← Book details Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 46

Sashe 30

Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

K'arfe 6:57pm suka Isa Adamawa, lokacin har an idar da sallar magriba, damma ba k'aramin gudu Dr Nabeel yayiba, har sanan Iman barci takeyi.
Dr Nabeel ya kalli Xoxo toku yanzu wace anguwa zamu kaikune?.
E to saidai nakirata Dan na manta gashi kuma har yanzu iman barci takeyi tafad'a tana lek'a su iman.
Dr Isma'il yad'an lek'a fuskarta iman da tuni ta juya kwanciyarta, yanzu tana fuskantar cikinsa, Dan har cikin cibiyarsa yanajin saukar numfashinta ahankali.
Xoxo takira Reefat 'yar uwa gamufa a adamawarku, yama sunana anguwar?.
Wani ihu Reefat ta kwala Wanda yasa dole Xoxo tacire wayar d'aga kunnenta tana dariya.
Reefat ta ce, "kuna tasha bari muzo mu d'aukeku.
A'a bana gaya miki za'a kawomu bane kifad'i sunan anguwar kawai.
Bayan Reefat tafad'i sunan anguwarsu Xoxo ta sanarda Dr Nabeel.
Ya ce, " to kenan anguwa d'aya zamuje, waima yaya ainahin sunan amaryar?.
Xoxo tace aysha, amma anacemata shareefat.
Angonfa?.
Usman.
Dariya Dr Nabeel yayi Ashe biki d'aya zamuje.
Xoxo ta ce, "dawasa koda gsk?.
Wlhy gsk.
Tofa kaji ikon ALLAH Cewar Dr Isma'il.
Dr Nabeel ya CE, Aida baban angon da mom d'ina mamansu d'aya babansu d'aya.
Xoxo ta ce, " lallai bikin nakune ashe
Ak'ofar gidan su Reefat sukaja tunga, Xoxo takirata ta ce, mun iso.
Da gudu Reefat ta fito d'aga mak'ota taxo ta rungume Xoxo data fito tana mai farincikin ganinta, INA iman Cewar Reefat.
Aii ko bata zoba Doctor ya hana.
6ata fuska Reefat tayi wasa ko gsk?..
Dariya kawai Xoxo tayi batace komaiba.
Amota kam Dr Isma'il yashafa fuskarta iman, ahankali ta bud'e idonta, jin kanta acinyar mutum yasa ta ta tashi da Sauri.
Ido ta waro Dan ganin Dr Isma'il dake binta da kallo, ya ce, "kinsha barci?.
Batace komaiba sai duk'ar dakanta datayi saboda wata irin kunyarsa datakeji yau.
Shima ya lura da hakan shiyyasa yayi murmushi, itakuma tabud'e mortar da Sauri tafito..
Da gudu Reefat Tazo ta rungumeta kai iman Ashe kina ciki?, wlhy da harna yarda da zancen hafsat.
Murmushi iman tayi ta ce, " amarya kinsha k'amshi.
Bayan Reefat sun gaisa dasu Dr Isma'il, ta ce, "lah ya Nabeel da harda kai?, wlhy kuwa Aysha aii bammasan ke k'awarsu my hafsat bace.
Wlhy kuwa in k'awayenane, tunsanda kazo makarantarmu d'aukar Doctor naganeka bandai fad'a musu bane kawai.
Ayya to bari muma muk'arasa cikin gida ko?.
Okey to sannunku da hanya.
Yauwa kema sannu.
Dr Isma'il yamatso Kusada iman, ya ce, " kisamu ruwa mai zafi kiyi wanka zakiji k'arfin jikinki zuwa anjima zan kawo miki magani tunda kusane.
Kanta ak'asa tace to.

