← Book details Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 46

Sashe 17

Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

..................da sauri deexerh ta rik'eni nafaďo hannunta dan tuni numfashina ya tsaya, k'arar da deexerh ta kwallace ta jawo hankalin jama'ar gidan harda yaya dadyn su deexerh.
Da gudu suka iso 6angarenmu suna tambayar lafiya??, ganina akwance yabasu tabbacin nice babu lafiya ba deexerh ba, aunty ce tafara cewa akira doctor, amma yaya yahana, wani abokinsa aka kira, kafin ya iso yaya yazare takardar daya gani ahannuna, tuni zufa ta wanke masa dukkan sassan jikinsa, sai k'ara maimaita karanta takardar yake kamar wanda akabama hadda.
Ya maimaitata yafi ak'irga, tuni kuwa ya haddace komai dake cikin takardar, mama tana lura da halin dayake ciki, zuwan doctor ne yahanata tambayarsa.
Dr Auwal yadubani tareda mak'alamin k'arin ruwa, ya ce, "insha ALLAHU zuwa anjima zan tashi normal, yanzuma wani abune ya firgitani na suma, amma na farfaďo.
Godiya sukai masa sanan yatafi.
Dama tuni yaya yabar wajen, yana 6angaren mama, acan mama tasamesa zaune akujera kamar gunki, idonsa cike da kwallah, zuwan mama yasa yatashi sosai, yasa gefen rigarsa ya share kwallar data gangaro masa kaďan agefen ido.
Jiki asanyaye mama ta zauna dan tabbas tasan ba lafiyaba, yaya yanada k'ok'arin 6oye damuwa komai tsananinta, amma yanzu hakan ya gagara, cikin sark'ewar murya mama ta ce, "Mansur miya faru ne?.
Yaya yaja ajiyar zuciya, muryarsa naďan rawa ya ce, "mama Isma'il ya saki iman!!.
Cikin wani irin yanayi mama take kallonsa, ta ce, "ban ganeba Mansur mikakeson faďamini?.
Takardar hannunsa yamik'a mata, ta kar6a takaranta.....
*ni Isma'il Muh'd basheer!. Nasaki matata saudat sulaiman saki uku!!. Idan tasamu miji tayi aure.*
Tuni gumi ya wanke jikin mama, bata buk'atar k'arin bayani danhaka tayi tagumi kamar yanda yaya yayi.
Yayane yay k'arfin halin faďin mama amma yaronnan ya cucemu, yanzu dan ALLAH dawane ido zamu kalli iyayen yarinyarnan?, ni abindama yake bani mamaki shine miya haďasu dahar zai mata saki har uku?, miya hau kan yaronnan haka?, kuma wlhy mama rubutunsane barema ya musa mana.
Mama taja ajiyar zuciya toni Mansur ai komaima ya kwace mini, bansan yanda zan kira wanan abinba kuma.
Haka mama da yaya sukaita tattaunawa, kuma wani abun mamaki sunkira wayar doctor arufe, mama ta ce, "tunda yasan miya aikata ai dole yakashe waya, kabarsa kawai.
Nikam ina ďaki ina barci, aunty da deexerh da Raihan suna 6angarena, saidai basusan abinda yake faruwaba, dan deexerh ma bata karanta takardarba tunda tana zuwa ina suma.
Haka akaita tafiya har zuwa yamma dana farka, mama dakanta ta taimaka mini nayi wanka, aka bani abinci naci kaďan har zuwa sanan kuka nake rurus.

