← Book details Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 46

Sashe 36

Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da asuba yatashi dak'yar yashiga bayinta, saida yayi wankan sanan yay alwala, bai tada iman ba dan yasan bata sallah, d'akinsa yanufa yasaka jallabiya yanufi masallaci.
Iman kuwa yana fita tabud'e ido, gwalo tamasa sanan tasakko daga gadon tashiga bayi, alwala tayi tazo tayi sallar asubahi, tamaida kayan barcinta ta haye gadon kamar komai bai faruba.
Saida gari yafara haske suka dawo daga masallaci shida marwan da Yaya, kowa 6angarensa yanufa.
Sanda yashigo d'akin iman takoma barci Dan bai barsu sunyi barci ishashsheba da daddare.
Kwantawa yayi shima tareda rungumeta sai barci.

*_7:48am_* iman ta farka, ahankali ta zare jikinta daga NASa gudun karya tashi ta saka masa filo, falo tafito, dukda babu wani datti mai yawa saida ta k'ara gywarashi, tabaza k'amshi, d'akinsa tashiga, tabi ko ina da kallo, ancanja komai bawanda tasani bane, tagywara d'akin tabaza k'amshi nanma, anan tayi wanka tad'anyi kwalliya sanan tanufi d'akinta.
Ahankali take komai dankar ta tadashi, tasaka kaya dasuka kara fidda tsarin halittarta, siket ne da Riga na atanfa, kai telan nan ya iya fidda d'inki gsky, ta nad'a d'aurin d'ankwali mai tsari sanan tafeshe lungu da sak'o najikinta da turare.
Ahankali Dr Isma'il yabud'e ido yana kallonta, tunsanda take d'aurin d'ankwali yake kallonta, tajuyo danufin fita saitaga idon doctor akanta, lallausan murmushi tasaki tana fad'in dama katashi?.
Baiyi maganaba saidai ya mik'o mata hannunsa alamar yanason tashi, matsawa tayi gaban gadon ta kama hannunnasa, ahankali yatashi zaune har yanzu idonsa akanta.
Ita kallon nasama kunya yake bata, ta daure ta ce, "kallonnanfa ya Isa haka.
Kamo hannunta yayi yazaunar saman cinyarsa, akunnenta yay magana wadda tasakata saurin saka tafin hannunta ta rufe fuska, da sauri tamik'e daga jikinsa ta gudu........ Yakatseta dafad'in ni wazaimin wankan?, ashagwa6e yay maganar.
Da d'an gudunta ta ida fita daga d'akin, yay 'yar dariya, my life sarkin kunya, mik'ewa yayi yashiga bayinta, tawanke bayin tsaf sai k'amshin dad'i yake, ga ruwan wanka anhad'a Wanda yakeda tabbacin nasane.
Wankan yafarayi zuciyarsa cike da tunanin iman, gabad'aya yarinyar ta canja masa, komai nata yak'ara girma musamman ma k'irjinta, duk motsin datayi saita kuma rikitashi, yakuma nutsa kansa cikin ruwan yana murmushi.

Iman tana fita sukaci karo da Raihan tafito sanye da kayan barci, da alama yanzu ta tashi, har iman tayi niyyar wuceta saikuma tadawo baya tana murmushi.
Taje gaban Raihan ta tsaya fuskarta fes, ta ce, " Raihan kin tashi lfy?.
Wani k'ududun bak'in ciki yatokare zuciyar Raihan amma saita dake, itama ta CE, "lfy lau. Ashe kin dawo?.
Iman tayi murmushi danjin tambayar rainin wayo daga Raihan, tad'an dafa kafar Raihan tana cigaba da murmushi, nadawo Raihan cikin huncin ALLAH, mammallakin zuciya da abinda ta sak'a, tad'aga mata gira, ina fata kema bazaki tafiba zaki zauna murayu tare, harmu haifo k'annan misayeef k'yautar ALLAH...... Tana gama fad'a tayi gaba tana wata irin dariyar rainin hankali, saida taje dai dai k'ofar shiga d'akin doctor sanan tajuyo, cikin wani salo ta ce, *_" BAN SAKETA BA!."_* tadafe saitin zuciyarta sannan tayima Raihan jinjina da hannunta d'aya👍🏻😉tad'an gira sannan tashige.
Sagade Raihan tayi tanabin iman da kallon harta shige d'akin Dr, zuciyarta cike da d'aci, wai waccan 'yar yarinyarce take gaya mata bak'ar magana a fakaice?.
Hummmm iman kikira kanki sorry kawai, fuuuuuu tashige d'aki, tafasa kuka tareda fad'awa kan gadonta daya had'a kwana uku babu gyara.

