← Book details Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 46

Sashe 12

Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

*MIYAKAMATA NAYI??,*
_Komai ka rasa zaka iya samun wanda ya fishi, Amma banda kwanakin rayuwarka, idan sun tafi sun tafi kenan, Domin haka karka 6ata rayuwar ka wajen abinda bazai amfane ka ba, yi kokari wajan yin abinda zai amfaneka duniya da lahira...""_
_kyautata ibadarka domin danmu bautama ALLAH ya halicemu, idan baka iyaba ko kanada k'arancin ilimi nemi malami ya koya maka, ba'a ibada da jahilci, "ubangiji baya kar6ar ibadar jahili._
_muguji salwantar da yininmu da kwananmu akan duniya da abinda ke cikinta, domin lokacin ďan adam mai tsadane, asarar second ďaya ga mumini daidai take da asarar shekara dubu._
_Mizai hana mutsara lokacinmu domin ammafanarsa a ranar data dace_.
```Karka bari duniyarka taringa tafiya tamkar cin abinci, dakaci saikayi kashi, kaga kuwa sara kenan```.
_gyara yau da gobenka domin amfanar jibinka_
*ALLAH yasa mugane.*

_*wannan page ďin nakune 'yan group ďina, ina alfahari daku sosai, ina k'aunarku har bansan iya adadiba, ALLAH yabarmu tare, kuďin nadabbane agareni, luv u wujiga wujiga, 😂lol👌🏻.*_

~*Page.......12*~

..................Bayan tafiyarsu kowa yakama gabansa, deexerh da Raihan suka fita raka mama wani guri, aunty ma takama gabanta, nikam saina tashi nashiga gyara 6angaren mama wanda ayanzu nice nake gyarwa na hana masu aiki yi.
Bayan na kammala na koma 6angarena, wanka na sakeyi dan 12 ta wuce, yau banajin kwalliya dan haka nashafa fauda kawai da abinda ya sauwak'a, bak'ar doguwar riga nasaka nayi k'yau sosai saboda k'ibar dana ďan k'ara, ga fatata ta murje gwanin sha'awa.
Falo nadawo na kwanta saman doguwar kujera tareda lumshe idanunana ina tunanin karatuna, inason na koma makaranta na k'arasa karatuna.
K'amshi yacikamin hancina, na buďe idanu ahankali, doctor nagani tsaye akaina yana min murmushi.
Na mik'e da sauri ina faďin sannu dazuwa, ince dai lafiya??, ya ce, "saiba lafiya mai gida yake dawowa gidansa?."
Na ce, "a'a, na kar6i ledar hannunsa dayake mik'omin, ya ce, "rakene nagani ahanya shine nasiyo miki ban saniba kozaki sha?.
Murmushi nayi na ce, "ina sha mana".
Na ajiye ledan saman tebir nanufi kicin, ruwa nakawo masa yasha, ya ajiye kofin yana faďin ngd sosai _gimbiya_, nikam duk kunya ta isheni dan haganin mayataccen kallon dayake bina dashi.
Kamar daga sama mukaga an banko k'ofa, gaba ďaya muka maida kallonmu wajen, aunty sadiya ce, ta ce, "lallai Isma'il dawowa kayi da wuri haka, lafiya kuwa??.
Ya daure ya ce, "lafiya lau aunty nazo ganin k'anwarkine.
Ta ta6e baki yo har yanzu batada lafiyar??.
Yaďan rage fara'a ta warke ina kwaďayin gani k'yak'yk'yawar fuskartane kawai.....nikam gaba nayi zuwa kicin domin haďo mada abin motsa baki.
Batace komaiba tanemi guri ta zauna, ta jawo ledan raken gabanta mikuma aka kawo mana ne??, baice mata komaiba dan al'amuranta sun fara bashi haushi, nashigo falon da sallama, shikaďai ya amsa mini, naje gabansa na ajiye filet đin kayan marmari.
Ya ce, "ngd babyna".
Nayi ďan murmushi kawai sanan nakoma kujerar nesa dashi na zauna.
Ya kalleni taso kisha mana?, na ce, "a'a duk nakane......kafin yayi magana aunty ta ce, "nida ba'amin tayiba bari nazo nasha, kan kujerar dayake zaune tadawo ta zauna kusadashi daf, taďauki cokali tahausha.
Ya ce, "a'a aunty mu mun isa muk'i yimiki tayi yafaďa yana matsawa, dayake doguwar kujerace.
Nikam nayi gum dan mamaki take bani idan tana wani 'yan kamancin, ya kalleni iman yadai?, ďan murmushin k'arfin hali nayi na ce, "babu komai.
Itakam ko kallo ban ishetaba sai danna abinta take.
Ya mik'e bari naje na watsa ruwa dan duk nagaji, na ce, "afito lafiya.
Ya nufo inda nake ya kama hannuna yana faďin aikece zakimin wankan, baibi takan auntyba muka nufi ďakin yana faďin aunty muna zuwa.
Wata uwar harara tarakomu da ita wadda nikaďai nagani, taja tsaki tatashi tafita, azuciyata na ce, " *kishin banza*.
Miss xoxo ta ce, " *kishin banza kam* tunda ba miji kuka haďaba, wai dama ana samun irin haka??.
