← Book details Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 46

Sashe 20

Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

*(page 17)*
'Dan murmushi yayi Dan ganin yanda tawani d'aure fuska. Yajuya yakali su deexerh, yaga hankalinsu baya kansu, ta waya sukeyi.
"Juyowa yayi kan iman, data maida kallonta ga Gila's, *_"Imman!"._* yafad'a dawata irin murya mai cike da kasala.
Banza tayi masa kamar batajiba, ya ce, " wlhy koki juyo kona k'ara bud'e Gila's d'inan, nanama shiru tayi masa bata tankaba.
Ganin bazata juyoba yasashi sauke Gila's d'in, wani sanyi yafeso harda k'ank'ara, babu shiri tajuyo tana sauke ajiyar zuciya, Gila's d'in yarufe yana 'yar dariya, haushine yaturnik'e zuciyar iman, sai Kawai tafashe da kuka.
Jingina bayansa yayi da murfin k'ofa yadasa mata mayun idanunsa, ko k'yafatawa bayayi, sai yanzu yay mata kallon tsaf, ganin yayi tak'ara k'yau harda 'yar k'iba, dakaga Iman zakasan tana cikin kwanciyar hankali, atake zuciyarsa takawo masa wani tunani.
"Koadai Iman k'arya take ita tarubuta takardar sakin nan Dan bata sonsa??, wani irin d'aci ya turnik'e zuciyarsa"..
K'irjinsane yafara masa nauyi, indai hakane Iman taci Amanarsa, tajefashi cikin mawuyacin hali, ga ciwo ga matsananciyar sha'awarta dake addabarsa, saboda gudun fad'awa halaka yasashi kullum yake kasancewa cikin azumi, gashi yanzu dukda yana azumin dauriya kawai yakeyi, yarintse idanunsa, Azuciyarsa ya ce, " *BAN SAKETA BA!* miyasa zatace nasaketa?, shin dama bata k'aunatane?, wani dogon tsaki yaja, Wanda baisan yafitiba, gaba d'aya suka d'ago suna kallonsa.
Tada motar yayi yafisgeta da k'arfin tsiya.
Gaba d'ayansu hankalinsu atashe yake, ganin yanda yafisgi motar yasa deexerh datasan halin dayake ciki, kuma taga Iman na kuka sai hankalinta ya tashi.
"Ta ce, ''Uncle lfy kuwa?".
Baice mata k'alaba Dan yafara fita hayyacinsa, shikansa baisan ayanda yake tuk'inbama.
Ganin sunfara yawo a titi yasa hankalin Iman komawa Kansa.
" innalillhi wa'inna ilaihirraji'un", Doctor! Pls karka kashemu, kayi hak'uri Dan ALLAH.
INA baimasan tanayiba, da sauri deexerh ta taso tayi nasarar tsaida motar, danta iya, gefen titi suka gangara, saura kad'an subigi wata bishiyar Tsamiya, Xoxo da deexerh suka k'ank'ame juna suna Addu'a, Iman ma Dr isma'il ta k'ank'ame tana kuka, dukda baya cikin Nutsuwarsa saboda nauyin da k'irjinsa yayi masa, wannan bai hanashi rungume Iman ba sosai.
Ya kwantar dakansa jikin kujera yaruntse idanu, ga Iman rungume ak'irjinsa, sai wani irin Numfashi yake saukewa awahale.
Jin motar ta tsaya dakuma saukar Numfashin Dr Isma'il yasa deexerh d'agowa da Sauri, gabantane yafad'i, afili ta ce, "nashiga uku, kardai ciwon Uncle ne yakeson tashi?.
Sai asanan Xoxo da Iman suka d'ago, Iman tafara mutsu2n kwace kanta, amma takasa danba k'aramin ruk'o yaymataba.
Da sauri deexerh ta kwantar da kujerar, Yakuma k'ank'ame Iman kamar za'a kwace masa ita.
Motar tayi shiru bakajin motsin kowa sai saukar numfashin Dr Isma'il, da hannu yayma deexerh Nuni data bashi magani, cikin hanzari tabud'e motar tafita, gaban motar takoma, tabud'e wani waje, magungunansa tagani awajan, wani d'an farin roba tad'akko, Wanda tagani yana amfani dashi idan ciwon ya motsa kafin aje asibiti.
Abaki tasaka masa yazuk'a sau uku, yajanye bakinsa, Yakuma rungume Iman yanda bazata samu hanyar barin jikinsaba, cikin 'yan sakwanni barci yay gaba dashi.
Xoxo da deexerh bud'e mortar sukayi suka fita sabida an daina ruwan, said'an yayyafi.
Ga Iman so kawai take takwace jikinta, amma dukda barci ya d'aukeshi ta kasa.
Saida suka fita Xoxo talek'o.
"Iman pls kiyi hak'uri kinutsu waje d'aya, dadyn Musayeef yana buk'atar taimakonki, kitausaya masa halin dayake ciki, mu zamu zauna a waje harya farka idanma kunyarmu kikeji.
Shiru tayi dantasan maganar Xoxo gsky CE, to Amma aii babu dacewa, tunda ayanzu Shiva mijinta bane, gani take zunubi kawai zata kwasa abanza a wofi.
Wasu zafafan hawaye suka zubo akumatunta, addu'a tashiga karantowa ahankali harta samu nutsuwa.
K'ara gyara kwanciya tayi sosai, tak'ara kwantar da kanta visa faffad'an k'irjinsa, tunanin rayuwarsu tabaya tashiga yi da Doctor, taringa tuno so da k'auna gamida tattali daya ringa nuna mata, amma gashi yanzu k'addara ta rabasu, sunyi nisa da juna, ahaka taringa tunani da shak'ar kamshin daddad'an turarensa har barci yay ayon gaba da itama.
(Nace da k'yau iman, anji k'irjin boss😜).