*bayan kwana uku*
Yau tsawon kwana uku kenan angaza samun number doctor kwata2, nikuma namatsa zanje gida, dan yakama iyayena su san halin da'ake ciki, mama da yaya basaso natafi, hakama deexerh da marwan, amma yaza'ayi da k'addarar ALLAH, ganin namatsa yasa mama da yaya suka kaini har gida.
Bak'aramin ruďani gwaggo tashigaba itada Abbah dajin abinda yafaru, dan su yaya basu 6oye musu komaiba, suka ďora dabasu hak'uri.
Abbah ya ce, "babu komai haka ALLAH ya k'addara aii, bayan ďan tattaunawa dabawa juna baki su yaya suka tafi aka barni agida.
Tunda nadawo gida banida wata walwala, kulum cikin kuka nake, ga rashin lafiya data tasoni gaba, dandanan nayi bak'i na rame kamar baniba, lokacin da labari yakai kunanen aunty salma da ya majeed ransu ya 6aci matuk'a, ya majeed ya ce, "bazai k'yaleba saiya ďauki mataki akan doctor, da k'yar abbah da gwaggo suka shawo kansa ya hak'ura.
Ganin yanda na k'untata kaina agidan yasa ya majeed rok'on abbah yabari nakoma wajensu k'ila zanfi samun sakewa, abbah baiyi musuba dan dama farin cikina yakeso, aranar muka tattara muka koma.
Acanma haka nayita rashin lafiya wadda tasa dole suka kaini asibiti, tofa wata sabuwa, bayan gwaje2 da likita yayi ya tabbatar mana inada ciki na sati uku, tun agurin nasa kuka sai anzubar dashi, amma ya majeed ya hana.
Ranar nayi kuka harna godema ubangijina, duk wanda yaganni saiya tausaya mini.
Muna dawowa gida ya majeed yasanarma su abba halin da'ake ciki, aranar kuma aka sanarma gidansu doctor, mama da yaya sunyi matuk'ar murna da wanan abin farinciki, dan cikin zai zama sanadin cigaban zumincin mu.
Har tsawon wata ďaya babu labarin doctor kota waya bare kuma ayi maganar dawowa.
Nikam inanan a6oye inata k'ok'arin zubar da ciki, duk abinda naji ance yana zubar da ciki saina sha a6oye, amma abanza wai man kaza, dan ciki ko gezau, saidai nasha azabar ciwon cikina.
Ahaka aka akai wata biyu da sati ďaya.
Awata ranar alhamis doctor yazo kano, saidai kuma yatarar da sabon tashin hankali, dan kowa ya ďauke masa wuta agidansu.
Kowa ya tambaya iman sai suyi masa banza harsu marwan da deexerh.
Hankanlinsa yatashi matuk'a, inda yaga sunk'i bashi wata amsa ta gamsarwa sai kawai ya tsare deexerh da marwan da bulala.
Tsoro yakamasu sosai dan ganin yanda yaburkice musu ďinnan zasu iya shan duka abanza, aiko suka sanar dashi komai, atake jikinsa yay sanyi, yanufi wajen mama hankali tashe.
Agabanta yashiga rantsuwar wlhy *BAN SAKETA BA!* mama, na rantse da ALLAH k'arya takemini.
Mama tayi masa banza, wuni guda yana magiya da rok'o amma kowa yak'i saurarensa, dayaga nan babu ci saiya nufi gidanmu, to gara nan abbah yayi masa nasiha da nuna masa muhimmancin yarda da k'addara.
Shidai doctor bashida wata magana sai *ban saketa ba*, tun suna kallon abun amatsayin wasa harya fara zarta tunaninsu, dan doctor neman zare musu yakeyi, awani daren litinin sai a asibiti ya kwana.
Wasa2 dai al'amira sun fara tsauri, doctor baisan waye akansaba, kuma indai idonsa biyu bashida magana saita *ban saketa ba*, wannan yasa hankalinsu yayansa yafara tashi suka fara tausayinsa kuma, dan abin yafara wuce makiďi da rawa.

