← Book details Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 46

Sashe 9

Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

.............Yau 6angaren mama mukaje cin abinci sa6anin da damukeci a 6angaren yayansa.
Muka shiga da sallama.
Tana zaune akujera mai zaman mutum biyu, k'yak'yk'yawace itama fara tas, tana matuk'ar kama dasu doctor, idan bama kasaniba saikace itace ta haifesu.
cikin fara'a taďago tana amsa mana sallamar, ta ďora dafaďin lale da ďiyata, zonan kinji.
Cikin jin kunya nak'arasa wajenta, kusada k'afafunta nazauna, na ce, "ina yini?.
Ta amsa da lafiya lauw ďiyata ya bak'unta?".
Nayi murmushi batareda na amsaba, suma sauran suka gaisheta.
Bayan an gama gaishe gaishe muka ci abincin rana anan, sanan muka dawo falon aka sake zama.
Doctor ya ce, "Saudat".
Na ce, "Na'am".
Ya gyara murya to kinga family ďina kamar yanda na sanar dake abaya, kuma kema yanzu kinzama 'yar cikin wannan family ďin.
Da farkodai ga mahaifiyarmu wadda muke kiranta mama, ya nunan yayansa wanan kuma shine yayana Mansur, muna kiransa yaya, wanan itace matarsa ina kiranta aunty, yanuna matarnan dabatiminba.
Yacigaba waďanan kuma sune yaranmu Hadeeza da Marwan.
Dan haka ina rok'onki ki girmama family ďina kamar yanda kike girmama naki, gaba ďaya family ďina suna sonki suna farincikin kasancewarki acikinmu.
Kaina yana k'asa na ce, "insha ALLAHU zaka sameni yanda kake buk'ata, kuma nima inason family ďina nabiyu, nayi alk'awarin zan zauna da kowa lafiya, kuma ina matuk'ar farincikin kasancewa daku nima.
Ya ce, "to Alhmdllh".
Nakula dukansu maganata ta burgesu, musamman dasukemin kallon k'aramar yarinya mara wayau, amma sai sukaji zance raďam kamar wata babar mace.
Mama ta ce, "mungode ďiyata ALLAH yay miki albarka kinji, yakuma bamu zaman lafiya da zuri'a ďayyiba.
" Duk suka amsa da amin".
Amma bandani.
Yaya ya ce, "to aini duk abinda zance kunriga kun faďa, saidai na ce, "ALLAH yabamu zaman lafiya.
Nanma akace amin".
Aunty kam batace komaiba, da doctor ya ce, "auntynafa mizakice??.
Ta ce, "a'a ni banida abin faďa, wanda kuka faďa yawadatar.
Nakula kamar maganar bataima kowa daďiba, musamman yaya, deexerh ma baki naga ta ta6e tareda gallama aunty harara.
Daganan hira aka cigaba dayi, wadda sukaďai suke abinsu bandani, itama auntyn saita gadama take saka baki.
Munďan daďe muna hira daga baya suka tafi sallar la'asar, nima muka tafi 6angarena nida deexerh.
Inason deexerh kasancewarta k'yak'yk'ya nutsatstsiya, gata alamunta suna nuna mai hak'urice da kawauci.
Muna idar da sallah muka dawo falo domin yin kallo, muna nan zaune doctor yadawo, yashigo da sallama muka amsa.
Kusadani ya zauna yana faďin kundaiyi sallar ko?.
Atare muka amsa da eh munyi.
Ya ce, "masha ALLHU".
Namik'e nakawo masa ruwansha, cikin murmushi yakar6a yana faďin ALLAH yay miki albarka.
Na ce, "amin ngd".
Deexerh ta shagwa6e fuska, uncle anbamu aikifa tun wancan satin, kuma gobe idan ALLAH yakaimu za'a amsa, nikam nakasa yin nawa.
Dictor ya ce, "haba my daughter keďin aiba abinda zai gagareki saboda nasan kwakwalwarki akwai jaa.
ALLAH uncle bawasa nakeba.
Okey, tojeki ďakko nagani.
Da gudu tafice daga falon, yayinda shikuma yadawo kujerar dana koma, yazauna kusadani tareda rungumoni zuwa jikinsa.
Ina masifar son turaren doctor dan haka nak'ara kwantar da kaina ajikinsa ina shak'a.
Shikuma yasake nutsani sosai a jikinsa, ahankali yafurta my iman ina k'yaunarki dayawa wlhy.
Nima na ce, "ina k'yaunarka doctor.
Da sauri yaďago fuskata yana kallo, yak'ara k'ank'ance idanunsa yana k'aremin kallo kasa2, da gsky Imaniiii!!!??.
Yanda yaja sunan nawa saida tsigar jikina tatashi.
Na ďaga kai ahankali".
Yasaki k'ayataccen murmushi, ashe yau zaki amince mukwana gado ďaya kenan?, saboda na nuna miki tsantsar k'aunarki dake kwance acikin jinina da zuciyata.
Kaďan naďago ina kallonsa, na maida kaina da sauri dan ganin ya kafamamin idanunsa......ahankali ya matso da fuskarsa kusada tawa danufin bani sumba sai deexerh tashigo ďakin.
Yay saurin janye fuskarsa yana 'yan kame2 narashin gsky, yabani dariya amma saina gimtse nima nayi saurin tashi daga kujerar na canja wata.
Deexerh tak'araso kusada shi ta zauna ta bashi littafin nata.
Kar6a yayi yana satar kallona, nikam kaina yana k'asa.
Bayan yagama dubawa ya ce, "my dee....bari nagaya miki kiringa rubutawa, babu musu deexerh tayarda dan kwakwalwar tata tanaja yanda yakamata.
Ina zaune ina kallonsu yana faďa mata tana rubutawa har suka gama, yakar6a yagyara mata inda batayi daidaiba.
Ya ce, "wai ina Marwan?."
Deexerh ta ce, "yana ďakin mama uncle barci yakeyi.
Barci da yammarnan haka?.
Ta ďaga kai alamar eh.
Baice komaiba yamik'e yashige ďakinsa, mukuma muka cigaba da kallo.

