← Book details Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 46

Sashe 32

Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai wajen shabiyu suka tashi tare sukayi wanka, Raihan sai salo takeyi ita matar so, (nace hummm), bayan sun shiryane yasata ta gyara falon da duk Inda yadace, 6angaren mama yaje sukaita hirarsu har aka kira sallar azuhur, daga nan yanufi masallaci.
Koda yadawo bainufi wajen mamaba saiya wuce 6angarensa, harya gota d'akin Raihan saiyaji magana k'asa2 Dan haka yadawo bayan, ak'ofar d'akin ya tsaya cak danjin furicin aunty.
Hummm ammafa auta kinyi k'ok'ari gsky, shiyyasa duk cikin k'annena nafi sonki, yanzu kina nufin yau da safe ya kusanceki?, kuma da maganin kikayi amfani?.
Wlhy kuwa aunty, Aida ya had'e girar sama data k'asa zaimin buyagi, naje na rungumeshi, narigaya na gano lagonsa na Shiga aika masa sakwanni, ai tuni yakwasheni muka tafi d'akinsa.
Da k'yau k'anwata, kidage amfani da maganinnan kamar yanda malam yace, ''saiya manta da waccan banzar dayake ik'irarin akanta ciwon zuciya ya sameshi, yanda mukayi nasarar fiddata agidannan haka zamuyi nasarar gogeta azuciyarsa.
Idanu Dr Isma'il yazaro waje..... Raihan taci gaba da fad'in, aii ni wlhy aunty har yanzu lamarinki mamaki yake bani, yanda har kika iyayin rubutun Yaa Isma'il kamarshi ya rubuta, kuma kowa ya d'auka da gsk shiyya rubuta sakin.
Dariya suka kwashe da ita suka ta6a kamar wasu k'awaye..........da k'arfi Dr Isma'il yadaki k'ofar d'akin, arikice suka d'ago suna kallonsa.
Wani kukan kura yayi yadamk'i Wuyan rigar Aunty ya sharara mata mari saubiyu, yacigaba da jibgar banza.
Ihun aunty da kururuwan Raihan yasa mama da mom da marwan isowa da gudu, sai janye Dr Isma'il suke amma bai daina dukan aunty ba.
Su mama sunrasa yanda zasuyi gashi ya fasa mata kai Dan dukanta yake ta ko ina, waya mama tasa takira Yaya.
Mansur komi kakeyi kazo gidan yanzunan babu lafiya, bata jira amsarsaba ta yanke wayar.
Cikin minti 20 saiga Yaya sanan Dr Isma'il Yakoma dukan Raihan yabar aunty tana sauke numfashi da k'yar.
Marinsa Yaya yayi, Isma'il wai bakada hankaline misuka yimakane?.
Hawaye yafara yanna nuna su aunty dake kwance suna jiyyar Kansu, bakinsa sai rawa yake alamar yanason yayi magana amma ya kasa, ya dafe k'irjinsa da sauri, luuuuuu yayi baya zai fad'i da sauri Yaya ya rik'eshi yafad'o a hannunsa.
Yaya ya girgizashi Isma'il! Isma'il!!, shiru, da sauri ya CE, marwan muje mota ya suma.
Mama tafashe da kuka, tana fad'in wayyo Isma'il kana ganin rayuwa kaidai Dan ALLAH karka mutu kabarni.
Marwan yana gyara mota za'a saka Dr Isma'il saiga Nabeel ya shigo, da sauri yak'araso yana tambayar lfy?.
Suma yayi cewar Yaya, Dr Nabeel ya ce, "Yaya amaidashi ciki saina dubashi bama sai Anje asibitiba.
Haka kuwa akayi aka maida Dr Isma'il d'aki, taimakon gaggawa Dr Nabeel yashiga bashi, bayan kamar Minti goma ya farfad'o.
ALLAH yasama akwai allurai da ake MASA, Nabeel yay masa allura yasamu barci, saida yak'ara kwantar musu da hankali sanan yatafi.

Mama takali su aunty da duk hankalinsu yake atashe tun d'azu, zuciyar Raihan tayi rauni sosai, bata ta6a ganin ciwon Dr Isma'il ba, batayi zaton haka yake shan wahalaba, tayi danasanin biyewa aunty, gashi tun ba'aje ko inaba komai ya rikice, tasamu Dr Isma'il kuma zai kufce mata alokacin datake buk'atar zama taredashi.
Yaya ya katse mata tunani da fad'in saikumuje k'yamis kukuma Dan tabbas akwai wani babban Abu da kuka aikata ga Isma'il, kowa yasan hak'uri irinna Isma'il, amma har kuka kaisa mak'ura...... Aunty ta bud'e baki zata fara rantse2 yadaka mata tsawa, bana buk'atar jin komai daga bakinki harsai Isma'il ya farka.
Shiru tayi Dan tasan halinsa zaiyiya k'ara mammaujeta ne.
Marwan kam sai hararsu yakeyi, dama haushi suke bashi.

