← Book details Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 46

Sashe 43

Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*_(page 45 & 46)_*
A yau Reefat ta iso kano itama, kai tsaye gidan iman ta sauka, Xoxo ma tana gidan suka rungume juna cike da kewa, iman ta ce, "madam Reefat mizan gani haka?, kina bakiso bakiso harkin k'unso mana baby.
Hararta Reefat tayi cikin wasa, ALLAH bana son iskanci iman, ni banida komai.
Ki rantse Xoxo tafad'a tana dariya.
Kukam ALLAH yayi 'yan iska, nidai babu ruwana, 'Yar rainin hankali kema aii cikinne dake.
Iman ta gwalalo ido ke 'yammata rufamin asiri, musayeef ya isheni.
Wata dariya Reefat ta tuntsure da ita suka tafa da Xoxo, my hafsy kinjifa wani sa6o, idan k ya isheki Dr yana buk'ar wasu, gashima harya bayar.
Iman takalli cikinta kamar zatayi kuka Dan ALLAH Reefat kidainamin wanan fatan, ni ALLAH banida komai.
Ahakan Reefat tafad'a tana kallonta?.
Eh wlhy tafad'a tana 6ata fuska.
Hummm wlhy sisi kiyi gwaji ammafa kinada ciki, kokuma kisa daddyn musayeef yayi miki.
Xoxo ta toshe baki tana dariya, cikin dariya ta ce, " Ku yanzu idan aka koma makaranta haka zaku koma mana da baby's?.
Harararta iman Take, haba 'Yar iska indai cikine kema dashi zaki koma da izinin ALLAH.
HHHHH ta yaya 'Yar fatan tsiya?.
Dariya Reefat da iman sukeyi harda tafawa, Reefat ta ce, amsarki tana wajen Dr Nabeel, wanan rawar kan dakikeyi kina tunanin zai d'aga mini k'afane hhhhhh suka kwashe da dariya.
Jikin Xoxo kuma saiyayi sanyi, ta ce, "Dan ALLAH kubar tsoratani, ALLAH zaku sakani kuka.
Kuka kuma Reefat tafad'a tana gwalalo ido?.
Eh wlhy Xoxo tafad'a cikeda gsky.
Iman tayi murmushi tana dafa kafad'ar Xoxo, kinga kwantar da hankalinki kinji, komai zaizo da sauk'i aii.
Xoxo ta jinjina kai tana had'iye yawu da k'yar.
Haka sukasha hirarsu suna k'ara bama Xoxo haske akan zaman aure.

Haka biki yacigaba da gudana cikin nasara sosai, can naga 'yan *_HOME OF NOVELS_* suna baza kala, Dan bikin nasunefa😁.
Can nahango su Zarah Bukar dasu Rano su 'yar ficika autar hajiya su Nafi anka, mjey, hajja ce, waliyya, khadija Kandy, Basma er Lele, anata hidima, manyan k'awayen amarya kenan tun na yarinta🤣😜.
Tom nimadai bilyn Abdul angayyaceni kuma na gayyaci 'yan group d'ina, muma zamuci Rangam da lemon roba💃🏻😜.
Biki yayi bikifa anata shagali, naira nakuka tamkar ba'asan ciwontaba, amarya da ango sunata bada ma'ana cikin kwalliya ta alfarma kai lamarin sai fa Wanda yagani.
Ni bilyn Abdul nama rasa ta Inda zan sambad'o muku rahotanni.
Umma bakinta har kunne zata aurar da 'Yar d'iyarya abar alfaharinta, Abba kam ba'a magana, yau ranar tasace zaikai hafsat gidan miji.
Su Dr isma'il sune na hannun damar ango, duk sunyi busy anata hidima.
Hakama gidansu Nabeel momynsa sai farinciki take, da 'yan k'annensa Ayeesh da maimuna (kakus), suma sun gayyato k'awayensu anata hidima.
Biki yayi biki, ayau aka d'aura auren Dr Nabeel Sageer Alhasan, Da amaryarsa Hafsat (miss Xoxo) to saimuce ALLAH ya sanya alkairi, yabama amarya da Ango zaman lafiya, ALLAH yasa bad'i mudawo suna.

