← Book details Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 46

Sashe 13

Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Da sallama yashigo ganin inama mama matsar k'afa sai yayi turus.
Mama ta kallesa a'a auta kadawo?, ince dai lafiya?.
Ya ce, "lafiya lau mama nadai dawone kawai, zaman kasuwarnan saisu yaya surutun yayi yawa, har kaina yafara juyawa shiyyasa nagudo.
Yazauna yana hararata.
Mama ta ce, "mitayi maka kake harararta ne?.
Da sauri ya ce, "babu komai mama, yana magana yana sosa gefen wuyansa.
Nayi k'asa dakai ina murmushi danya bani dariya sosai.
Mama data fahimci inda muka dosa saitace yauwa ďiyata barshi haka ai k'afar tama saki sosai ngd.
Nayi murmushi ta reda faďin to mama sannu.
Namik'e nafita batareda na kalli doctor ba.
6angaren auntyn nanufa, kai tsaye nanufi kicin dan nasan sunacan da masu aiki.
Koda nashigo saita haďe girar sama data k'asa, na ce, "sannunku da aiki, masu aiki kaďai suka amsa amma ita ko kallo ban ishetaba.
Nima banbi takantaba dan indai miskilancine gidan ta taras.
Haka mukayi aikin muka gama batareda mun kula junaba.
6angaren mama muka kai abinda yadace, har yanzu doctor yana can suna hira da mama, muka gama jere komai, sanan muka fita.
Saida mukayi sallar azuhur sanan aka ci abincin, yauma saimu huďu kawai, tunda muka zauna cin abincin doctor yaketa haďe rai, nasan saboda aunty yakeyi dan haka abin bai dameniba.
Muna gamawa na nufi 6angarenmu dan naji zufa ta tasomin, gashi arayuwata idan ina cikin al'ada sainatayin k'yan k'yamin kaina, sainayi wanka sau shida arana bai wadaceniba.
Babu daďewa saiga doctor yabiyoni har yanzu fuskarsa babu walwala sosai.
A bedroom yasameni ina shirin shiga wanka, nayi k'asa da kaina dan ganin ya nufo inda nake, gashi dagani sai guntun tawul, kama tawul ďin yayi kamar zai kwance, da sauri narik'e tawil ďin da hannunsa ina zaro ido ..........yaďan murmusa kaďan iman kincika tsoro wlhy, ahaka wai zaki haifamin yaran danake mafarki? , hannu nasa narufe fuska yayinda shikuma yasamu damar zame tawul ďin daga jikina.......
Kai jama'a mutashi muyi sallah, miss xoxo ta harareta kai iman ALLAH kina jamana rai, wlhy kuwa xoxo Reefat tafaďa tana kwa6e fuska, yakamata kiďan k'ara mana nan.
Dama muna binki bashi akan sanin wacece Raihan?.
Mik'ewa iman tayi tana faďin 'yan duniya kudai wlhy sai gyaran ALLAH, yara baku tafasaba zaku k'one.
Raihan kuwa kumanta da batunta ita bakomai bace.
Xoxo da Reefat suka tuntsure da dariya suna faďin keda kika tafasa har kika k'one aii saiki nuna mana hanya.
Dan wlhy duk kawaice2nki saikin bamu bayanin _firstnight_ , saikuma munsan wacece Raihan?.
da sauri iman tashige bayi tana dariya, sumadai aminan nata dariyar suke tuntsurawa sosai...................

*To nima bari na k'yak'yata*😂😂😂😂😂😜👌🏻
_lol._

_*((S)).........2017*_
_*luv u oll my fan's*_
_*battery low*_
[8/6, 6:01 PM] mrs bilkisu: *_______________________________*
*BAN SAKETA BA!!!*
*________________________________*
*NA*
*BILKEESA IBRAHEEM*
_*{bilyn Abdul}*_
*________________________________*
https://mrsbilkisa.blogspot.com

_sadaukarwa_ *~ya Abdul {city phone's}*

*MIYAKAMATA NAYI!??.*
_ZAKA IYA MUTUWA YANZU_
_SHIN BA ZAKA JI KUNYAR ALLAH BA??, YA KAI 'DAN ADAM!!, Shin ba zaka ji kunyar ALLAH ba?? Kullum SHI yake baka ci da sha da numfashin da kake shk'a, Amma godiyarka ta tafi zuwa ga waninsa, Sa6onka kuma ya tafi zuwa ga ALLAH mahaliccinka._
_Kana nuna ma mutane kamar cewa kai mutumin kirki ne, alhali akwai Miyagun ayyukanka da kakeyi a 6oye, da kuma Miyagun tunanin dake Qunshe a zuciyarka._
_*Ubangiji* Ya san dasu amma bai ta6a tona maka asiri ba, Kullum rufa maka asirinka yakeyi, amma kai kuma kana Qara butulce masa._
_Kullum Qara turo maka_
_Ni'imominsa yakeyi, amma_ _Maimakon ka gode Mai sai kake_ _ganin kamar hikimarka ce ko kuma wayonka ne suke baka,_ _Yanzu idan kana dauke da Olsa_ _*(Ulcer)* ko Hawan jini ko_ _*Diabetes* (Ciwon Sugar) duk_ _abincin da likita ya hanaka ci,_ _Sai kayi shekaru baka cishi ba,_
_saboda mi??, Saboda kana_ _tsoron_ *MUTUWA!!!.*
_Amma Ubangijinka wanda Ya hakicceka Yace maka_