Xoxo takalli deexerh, kinga gawata rumfa can kozamu koma Canne?. eh wlhy kuwa muje can, Dan naga ruwan yanad'an jik'amu ahankali.
Kafin su wuce deexerh talek'a Dan taga halin da Uncle d'inta yake ciki, murmushi tayi tareda share hawayen tausayi, Dan ganin yanda itama iman barci ya d'auketa.
Xoxo ta k'araso tana fad'in lfy kuwa?.
Murmushi deexerh tayi tana nuna mata su iman, itama d'an murmushi tayi, sun bata tausayi matuk'a, suna kewar junansu sosai, amma zalunci yasa an rabasu, (tana k'ara tsinewa azalumin dayayi wanan zalincin, Dan tasan ALLAH bazai barshiba).
Hannunta deexerh taja suka tafi runfar, wadda da'alama an tanajeta saboda irin hakan.
Wuri suka samu suka zauba sunata hira, da tattauna yanda zasu taimakawa su iman.

*Reefat*
A6angaren Reefat kuwa, tunda suka tafi ta kifa kanta saman cinya tanata kuka, ya Usman bai hanataba Dan yasan zafin rabuwa da masoyi, tuk'insa kawai yakeyi, gashi yaga alamar hadari agarin.
Saida sukayi tafiya mai nisa sanan yaga kukan na Reefat bamai k'arewa bane, Dan haka yay gyaran murya, tareda fad'in Shareefat!.
Ahankali ta ansa, batareda ta d'agoba, ya ce, "d'ago mana kiji wani Abu.
Bata musa masaba, tad'ago kanta, idanunta sunyi jajur, ya ce, " kalleni mana.
Ahankali tad'ago tana kallonsa, yasakar mata lallausan murmushi, da Sauri tayi k'asa da kanta itama tana murmushin.
Kokefa yafad'a yana dariya, kukan ya Isa haka, muyi hira.
Nanma murmushi tayi, ahankali yarink'a janta da hira harta saki jikinta aka koma soyayy😜lol.
Chapter 20 · 0% Book details