Sashe 2
Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
SAUDAT SULAIMAN UMAR, shine cikakken sunana kamar yanda kuka sani, amma ana kirana da iman kasan cewar naci sunan kakata ta wajen uba, mu uku iyayenmu suka haifa, Aunty Salma itace babba saini saikuma auta Shamsuddeen muna kiransa da deeni.
Asalinmu mu 'yan jihar katsina ne a 'karamar hukumar musawa, aikine ya kawo Abbah kano.
Aunty salma ta girmeni sosai gsky dan tsakanin mu akwai mutum biyu amma sun rasu, ni 'yar gatace agidanmu saboda kasancewar naci sunan kakata dan haka Abbah yake jidani sosai, to itama gwaggo haka, inada muskilanci dan bakowa nake kulawaba shiyyasa natashi banida 'kawaye, lokacin dana gama primary ne muka dawo kano, ita kuma aunty Salam ta kammala secondary ďinta.
A nana kano taci gaba da karatunta a FCE kano, nikuma secondary, deeni kuma yacigaba da primary kasancewar mahaifinmu ďan bokone, balaifi munada hali iya gwargwado dankuwa ba'a kiramu talakawa ti6isba, komai muka bu'kata mahaifanmu suna mana iya bakin gwargwado.
Ina js 2 akayi bikin aunty salma da ya Abdu'majeed wani ďan uwanmune dake can katsina, shekarar su biyu a Kt aka dawo da ya majeed kano a wajen aiki, zuwa sannan sun haifi ďansu Bello suna kiransa Affan saboda sunan baban ya majeed ne.
Agidanmu suka fara sauka, bayan kwana biyu suka shirya komawa gidansu sanan an kammala gyarawa.
Ya Majeed ya bu'kaci su tafi dani nayi musu kwana biyu tunda muna cikin hutu, da Abbah ya'ki amma dasuka dage saiya yarda akan sharaďin danayi sati ďaya zan dawo gida, ba musu suka amince..
Ranar adaren muka tafi, gidan ya haďu dan ya Majeed ya gyarashi da 'kyau.
Kwananmu uku da zuwa gidan ya majeed natashi da matsanancin ciwon ciki, haka na rin'ka kuka ina kiran gwaggo da Abbah, dan tunda nake ban ta6a ciwo mai kama da wannanba.
Aunty Salma tashiga ruďu gashi ya majeed baya nan yafita aiki, tayi 'kokarin kiransa a waya ta shaida masa halin danake ciki, ya ce, "gashi nan zuwa dama baiyi nisaba.
Cikin minti 15 ya Majeed ya iso, bai jira komaiba ya ďaukeni muka nufi mota, aunty Salma ta biyomu abaya, a bayan motar yasakani aunty Salma tashiga ta ri'keni ya amajeed yaja motar muka tafi asibiti.
Waya yaďauka yakira wani abokinsa dake aiki a asibitin kansa, muna zuwa akayi mana tarbar gaggawa, aka kuma bamu taimako na musamman.
Sai wajen 'karfe uku na yamma na farka, aunty Salma ce zaune akusadani sai kuma ya majeed zaune akujerar dake gefen gadon.
Ahankali na buďe ido ina kallon silin, aunty Salma ta ce, "iman kin farka?, kai na ďaga mata alamar eh, ya majeed ya ce, "sannu iman ya jikin naki?, na ce, "da sau'ki yaya, ya kuma faďin yanzu ina yake miki ciwo?, ahankali na ce, "yaya babu ko ina saidai inajina akan laima.
Aunty salma ta ce, "laima kuma?.
Na ce, "eh.
Aunty salma tasaka hannu a 'kasana saiga jini, ta ce, "jini kuma iman? miya sameki haka?, da sauri ya majeed ya ce, "jini kuma?, aunty salma ta ce, "wlhy kuwa yaya jini, ya mi'ke kinga bari nakira Isma'il yagani.
Babu daďewa yaya yadawo tareda Dr Isma'il, yaďanyi dube2nsa sanan ya kalli ya majeed abokina karku damu, bawata damuwa bace yanzu ta tashi ta gyara jikinta bari na turo Nurse ta taimaka mata.
Kai kuma mije na ganka a office.
Suna fita saiga Nurse tashigo, itada aunty salam suka taimaka min na gyara jikina, Nurse ďin ta gyara gadon kamar komai bai faruba, nadawo na sake kwanciya dan jikina babu kwari ................✍🏻
Luv u oll my fun's
©2017
Battery low🔋😜👌🏻.
