← Book details Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 46

Sashe 14

Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_*bayan kwana uku*_
Bayan kwana uku nadawo normal, nayi wankan tsarki, dukda ban sanar da doctor ba yasani dan yana rik'e da adadin kwanakin danakeyi.
Muna zaune nida deexrrh da Raihan muna kallo, dan takan shigo tareda deexerh, saidai bansan dalilintaba tunda har yanzu bansan abinda ke tsakaninta da doctor ba, kuma nakasa tambayar deexerh.
Munacikin kallon saina farajin barci, dan haka nazame saman doguwar kujera na kwanta, nabarsu suna kallonsu.
Doctor bayanan yafita tun ďazun.
Cikin barcina nakejin k'amshin turaren doctor, nasake ware hancina dan ina matuk'ar son turaren, zan iya cemuku awajensa kawai nata6ajin turaren nan, nabuďe idanuna ahankali saboda kusantowar turaren sosai kusada hancina.
Ware idanu nayi saboda ganin fuskar doctor kusada tawa, harma munajin saukar numfashin juna, naďan kauda kaina gefe saboda kunyarsu deexerh.
Cikin jin kunya na ce, "doctor yaushe jadawo??.
Hannunsa yasa yadawo da fuskata inda take da, idanuna naruntse dan bazan iya kallon kwayar idanunsaba.
Bakina yasumbata ahankali yafurta my iman inason kunyarnan taki wlhy.
Bance komaiba sai mik'ewa danayi dan nagashi bayajin kunyarsu deexerh dake folon.
Karaf na haďa ido da Raihan tana kallonmu, ta haďe fuska tamkar zata haďiyi zuciya tamutu, tai k'asa da kai saiga hawaye sharrrr akan kumatunta, da sauri tashare dankar agane, saidai ta makaro dan duk mungani, deexerh ta ta6e baki.
Amma fuskar doctor ta nuna alamun gizago.
Deexerh ta ce, "sannu da zuwa uncle.
Yauwa babyna ya gidan??.
Ta ce, "Alhmdllh.
Ganin haka itama Raihan ta ce, "sannu dazuwa yaa Isma'il.
Itama ya amsata damar yanda ya amsawa deexerh.
Dukda bansan matsalartaba tabani tausayi.
Najuyo ina kallon doctor danufin tambayarsa mizan kawo masa, saiya saki murmushin basarwa kawai.
Na ce, "mikakeso akawo maka?.
Yaďan sosa sumar kansa yana satar kallon deexerh da Raihan, sai kawai yamik'e yakama hannuna muka nufi ďakinsa.
Hummm wai kunsan miya faru?.
Sukace a'a".
Damuka shiga saiya hau tambayata wai miye matsalar Raihan??, yabani matuk'ar dariya, saboda kular danayi yana matuk'ar yimini kallon k'aramar yarinya.
Sai kawai nayi amfani da damata na ce, "saboda kai take kuka mana.
Aďan razane ya ce, "kamarya sabodani?.
Nayi murmushi ina kallonsa, na ce, "nima amsar wanan tambayar nakenema, ina gama faďa nayo waje.
Bina yayi da kallon mamaki, yakasa koda yunk'urin ďaga yatsa bare ya iya kiran sunana, nikam wallahy maganar tazominne kawai amma bada niyya nafaďaba.
Abubuwan motsa baki nahaďo masa, har nadawo bai matsa daga inda nabarsaba, na ajiye tiren hannuna ina murmushi, naje nakamo hannunsa na zaunar abakin gado, nazuba ruwa akofi na đora masa abaki.
Yako buďe baki yashanye dan yana buk'atar buk'atar abinda zai jik'a masa mak'oshi yasamu damar haďiyar yalwataccen yawu.
Yanasha idonsa akaina, nima kaina mamakin kaina nake da irin wanan abubuwa, kwata2 babu kunya ataredani, ya shanye tas, sanan najanye kofin.
Kusada shi na zauna ina faďin lfy kuwa doctor?.
Wata wawuyar ajiyar zuciya yaja, yay saurin basarwa dan fuskarsa tana da k'ok'arin 6oye sirri, ya ce, "mamaki maganarki tabani kawai.
Wata 'yar dariya nayi na ce, "lah nifa tsokanarka nake, bammasan maganartawa tayi kama da abin mamakiba aii.
Nafaďane kawai dannaji tabakinka.
Ya rausayar da kai gefe yana bina dawani shu'umin kallo, tabbas yasan nacanja salone, amma na burgeshi, dan hakan ya nuna masa bayyanar wayona, shima saiya basar kawai yay dariya.
Amma iman kin iya kulli wlhy, harkinsa hankalina tashi, dan banason abinda zai 6ata mini ranki ko kaďan.
Na ce, "ko?"
Yajinjina mini kai alamar eh".
Yayi k'yau nafaďa ina k'ok'arin mik'ewa, da sauri yajowoni saman cinyarsa, yamatseni akan faffaďan k'irjinsa daketa tashin k'amshi.
Cikin kunnena ya ce, "kishi ko iman??, nasaki sassanyar dariya wadda yakejinta harcikin kwakwalwarsa, na ce, "a'a wlhy, tsam ya rungymeni a k'irjinsa yana fidda numfashi a sark'e.
Yanda yake fidda numfashin sai tsoro yakamani, na ďago daniyyar tambayarsa lafiya saiya haďe bakinsa da nawa, naga takaina nafaďa azuciyata dan nasan saina sha murza bata wasaba.
Aiko nashata dan yau har inda hannunsa baya kaiwa saida yakai, tuni tsoro da rawar jiki sun shigeni, nafara tsunguninsa da k'ok'arain zame jikina amma nakasa.
Saida yayi mai isarsa sannan ya sakeni yana murmushi da fidda hakki, idanunsa sunyi matuk'ar ja.
Da sauri na nufi k'ofa zan fice, ahankali ya ce, "plz karki fita su Raihan suna falon, zasu ganki awani iri.
Cak natsaya amma ban juyoba saidai nabi jikina da kallo, gsky yafaďa dankuwa duk ya yamitsemin jikina da kayana, maimakon nadawo saina jingina kaina da k'ofa.
Azatonsa kuka nake dan haka cikin nauyin jiki yataso gareni, tabaya yarungumeni yana magana ahnkali, sorry iman kibar kuka, badan na6ata miki raiba nakemiki hakan, saidai tsananin k'aunarki danakeyi, amma indai bak'yason hakan danakemiki nayi miki alk'awarin zan daina har saikin buk'ata da kanki.
Da sauri najuyo dan muryarsa kamar yana kuka, ganin idona k'amas babu akamar kuka yasashi zaro idani waje.
Sai kuma ya rungumeni, ya ce, "tsokana ko iman?, babu komai zan ramane.
Nayi shiru dan nakasa bashi amsa...
Bayan kamar minti talatin mun daidaita sai muka fito falon, amma wayam babu deexerh babu Raihan.
Sainaga kamar doctor yaji daďin hakan.
Amma ni sainace doctor bari nakira su Raihan su dawo ko?, kaga ka koresu.
Da sauri ya ce, "A'a barsu kawai, aii hakan dasukayi shine daidai.
Shuri nayi ina kallonsa dan ni aganina babu k'yau.
Kallo ďaya yamin ya kauda kai, dan yakula zancen bai shigeniba.
Babu yanda zanyi dole nazauna na barsu.