Haka rayuwar take tafiya, ina gidansu doctor amatsayin amarya amma ta nesa, dan babu wata alak'a dake tsakanina dashi.
Har yanzu bana shiga kicin aunty take mana girkin gidan itada 'yan aiki.
Komai na rayuwar gidan yana tafiya yanda yakamata, saidai matsala ďaya nake fuskanta itace auntynsa, nakula ko kaďan bata sona agidan, tana nunamin abubuwa dayawa kawaidai ina sharewane.
Kuma banta6a faďama kowaba, dan ba itabace agabana.
Ana cikin haka kiran gaggawa yasamu doctor awajen aikinsa, dan haka yashirya yatafi badan yasoba.
Ranar dazai tafi harda kuka nayi kashir6an mama na lallashina.
Bayanda zanyi dole na hak'ura, deexerh tacigaba da tayani kwana, kodayaushe muna tare, dan haka shak'uwa ta musamman tashiga tsakanina da ita.
Kullum kuma sai munyi hira da dictor ta waya indai yasamu lokaci kunsan soja sai ahankali.
Wani abin mamaki shine tunda nazo gidan banyi al'adaba, dan haka babu zancen ciwon mara.
Hakan yayimin daďi, duk wata kuma sai doctor yatanbayeni, cikin jin kunya nake cemasa banyiba.
Ana haka doctor yadawo a safiyar wata juma'a.
Babu wanda yafaďama zaizo saidai muka gansa kawai, munyi farinciki sosai da ganinsa dan watansa na uku kenan da tafiya.
A6angaren mama ya ara sauka.
Sai bina da kallo yake cikin mamaki dan ganin nayi k'iba kai harma da k'ara tsawo.
Nikam duk kunya ta dabaibayeni dan ganin irin mayen kallon da yake bina dashi ko kunyar mama bayaji bare aunty..
Bayan angama gaishe2, yaci abinci yak'oshi, sannan yamik'e yana faďin mama bari naje nayi wanka na huta kafin lokacin masallaci.
Mama ta ce, "to auta afito lafiya.
Aunty ta ce, "nibazakamin sallamaba kenan, ko kallonta baiyiba yafice daga falon mama yana faďin ke asuwa kuma?.
Dukda ta dake nasan maganarsa ta 6ata mata rai.
Mama ta kalleni iman tashi kije wajen mijinki mana.
Akunyace namik'e nafice, dan dama kunyartace ta hanani bin bayansa.

