← Book details Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 46

Sashe 1

Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

[8/6, 5:59 PM] mrs bilkisu: ________________________________
BAN SAKETA BA!!!
________________________________
NA
BILKEESA IBRAHEEM
{Bilyn Abdul}
________________________________
https://mrsbilkisa.blogspot.com

ALHAMDULILLAHI ALA KULLI HALIN.
ya ALLAH kabani ikon faďin abinda zai amfani al'ummarka ka tsare harshrna daga faďar abinda zai cutar da al'ummarka.AMeen.
😂ina farincikin sake haďuwa daku a sabon littafina, mai suna BAN SAKETA BA😂👌🏻.

Duk wanda ya canja mini wani abu aciki ban yafe masaba😎.

Ina mi'ko ďunbin godiya da gaisuwa tareda fatan alkairi ga dukkan masoyana, ina godiya da ďubin gaisuwarku gareni, dason fara rubutun BAN SAKETABA,, da nabari sai bayan biki amma 'kaguwarku tasa bazan iya share bu'katunkuba,, dan haka zan fara, saidai zakumin uzuri dan zan gaza baku posting akowace rana, sakamakon nayi busy dayawa, ALLAH yasa mudace,, muje zuwa LABARI😁👌🏻.

Sadaukarwa~ ya Abdul {city phone's}

Page......1⃣

.......Yauma kamar kullum tana 'kasan dalbejiyar data zame mata tamkar ďakinta aduk lokacin da bata da lecture's.
Kallo ďaya zaka mata kagane tana cikin duniyar tunani, da sauri taďago kai tana dube2, taja numfashi mai 'karfi, cikin sanyin murya ta ce, "hancina kadaina faďa min 'karya, ka daina sha'ko min abinda ba gsky ba, tunda nake awajen mutum ďaya nata6a jin wannan 'kamshin, kuma tunda yanisan ceni ban sake jiba, ban bashi damar dazan sake jiďinba, domin shi ya kasance mugu azzalumi, macuci!!!....ta faďa tana mai zubar da hawaye.
Wlhy na tsaneka Isma'il!!! mayaudari kawai ta fashe da kuka mai ban tausayi.
Haba iman kina ganin haka rayuwa zata kasance kullum cikin kuka da tunani??, maganar miss xoxo takatsema iman surutan datakeyi, iman mu masoyankine masu 'kaunarki 'kauna irinta 'yan uwan juna, tundaga randa muka fara ganinki a school ďin nan mukaji muna 'kaunarki, dan ALLAH badan muba ki sanar mana damuwarki kozaki samu sau'ki, idan kuma munada taimakon dazamu yimiki saimu taimaka miki koda da addu'ane.
Gsky ne Miss xoxo yakamata iman tasanar mana damuwarta inhar ta yarda damu kamar yanda muka yarda da'ita, yau kusan shekararmu biyu da watanni tare bamu ta6a 6oye miki sirrinmuba, duk abinda yadamemu muna sanar da junanmu, ke kaďaice acikinmu kike 6oye mana sirrinki, bamusan dalilin hakanba kokuwa bamu cancanci sanin taki damuwar bane oho??, amma kinsan damuwarki itace tamu, farincikinki shine namu, wlhy inaji ajikina tamkar uwa ďaya uba ďaya suka haifemu.