Har zuwa dare yahanani zuwa ko ina, hakan ba k'aramin haushi yabaniba, nayima deexerh test akan sudawo.
Amma saita turomin...👇🏻
_*hhhhhhh haba auntyna, babu wani dawowa dazamuyi, munbama uncle filine ya huta, dan haka saida safe, asamo mana baby mudai dan ALLAH😜.*_
Na ce, "ALLAH yashiryaki deexerh, zamu gauraya da safe aii.
Har isha'i ban je ko inaba, saida yatafi masallaci sanan naje nayoma mama saida safe, natarar deexerh da raihan suna 6angaren aunty, dan haka najuyo danba zuwa wajen nakeba da daddare saidai idan takama dole.
Ana idar da isha'i doctor yadawo, hannunsa ďauke da leda, bayan nayimasa sannu yabani umarnin juye abinda ke ledar.
Nasamo filet najuye gasassun 'yan shila lafiyayu da madara mai sanyi.
Gabansa natura duka yabini da kallo yana faďin kefa??, naďan marairaice murya na ce, "nak'oshi".
Dariya yayi ya ce, "ko?".
Na ďaga kai".
K'asa yasauka yana cigaba da dariyarsa wadda bansan inda ta dosaba dan bansan *Sirrin zuciyarsa ba* sabon littafina mai zuwa insha ALLAHU, *(SIRRIN ZUCIYA)*.
Baikuma cemin komaiba yajawoni jikinsa, yafara danna mini naman abaki, dole nakar6a inaci, yana koramin da madara mai sanyi.
Bayan munci munsha yasa tishu yagoge min baki, daganan yamik'e zuwa ďakinsa, nima na gyara wajen nayi nawa ďakin.
Na kalli agogo ko goma batayiba amma naga yau doctor kwanciyar wuri yake shirinyi.
Nidama banida matsala da wuri nake barci.
Nayi shirin barci tsaf na gyara kaina, nahau gado zan kwanta zuciyata fes babu wata damuwa.
Doctor yaturo k'ofar da sallama yashigo, na amsa ina kallonsa dan ganinsa da jallabiya sa6anin kayan barci.
Saida ya shimfiďa sallaya sanan ya ce, "taso kiyi alwala.
Kaina tsaye na ce, "nafayi sallar isha'i.
Eh nasani aii, zamuyi nafilane.
Na ce, "yanzu nayi alwalar kwanciya ma.
"Okey to taso".
Tashi nayi na ďora zani akan kayan barcina, nasaka hijjabin sallata, shi yajamana sallah raka'a biyu, bayan munyi sallama ya dafa kaina tareda karanta addu'a kamar yanda addininmu ya koyar damu, daganan kuma yacigaba da kwararo mana addu'oi na musamman, tun yanayi har muryarsa tafara zuga alamar zuwan kuka, dan yanama iyayensa addu'ane, tonimadai tayasa nafarayi dan yabani tausayi.
Yashafa nima nashafa sanan yajuyo yana kallona fuskarsa ďauke da murmushi.
Nayi k'asa dakai dan kallonnasa yana bani kunya.
Tambayoyi yaymin afannonin addinina.
Alhmdllh nabashi amsa yanda yatambaya saboda ina zuwa islamiyya.
Nakula ba k'aramin daďi yajiba.

