← Book details Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 46

Sashe 29

Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

**************
Wajen k'arfe 12 Dr Isma'il yaje gidansu iman maida musayeef, Yama Tarar bata nan, saidai sungaisa da gwaggo da Abbah dayay mantuwa yadawo gidan, annan yabar Musayeef Yakoma gidan.

*_8:00pm_*
Iman zaune agaban abbah, kanta ak'asa tana wasa da yatsun hannunta.
Ya ce, "iman dadai inata damuwa da tafiyarnan taku Adamawa Ku kad'ai babu wani babba, amma yanzu hankalina ya kwanta, Dan Isma'il ya cemin tare zakuje, shima zaije wani d'aurin aure acan ko?.
Abbah nima ban saniba.
Okey to d'azu dayazo kawo Musayeef yake gayamin, Dan haka saiku shirya da wuri Dan gurine ba kusaba.
Kanta Yana ak'asa tace to abbah.
Tana mamakin yanda iyayenta suke son Dr Isma'il sosai, sun yarda dashi 100%, itakam da batayi niyar tafiya dashiba amma babu yanda zatayi tunda abbah yasaka baki.
Bayan sun mata nasiha akan ta tsare mutuncinta takula da kanta ta tafi d'aki.

Tana kwance akan gadon sai tunani takeyi, wayarta tashiga ruri, da sauri ta d'auka azaton Xoxo CE amma saitaga *_DM_* kamar bazata d'aukaba amma ta daure ta d'auka.

"kodata kara wayar akunne saitayi shiru, shikam Dr yana falone zaune Duk kewar musayeef ta isheshi shiyyasa yakira iman."
Assalamu alaiki, yafad'a ahankali.
Saida taja lokaci sanan tace wa'alaikassalam.
Shiru yabiyo baya babu maiyin magana, saican iman ta ce, "miyasa kazo gidanmu kace tare zamu tafi?.
Murmushi yayi sanan ya ce, " saboda na Isa.
Le6enta ta cije danjin furcinsa, yacigaba da fad'in ki shirya da wuri, Dan k'arfe 7 munafata mun kama hanyar Adamawa.
Saidai kanemi da Wanda zaka tafi amma badaniba tafad'a tana murgud'a baki.
Wata sassanyar dariya yayi yay k'asa da muraya ya ce, "ada idan akacemin Saudat ta'iya rashin kunya bazan yardaba, musassamman idan na tuno ranar data bani k'yautar budurcinta.........d'iffff ta Yanke wayar tareda cije le6e, afili tace wai yaushe mutuminnan yakoma Mara kunya hakane?, ALLAH ya shiryaka, haka zan bika kaje ka matseni ahanya.
Shikam yanacan yanata dariya abinsa, my life sarkin kunya, har yanzudai ana nan da hali.
Raihan dake tsaye kansa taja dogon tsaki Wanda yasa Dr juyowa yana kallonta.
Ta k'ank'ance idanu tana fad'in wlhy andai fad'o kuma wanan iskancine tunda ayanzu ba matarka bace, kunzauna kuna aikata *Zinar baki*.
To malama Raihan saka lasifika mana, yafad'a a harzuk'e.
Shuru tayi Dan taga ya hau sama, shikuma yadoka tsaki yatashi yay shigewarsa d'aki yana had'a kayan tafiya.