A6angaren iman kuwa komai Normal, bayan taraka Xoxo tadawo tahad'a wankin gwaggo da musayeef tanayi musayeef yana tayata konace yana wasan ruwa.
Tana gamawa tayima musayeef wanka suka shige d'aki, wasa suketayi tana biye MASA sunata dariya cike da farinciki, yau tunda tatashi takejin wani irin nishad'i na musamman Wanda ita kanta batasan na miyeba, jitake tamkar an sauke mata wasu kaya masu nauyi aka.
Suna cikin wasansu duksun hargitsa gadon gwaggo talek'o, oh ni ALLAH ya shiryeku, kaidai ka maida uwar taka kamar wata kakarkama.
Nidai kutaso kuyi mama girki da wanan shashancin.
Iman tayi dariya to gwaggo.
Fitowa tayi tana dariya Musayeef nabinta waisaita MASA goyo, tsugunnawa tayi ya d'ane bayanta suna dariya, ahaka suka Shiga kicin , gwaggo tabisu da kallo tana murmushi, ta d'aga hannu sama tana fad'in Ya ALLAH ka kawo farinciki da alkairi a rayuwar wanan yarinya da d'anta, ALLAH ka bayyana gsky itama takoma gidan mijinta kokuma tayi wani aunren...
*_(Araina nace gwaggo addu'arki aii tadad'e da kar6uwa😁).............._*

*luv u oll my fan's*
*(((S))).........2017*
[8/6, 6:02 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_*

*_NA Bilyn Abdul_*

_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*

https://mrsbilkisa.blogspot.com

*Gargad'i!!!.*
_hummm namiki magana karki k'ara sakani group dabai daceba kink'iji ko?, wlhy idan kika k'ara kaini Group na iskanci kowanda aka danganta dawani Abu sainaci.......humm bana zagi, amma tabbas zakisha mamaki, banason ciki da iskanci kinjiko, banmiki kama da 'yar iskaba, Dan haka kishiga hankalinki_
_sauwajen uku ina tsintar kaina agidan banza, kuma idan naduba sainaga kece kika kaini, nafarko namiki nasiha k'ink'iji, nafita anabiyu bantankakiba, yanzu kinkaini na uku, to wlhy ana hud'u ubanki zanci, bazan fad'i sunankiba amma kinsan kanki, kuma kika k'ara zan yayatakine wlhy._
_Kikama kanki kafin watan cin ubanki yatsaya, shaid'aniya kawai maikafa gidan banza mtsooooww._
*idan kunne yaji👉🏻😡*

*(page 30)*
Gaba d'aya ahalin gidan suna falon mama, kowa yayi jigum jugum Dr Isma'il kawai ake saurare, ya share kwallan dasuka cika MASA ido tareda cije le6e.
Yaya ya ce, "isma'il kayi hak'uri kasanar mana abinda ke faruwa, gaba d'aya kunsakamu aduhu wlhy.
Dr Isma'il yawatsamasu Raihan harara tareda girgiza kai, idonsa yak'ara cikowa da kwalla yanuna aunty Yaya dama matarka itace silar shigata Matsala arayuwa, itace ta rabani da farincikina matata.
Haba sadiya minayi miki?, mina tare miki agidanan?, mi saudat tayimiki ne haka da zafi?.
Tunda yafara maganar suke binsa da kallon ikon ALLAH, su kalleshi su kalli su Raihan, mama ta ce, " Isma'il bamufa ganeba har yanzu.
Raihan ta fashe da kuka wlhy mama nidai ba laifina bane aunty CE tace muyi haka, amma ALLAH bani baceba, Dan ALLAH ya Isma'il karka sakeni INA Sonka wlhy, rashin mafitane yasa na yarda da shawarar aunty alokacin...... Wata razananniyar tsawa Dr Isma'il yadakama Raihan, walhy kokimin shiru kona shak'eki kimutu!!!!!.
Yaya Yakama hannunsa yamaidashi zaune, ya ce, "Raihan fad'a mama mike faruwane?.