Bayan d'aurin aure hidimomi suka cigaba da gudana, Dan 'Yar bidi'ar nan saida aka d'ana, muntaka rawar ak'ame k'am, munci rangam da ruwan roba, harda lemon gwangwani, kai munfa Shana abikinga wallah.
Bayan hidimomi da 'yan bidi'oi aka mik'a amarya Xoxo d'akinta cikin tangamemen gidanta na alfarma, tasha kukan rabuwa da ummanta da Abba harda 'yan k'annenta.
Zuwa k'arfe tara kowa Yakama gabansa sai k'awayen amarya mafi kusanci aka bari, zuwa k'arfe tara da rabi gayyan anguna suka shigo akasha shafta da nasiha ga ango da amarya kowa Yakama gabansa aka barsu cikin aminci.
Dr Isma'il yad'auki iman d'insa sukai gida harda Reefat, Dan sai jibi zata wuce.

Gida tsit kamar bai tara mutaneba daga Ango sai amaryarsa.
Dr Nabeel yana gaban Xoxo yak'ura mata idanu kamar za'a kwace masa ita, itakam tayi k'asa da kai cike dajin kunya dakuma kewar gida da fargabar sabuwar rayuwa.
Yasa hannunsa yad'ago fuskarta datasha kwalliya sai k'yalli take.
Ta lumshe idanu Dan bazata iya had'a ido dashiba, yay murmushi mai sauti yana cigaba daraba ido afuskarta, 'yammata yau babu tsiwa ko, anrufe bakin magana ruf.
Itadai Xoxo ko motsi batayiba, ahankali yamatsar da bakinsa Kusada NATA, sunajin saukar numfashin juna, magana k'asa2 yace tunda bakin arufe yake bayan su isma'il sun siya, nima bari nayi nawa siyen bakin, kafin tayi wani yunk'uri ya......... Hum baridai nayi shiru, (Tawan saida safe nabarku lafiya asha amarci k'alau😉).

*_Washe gari_*
Na ce, "bari nad'an lek'a muku amarya, wajen misalin k'arfe 12 nashiga gidan, a get nagamu da gayyar mutane sun fito daga gidan, da'alama bak'ine masu tafiya sukaga d'akin amarya.
Nidai bayan mun gaisa na ra6a nashige, afalo na iske mutanen gidan, Xoxo kwance tayi fillo da cinyar Dr Nabeel, hannunsa na shafa gashinta ahankali, itakam ta shagwa6e fuska wai barci takeji.
Ya sumbaci goshinta yana murmushi, aidole kiji barci my hafsat Dan jiya kin....... Da Sauri tarufe masa baki da lallusan hannunta plzz nidai karka fad'a ga bilyn Abdul nan tsaye, yanzu saita iya sambad'awa ashafin littafi nikam gsky banaso.
Yacire hannun yana 'Yar dariya to shikenan nafasa fad'a aii, yamik'e tareda d'aukarta kamar wata baby yay bedroom yana fad'in ALLAH yasa kada wani bak'o yasake zuwa subarmu musha barcinmu.
Tsuru nayi tamkar munafuka, to masu karatu tunda sungudu Nina aii saina kama gabana (nimafa soyayyarna inada gwarzona agida, to aii gwara na lalla6a gurin kayanaba😂).

Yauda gobe kayan ALLAH, su Xoxo anashan amarci kamar babu gobe, tayi k'yau bul bul da ita, alamomin jin dad'i sun k'ara bayyana sosai atareda ita, wanan kad'ai ya Isa yanuna Dr Nabeel yana kula mana da ita sosai.
Suna shan amarci kam, yayinda iman taketa fama da laulayin ciki, Wanda tunda oga Isma'il yagane yaketa faman murna, jiyake tamkar ya had'iyeta Dan dad'i, sai kaf kaf yake da ita.
Hummm xoxo mafa kamar ansamu, Dan naje gidan daga fara gaisuwa naga tayi bayi da gudu sainajiyo yunk'urin amai, lallai Dr Nabeel mai sa'a ne, lol.