*Washe gari*
Tundaga sallar asuba Xoxo da iman basu koma barciba shiri sukayi sosai sanan suka zauna zaman jiran Dr Isma'il.
To shimadai bayan yadawo masallaci wanka yayi ya shirya cikin k'ananun kaya, yaje sukayi sallama da Yaya da mama, kamar bazai Shiga d'akin Raihan ba amma ya daure Dan tanada hak'k'i akansa, Dan haka yanufi d'akin.
Tana kwance a gado rufda ciki kuka takeyi jin motsinsa yasa tak'ara k'arfin kukanta cike da kissa.
Abakin k'ofa yatsaya ya ce, "kenifa zan tafi, banza tayi MASA kamar batajiba, danhaka yajuya yafice.
Da gudu tabiyoshi ta rungumeshi ta baya, tsayawa yayi cak itakuma tak'ara fashewa da kuka.
Tausayi tabashi Dan haka yajuyo Yakama hannunta suka zauna akan kukera, share mata hawayen yashigayi batareda yayi maganaba, aii saita k'ara mai tamkar yana zugata, ganin tana 6atamasa lokaci ya had'e bakinsa da NATA, humm shiru kakeji wai malam yaci shirwa, bakajin motsin komai saina saukar numfashinsu, bayan kamar Minti Biyar Dr isma'il yazare bakinsa yana maida numfashi, hannunta yaruk'o kinga kiyi hak'uri kimin addu'a kinji, baki ta turo gaba yaa isma'il yanzu ka daina sona ko?.
Kallonta kawai yakeyi batareda yayi maganaba, ganin haka yasa tafara hawaye yad'an cije le6ensa, muryarsa da alamun k'osawa ya ce, " waye gayamiki na daina sonki?.
Eh mana kadaina sona sai iman.
Murmushi yayi tareda rungumeta yana shafa bayanta cikin sigar lallashi, kinga kibar wanan maganar INA sonki kema danhaka kimin addu'a kinji, yafad'a yana d'agota saga jikinsa.
Dukda bata yadda da maganarsaba saitayi murmushi, ta ce, "ALLAH ya tsareminkai yasa kaje lfy kadawo lfy.
Amin yafad'a yana murmushi tareda shafa kumatunta.
Har tsakar gida tarakoshi Inda sauran 'yan gidan suke tsaitsaye, yabud'e mota yashiga Inda Dr Nabeel yake aciki, Dan shima anan gidan ya kwana, suka fice daga gidan ana d'agama juna hannu, Raihan harda yima hannunta kiss ta huro masa, ko kunyarsu Yaya bataji, shikuma yay saurin dafe k'irjinsa alamar sak'onta ya iso.

Dr Nabeel yay dariya kai baban soyayya nanma harka afka?.
d'an tsaki Dr Isma'il yayi kai wlhy babu wani afkawa, mazurai nayi mata saikuma tadawo tana bani tausayi, shiyyasa kaga INA biye mata Dan kawai hankalinta yakwanta, so ka gane?.
Na fahimceka na iman Dr Nabeel yafad'a yana d'aga MASA gira.
Fad'i kanka tsaye malam na imam nake baban musayeef.
Angon Raihan amarya kuma Cewar Dr Nabeel.
Hararsa Dr Isma'il yayi, ALLAH saima kaja afasa tafiyarnan da Hafsat.
No Sorry sir karmuyi haka dakai, Kasan kuwa yanda namatsu naganta, jin tafiyar harda ita nak'ara samun kwarin guywar tafiyar wlhy.
Dariya Dr Isma'il yayi, Nabeel kaimafa munafukine a 6angaren soyayya, shima ya tuntsure da dariya, to aii kasan zama da mad'aukin kanwa shike kawo farinkai inji masu iya magana, malam INA taredakai ban koyi soyayyaba aina fad'o wlhy, dolene ayimini jaje.
Kaifa shugaban masoyane.
Dariya kawai Dr Isma'il yayi batareda yace komaiba...........

*luv u oll my fan's*
*(((S))).........2017*
[8/6, 6:02 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!._*

*_NA Bilyn Abdul_*

_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's*

*_"wannan page d'in nakine my Ikilee amarya, ubangiji ALLAH ya Sanya Alkairi yabaku zaman lfy keda angonki, ALLAH yasa bad'i mudawo sunan baby😉."_*

*(page 27)*

Kaitsaye gidansu iman suka nufa Dan a can itama Xoxo ta kwana, mintuna kad'an suka fito harda Abbah da deeni, su Dr Isma'il suka fito suka kwashi gaisuwa a wajen abbah sanan yaymusu 'yar nasiha da Addu'ar ALLAH ya tsare.
Iman da Xoxo suka Shiga baya suma Dr Isma'il suka Shiga su deeni suna d'aga musu hannu.
Su iman suka gaishesu, cike da fara'a Dr Nabeel ya amsa, amma Dr Isma'il gaisuwar Xoxo kawai ya amsa yashare iman.
Ko ajikinta wai antsikari kakkausa, ita dama zai had'e ran harsuje Inda suka nufa hakan zaifiyimata dad'i, tunda suka shigo bai kalli Inda takeba ammafa yana satar kallonta ta madubi batareda ta saniba.
Tun bayan gaisuwa babu Wanda yasake cewa komai, da Alama iman da Xoxo ma barci sukeyi, Dan barcin bai ishesuba aka tasosu.
Jin shirun yayi yawa yasa Dr Isma'il lek'owa saiyaga Duk sunyi barci, ya ce, "kai sufa wad'annan barci sukeyi.
Aii gara suyi anjima manna maka tuk'innan zanyi Musha hirar soyayya.
Ashe zaka dad'a Baka shaba malam, dama ka ajiye wata soyayya saimun sauka kawai.
Tab wanan ganganne aii idankai anyi maka fuskar shanu nikam Baka hanani.
'Yar dariya Dr Isma'il yayi batareda yayi maganaba.