Kutashi muyi sallah ko sisters.
Xoxo da Reefat suka mik'e kowa baiso aka katse labarinba.
Amma damun idar da sallah zakicigaba ko??, xoxo tafaďa tana bin iman da kallo.
Insha ALLAHU my hafsy zan cigaba damun idar..................✍🏻

Am busy 😂👌🏻

Luv u oll my fan's
((S))......2017
Battery low 🔋😁👌🏻

.a
[8/6, 6:00 PM] mrs bilkisu: *_________________________________*
*BAN SAKETA BA*
*__________________________________*
*NA*
*BILKEESA IBRAHEEM*
*{bilyn Abdul}*
*___________________________________*
https://mrsbilkisa.blogspot.com

_Sadaukarwa_~*ya Abdul {city phone's}*

*MIYA KAMATA NAYI??.*
_amatsayina na *MUSLIMI* baidace daniba nashagala da duniya da abinda kecikinta, a *DUNIYA* ake neman lahira, to tayaya zan nemi tawa_ *LAHIRAR?*.
_mun shagala aduniya, kalon *FILM* karatun *NOVELS* awaya zuwa *biki*.......da sauransu sunsa mata dayawa mantawa da zan *MUTU* na riski *"UBANGIJINA"* ya salam, 'yar uwa ringa tunawa da mutuwa mai zuwa babu ďan aike, ringa tunawa da *sallah* ringa nafila, zikiri akowace rana, karkibari nishaďin duniya yasaki dana sani awata rana mai cike da *hargitsi,* tsarama kanki lokaci yanda ke da mijinki da 'ya'yanku zaku amfana, a duniyarku da lahirarku, duk wanda yay asarar *aljanna* amatsyinsa na *musulmi* to dolene atayashi kuka da jaje_.
_muhaďu agaba domin jin yanda yakamata ki tsara_ *Duniyarki 'yar uwata*_domin keda *zuri'arki*ku amfana_ *a lahirarku*
*ALLAH yasa mugane*.

~page.......~1⃣0⃣.

*............*da sallam nashiga falon babu kowa alamun *doctor* yana cikin _bedroom_ kenan.
Dukda inajin kunya wannan bai hanani nufar ďakinba, nashiga da _sallama_.
Yana tsaye atsakiyar ďakin yana k'ok'arin cire kayansa, yajuyo ahankali yana kallona, nikam nayi k'asa da kai saboda kunyarsa danakeji.
Yasaki _murmushi_ mai k'yatarwa, ahankali ya ce, " *my iman* k'araso mana.
Nak'ara k'asa da kai saboda kunya, na ce, "bari naje falo idan kagama saina dawo, wlhy bammasan kana shirin wanka bane.
Takowa yayi cikin takun k'asaita har inda nake tsaye.
Nikam jinake tamkar na zura da gudu, amma babu dama.......kusantowarsa gareni tasa na ďago da sauri muka haďa ido.
Nai saurin maida kaina k'asa.
Baice min komaiba sai kama hannuna dayayi muka k'arasa cikin ďakin sosai.
Ya zaunar dani abakin gado sanan yacigaba da cire kayansa.
Araina na ce, "waishi doctor baisan inajin kunyarsa bane?.
Ina nan zaune harya gama cire kayansa, ya k'araso yazauna kusa dani dagashi sai gajeren wando.
Yaďan rungumoni jikinsa yana magana ahankali tamkar mai raďa ko baisan tada yaro mai barci.
_farin cikina abar alfaharina, har yanzu kunyar tawa bata k'arebane?_.
Maimakon nabashi amsar tambayarsa sainace kadawo lafiya?.
Yakama hannuna danake wasa dashi yaďan matsa, naďago da sauri ina kallonsa dan naji zafi.
*Ya ďaga min gira*
Miyasa baki bani amsar tambayataba??, saikika sakko taki tambayar??.
Nayi murmushi wanda yakeso yaga nakasance akoda yaushe inayi, amma ina niďin _muskilancina_ bazai barniba.
To kayi hak'uri nafaďa atak'aice.
To nahak'ura *saudat* nasameku lafiya?.
Lafiya k'alau.
Ya aiki?.
Aiki *Alhmdllh* saidai kewarki da begenki sunta addabata musamman alokacin barci.
Ban bashi amsabama yanzu.
Ganin haka yasa yasake matseni sosai ajikinsa, saikuma nafara masa rawar jiki, nakan bashi mamaki idan yaga nashiga wani hali alokacin daya haďani da jikinsa, amma saiya basar.
Yamik'e tareda mik'ar dani tsaye, zomuje ki haďamin ruwan wanka.
Chapter 9 · 0% Book details