palon hajjo ta nufi dining ta zubo spaghetti kadan da salad tadawo ta zauna gurin hajjo suna Yar firarsu akan rashin lafiyan Hanifan da tuni Dad dinta yafara Kira sbd hajjon data fada Masa
Shima Isma'eel mijinta tun Naj na office yake Kira sbd Hanifa Bata daukan wayan kowa.

Tana Gama cin abincin kicin kenan saiga ummanta tashigo tareda zainab Yar gaban goshinta ayanzu kenan 'yar anty Amina.

Zama umma tayi ita Kuma zainab Naj ta miqa Mata plate din hannunta tana cewa"

Ki Kai kitchen.

Sosai umma ke girmama hajjo tamkar mahaifiyarta Dan Haka firarsu suka Dora daga nan Naj na gefe tana aiki a laptop dinta saiga Kiran Abaas yashigo wayarta ta dauke ido daga kan wayar tana cigaba da aikinta yasake Kira Bata daukaba har so uku ko kallon wayar Bata sake yiba.

Sai yamma sosai bayan ma Hanifa ta farka su umma suka tafi Takoma gurin Hanifan wadda video call din marshal yashigo wayarta daidai shigowan Naj din.

Qarasowa tayi gurinta tana Kiran sunanta cikin taushin muryarta tana cewa"

Yaya wuyan?

Nuna tayi Mata da wayarta ahankali tana cewa"

Please ki amsa mun Kiran.

Kallon wayar Naj tayi taga sunansa baro baro ajiki takai hannunta ta dauka wayar tana dawowa gefen Hanifan ta zauna ahankali tareda daukan Kiran ahankali kyakkyawar fuskarsa ta bayyana akan wayar Yana zaune palon gidansa dake _Honolulu Hawaii US_ sanye cikin black three quarter da black armless shirt dasuka matuqar bayyanarda hasken fatarsa data Gama renuwa acikin hutu da lafiya sai daukan ido fatar jikinsa takeyi sbd yanayin kayan dake jikinsa dauke Kai Naj tayi tareda miqawa Hanifa wayar tana tashi daga gurin Dan gidansu takeson Shiga Dan Haka Kai tsaye ta fice.

Wayarta ce kawai a hannunta ta fito daga gidan ta nufi kofar gidansu ta shige ta nufi sashensu Kai tsaye saidai tana Shiga ta tadda Dattijo tsaye ga Dadah a zaune hakama ummanta dukkaninsu suka zubo Mata ido Banda ummanta da abun duniya ya taru yayi Mata yawa idanuwanta sun kada sunyi jajir da alama dai ba lafiya ba.

Qarasowa tayi cikin nutsuwa tace"

Dattijo Ina wuni,
Dadah barka da yamma.

Ko kallonta dadan bataiba sbd wannan karon tsaf tagama shirya duk wani rashin arziki da Naj din Bata tunani akan wannan maganar.

Kallonta Dattijo yayi da kyau Yana gyara tsayuwa da gyaran murya yace"

Ki saurareni da kyau kiji abinda Zan fada Miki sbd nafadawa mahaifiyarki kalma bayan kalma Amma Naga kamar ke din kinason watsar da maganar Kamar yanda kike watsi da masu neman aurenki,
Nafada naqara fada wallahi tallahi wannan karon kika Kori abbas da halinki yace yafasa auren Nan wallahi duk Wanda nasamu aura Miki zanyi bazaki maida wata a gidan Nan ba,
Yafara gajiya da halinki yazo ya sameni dazu ransa amatuqar bace na bashi hakuri akan za'a matso da bikin Nanda wata daya ma ayi a huta Dan Haka acikin watan Nan daya Kikai Masa abin dayasa yafasa wannna auren keda mahaifiyarki ku shirya hukuncina dazai biyo baya.