[8/6, 5:59 PM] mrs bilkisu: ____________________________
BAN SAKETA BA
_______________________________
NA
BILKEESA IBRAHEEM
{Bilyn Abdul}
________________________________
https://mrsbilkisa.blogspot.com
Sadaukarwa ga~ ya Abdul (City phone's)
MIYAKAMATA NAYI???.
Kasancewata uwa yakamata nayi 'kyakykyawan lafazi ga ďan daba nawaba alokacin danaga yayi ba dai2ba, karna la'anci ďan wani kona kirashi lalatacce, shiriyar ALLAH yakamata na ro'ka masa, domin ďa na kowane, bansan mi gaba zata haifarba akan nawa 'ya'yan.
ALLAH yasa mu gane.
Page...3⃣
Ya majeed kam yana office ďin Dr Isma'il, bayan sun zauna Dr Isma'il ya kalli ya majeed abokina ba wata matsala bace take damun 'kanwarmu ba, ciwonsu ne na mata, dan tafara period ne, saidai yazo mata da matsalar ciwon mara, amma karku damu dama hakan yana faruwa, zamu bata magani insha ALLAHU komai zaiyi dai2, inagama zuwa anjima zan sallameku inasha ALLAH.
to abokina mungodefa sosai ALLAH yabar zuminci.
Daga nan sukaďanyi hira ya majeed ya fito dan Dr Isma'il yanada masu jiransa.
Aranar aka sallamemu muka dawo gida, washe gari da yamma saiga Dr Isma'il yazo gidan ya majeed.
An masa tarba ta mutunci, bayan an gama gaishe2 ya ce, "ni banga patient ďinaba kumani ita nazo dubawa.
Aunty salma ta ce, "tana ďaki tanakuma jinmu inaga miskilancinne ya motsa mata, bari nakirata, bayan aunty Salma ta kirani na saka hijjab nazo, suna zaune a falo Affan yana cinyar Dr Isma'il, na zauna a'kasa cikin jin kunya na gaidashi, duk miskilancina da shagwa6a inada tsananin kunya.
Cikin fara'a ya amsa, ya ce, "my patient ya jikinki??,
"Na ce, "da sau'ki.
''Ya ce, "ALLAH yakara sauki.
Na ce, "amin.
Nami'ke da nufin komawa ďaki, Dr Isma'il ya ce, "a'a my patient sai ina kuma??, Na ce, "zanje cikine, ya ce, "da wuri haka?, kofa gaisawa bamuyiba kuma zuwannan nakine.
Nayi murmushi wanda mutane dayawa suke faďamin yana 'kara min 'kyau, kasancewar ban cika yiba saboda miskilancina, idan nayi kumatuna sukan lotsa.
A zuciyarsa ya ce, "ya salam yarinya 'karama zata haukatani.
Ganin kallon dayake mini yasani tashi da gudu na shige ciki, yabini da kallo yana murmushi harna 6acema ganinsa sannan yaja ajiyar zuciya.
Ya majeed ya ta6ashi abokina miye damuwarka??, Dr Isma'il yasaki sassanyar ajiyar zuciya sanan ya ce, "brother 'kanwarka ce damuwata, saidai tayi 'kan'kanta dan na lura bata wuce sha biyarba.
Ya majeed ya tuntsure da dariya kai Isma'il wlhy kaidai baka rabo da wasa, kai yanzu idan ance ka tsaya jiran iman saika tsaya??.
Dr Isma'il ya ce, "kajika da wata magana, aini koba ace najirabama zan jira kuma zaka sha mamakina..
To ALLAH ya taimaka amma saidai ta biyu ko??, harararsa Dr Isma'il yayi, ta biyu kota ďaya, aini kasan babu mata biyu a tsarina saidai kaddarar ALLAH, dan babu inda bata kai mutum.
Ya majeed ya jinjina kai yana murmushi, amma abokina kana ganin ya Mansur da mama zasu yarda, yakamata fa ace kayi aure tuni, kosaika zama tunzurun zurun ne?.
Dr Isma'il yay dariya, kana min wula'kanci wlhy majeed kaima naga duka shekararka nawa da auren?, su yaya kuwa banida matsala dasu, abinda nakeso suma shi suke so, kaidai katayani da addu'ar neman za6in ALLAH kawai.
Shikenan ALLAH yaza6a mana abinda yafi alkairi.