Reefat ta ce, "oh ke iman ashe kinsan turaka..........iman tabuge mata baki kafin ta k'arasa suka tuntsure da dariya.
Miss xoxo ta ce, "ai gskyar Reefat wlhy, ashemu nan duk kallon kitse kike mana.
Tashi tayi tana dariya da faďin kudai kuka sani..................

_*((S))........2017*_
_*luv u oll my fan's*_
_*Battery low*_
[8/6, 6:01 PM] mrs bilkisu: *________________________________*
*BAN SAKETA BA!!!*
*________________________________*
*NA*
*BILKEESA IBRAHEEM*
_*{bilyn Abdul}*_
*________________________________*
https://mrsbilkisa.blogspot.com

_sadaukarwa_ *~ya Abdul {city phone's}*

*MIYAKAMATA NAYI??.*
_da mutuwa tana duban girma dabata ďauki tsofaffiba._
_da mutuwa tana duban milki dabata ďauki masu mulkiba._
_da mutuwa tana duban tsantseni dabata ďauki malamaiba._
_da mutuwa tana duban tausayi, dabata ďauki talaka da yaraba._
_da mutuwa tana duban jarumta, dabata ďauki matasa ba._
_da mutuwa tana duban addini, dabata ďauki musulmaiba._
_da mutuwa tana duban jin daďi, dabata ďauki turawaba._
_da mutuwa tana duban imani, dabata ďauki kafiraiba._
_da mutuwa tana duban kunya, da bata ďauki 'ya'ya, agaba iyayensuba, maza agaban matansuba, mata agaban mazansuba, iyaye agaban 'ya'yansuba._
_da!. da!!. da!!!!..........dayawa, sabodasu da mutuwa tabar kowa aduniyarsa._
_amma kash, itama tana cika umarnin *ubangijinta ne*, tunda mala'ikan mutuwa ya iya ďaukar ruhin mafificin halitta,_ _ma'abocin_ milki, imani, tausayi, talaka, _masoyi, mafifici, domin_ _addinima shine mai koyar da_ _muminai, dukiya,_ _(domin annbinmu baya cin sadaka,_ _kunga kuwa wadataccene,_ _danba tarin dukiya bace_ _wadata, a'a wadatar zuci,_ _dukmai wadatar zuci yawuce akirasa talaka), amma wanan bai hana yakusanci ubangijiba._
```To yakamata, nida kai da ke da su da ku damu gaba ďaya, muringa tunawa akwai mutuwa maizuwa maka akowane irin hali, akowane kuma irin lokaci.```
~Idan ko hakane yakamata kasancewarka musulmi mai imani, yaringa tunawa da zuwan mutuwa aduk halin daya tsinci kansa, walau alkairi ko sharri, inaganin idan muna tunawa da mutuwa zamu ringa rage aikata aikin sa6o.~
_Ka gwada na gwada ki gwada mu gwada mugani kozamu dace._
*ALLAH yasa mugane*

~*page........14*~
Chapter 14 · 0% Book details