Iman kam tana d'akkoma Dr kaya tana faman murmushi kamar wadda akayima albishir da aljanna, k'anan kaya ta d'akko masa masu k'yau, tafeshesu da turare sanan fito.
Tayi murmushi Dan ganin babu Raihan, tayi zaton zata fito ta isketa aii.
Dakinta tawuce, agurguje tagyara ko'ina tabud'e d'akin da k'amshi, sanan tadawo falo ta zauna.
Fitarta babu dad'ewa Dr tafito, yabi d'akin da kallo yana mai jin dad'i, iman akwai tsafta, amma awannan karon tazo masa da sabon salon k'amshi na musamman.
Tsaf yashirya tamkar wani matashin saurayi, babu Wanda zaiga Dr ya ce, "iayi aure harda d'a, falon yanufo shima.
Musaueef yashigo falon da d'an gudunsa, cak yatsaya yana kallon iman, fuskarsa d'auke da mamaki, tayi masa murmushi tareda bud'e hannayanta alamar yazo.
Zuwa yayi yashige jikinta yana 'yar dariya, aunty maa yaushe kikazo?.
Bata bashi amsaba sai faman murmushi take zabgawa na jin dad'in ganinsa, ta ce, " I miss u my derling.
Dr Isma'il yana tsaye yana kallonsu fuskarsa d'auke da murmushi.
Iman tashare 'yan kwallan dasuka taru mata agefen ido najin dad'i, tad'ago Musayeef daga jikinta ta sumbaci kumatunsa sanan tamik'a masa nata, shima sumbatarta yayi.
Sai asanan yaga dadinsa, dagudu yasaki iman yanufi Dr dake tsaye.
Dr yatsugunna tareda ware hannunsa musayeef yazo yashige.
" daddyna!."
"Musayeef d'ina!."
Shima yafad'a cike da jin dad'i.
Yad'agosa yana dariya, katashi lafiya?, lfy lau daddyna, da k'yau na gwaggo.
Musayeef ya ce, daddy!.
Ma'am, Dr Isma'il ya amsa.
Daddy itama aunty maa tadawo gidanmu.
Saida ya kalli iman suka had'a ido tayi k'asa da kanta tana murmushi, sanan yadawo da dubansa kan musayeef, kai ya d'aga masa tareda lumshe ido yana murmushi.
Yeeeeeeee musayeef yashiga fad'i yana tsallen Murna, Dr da iman kallonsa suke sunata dariyar jin dad'in ganin farincikin tilon d'ansu.
Raihan dataji ihun Musayeef tafito tawani doka uban tsaki tashige cikin, babu Wanda ya kulata danshi Dr ko kalloma tata isheshiba, da ita da babu duk d'ayane agurinsa.
Mik'ewa yayi yad'auki musayeef suka k'arasa Inda iman take zaune, zama yayi Kusada ita yad'ora musayeef kan cinyarsa.
Kinga yanda musayeef yake farinciki momynsa tadawo ga daddynsa.
Murmushi iman tayi batareda ta ce, komaiba.
Musayeef ya ce, "aunty maa ina uncle deeni da gwaggo da abbah.
'Yar harara tamasa ta ce, "sai yanzu katuna dasu?.
Musayeef ya kalli daddynsa, daddy aii dai Kaine kace zaka kaini ko?.
Kai yad'aga masa ya ce, " insha ALLAHU big boy. Dariya sosai musayeef yakeyi wadda tasaka iyayen NASA dariya suma.
Iman tamik'e kunga bazan iya wannan shiritarba bari naje na gaida mama dasu Yaya.
Shima Dr mik'ewa yayi d'auke da musayeef muma Baza a barmu abaya ba aii, muje muyi breakfast ma.
Haka suka rankaya abin sha'awa kamar kasacesu ka gudu, sunsan su yayama suna 6angaren mama, Dan haka suka nufi can kai tsaye, ilai kuwa suna can.
Sunbama su mama sha'awa, marwan ya ce, "family ya had'u dee.... CE kawai babu, dariya akayi harda su Dr dake shigiwa.
*_(Ni bilyn Abdul na ce, " tofa, mi marwan yake nufi, bayan babu aunty da Raihan agurin, naga suma duk suna cikin family🙊😜)_*.

