Sashe 3
Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Awata Asabar datayi dai2 da dawowar Dr Isma'il kano, dan ayanzu yazama soja, ALLAH yacika masa burinsa, yazama likitan sojoji, gashi likita gashi babban Soja.
Aranar natashi da matsanancin ciwon mara wanda zan iya cemuku tamkar yafi na kullum ma dan har suma nake, gaba ďaya hankalin iyayena yatashi, ankira likitan dake taimaka min yaymin allurar amma abanza dan babu abinda ya canja agareni, har zuwa 'karfe huďu na yamma, saidai yalafa yadawo.
Awanan lokacin tuni Dr Isma'il yana gida yana hutawa, amma sai barcin ya gagari idanunsa, dan tunda yashigo kano gabansa ke faďuwa zuciyarsa tanata kwaďaita masa son ganina, dan ba 'karamin kewata yayiba acikin shekara ďayar nan..
Zumbur yami'ke yacanja kayansa zuwa shadda mai 'kyau ďinkin zamani, dan Dr Isma'il yanada 'kyau babu laifi, yafito falo yana ďaura agogo, auntynsa matar yayansa ta ce, "a'a angona sai ina kuma??.
Dr Isma'il yay dariya angon iman dai, kekam ga angonki nan akusada ke, ya nuna yayansa dake zaune yana masu dariya.
Ta ce, "wacece iman kuma??.
Dr Isma'il yay murmushi karki damu zaki santa kwanan nan, yanzuma sauri nakeyi amma kibini bashi idan na dawo zan sanar dake iman, yafice yana faďin yaya aunty saina dawo, yanaji tana kwala masa kira amma bai sauraretaba, motar yayansa ya ďauka yafice danshi bashida mota sai mashin, yayansa kuma baya masa shamaki da nasa motocin.
Yayansa ya tuntsure da dariya nikam kina bani mamaki keda Isma'il ke yanzu har kin yarda da zancensa ne??.
To ya bazan yardaba tunda bai ta6a kawo mana makamanciyar wanan maganarba.
Ito hakane ALLAH yasa da gsk yakeyi.
Dr Isma'il kuwa kaitsaye gidanmu yanufo, yay parking a kofar gida, yana tsaye gaban motar saiga deeni yadawo daga aika.
Dr Isma'il ya ce, "zomana abokina, babu musu deeni ya'karasa garesa, ya gaishesa.
Dr Isma'il ya ce, "dan ALLAH shiga gidanan kamin sallama damai gidan.
Deeni ya ce, "wai Abbah??.
Eh shinake nufi, ko kaima ďan gidanne ?, dan naga kana kama da Iman.
Ya ce, "lah ina kasan aunty iman??, Dr Isma'il ya ce, "anan gidan, to aii yanzuma itace batada lafiya dan har suma takeyi, aruďe Dr Isma'il ya ce, "suma kuma??, deeni ya ce, "eh suma, to yanzun Abbah na nan?, eh yana ciki, jeka ce masa Isma'il ne yazo gunsa.
Deeni yazo ya sanar da Abbah, Abbah yanajin Dr Isma'il ne da hanxari yafito, bayan sun gaisa Dr isma'il ya ce, "yanzu wani yaro yake sanar dani Iman babu kafiya?.
Eh hakane Isma'il.
Sun shigo gidan, sanda suka shigo inata mur'kususu ajikin gwaggo dan har wani shiďewa nake saboda azabar ciwo, gwaggo sai kuka take.
Dr Isma'il yakalli Abbah aruďe Abbah idan bazaka damuba na ďauketa muje asibiti mana.