Koda suka Shiga gida Reefat sai tsiya takema iman, iman ta ce, "aii banibace abar yima surutu hafsat CE, saiwani 6oye manager take tsakaninta da Nabeel.
Dariya Xoxo tayi kawai Dan sunxo k'ofar Shiga falon su Reefat.
Tarba akaimusu ta mutunci Maman su Reefat taji dad'in ganinsu sosai.
Liyafa aka shirya musu sosai suka koma gidan makwafta Inda su Reefat suke zamna kunshi, Dan gidansu Reefat cike yake dam da mutane.
Saida suka fara yin wanka sanan suka zaunasukaci sukasha, aka baje kolin firar yaushe gamo, jisuke tamkar sun shekara BASA tare da juna.
Acikin firarrne iman takecewa wai Reefat ya akayi hakane?.
Idanun Reefat suka ciko da kwalla kubari kawai 'yan uwa, wlhy duk baffane da wannan aikin, wai tunda ba'asan randa za'a koma yajin aikinba to ayi auren kawai, dukda INA bala'in son yaa usman kuma kun sani amma wlhy banso hakaba, naso saina gama kawai.
Xoxo ta ce, " to kiyi addu'a ALLAH yasa haka shiyafi alkairi, Dan wlhy nimafa aurennan zanyi.
Gaba d'aya suke kallonta da mamaki.
Nan ta labarta musu yanda sukayi da Dr Nabeel amota, ya ce, "shifa Sam baixo da wasaba, suna komawa daga bikinnan zaizo gidansu wajen iyayenta daganan aturo manya.
Sunyi murna dajin haka danhaka suka rungume juna suna kukan dad'i.
Xoxo ta ce, " saura iman kema muna addu'ar ki koma kwanannan gaky, Dan muna buk'atar k'anin musayeef.
Hummm 'yana iska kunkuma dawo kaina.
Bawani iskanci anan, Reefat yaufa acinyar Dr Isma'il taxo.
Kai gaba?.
"ALLAH kuwa".
Iman wai haka?.
Matsalarkuce iman tafad'a tana kwanciya.
Kwashewa sukayi da dariya Reefat ta ce, " kice soyayya akasha amota?, lallai kallo ya wuceni.
Aii kuwadai kallo ya wuceki, shiru iman yayi musu.
Haka suka raba dare ranar suna hira.

6angaren su Dr Isma'il makuwa, komai daidai, tarba suka samu sosai dama mom d'in Nabeel tana nan tazo itada k'annensa.
Bayan sun huta Dr Isma'il yamatsa sai sunje an siyoma iman magani, Dr Nabeel ya CE, "kaima kasan rashin Sabon tafiya mai nisane yasata aman bawani abuba, kuma datayi barci normal zata tashi.
Badan yasoba ya hak'ura amma saida yakirata ya ce, tasamu farasitimol tasha.

_" washe gari 2:30pm aka d'aura auren Shareefat da yaa usman"_
To saimuce ALLAH yasanya alkairi.
Bayan angama d'aurin aure Dr Isma'il yaso ganin Iman amma hakan ya gagara, gashi yakira wayarta akashe, hakama ta Xoxo arufe, yasan sunacan sauna hidima, balle sune amararori k'irjin biki lol.

K'arfe 7:30pm akakai amarya d'akinta, k'arfe 8:30pm za aje liyafar cin abincin dare, Dan haka su iman suna zuwa gidan suka hau shiri na k'asaita.
Humm fad'a muku yanda suka had'uma aii 6ata lokacine ammafa sun kashe kalla, kuma dolene ido ya kallesu, babu Wanda zaiga iman ya CE, "ta ta6a aure barema harda haihu.
Hakama amarya tayi k'yau sosai cikin kwalliyar amare abin sai Wanda yagani komai zam zam.
Bayan sungama shiri abokan Ango suka fara kwasar k'awayen amarya Dan ance babu African time.
Dr Isma'il da Dr Nabeel gafe suka tsaya Dan babu budurwar dazasu d'auka saisu Xoxo.
Sukam sune k'arshe Dan tare suka fito da amarya, bayan amarya tashiga mortar da Ango ke zaune sukuma suka fara k'ok'arin Shiga wata motar guy.
Da Saudi Dr Isma'il yaymusu magana suka juyo, su bamasu lura dasuba sai yanzu.
Sunshiga motarsu Dr Nabeel suka tafi, Duk sunwani susuce da ganin kwalliyar su iman, dukda suma sunyi gayune cikin farar shadda d'inkin boda, yayi bala'in musu k'yau sosai, kowa yagani said k'yasa😉lol...................

*_"Kuyi hak'uri dajina shiru wani d'an uzurine yarik'eni."_*

*luv u oll my fan's*
*(((S)))..........2017*

*_BAN SAKETA BA!!._*

*_NA Bilyn Abdul_*

_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*

*miya kamata nayi?*
_Humm *Mad'igo wa'iyazubillah* Kai jama'a wanan rayuwar ko dabbobi basayinta wlhy, haba 'yar uwa mizakiji ajikin 'yar uwarki mace?, miyasa zaki bari shaid'an yayi tasiri akanki?._
_tawani 6angaren ina ganin laifin iyaye, wata yarinyar datakai shekara goma zaka fara ganin tana buk'atar aure, zuwa shekara 15 tayi nisa da sha'awa, amma zakiga wata uwar bata kulawa._
_dayawa wasu yaranmu sunada tsoron yin iskanci da maza, saboda iyaye sunfi tsoratar damu akan karmu yarda da namiji, basu cika kulawa akan gargad'in tarayya da k'awayeba, shiyyasa saikiga k'awa ta dilmiya yarinyarki wajen biyan buk'atar juna, saboda wanan hanyar mai sauk'ice_.
_zata samu biyan buk'atarta cikin sauk'i batareda an ganeta kai tsayeba, humm wata sa'in k'awanfa bala'ine wlhy_.
Muhad'u a page nagaba.
*ALLAH yasa mu gane*