Gskyarki ne Reefat xoxo tafaďa tana gyara zama, takamo hannun iman ta rumtse anata, iman inhar kin ďaukemu a matsayin 'yan uwa ko 'kawaye na kwarai to ki sanar damu damuwarki, koda addu'ane mutayaki, mungaji da ganinki haka iman, shekara biyu ba kwana biyu bace, inkuma bazaki faďa manaba bazamu takurakiba, saidai zamu taimaka miki da addu'a insha ALLAHU.
tami'ke Reefat tashi mutafi xoxo tafaďa tana kama hannun Reefat.
Iman ta fashe da kuka dan ALLAH xoxo karku tafi, kuyi ha'kuri ku saurareni.
Ya za'ayimu saurareki iman kullum haka kike faďa mana amma kin kasa faďa mana komai, kina ganin zamu cigaba da takuraki harsai kin sanar damune??, dammi zamu takura miki akan abinda bakida ra'ayin faďa mana???.
Naji na amsa laifina amma dan ALLAH kudawo karkuyi fushi dani, wlhy nima ina 'kaunarku inajinku tamkar 'yan uwana najini.
ALLAH sarki xoxo akwai tausayi dan haka saita jawo hannun Reefat suka dawo suka zauna, tsakiya suka saka iman, Reefat ta ce, "iman muna jiranki dan ALLAH ki sanar damu damuwarki kinji, 'kila mu iya taimaka miki da wani abu.
Iman tasa hannu ta share hawayenta tareda ďanjan hancinta, tabi aminan nata da kallo, miss xoxo Reefat kuyi ha'kuri ban ta6a 6oye muku wani abu daya danganci rayuwata saboda rashin yarda daku ba, a'a ina ganin abinda yafaru dani tamkar sirrinane tunda yafaru dani a shekarun bayane kafin na haďu daku, sannan ina ganin abinda yafaru dani yariga ya faru ya wuce, amma ina neman afuwarku gareni, insha ALLAHU a wanan karon zan faďa muku wacece SAUDAT!?" saidai kuyi ha'kurin zuwa weekend sanan muna free saimuyi maganar atsanake.
Zan faďa muku tushen rugujewar rayuwata da tushen tubalin ginin damuwata......ta fashe da kuka mai tsuma zuciya da ruhi, ganin haka Reefat da xoxo suka shiga tayata suma, saida sukayi kuka mai isarsu babu mai lallashin wani, saida suka gaji dan kansu sanan sukayi shiru.
Mi'kewa sukayi suka nufi class kowa zuciyarsa babu daďi, iman sai waige2 takeyi danjin tamkar 'kamshin turaren yana bibiyarsu, Xoxo ta ce, "iman wai mikike nemane??, lokaci da dama nakan ganki kina waige2 miyasa??.
Murmushi Iman tayi na takaici, wanan duk yana cinkin tarihin rayuwata xoxo karki damu asannu zaki gano abinda yakesani waige2 a wasu lokuta da dama.
Daga nan suka shiga aji, babu daďewama malami yashigo suka fara ďaukar darasi...............✍🏻

