← Book details Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 46

Sashe 42

Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Afalo suka iskeshi kwance kan doguwar kujera, suna shigowa yatashi zaune, deexerh tak'arasa kusada k'afafunsa ta zauna a k'asa, iman kuma tafice dasu had'a break itada mom.
Kalon minti d'aya yayma dee.... Ita kuma kanta yana k'asa tana wasa da zoben hannunta Wanda Umar yabata, gabanta sai dukan tara tara yakeyi.
Dr yay gyaran murya tareda jingina bayansa da kujera, khadija yakira ainahin sunan deexerh.
Muryarta nad'an rawa ta ce, "na'am uncle.
Yad'anja numfashi sanan ya ce, " waye Umar farukh??.
Gabantane yafad'i, tad'an d'ago atsorace tana kallonsa saitaga shima ita yake kallo, da sauri ta maida kanta ak'asa, muryarta na rawa ta ce, "wanine.
Wanine kamar ya?, inason nasan matsayinsa agurinkine.
Ido tad'an zaro kanta na kallon k'asa, tayi shiru Dan bazata iya cewa saurayinta bane.
Ya ce, "ke nake saurarefa.
Iman tashigo falon da sallama zata d'auki Abu akicin d'intane, harta gotasu zata shiga kicin saitaji Dr yana fad'in bakida bakine???.
Iman tadawo baya tana kallon Dr, daddy musayeef miya farune?.
Babu komai my life, kawai ina tambayarta matsayin Umar agareta tamin shiru.
Murmushi iman tayi, tazauna kan hannun kujerar dayake zaune, ta ce, " Dr tanajin kunyane fa, kasan babu yanda za'ayi tabud'e baki tace maka saurayintane.
Hummmm to Ashe bata sonsa kenan?, ni inasonjine daga bakinta, Dan muyi magana nida yaya anjima shiyyasa.
Iman dai batace komaiba, yajuya kan deexerh ya ce, "khadija kina sonsa?.
Da gudu dee.... Ta tashi tafice.
Iman ta tuntsure da dariya, Dr kam yasaki baki yanabin hanyarda dee..... Tafita da kallo, juyowa yayi yana kallon iman baki bud'e, my life kigammin yarinyafa, daga tambaya ta gudu.
Cikin dariya iman ta ce, " amsar kenan aii, hakan yana nufin tana sonsa.
Jin jina kai yayi tareda fad'in to ALLAH ya k'yauta.
Iman tamik'e itama tana cewa ameen.

+++++++++++++++++++++
Bayan Dr sunyi maganar dee.... Da yaya, yaya ya ce, "shi miye nasa, aii shine babnta duk abinda yadace yayi, su 'yan ALLAH ya Sanya al'kairine.
Dr yaji dad'in furucin yayansa sosai, Dan haka yasanarma mama itama, tayi murna sosai da fatan alkairi, mom ma yasanar da ita, itama bakinsu d'aya da yaya Dan cewa tayi ita ina ruwanta shine babanta duk yanda yayi daidaine.
*_(ni bilyn Abdul na ce, " su dee.... Ankusa shiga daga ciki🤣.)_*

💎+💎
Washe gari aka tashi da hidimar tarbar Umar, hummm masu karatu yau naga hidima, saikace shugaban k'asa zaizo, girke girke akayimasa na musamman, wanan duk aikin iman ne, dee.... Sai dad'i takeji.

K'arfe hud'u bayan idar da sallar la'asar Umar ya iso tareda abokansa guda biyu, an tarbesu abin gwanin ban sha'awa, afalon su iman akai musu masauki.