Abbah ya ce, "babu wata matsala Isma'il......aibai bari Abbah ya 'karasa faďaba ya sunkuceni yay waje, amota yasakani Abbah yakaraso da hanzari yashige muka tafi asibiti, acanma ďaukata yayi, ďaki guda aka waremini nikaďai, ya shiga bani kulawa ta musamman, cikin 'yan mintina ya shawo kan matsalata harna samu barci................✍🏻
💕💚💕
Page~4⃣
..........Washe gari nadawo dai2 ina kwance agado gwaggo tana zaune akusa dani, aunty Salma kuma tana tsaye tana waya, Dr Isma'il yaturo 'kofa yashigo da sallama, rissinawa yayi ya gaida gwaggo, gwaggo tami'ke tafita dan tanajin kunyar sirikin nata, itama aunty Salma saitayi waje, Dr Isma'il yajawo kujerar da gwaggo ta tashi ya zauna kusadani ya tsuramin idanu Iman ya jikin naki?.
Cikin jin kunya na ce, "da sau'ki.
yanzun babu inda yake miki ciwo?.
na ce, "babu, ya ce, "Alhmdllh.
Ince dai kinci abinci ko?, naďan kalleshi ta gefen ido na ce, "a'a na koshi, ya ce, "mikikaci da har kika 'koshi?, na ce, "nasha tee ďazu.
Yay murmushi kice na shirya nemo maganin cin abinci matata batason cin abinci, da sauri na kalleshi, ya kannemin ido ďaya tareda ďaga gira, hannu nasa na rufe fuskata saboda kunya, ya ce, "inson mace mai kunya ashe ALLAH zai bani, na kuma cusa kaina cikin cinyoyina.
Yay dariya sanan ya ďauki filet, kulan da aunty salma tazo dashi ya buďe, ya ce, "iman lallai ke 'yar gatace, wannan irin farfesu haka, nidai kaina na tsakiyar cinyoyina nakasa ďagowa saboda kunyar maganganunsa.
Ya zuba farfesun yace nazo naci nasha magani.
Na ďago kaina cikin jin kunya na ce, "kawo to, ya ce, "waneni da barin gimbiya cin abinci da kanta, aii da hannuna zan baki, na ce, "A'a ngd zanci da kaina, ya ce, "nikuma ban yardaba, haka dole na hakura yabani da kansa, saidai cikin matu'kar jin kunya nake kar6a, shikam sai dariya yake mini.
Aranar aka sallameni muka koma gida..
Kunaga kutashi muyi sallar la'asar sanan saimu cigaba.
Bayan sun idar da sallar la'asar iman ta ďora labari.
Iman tabi Reefat da Xoxo da kallo tareda jan numfashi, wato 'yan uwa bayan kwana ďaya da sallamata Dr Isma'il yazo gidanmu, an masa tarba ta mutunci, dan su gwaggo suna son Dr Isma'il sosai.
Bayan sun gama gaisawa Dr Isma'il ya ce, "Abbah dama nazone nayi muku bayani akan ciwon iman.
Abbah ya ce, "ina saurarenka Isma'il.
Dr Isma'il yay 'kasa da kai sanan ya ce, "wato Abbah naďanyi bincikene akan ciwon iman, saina gano ta hanya ďayane kawai zata iya rabuwa da ciwon, hanyar kuma itace......saikuma yayi shiru, Abba ya ce, "inajinka Isma'il karkaji komai ka sanar dani, Dr Isma'il ya 'kara kasa da kai dan maganar tayi masa nauyi abaki, amma ya daure ya ce, "hanyar itace aii mata aure, ta wanan hanyar kawai nake ganin za'a samu mafita.
Abbah yay murmushi to aii Isma'il inadai hakane banida damuwa tunda lafiyarta muke bu'kata, inaga indai har iyayenka sun amince saisu turo, inyaso saita cigaba da karatun a ďakinta, dan haka nabaka dama kaje kayi shawara da nagabatanka, nima zanyi da gwaggonsu dakuma 'yan uwana.
Dr Isma'il ya ce, "to ngd ALLAH ya 'kara girma.
Abbah ya ce, "amin, yami'ke yana faďin bari na turo maka maman tawa.
Bayan Abbah yashigo ya ce, "naje falon ba'ki ana jirana, na ce, "to, hijjabi nasaka na nufi falon, yana zaune akujera mai zaman mutum ďaya, yana cikin farar shadda ďinkin boda amma babu hula akansa, yayi min 'kyau sosai, dan Dr Isma'il farine 'kyakykyawa, yanada suma mai 'kyau wadda take shan gyara, bayida saje saidai wani ďan gemu na gayu daya ajiye, wanda ya'kawata 'kyawun fuskarsa, dogone sosai yanada 'yar kiba daidai misali, akwaishi da yawan fara'a, dan a yanda nakula kamar ba miskili bane.