Tofa masu karati komi wanan littafi ya kusa??, shin miye damuwar kawarsu Miss xoxo ne??, dani daku duk akan tambaya ďaya muke, domin nima bansan komai gameda hakaba, sai munbi wanan labari sannu ahankali sannan zamu samu amsar tambayoyin dake fal a zuciyarmu.

Takuce dai Bilyn Abdul.
Saikunjinei!!!!!!👌🏻

Luv u oll my fan's
©2017
Battery low🔋😜👌🏻
[8/6, 5:59 PM] mrs bilkisu: ________________________________
BAN SAKETA BA
________________________________
NA
BILKEESA IBRAHEEM
{Bilyn Abdul}
________________________________
https://mrsbilkisa.blogspot.com

Sadaukarwa~ ya Abdul {city phone's}

MIYAKAMATA NAYI???.
amatsayina na uwa miya kamata nayi??, alokacin dana fara mallakar 'ya'yana 'kyautar ALLAH, 'kyakykyawan lafazi, yawan addu'a, nasiha alokacin dasukayi ba dai2ba, cusamusu tsoron ALLAH azuciyarsu tun suna 'kanana, domin icce tun yana ďanye ake lam'kwasashi,
ALLAH yasa mu gyara.

Page~2⃣

...........miss xoxo & Reefat matasan 'yammata 'kyawawa, ga nutsuwa da ilimi, tundaga randa aka kawo iman school ďinsu suka haďu suka 'kulla abota mai 'karfi da zuminci, suna 'kaunar junansu, wanda bai saniba idan yagansu saiya ďauka 'yan uwan junane dama can, amma abin ba haka bane..
Miss Xoxo 'yar Kano ce karatune yakawota garin na ZARIA...Reefat kuma 'yar Yola ce ADAMAWA itama sanadin karatu tazo garin na ZARIA, itakam iman 'yar katsinace & kano .
Bayan sun kammala luctures ďinsu suka nufi ďaki agajiye, Reefat tazube a tsakar ďaki tana faďin wash ALLAH na, nagaji wlhy, malamin nana yayi mugun wahalar damu gsky.
Miss xoxo ta ce, kibar ďan iska Reefat saikace daga kansa aka fara ilimin boko, ALLAH na tsanesa tamkar mutuwata, shege gashi mummuna sai girman kan tsiya kamar ďan wani da wata.
Kudai ALLAH ya shiryeku iman tafaďa tana fitowa daga bayi, kuzauna kuyita zagin malamanku saikace wasu 'kawayenku.
Reefat ta harareta ai dama ke bazaki ganewaba, wannan ďan iskan malamin bashida kirki, kidubafa yanda yadaka miki tsawa ďazu ALLAH yabani haushi.
To kuyi ha'kuri malamin mune, kunga yanada ikon nuna mini kuskurena kenan..
Xoxo ta ta6e baki kinga Reefat barta indai iman ce babu abinda zaki faďa akan malamai ta amince.
Iman ta ce, "kudai kuka sani nikutaso muci abinci ALLAH yunwa nakeji.

Yau juma'a 'yammatan suna free basuda lectures ko ďaya, suna gida, dawuri suka gama komai na al'adar rayuwarsu dan sonjin labari, suduka suna cikin ďakinsu sun saka tiren indomi a tsakkiya kowa da kofin shayi agabanta.
Iman ta mi'ke domin ďakko wayarta dake ajikin caji, kamar jira ake ta kunna kira yashigo, tayi murmushi sanan ta ďaga, hello my bro's ya gida??.
Daga can 6angaren aka amsa mata, ta ce, "yasu gwaggo??,
Kowa 'kalao aunty, ya karatunki??.
Muna nan muna bugawa.
To ALLAH ya taimaka.
Amin autan gwaggo.
Dama Musayyeef ne ya ce, "nakira ki ku gaisa, okey yana ina??, gashi.
Hello aunty Maa! kina lafiya??, lafiya lau musayyeef ykk ya makaranta??.
Aunty maa! lafiya lau.
To kana dai 'kokari ko??, eh mana, harma anty tace nafi kowa 'kokari a class ďinmu.
Da 'kyau ďan albarka, to mikake bu'kata??, babu komai aunty maa! dama inaso na sanar miki jiya da dare uncle ďi na yazo.
To naji sai anjima na kiraka muyi hira yanzu ina karatu.
To aunty maa! sai anjima....yaron ya faďa cikin tsallen murna.
Bayan ta kashe wayar tadawo ta zauna saidai fuskarta babu walwala.
Xoxo ta ce, "lafiya naga kin canja fuska dawa kikayi waya??, tayi murmushin ya'ke lafiya lau mikika gani??, da Musayyeef nayi waya fa.
Reefat ta ce, "miyasa baki bani shiba mun gaisa, autan gwaggo sarkin wayo, inason yaronnan wlhy kamar gwaggo tabani, iman tayi dariya mizai hana tabaki indai kinaso??.
Xoxo ta ce, "aii koni ina 'kaunar yaronnan, duk yafi 'yan gidanku 'kyau, kamar ba ďan gidanba.
Iman tayi dariya hakadai kukace, amma yama za'ayi yafimu 'kyau, aii banma yardaba, hakadai sukaita hirar Musayyeef har suka gama cin abincinsu.
Bayan sun gaba duk suka nutsu suna sauraren iman, iman ta gyara zama sanan taja ajiyar zuciya mai 'karfi.
Chapter 1 · 0% Book details