Sunyi tafiya sosai wadda had k'arfe 12:47pm su iman suna barci abinsu, Dr Nabeel da Dr Isma'il suna 'yar hira ahankali.
Isarsu wani k'aramin gari suka tsaya, sai anan su iman suka farka, sunyi mamakin barcin da sukayi, bayan su Dr Isma'il sun fito sukace su iman suka fito, iman dai saifaman had'e fuska takeyi.
Wani gurin cin abinci sukaje, bayan sun zauna masu kula da wajen suka tanbayi mi sukeso, su Dr Isma'il suka fad'a, ya maida kallonsa Kansu iman ya ce, " mikukeso?.
Iman ta ce, "tak'oshi.
Dr Nabeel ya ce, " kinga 'yammata kawo mana iri d'aya kawai.
Bayan sunci sunsha suka mik'e wadda iman tacine kawai visa tursasawar xoxo, Dr Isma'il yabiya suka fito.
"Hanya suka k'ara d'auka bayan sunyi sallar azuhur".

Tunda suka fara tafiya abincin yake juyama iman, sai yatsine fuska takeyi, Dr Isma'il yana kallonta ta madubi.
Tafiya yayi nisa ha suka k'ara tsayawa sukayi sallar la'asar, sanan suka ci gaba.
Sosai iman takejin amai tana dannewane kawai, ruwa tad'auka tasha kozata samu a man datakeji Yakoma, amma INA lamarin k'ara ta azzara takeyi, candai ta ce, " atsaya zatayi amai, gaba d'aya kallonta sukeyi, Dan yanzu Dr Isma'il yake tuk'in, gefen hanya ya gangara.
Tun kafin yagama tsayawa tafita da gudu, amai tafara shek'awa, da Sauri Dr Isma'il shima yafito, ko motar bai kasheba sai Dr Nabeel ne yakashe.
Rik'e iman yayi tacigaba da aman, duk d'an abinda taci ta amayar dashi, saida tagama sanan yad'agota yana mata sannu, Dr Nabeel yamik'o MASA ruwa, da Kansa ya wanke mata bakinta da Inda tad'an 6ata ajikinta, duk tayi laushi so kawai take ta kwanta.
Xoxo ta ce, "sannu iman, agalabaice ta d'aga kai, Dr Nabeel ya ce, " kozamu koma bayan asamu k'yamis.
A'a mudaije gaba koza'a samu.
d'aukarta Dr Isma'il yayi cak yakai cikin mota, bayan shima ya zauna ya CE, Xoxo takoma gaba Inda Dr Nabeel yacigaba da tuk'in.
Kwantar da ita yayi yasaka kanta acinyarsa yana shafa fuskarta babu dad'ewa barci yay a won gaba da ita, ajiyar zuciya ya sauke yasunkuya ya sumbaci goshinta, tsurama fuskarta ido yayi nawani lokaci, saikuma ya kwantar da bayansa jikin kujera ya lumshe idanu.
Duk abinda ke faruwa Xoxo da Nabeel suna kallon ta madubi, Dr Nabeel yay ajiyar zuciya tareda d'an kallonta gefen Xoxo yamaida Kansa ga titi yana fad'in toke 6arauniyar zuciya INA muka kwana?.
Harararsa Xoxo yayi ta ce, "saika gayamin zuciyar Wanda na sata?.
Yayi murmushi tawa mana, duk kinbi kin wani sukukutani yakamata aji danifa, kafin na koma Romeo irin Isma'il.
Dariya abin yabama Xoxo Dan haka tadara.
Dr Nabeel ya ce, " ngd da aka kar6eni.
Ta kalleshi da Sauri waya gayamaka ka kar6u?.
Dariyarki da fuskarki.
Humm to Baka fahimta bane, abinda yabani dariya daban.
Haba 'yan mata aii kuma kinzo hannu matar Dr Nabeel.
Shiru Xoxo tayi masa shikam yacigaba da tsarata, _(aii ko kafin na farga har Xoxo ta afka, dama itama tanaso 😉lol.)_
Chapter 29 · 0% Book details