Daga fadar Haka ya juya ya fice Bai qara da komaiba sbd bacin ran al'amarin auren Naj din dayake kaisa maqura.
#MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_Ina masoyan Kuma mabiya littaffan zafafa biyar wainda sukai fice gurin kawo muku littafansu masu tsafta da ilimantarwa tareda nishadantarwa,_*
*_Wannan shekarar sun dawo muku da wani sabon salon Kamar kowane zuwan inda suka kawo muku dada'dan labaransu da bazaku taba Dana sanin biya ba,_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

*_DM 6_*
Shiru ummanta tayi zuciyarta na suya da bacin rai da damuwa hadda sirkin takaicin Naj din wadda take ganin duk itace take qara tsimar da duk wani bacin Rai dake faruwa tsakaninta da Dattijo da Dadah wadda ita kaf duniya Bata ganin laifin kowa akan rashin auren Naj face ita mahaifiyarta sbd ganin suke idan su Naj tana Shure maganarsu ta lalacewar da neman aurarrakinta keyi it's uwarta ta tsaya ta ganar da ita Amma Ina ganin suke itacema take qara daure Mata acewarsu hamshaqin dayayi mugun ci ya tada wuya suke jira Wanda Allan daya halicceta yafita sanin cewan wlh a duniya tafi kowa farin ciki da qaunar ace yau taga 'yarta Naj tayi aure kodan irin daukan ido da fizgar maza datake dashi Amma saigashi qaddara ta Allah tasa duk kyawu datafi Yan zuriar gidan kowa yayi aure yabarta hatta qannenta da dama wainda suke Yan uba dama na dangi sunyi aure sun barta.

Ahankali Naj din ta juyar ta nufi dakinta ta Murda kofar ta bude tashige a Karo na farko dataji zancen Dattijo akan rashin aurenta ya daketa badan komaiba sai Dan yanda ako yaushe ake Dora laifin akan ummanta wanda keda kalamai na cin zarafi.

Bakin gado ta zauna ahankali tareda sauke numfashi tana Dan dafe goshinta ta lumshe ido tana tunanin itafa duk yanda akaso tayi aure da yanda ake ganin kamar taqi auren bazata jawo namiji da aura ba da qarfi Amma meyasa su basa gane hakan?
Shin menene akewa maza su tsaya su aureka Wanda ita Bata saniba ko shine yasa ake fasa auren nata bayan dai tasan acikin wainda sukai neman aurenta suna fasawa kowanne tana Dan iya nata kokarin gurin kulasa da Yar sake fuska tana iya kokarinta gurin aje miskilancinta ta kulasu yanda ya kamata Amma duk da hakan suke fasa aurenta bayan kowannensu Saida ya Aiko magabatansu dayanma har fara bikin anyi aka fasa sakamakon Wai yagano gabaki daya taba sonsa Bata taba sonsaba kawai aurensa zatayi Dan Ana cewa Bata aure.
Wannan shine yafi konawa Dattijo Rai aduk cikin masu neman aurenta suna fasawa sbd har Gama komai anyi Amma zancen ya watse tun akan wannan al'amarinta yaqara baqanta ransa shiyasa yanzu ya dage ya tsayawa Abaas sbd kada shima ya fasan duk da kuwa yagama karantar halayen Abaas sunada matuqar wuyar zama sbd zafin ransa yasa wani lokacin harshi rufe ido yakeyi Yana fada Masa magana musamman daya Gama gano sun Kai maqurar matsuwa a son aurarda Naj dayasa suke lallabashi shiyasa yasamu damar yimata duk kalar abinda yaga dama sbd yasan kome zaiyi baza'a fasa auranba tunda auren akeso ido rufe.