Dee.... Da iman suna d'aki, dee.... Anci kwalliya ta musamman sai baza k'amshi take, marwan yashigo da sallama, suduka suka juyo suna kallonsa.
Yay dariya aunty sirikinkifa ya iso, yana falo tareda abokinsa.
Alhmdllh iman ta fad'a.
Dee.... Kuma ta sauke ajiyar zuciya, marwan ya ce, ALLAH ya shirya aunty dee..... Irin wanan ajiyar zuciya haka, idan uncle ya ce, "baimasabafa yazakiyi?.
Dee..... Ta watsama marwan harara, to d'an fatan tsiya bakinka yasari d'anyen kashi, shiyyasama wlhy nak'agara nabar maka gidan d'an buk'ulu kawai.
Dariya iman da marwan sukeyi sosai danjin bal'in da dee..... Takeyi, ko had'iyar yawu batayi.
Dr yaturo k'ofar yashigo da sallama, yana sanye cikin manyan kaya, jar shadda sai maik'o take amma kansa babu hula.
Kukuma lfy kuketa dariya haka?.
Iman ta ce, "yarka mukema dariya, Dr yakalli dee..... Daketa Harar marwan.
Tofa amarya miya faru?.
Hannu tasa tarufe fuska tana fad'in kai uncle.
Marwan yashiga zayyane masa komai.
'Yar dariya Dr yayi, ya ce, " kwantar da hankalinki Indai umarne kin samu da izinin ALLAH, yanzu kitashi kije wajensu, bayan sund'anci wani Abu saiki kirani.
Akunyace ta tashi tafita, marwan yana rakata da sheri irinna sako da sako.
Suna fita Dr yarungume matarsa suna murmushi, acikin kunnenta ya ce, yaran zamani babu kunya my life.
Dariya yayi ta ce, "tomukuma 'yan wane k'arnine?.
Ya juyo da ita suna kallon juna, kinason sani ne?.
Tad'aga masa gira d'aya tana murmushi, bakinta yasumbata hannunsa yana shafa bayanta.
Tajanye bakinta Dan ganin zai zarce, habibi bak'ifa garemu.
Hannu yasa yadawo da fuskarta Inda take da, ya kafeta da idanunsa Dan munyi bak'i sai akace baza abani sweet na shaba, lumshe idonta tayi tana murmushi, ahankali ta ce, " nid'in takace aii.
Ya k'afta idanunsa idan hakane miyasa aka hanni bayan gobe iyanzu nayi missing naki, wlhy jinake tamkar karna koma, shiyyasa dolene na nemi taransfa da wuri.
Iman tad'an canja fuska, wlhy Nima banason katafi habibi, kasa nasaba da abubuwa dayawa, Wanda rashinka zaisa bazan jureba, ALLAH yasa mu koma yajin aikinnan akusa kodan nakusata dakai.
Idanu yalumshi ya had'e bakinsa da nata.
Kowa aikama d'an uwansa sak'o yake cikin alamun nuna kwarewa....
Hummmm kunga bari na lek'a dee..... Wad'an nan sunfi k'arfina.

Tad'an dad'e tsaye ak'ofar falon Dan kunyar shiga takeyi, amma saita dake tashiga da sallama kanta ak'asa.
Umar dake zaune akujerar farko yad'ago manyan idanunsa yana kallonta, ahankali yamik'e cike da d'okin ganinta, jiyake tamkar ya rungume kayansa amma babu dama.
Nawas yakamasa yazaunar, kai malam bi ahankali mana agidan surukai mukefa.
Dee..... Dake tsaye tana satar kallonsu tayi murmushi, cike da ladabi ta gaishesu, Nawas da Abbas ne kawai suka iya amsawa, amma Umar tuni yafad'a koginso.
Takuma gaisheshi, nanma bai amsaba saida Abbas ya zungureshi.
Ya sauke ajiyar zuciya, matana duk kin wani rud'ani wlhy, miye sirrin?.
K'asa dee..... Tayi dakanta tana murmushi, tak'arasa gaban tulin kayan abincin ta ce, "bismillafa kuci abinci k'arfe biyar uncle zai shigo Ku gaisa.
Hummm Abbas yafad'a danganin irin romon lagwada da'aka shirya dansu kawai, lallai shima ALLAH ya bashi surukai irina Umar wad'anda sukasan darajar mutane.
Basu kwari kansuba suka nad'e hannun Riga suka kwashi gara.
Bayan sunci sunyi nak sunata santin girki dee.... Tagyara wajen tsaf, sanan tankoma ciki kiran uncle.
Abin yabata mamaki Dan ganin uncle da iman sun canja kayansu, tararwama tayi iman nasake sabuwar kwalliya, bayan kuma agabanta tayi kwalliya d'azu.
(Na ce, " hummm dee.... Bazaki ganeba, bayan fitarki akasha soyayya).
Shikanshi Dr yalura da kallon da Dee.... Take musu Dan haka ya maze ya fita.