Da sallama na shigo 'kamshin turarensa ya bigi hancina, inason kamshin turaren tun sanda aka fara kaini asibitinsa, yaďanja gilas ďinsa kaďan zuwa 'kasan ido, yakuramin idanunsa matsakaita girma, na zauna saman carpet, yay saurin faďin a'a ban yardaba tashi ki hau kujera, cikin jin kunya na ce, "nanma ya isa.
To shikenan nima bari na sauka kasan tunda nan kikeson mu zauna, ganin zai zauna kasa nayi saurin hawa saman kujerar, ya tuntsure da dariya to shikenan gimbiya, nidai kaina yana 'kasa na gaisheshi, ya amsa cikin fara'a, sanan ya ce, "ya jikinki??.
Na ce, "aii ni na warke.
Ya ce, "zakidai warke in sha ALLAHU nan gaba kaďan.
Murmushi kawai nayi batareda nayi maganaba.
Ya gyara zamansa sosai, tareda 'kara daidaita nutsuwarsa, yayďan gyaran murya alamar maganar dazaiyi tanada muhimmanci.
Ya ce, "imaniii nasan kin sanni tunba yanzuba, tun sanda aka fara kaiki asibiti a matsayin patient ďina??, na ďaga kai alamar hakane, ya jin jina kai, to tun aranar naji kin kwanta min arai, nakamu da sonki na gsky, dalilin dayasa na sanar da majeed abinda ke raina kenan, shine ya shige mini gaba zuwa wajen abbah, banyi kasa aguywa ba wajen sanar da abbah sirrin zuciyata.
Alhmdllh Abbah ya fahimceni yakuma kar6eni amatsayin siriki, tunkuma a wancan lokacin ya mallaka minke, yakuma bani damar neman so awajenki.
Alokacin nayi wani nazari akanki, dan na lura ke yarinyace karama, wanan dalilin yasa na ce, "abarki sainan gaba, dama na sanar dasune kamar yanda addinina ya koyar dani, to saikuma wani uzuri yatasomin alokacin, natafi training ďin soja saboda tuni inason zama soja, saidai yayana yafison nazama likita, ina girmama bukatarsa dan haka nacika masa burinsa nazama likita, tonima sai ALLAH yacika min nawa burin nasamu damar zama soja ayanzu.
Ranar dana iso kano saina tarar bakida lafiya, danayi bincike akan ciwonki saina gano nine maganinsa, dan haka nazo yaunayima abbah bayanin komai.
Ya gyara zamansa to yanzudai zancen danake miki abbah yabani izinin turo iyayena su nemamin aurenki, shiyyasa nakeson jin tabakiki dan kar asoya mai amanta da albasa iman kina SONA kuwa???, nayi miki??, karki 6oyemin sirrin zuciyarki kinji..
Gsky naji kunyar zancensa dan haka na 6oye fuskata da tafin hannuna, Dr Isma'il yazare gilas ďinsa karkimin haka Saudat!!, ki daure kisanar dani kina SONA???.
cikin jin kunya naďaga kaina alamar eh.
Yasaki murmushinsa mai 'kayatarwa ya ce, "Alhmdllh, iman nagode da soyayyarki gareni, ALLAH yabarmu tare har abada, yakuma kaďe duk wata fitina dazata wanzu a tsakaninmu, ala66ana na ce, "amin ya rabbi.
Ya kalli agogon hannunsa idan bazaki damuba zan sanar dake koni wanene dan naga munada sauran lokaci.
Na ce, "babu damuwa.
Lemo ya ďauka ya tsiyaya acikin kofi, yasha kaďan sanan ya ajiye, ya ďauki gilas ďinsa yasaka, gilas ďin yana matu'kar kara masa 'kyau sosai.
♡☆♡