Gaisuwa aka shigayi, kowa saiji da imam yake, itakam kunyarsuma takeji, ta ce, "marwan yaushe dee...... Zata zo?.
Aina San weekend d'innan saitazo, dan taji haushi kin dawo bata nan, murmushi iman tayi ta ce, ALLAH yakaimu lfy.
Ya CE Ameen.
Sun dad'e anan anashan hira, sannan suka koma 6angarensu.
Suna zama wayar iman tahau wringing, takalli wayar.
My sweet hafsy tagani, tasaki murmushi tareda d'agawa...................

*_" kuyi hak'uri idan nadad'e INA typing wayar k'amewa takeyi"_*

*luv u oll my fan's*
*(((S)))...............2017*
[8/6, 6:03 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_*

*_NA Bilyn Abdul_*

_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*

https://mrsbilkisa.blogspot.com

*miya kamata nayi?*
_6arna NATA yawa a bayan k'asa, amma anrasa miye tushenta?._
_hummm akwai tushe tushema ba tusheba, misali idan na d'auki yanda al'ummarmu suka maida zina a yanzu._
_zakiga uba mai cike da kamala ariga da fuska, amma idan yaje office shida sakatariyarsa saidai addu'a, zai makad'awa matarsa k'arya yatafi k'asar waje kasuwanci amma yana hotel da 'yammata, k'ilama harda k'awar 'yarsa, ko k'awar matarsa, ko k'awar k'anwarsa._
_to jama'a Dan ALLAH, indai maganarnan da ake fad'in Wanda yayi zina da uwar wani sai anyi da tasa mizai hana matar magidancinnan fad'awa tarkon zina, tunda k'ila harda matar wani yakeyi, mizai hana 'ya'yan magidancinnan fad'awa zina, tunda yayi da 'yar wani, mizai hana k'anwar magidancinnan fad'awa zina, tunda yayi da k'anwar wani, mizai hana yayar magidancinnan fad'awa zina tunda yayi da yayar wani._
_kunga tadalilin mutum d'aya mutane dayawa sun fad'a tarkon 6arna, shikad'ai ya wargaza family d'insu, Dan abin zaita bibiyarsune har 'ya'ya da jikoki._
_wa'iya zubillah, Dan ALLAH magidanta kuji tsoron ALLAH kodan katange family naku fad'awa cikin bala'in fasik'anci, saimun gyara ALLAH zai gyara mana, sakawa 'ya'ya da k'anne sasari na hana Fita bazai hana ubangiji ya aiko wani k'ato har gidanka ya6ata maka rayuwar mata, 'ya'ya, k'anne, yayye, ba a yima ALLAH wayau d'an uwa._
*ALLAH yasa mugane*
Chapter 36 · 0% Book details