Reefat ta ce, "sosaima, wannan shi ake kira kishin sauri, wlhy wasu irin wanan kishin yakesa suraba zumincin family ďin mazansu, akwai mata dayawa dake kishin banza kamar haka, kiga matar k'ani ta tsani matar wa, matarwa tana kishi da matar k'ani, tamkar mijinsu ďaya.
Miss xoxo da iman sukace to ALLAH ya shiryamu
*(ni bilyn Abdul na ce, "wanan asarar lokacine, yakamata mata kugane badan kishi aka haliccemuba bare ki 6ata lokacinki awajen kishin, garama ki nutsu kisan inda yake miki k'aik'ayi ki sosa, baki k'are akan kishin banza mara amfaniba, ALLAH yaganar damu)*
Reefat tamik'e taje tayo fitsari tadawo, drinks ta ďakko musu tazubo cincin afilet ta ajiye musu dan labarin sai anayi ana jik'a makoshi.
_(nima bilyn Abdul ina gefe danawa na katsire ina korawa dan inji daďin kwaso muku rahoto *lol*)_
Miss xoxo ta ce, "sis....jamije mana."
Iman ta haďiye lemon dake bakinta, taci gaba.
Bayan mun shiga ďaki ya zaunar dani bakin gado shima ya zauna kusadani, naďan takure jikina dan bako yaushe nakeso yata6aniba.
Hannuna yakamo ya damk'e anasa yamatso kusadani sosai, yana faďin abinda bak'ya son, dan tuni nakula bakison na ra6u jikinki bansan miyasaba?.
Na duk'ar dakai k'asa, ya ce, "faďamin kobaki sonane??, na girgiza kai alamar a'a, ya ce, "to minene dalili?.
Ahankali nađago kai ina kallonsa, ganin ya tsura min idonsa yasa nayi saurin maida kaina k'asa, na ce, "dama umma ta ce, "mana karmu yarda namiji yarik'e hannunmu, inkuwa ba hakaba zamu samu ciki.
Bai san sanda ya tuntsure da dariyaba harda kwanciya akan gado, nikam nasaki baki ina kallonsa, dan ba k'aramin k'yau dariyar taimasaba, inason sa sosai, harma bansan yanda zan musalta ba.
Jinayi an huremin idanu, naja wata ajiyar zuciya mai k'arfi, yay murmushinsa mai k'ayatarwa, sannan yagyara zamansa ya ce, "saudat!....yakira sunan dawata irin murya mai cike da kasala.
Na ce, "na'am".
Ya ce, "aii gwaggo tafaďa miki hakane danki kare mutuncinki ga wanda ba mijinkiba, nikuma mijinkine yafaďa tareda nuna kansa, aii ni yanzu ko rik'e hannun naki nayi kika samu ciki babu matsala, su gwaggoma murna zasuyi da samun jika.
K'asa nak'arayi dakai, shikuma yarungumoni sosai zuwa kikinsa yana faďin inasonki dayawa iman, ya ďago ya mannamin summba akumatu mai shiga jiki da 6argo.
Nikam sai k'ara sinne kaina nake ajikinsa ina k'ara shak'ar daddaďan k'amshin turarensa.
Jin anturo k'ofa ko sallama babu yasa yaďago kai da sauri yana kallonta, nima namik'e zaune sosai inaďan janye jikina daga nasa.
Lafiya kuwa?, doctor yafaďa yana kallonta.
Ta juya idanunta dasuke manya sosai nazo kiran iman ne mu ďora abinci.
Ya ce, "to tana zuwa, ta kalleshi yanda yawaniyi kicin2n da rai, tasan halinsa sarai idan ransa ya6aci dan haka tayi waje tana kun kuni.
Na kallesa ya haďe rai sosai kamar bashine yagama dariyaba yanzu, tsaki yayi sanan yamik'e yana faďin kwanannan zanyi maganin 'yar isakar matannan wlhy, nidai bance komaiba, yashige bayi.
Nimadai abin mamaki yake bani dukda k'arancin shekaruna, kuma gidanmu bantaso naga kishiyaba, bare nasan yanda ake kishi, saidai nakanji ana faďar kishi kishi.
To amma su waďancan ai mijinsu ďaya, nikuma ba mijinmu ďayaba, to kenan wanan kishin banzane takeyi??.
Maganar mama naji tana faďin ina iman ďin takene?, namik'e da sauri na nufo falon ina faďin mama ganinan kundawo??.
Ta ce, "eh nadawo su nabarasu acan.
Na ce, "sannu dazuwa."
Ta ce, "yauwa sannunki kema"
Makullin 6angarenta naďauka muka tafi, nabuďe muka shiga, ruwa maisanyi naďako nabata tasha, ta ce, "ALLAH yayimiki albarka.
Na ce, "amin mama".
Doctor yafito daga bayi yaga bana nan, sai zuciyarsa tak'ara tunzura, wato yarinyarnan tafiya tayi wajen girkin tabarni saboda kiranta yafini ko??, yaja dogon tsaki yafice, ďakinsa yanufa yashiga wanka, yafito yay shirinsa cikin k'ananun kaya, yayi k'yau sosai.
Yadawo falon yazauna, yana kallo yana shan raken daya siyo.
Yaji shirun yayi yawa dan haka yamik'e yanufi 6angaren mama yagani idan tadawo.
Chapter 12 · 0% Book details