Anty Amina ce tashigo dakin ranta Babu Dadi itama sbd tsakani da Allah suna Jin zafi da 'dacin dukkanin wani fadan cin zarafi da akewa mahaifiyarsu saidai Kuma Babu yanda zasuyi tunda mijine agareta hakama Dadah uwace to Amma Kuma meye laifinka Kai idan anqi aurenka¿

Cikin nutsuwa anty Amina ta zauna kan kujeran madubin dakin ta kalli Naj din a natse tace"

Najma hakuri Zakiyi ki daure ki Kuma qara daurewa da halayen Abbas ayi auren Nan ki huta da wannan fitinar umma ma ta huta da wannan fitinar muma masu gani zuciyoyinmu na daci mu huta,
Idan Kuma kina ganin bazaki iya auren Abbas din ba ki dakatar dashi Kai tsaye saiki bawa Dr sa'id damar fitowa sbd yamafi Abbas din cancanta da mutunci tareda nutsuwar aura tako Ina,
Auren Abbas tabbas idan ba wani rahaman ubangiji babu ta inda zaku samu nutsuwa tako Ina Dan zafinsa yayi yawa kekuma miskilancinki yayi yawa zaku wahala ku duka.

Kallon anty Amina ta dago tayi da fararen idanuwanta dasuka Dan sauya Wanda iya Nan kake iya ganin damuwarta sai Kuma ahankali ta saki Dan guntun murmushi tareda bude Baki tace"

Nagode anty Amina.

Shiru sukayi tsawon mintuna biyar kowa kowa da abinda take tunani cikin ransa kafin ta miqe ta fice daga dakin Kai tsaye ta nufi dakin ummansu dake zaune kan kujera shiru da alama damuwace take cinta bakuma yanda zatayi tunda itama tayi iya yinta bazata jawo mijiba ta daurawa Naj din aureba duk abinda sukeji Dole Haka zasuyita daurewa suna hadiyewa har Allah yakawo ranar auren.

Qarasowa tayi gaban umman wadda sai alokacin ta dago a sanyaye ta kalla Naj din ta dauke Kai tana cigaba da tunaninta.

Zama Naj tayi gaban umman tareda riqo hannayenta tana kallon fuskarta ta bude Baki ahankali tace"

Umma kiyi hakuri kadaki saka damuwa aranki,kinada ilimin addini umma kinsan cewa aure lokacine da ubangiji ya dibar maka wlh idan lokacin Nan baiyiba bazakayiba meyasa kike damun kanki da abinda su Dadah ke fada bayan kinsan kinamun addua Kuma insha Allah zanyi auren kila Wanda Allah ya zabarmun ne a mijin Bai bayyana ba kokuma kila lokacin ne haryanxu baiyiba da saura idan Kuma auren ne Allah baice nayiba harna bar duniya Yaya zakuyi da hukuncinsa?
Umma addua kawai Zakiyi Allah yasa hakan shine mafi alkhairi gareni dakuma iyayena.

Kallonta umman tayi idanuwanta na kadawa jajir sbd tabbas su yayanta basusan irin mugun zama da cusgunawa tareda tozarci da hantarar datake samu daga dattijon har Dadah akan wannan al'amarin,
Ta dauka,ta hadiye,ta danne,ta shanye,ta boye duk wani mugun wulaqanci da tozarcin dasuke Mata akan al'amarin Wanda matsi da fitinarsu yasa taji Kota Yaya sotake Naj din tayi auren kowama ya huta kishiyoyi masu Mata dariya su daina Yan gidan masu zundenta su daina,yan matan gidan masu cewa ilimin Boko da aikin office yasa Naj taqi auruwa duk kowa ya daina a zauna lafiya,
Da wanne zataji gata da tsohuwar bazawara a Naj din.

Sake kallon Naj tayi da idanuwanta dake jajir har lokacin ta bude Baki Kai tsaye da sanyin murya tace"

Najma nasan aure lokacine Amma Kuma Allah yakawo Miki mijin meyasa bazaki lallabashiba har ayi auren tunda dai haryanason auren naki¿
Abbas dinnan duk halinsa dakike gani idan anyi auren lallabashi Zakiyi zai sauya shikenan kowa ya zauna lafiya.
Chapter 6 · 0% Book details