*_Tuna baya_*
Kamar yanda kuka sani munso juna da yaa Isma'il sosai bayan bikin aunty da Yaya, harma anyi maganar aurenmu amma Mamana ta ce, " bata yardaba baza'a had'a mata yara agida d'ayaba, dagani harashi. Mumshiga damuwa har aka hanani zuwa gidanan gaba d'aya.
Bayan kamar shekara uku da faruwar haka sainaji auren yaa Isma'il dawata baniba, hankalina yatashi matuk'a amma babu yanda zanyi na hak'ura, kowa yazo bikin daga sokoto amma bandani saboda kishi, bayan komawarsu sukaita bani labari akan Yaa Isma'il yarinya ya aura amma sun dace, wannan yasa hankalina yatashi nakira aunty ta ce, "nashirya nazo kano.
Bansamu matsalaba su mama suka barni nazo domin itama tafara son Ya Isma'il sanan, amma bansan dalilintaba.
Hankalina yatashi sosai daganin matar ya Isma'il, gakuma soyayya dayake nuna mata wadda ni ko rabinta bai nuna minba sanda muna tare, wannan yasa muka fara k'ulle k'ullen rabashi da IMAN nida aunty, mun aikata abubuwa dayawa ga iman amma bata ta6a fad'awa kowaba, inaga sai deexerh, ganin munyi2 babu nasara yasa aunty takirani awani daren juma'a.
*(" Raihan kinason Isma'il da gsk?. Eh wlhy aunty inasonsa. Kinason samunsa?. Dasauri na ce, "eh mana. Dariya aunty tayi irinta muguntarnan, tamik'omin takarda, kar6i ki karanta wannan".)*
Takardar nakar6a na karanta wadda aka rubuta takardar sakin iman, nasan rubutun ya Isma'il sosai Dan haka nad'ago da sauri INA kallon aunty, aunty kina nufin Yaya dakanasa yarubuta sakinnan?.
Kallona tayi tana murmushi, miyasa kikamin wannan tambayar?.
" aunty naga irin rubutunsa.
Dariya, tobashine yarubutaba nice nan.
Kece kuma? To tayaya?.
Hummm auta haryau ke yarinyace, bazaki ganeba, nad'au tsawon lokaci ina kwaikwayon rubutunsa hardai ALLAH yabani nasara na iya, dama saboda irin ranarnan nakoya.
Jinjina kai nayi INA mamakin kalamanta, to aunty tayaya kike gani Yaya zaiba iman takardar sakinnan?.
Aunty tayi murmushi wannan ai mai sauk'ine kedai kisaka idanu kisha kallo.
Bayan kwana uku dayin maganarnan da yamma sai aunty takirani tabani takardar wai naje k'ark'ashin filon iman nasaka, cike da tsoro nake kallonta tadakamin tsawa, ke sakara idan bazakiyiba abarsa kefa nake taimako zaki zauna kina kallona.
Jiki tana rawa na kar6a na nufi 6angaren iman, babu kowa afalon sai TV daketa 6a6atu, asand'a nashiga d'akin iman nanma babu kowa saidai naji motsin ruwa abayi alamar tana wanka, da Sauri nad'aga filon farko nasaka takardar nafita da Sauri, gafff mukai karo da Ya Isma'il ak'ofar Fita daga falo, yanda jikina ke 6ari saiya tsaya yana kallona.
Kekuma lfy?, yafad'a idonsa akaina.
Da Sauri na daidaita nutsuwata na ce, "wlhy 6era Nagano Kasan kuma INA tsoronsa.
d'an murmushi yayi yana girgiza kai, kekam keda 6era kun k'ulla, amma ta inama 6era yashigo gidanan?.
Na ce, " halan ta k'ofar baya ko.
Hakane kuma, bari zan fad'ama saudat taringa rufe wajen idan yamma tayi.
Okey bari nawuce dama nazo Neman Deexerh ne Ashe bata nan.
Tom saida safe tafad'a tana shigewa.
Dagudu na Isa 6angaren aunty na rungumeta INA dariya na ajiye wlhy ammafa ankusa kamani, anan nabata labari tayi dariya kedai akwai shegen tsorone kawai.
Shikenan matsalarmu ta k'are muka tafa.
Washe gari bayan tafiyar yaya iman tasamu takardar....... Raihan tak'are maganar da shashshekar kuka, wannan shine abinda ya faru.

Gaba d'aya falon aka d'auki salati da tafa hannaye.
Aunty da Raihan sai kuka sukeyi.
Chapter 32 · 0% Book details