A6angaren Reefat ma dai cikinta harya fito abin gwanin sha'awa, ya usman yanaji da ita, ana shan soyayya kamar babu gobe.
Ana cikin haka makarantarsu takoma daga yajin aiki, haka suka tarkata suka koma makaranta kowa da k'aramin cikin, aiiko anashan shafta, idan weekend yazo mazansu suzo su kwashesu kowa yasha soyayya da matarsa.
Agida iman tabar musayeef hannun mom, bai damuba tunda yasaba dasu dama.
Bikin deexerh yanata matsowa Dan haka aka fara shirye shirye yanda yakamata.

####################.
Su aunty madai yau cikin hikimar ALLAH suka samu ku6ta daga hannun su zuby, anzubasune amota za'a kaisu legos Inda tushen k'ungiyar take, sukai had'ari ahanya, dayawan 'yan k'ungiyar sun mutu yayinda masu taimakon gaggawa suka ku6tar dasu Raihan, babu 6ata lokaci aka kaisu asibiti, yayinda hukumar 'yansanda tayi bincike aka gane 'yan ta addane abakin d'aya daga cinsu zuby Wanda bai mutuba, ram akayi dasu zuby dasauran 'yan k'ungiyarsu dake Legos, dama k'aramar k'ungiyace basuda wani fawa yanzu suke kafata shiyya suka baza group ta WhatsApp, to ALLAH ya kiyaye gaba.
Bayan su aunty sunsha jiyya a asibiti harna tsawon watanni biyu aka sallamesu tareda damk'asu hannun iyayensu.
Sunsha kuka da nadamar rayuwarsu, sun k'ara gane zancennan na hausawa dakance idan zaka Gina Ramin mugunta ka ginashi gajere Dan bakasan wazai afkaba.
Sud'inan da da suka Shana ga k'yau ga dama amma yanzu sune suka koma jemai jemai duk kamaninsu sun canja sunyi bak'i sun kod'e kai babu gashi, ALLAH ya yafe musu suma suzama mutanen kirki kamar kowa haka suke fata.

Lokaci ya shura sosai, gasu iman sun sami nasarar mammala karatunsu, zuwa yanzu cikinsu duk sunfito suduka ukun, Reefat ma tana gangarar haihuwa, Dan cikinta ya tsufa sosai haihuwa koyau ko gobe, dak'yarma ta iya kammala exam d'in.

Sunsha kuka lokacin rabuwa, su iman sukayo kano Reefat tayi Adamawa da alk'awarin data haihu zasu zo.
Sumadai akanon kowa gidanta mijinta yawuce da it a cike da farinciki.
Musayeef yayi murnar ganin aunty maa d'insa, yak'ara girma shima yayi tsawo sosai babu laifi, walima sosai Dr isma'il da Dr Nabeel suka shiryawa Matan Nasu na murnar kammala karatu lfy, to ranarmadai mun karya k'ashi aradu.

Bikin dee.... Ya kankama su iman duk sunzama busy, ga cikin ga hidima, hakadai tadaure tanata kai da kawo saboda mom Tanama iman kara, komai aka nema irin na uwa saitace aje wajen iman, hakama yaya ya mik'a ragamar komai ga Dr isma'il, shiyyasa bikin yazama Nasu iman.

Ina k'ok'arin shiga 6angaren iman Inda amarya da k'awayen ta suke, bayan mun gaisa da iman da Xoxo dake tsaye suna shawara akan walimar gobe idan ALLAH ya kaimu, saiga wasu mata su biyu.
Daga iman har Xoxo dani bilyn Abdul tsayawa mukayi muna binsu da kallonta mamaki...........

Tofa masu karatu kosu waye wad'an nan mata oho, muhad'u a page nagaba danjin su wanene??????..............

*luv u oll my fan's*
*(((S)))........2017*
[8/6, 6:04 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_*

*_NA Bilyn Abdul_*

_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*

https://mrsbilkisa.blogspot.com

*_gaisuwa da fatan Al'kairi gareki Ayusha muh'd, ya mura?, kisaurari zuwan gasassun kaji Dan sune maganin murarki, masu yaji za'a kawo miki😂😜._*
*```{zuciya, kowa da irin tasa}*```
Acigaba da gashi👌🏼
Chapter 43 · 0% Book details