Amin Dr Isma'il yafaďa.
Da dai ya majeed ya fahimci Dr Isma'il da gsk yakeyi, saiya shige masa gaba awajen Abbah.
Abbah yayima Dr Isma'il tambayoyi kamar yanda shari'a ta tsara, yako amsa masa yanda yadace.
Saiya bashi izinin neman SO a wajena, nikam bammasan abinda ake cikiba, dan lokacin da nadawo gida mun koma makaranta.
Kai kutashi muyi sallah ďaya ta wuce, kuma ALLAH yunwa nakeji, Xoxo ta harareta ALLAH iman kin iya wula 'kanci saida labarin yafara ďaukar daďi zaki 'kir'kiroma mutane wani jin yunwa, inama laifin muyi sallar??.
Iman tayi dariya sorry dear karki damu aii idan tunbi ya ďauka labarin saiyafi daďi ko??.
Reefat ta ce, "ALLAH ni ko yunwarma banaji, burina kawai naji 'karshen labarinnan, karku damu aii muna gamawa zan cigaba.
To gsky saidai asiyo abincin ko asake cin indomi dan in ba hakaba girki zai 6ata mana lokaci, gsky ne Xoxo kunga kuyi sallar tunda ni an hutar dani, kafin ku idar naje na samo mana abinda zamuci ko bai yiba??.
Sukace yayi.
Bayan sun gama cin abinci iman ta ce, "saitayi wanka sanan, saida tagama ja musu rai sanan taci gaba.
Dr Isma'il yakasa sanar dani sirrin zuciyarsa saboda yana min kallon 'karamar yarinya, dan gsky asanan ban wuce sha biyar ba.
Ahaka wata yazagayo al'adata tazo nasha wahala sosai, su gwaggo suka rasa yanda zasuyi dani, na daure na ce, "sukira aunty Salma.
Babu 6ata lokaci aunty Salma tazo muka tafi asibiti wajen Dr Isma'il, shiyya dubani yamin allura yaďan kwantar dani na yini ďaya.
Daga nanfa ciwon mara yazamemin jiki, har fargaba nake wata yazo, hakama gwaggo tana tausaya mini sosai.
Ana haka Dr Isma'il yazo ma Abbah da zancen zai shiga soja, dan dama burinsa kenan tun yana yaro, amma saboda yayansa yanason yazama likita ya ha'kura yayi karatun likita, to yanzu damace tazo masa, shine yakeson yayi amfani da ita.
Abbah ya ce, "ALLAH sarki, ai haka akeso Isma'il mutum duk inda yake yazama mai biyayya ga nagaba dashi, saiyaga yazama abinda baiyi zatoba arayuwa, dan masu iya magana nacewa dana gaba ake gane zurfin ruwa, to inamaka fatan Al'kairi arayuwar ka, domin kai yaron kirkine, ALLAH yabada abinda akaje nema, kuma ayo nasara.
Amin Abbah nagode da addu'arka gareni ALLAH yasaka da al'kairi, babu damuwa abba yafaďa, kaga bari naturo maka iman ďin kuyi sallama ko??.
Cikin jin kunya Dr Isma'il ya ce, "Abbah dama ka 'kyaleta.
Abbah ya ce, "sabodami Isma'il?, ba sallama zakuyiba?, Dr Isma'l yaďan sosa gefen wuyansa saboda jin kunya ya ce, "Abbah karka damu, iman tayi 'karamane yanzu, inason saita gama koda secondary ne, saina fahimtar da ita nufina akanta, amma yanzu za'a raba mata hankali gida biyu.
Abbah yay dariya to shikenan Isma'il ALLAH yay maka albarka, yakuma bada sa'a akan abinda akaje nema.
Dr Isma'il ya ce, "Amin Abbah ngd da 'kaunarka gareni.
Abbah ya ce, "karka damu aii kai yaron arzi'kine wanda ya cancanci a 'kaunacesa fiyema da haka..
Daga nandai sukayi sallama, Dr Isma'il yatafi training ďin soja na wata shidda..
Nikam ban saniba, nagadai bana ganin yana zuwa wajen Abbah yanzu kamar yanda yakeyi da, ban ta6a yun kurin tambayar waniba, dan babu wata ala'ka tsakanina dashi banda ta mara lafiya da likita, haka nacigaba da shan wahala duk 'karshen wata, dukda wani likita yana dubani a asibitin su Dr Isma'il, amma bai iya shawo matsalata kamar Dr Isma'il.