_*- QARYA BABU KYAU.*_
_*- GULMA BABU KYAU.*_
_*- SATA BABU KYAU.*_
_*- SHIRKA BABU KYAU.*_
_*- GIRMAN KAI BABU KAYU.*_
_*- ZINA BABU KYAU.*_
_*- TUNANIN AIKATA FASADI*_ _*KOWANNE IRI MA BABU*_
_*KYAU..*_
```Yace maka duk wad'annan HARAMUN NE, Kuma zasu kai ka Zuwa ga shiga Wuta, Amma duk da
haka gashi nan kana yinsu babu dare babu rana...```
*SHIN GASKATASHI NE BAKAYI BA?? KO KUWA LIKITAN ASIBITI YAFI* *UBANGIJINKA* *FA'DAR GASKIYA NE???*
_Ya Allah mun tuba Ka yafe mana... Idan mu halinmu ne muyi sa6o saboda raunin zukatanmu, To Kai kuma halinka ne yin Gafara da Rahama da Afuwa ga bayinka ba tare da hisabi ba, Ya Allah Ka_
_Tsaftace zukatanmu daga_ _dukkan abinda baka so._
_Ka sanyamu cikin bayinka Masu shiryuwa da kuma_
_shiryarwa zuwa gareka, Ba_ _Batattu ba, kuma ba masu_ _batarwa ba_
*ALLAH yasa mu gane*

*~page.......13~*

..................iman tacigaba da faďin, koda yazame tawul ďin sainayi saurin buďe idanuna, ganina zir yasa na ranta cikin na kare zan shige bayi, taku ďaya ya damk'oni.
Tuni jikina yafara 6ari dan haka nasa masa kuka, sakina yayi yana faďin sorry my iman jekiyi wankanki.......aii kafin yagama faďa nakai cikin bayin.
Ya zauna bakin gado yana fidda huci, idanunsa sunyi jajur, yasan iman tabbas yarinyace, amma zata iya ďaukar nauyinsa, saidai yakula yarinyar tanada tsoro sosai, baisan yanda za'ayi ta fahimcesaba, gashi bayason binta da k'arfi, yafison komai ya wakana cikin ilimi da fahimtar juna.
Wato da yardarta kenan.

Tuni nagama wanka amma nakasa fitowa saboda kunya, ina bayi da tunanin yanda za'ayi na fito sainaji maganar deexerh tana kwala kiran uncle!.
Ya ce, "baby shigo ganinan, daďan k'arfi yafaďa yanda zataji.
Tashigo da sallama, yatashi zaune yana faďin harkun dawo?, ta zauna kusadashi tana dariya eh uncle, ashe kadawo daga kasuwar?.
Nadawo tuni, kinsan banason hayaniya.
Tayi dariya akaro nabiyu, wlhy rayuwarka tana burgeni uncle, shiyyasa kullum nake burin nayi koyi dakai, amma bakina baya iya shiru bansan miya saba.
ďan murmushi yayi yana kallonta, to kizo nakoya miki.
Ta ce, "da gsk uncle."
Kai ya jinjina mata yana lumshe idanunsa.......kafin tabashi amsa Raihan tashigo ďakin.
Suduka suka amsa, saidai gogan kamar baiyi maraba da zuwan nataba, gefensa itama ta zauna suka sakashi tsakkiya itada deexerh, sai kawai ya haye gadon sosai ya kwantan.
Raihan tabishi da kallo dan tasan saboda ita yayi haka, suka haďa ido ya kauda kai, itakuma taja ajiyar zuciya, deexerh ta ta6e baki tana mik'ewa, uncle wai ina my aunty??.
Muryarsa aďan ďarare ya ce, "tana bayi wanka take.
Mik'ewa tayi tanufo k'ofar bayin tana kwankwasawa, da kiran aunty!!.
Nayi gyaran murya dan babu damar magana abayi.
Ta ce, "wai wanka kikeyi??.
Kaďan na buďe k'ofar nalek'o tunda ta juyawa gadon baya, dan haka bazanga su doctor ba suma bazasu ganniba.
Na ce, "dee.... kun dawo?.
Kai taďaga mini alamar eh, tabini da kallo wai bazaki fitobane??, zan fito mana amma ďan ďakkomin zani da hijjabi a duriwa.
Dariya tayi kai aunty kincika kunya, na ce, "babu komai nidai bani kawai.
Babu daďewa takawo min zani da hijjab, lokacin doctor da Raihan sun fice, abin ya6atama deexerh rai sosai, dan haka tana bani zanin tarufa musu baya.
Nikam dabansan wainar da ake toyawaba nafito nahau shirina.
Adurkushe deexerh ta tarar da Raihan gaban doctor; da alama rok'onsa takeyi kokuma wani abun daban, shikuma yaďan kauda kai gefe fuskarsa babu yabo babu fallasa.
Tana ganin deexeh tamik'e, tasamu kujera ta zauna, ďan siririn tsaki deexerh tayi itama tanemi guri ta zauna.
Koda nagama shiri saina nemi gado na haye, babu daďewa barci yay gaba dani, ni azatonama sunbar gidan.

Sai gab da magriba na farka, nabuďe ido ahankali saina ga doctor tsaye yana shirin masallaci.
Yak'araso kusada gadon yana faďin my saudat kin tashi?, na ďaga masa kai ina yunk'urin tashi zaune, da sauri yatadani ya zaunar, ya ce, "kinsha barci ko?.
Kai naďaga masa ina lumshe matsakaitan idanuna.
Ya summbaci kumatuna yana faďin bari naje masallaci naji suna shirin tada sallah.
Ban takashiba dan miskilancin yana kusa.
Chapter 13 · 0% Book details