Ahaka cikina yashiga wata biyar, nima kaina nazama mara lafiyar, kulum daga tunani sai kuka, duk sanda na kalli cikina sainayi kuka, har banason tuna inada ciki, duk halin da doctor yake ciki labari yana zuwa mini, dansu aunty salma suna zuwa ganinsa hakama su gwaggo.
Jikin doctor yay tsanani dole aka maidashi k'asar indiya, dan ciwon zuciya yana neman aikashi lahira, kowa yana tausaya masa.
Ban ta6a zuwa ganinsaba saidai kusan tare muke jinyar dan kullum zuciyata tana damuwa da halin dayake ciki.
Karna jaku da nisa, haka cikina harya cika wata tara, zuwa sanan jikin doctor da sauk'i amma ba'a dawo dashi 9ja ba yana indiya abinsa.
Awani dare juma'a na farka da nak'uda, cikin hanzari muka nufi asibiti, tun anasaran zan haihu acikin awa biyu har likitocin suka fidda rai, dan har washe garin ranar haihuwa shiru sai bak'ar azabar danake sha.
Har k'arfe sha biyun rana haihuwa shiru, zuwa sannan k'arfina yagama k'arewa, ko ďaga hannuna bana iyawa bare kuma nayi wani nishi, ganin halin danake ciki aka yanke shawarar yimini aiki.
Babu musu su abbah suka yarda, dadyn su deexerh yasa hannu a maimakon doctor, aka shiga dani ďakin tiyata.
Ancuromin yaro namiji k'ato mai kama da babansa kamar an tsaga kara, lallai yau naga farinciki wajen dangin doctor danawa dangin, kowa kamar yacinye yaron haka yakeji, haka nima kowa yana tausaya mini da addu'ar samun lafiya.
Duk wata hidima yayansa yayita, kuma shima ansanar dashi na haihu, yayi farinciki kuma yasha kuka, dan ranar saida ciwonsa yak'ara tashi, likitoci sunata faďa akan adaina gaya masa komai daya danganci 6acin rai.
Ina gadon asibiti har tsawon sati uku, dan haka ba'ayi taron sunaba, andai raďama yaro suna *Musayyeef*, to iman ALLAH yaraya mana musayeef, amin.
Bayan sati uku aka sallamemu, amma wannan karon gidanmu aka dawo dani, dan ina buk'atar kulawar gwaggona, haka nacigaba da rainon musayeef wanda kulum kallonsa yanasani tunawa da ubansa, dan kamarsu tayi yawa matuk'a, kullum mama tana k'ok'arin kwantar da hankalina, ahankali yauda gobe harna dake, komai yafara zama tarihi na maida hankalina akan rainon musayeef.
Musayeef yanada wata ďaya da kwanaki aduniya aka dawo da doctor gida, danya samu sauk'i sosai, shima yawan addu'ar da aka dage ana masa yasa yadake yanzu, kwanansa uku da dawowa yayansa yarakosa yaga musayeef, jiyayi kamar yamaida musayeef acikinsa, yana matuk'ar k'aunar ďansa gudan jininsa, dak'yar yayansa ya lalla6ashi suka tafi.
Yayi yayi yaganni amma nak'i amincewa, dole yahak'ura suka tafi wani abu na sukar zuciyarsa.
Daya koma gida saida aka haďa da lalashi, dan yanzu ba'aso yana tada hankalinsa.

Haka naci gaba da rainon musayeef nida gwaggo harya shiga shekara ďaya, asanane kuma ya majeed yabada shawarar nazana s,s,c,e ďina nakoma karatu, abbah ya yarda da shawararsa, dan haka nayi Exam, cikin amincin ubangiji nasamu result mai k'yau, dan haka ba'asamu matsalaba wajen nema mini makaranta.
ALLAH yacidani samun nan (A B U zariya), samun makarantar yasa na yaye musayeef na maida hankalina akan karatuna.
Shima doctor yakoma aikinsa yabarma ubangiji komai, amma lokaci2 yana zuwa duba musayeef, hakama yaya da mama da aunty.
To yanzudai ansaka musayeef makaranta kuma yayansa ne da wanan aikin, idan anyi hutu yana zuwa gidansu hakama weekend ana kaisa yayi kwana biyu.
Tunda nabaro gidan bansake haďuwa da doctor ba, bamma k'ara zuwa gidanba, idan yazo ganin musayeef kuwa bana yadda muhaďu, zadai akai masa ďansa, kuma susha hirarsu da gwaggo, ammani yagagara ganina, garama lokacin da maman su deexerh zata koma gidan naso zuwa amma ALLAH bai k'addaraba.
Xoxo ta ce, "oh maman su deexerh takoma??.
Eh yaya ya maidata yanzu hakama tana gab da haihuwa deexerh tace min.
ALLAH sarki kai natayata murna wlhy, musamman ma su deexerh dan babu abinda yafi karayu da 'ya'yanka daďi.
Wlhy hakane xoxo Reefat tafaďa.
Iman ta ce, "to wanan shine sirrin dana daďe ina 6oye muku.
"To miyasa kike yawan waige2? cewar Reefat.
Chapter 17 · 0% Book details