*(page 28)*
Iman sai satar kallon Dr Isma'il takeyi yayi bala'in yimata k'yau, azuciyarta ta ce, "inama zai koma saka manyan kaya koda yaushe, wlhy da yaringa yin k'yau.....
Tanacan tana zancen zuci saitaji wani lallausan hannu ya rik'o hannunta, da sauri tad'ago matsakaita idanunta ta sauke akan Dr Isma'il, Ashe sun dad'e da isowa bata saniba.
Ta sauke idanunta ahankali, sanan tayi k'ok'arin zame hannunta amma hakan ya gagara.
Muryarsa mai amo da alamun sark'ewa ta sauka acikin dodon kunnenta, ya ce, ''kifito mana, tun d'azun su Nabeel sun shige da amarya.
Da sauri takalli gefenta babu Xoxo, Gavan motarma babu Dr Nabeel, tafito da sauri, tareda tambayar kanta wai har yaushe sukama iso da har bataji fitar Xoxo ba.
Dr Isma'il yak'araso inda take gaff tamkar zai rungumeta, idanunsa akanta, ya ce, " wai tunaninmi kikeyi ne haka?.
Shiru tayi tana k'yafta idanu.
Yasaka d'anyatsansa d'aya akan le6enta dayasha uban janbaki sai walk'iya yakeyi, da sauri ta d'ago tana kallonsa, d'an yatsansa ya nuna mata Wanda ya dangwalo janbakin, wannanfa?, yafad'a yana d'aure fuska.
Idanunta ta sauke k'asa batareda tace masa komaiba.
"Tambayarkifa nakeyi?.
Ak'ufule ta ce, " janbaki.
Humm janbaki ya maimaita ahankali, ha6arta yad'ago yana kallon fuskarta, ita kuma ta lumshe idanunta dakeda gashi gazar gazar sunji maskara duksun mik'e. Yad'an cije le6ensa, dama wanan kwalliyar ta Matan aure ce?.
Bud'e idanunta tayi ta sauke akansa, ban ganeba tafad'a tana ture hannunsa, baijanye hannunba, itama saita k'yalesa, amma ta maida kanta k'asa, tana kallon bak'i agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunsa.
Muryarsa cike da kishi ya ce, "wannan kwalliyar bata dace dakeba saudat saidai a d'akinki, amma kiduba taron jama'ar dake wajenan maza nawane dazasu kalleki, yabi jikinta da kallo doguwar rigace ta jan material bata kamata sosaiba amma dukda haka yaji kishi barinta tashiga wajen ahaka, Dan ALLAH kalli rigar dake jikinki.
Iman ta ture hannunsa da k'arfi sanan tabi jikinta da kallo tad'ago tana kallonsa miye laifin rigarnan Dan ALLAH?, nifa gsky kafara takurama rayuwata, lokaci yayi dazaka barni nasha iska mai dad'i, kwalliya kuma nibanga aibuntaba koso kake nazo wajen kamar wata korarriyane, cike da tsiwa take maganar Dan haka ta k'ara tunzura masa zuciya.
Takowa yayi zai matso Kusada ita ta matsa, ya matso, ta matsa, dahaka har suka dangane da wata mota, ta matse jikinta da motar tana k'ara d'aure fuska, shima fuskarsa tamau take kamar ba Dr Isma'il ba uncle d'in Deexerh.
Wani irin tsorone yaratsa zuciyar Iman, Dan batasan miyake shirin yimataba, muryarta na rawa tace doctor please kayi hak'uri Dan ALLAH.
dukda idanunta arufe suke wannan bai hanashi hararartaba, yamatsar da fuskarsa GAF da tata har sunajin saukar numfashin juna, cikin wata irin murya tamkar mai rad'a ya ce, " kina tunanin zan iya d'aga mini k'afa kishiga taron jama'arnan da wannan janbakin?.
Da sauri ta bud'e idanunta kafin tace wani Abu ya had'e bakinsu waje d'aya, janbakin yashiga tsotsewa cike da nuna kwarewa, Iman sai dukan bayansa take amma a banza.
Chapter 30 · 0% Book details