Tunda Dr yashiga falon su umar suka sakko k'asa domin girmamawa, dak'yar yasa suka koma saman kujera bayan sun gaisheshi.
Yayaba da abinda sukayi kwarai da gsk, kuma sun burgeshi.
Su Umar kam duk Kansu na k'asa saboda kunya, Dr ya ce, ''tom waye sirikin nawa?.
Nawas ya nuna Umar dayay k'asa dakai yana murmushi, Dr ya ce, "masha ALLAHU.
Dr yashiga yima Umar tambayoyi gameda kansa.
Kan Umar ak'asa ya ce, " sunan Umar faruk Abubakar, anhaifeni anan garin kano, inada yayye biyu mace da namiji, sanan inada k'anne biyu duk maza, nayi karatu afannin likitanci yanzun haka ni likitan fatane, ina aiki a asibitin M. Aminu kano.

Masha ALLAH Dr yafad'a yana murmushi, lallai kayi k'ok'ari kuma na yaba, Dan haka nabaka dama katuro mayanka muyi maganar aunrenku da khadija, so bayana ta kammala karatu nanda wata takwas sai ayi biki, yaka gani?.
Yayi uncle kuma ngd sosai da karramawa, insha ALLAHU zanmusu bayani.
To shikenan Alhmdllh, yanzu kutashi muje ku gaida mamanmu kakar khadija kenan dakuma mahaifinta da mahaifiyarta dakuma matana.

Har cikin gida yakaisu, suka gaisa da mama dasu yaya, kowa ya yaba da Umar 100%, gashi k'yak'yk'yawa ga tarbiyya, Dan saida Dr yay bincike akansa sanan yabashi damar ganinsa.
Hakadai komai yagudana cikin girmama juna.
Bayan tafiyarsu dee.... Tasha tsokana wajen mama da marwan da aunty iman , barmusu falon tayi, tashige d'akinta tanata tsallen murna harda rawa, ta mallaki Umar abin sonta😁👍🏻.

Washe gari Dr Yakoma wajen aiki cike da kewar iyalinsa, tare suka tafi da dee... Zai sauketa a makaranta.
Tunda suka tafi iman saitaji gidan babu dad'i, kewar mijinta dukta addabeta, dauriya kawai takeyi, ga surutun musayeef ya isheta.
Samu tayi ta lalla6ashi yatafi wajen mom, itakuma tasamu tad'an kwanta tareda fad'awa duniyar tunani.

Haka rayuwa tacigaba da gudu da Sauri, dagari ya wayd sai dare yayi, saikaga rana ta bace dare yashigo, ahaka Dr yasamu wata biyu dakomawa wajen aiki, duk k'arshen sati yana zuwa gida weekend saidai idan baisamu damaba, sosai suke shan soyaya shida iman tamkar sababbun aure, kowa yagansu saisun birgeshi abin kamar majina bisa tuwon masara.

Ahaka aka shiga hidimar bikin Dr Nabeel da miss Xoxo, kwata kwata iman batada lokacin kanta shiri suke babu kama hannun yaro, masu karatu yakamata Ku shirya Dan sanan bikin yadace kowa yajeshi🤠.

A6angaren su aunty da Raihan kam lamarin sai addu'a, iyaye sun duk'ufa da nema, ada su yaya sunyi burus da zance amma ganin lokaci ya shud'a saisuka saka hannun wajen nemansu.
Yanzu hakadai Anbada cigiyarsu agidajen redio.
Duk abinda akeyi zubaida na ji saidai tayi dariyar mugumta Dan tad'an sun tafi kenan har abada baza a gansuba....

Nace hummm zubaida abin aii na ALLAH ne, wai yaro ya tsinci hak'ori..................

*_luv u oll my fan's_*
*((S))........2017*
[8/6, 6:04 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_*

*_NA Bilyn Abdul_*

_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*

https://mrsbilkisa.blogspot.com
Chapter 42 · 0% Book details