← Book details Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 46

Sashe 38

Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan sun idar suka nufo fallo daniyar tafiya 6angaren mama, a fallo suka iske Raihan zaune tana kallo Dan yau takeso ta ida cika aikin malam so take kawai imam tafita ad'akinta taje ta aiwatar.
Deexerh tasaki wani wawan tsaki tanabin Raihan da kallon banza, aunty yanzunan har kinyarda kowanne datti yazauna miki afalo?.
Da Sauri Raihan ta kalleta dantasan da ita take, imandai batace komaiba, Raihan har zatayi magana saikuma tayi shiru, dee.... Tayi dariya mai bakin ja6a yakuma kika kasafad'a, fad'i maganarki karta kasheki.
Iman taja hannun dee... Suka fice, kai dee.... Kibari Dan ALLAH matar uncle d'inkicefa kuma 'yar uwarki.
Hummm wannan duk ada ne, ayanzu kam babu wata alak'a atsakaninmu, yanzuma tafara gaini Indai nice.
Suna fita Raihan ta share hawaye, zanyi maganinki kema, baridai nagama da wad'annan sakar Karun, hankalinta kwance tanufi d'akin iman, katifarta tad'a tasaka wasu layu ko k'yan gani babu, tatsaya gaban gadon tana wani sirkulle.
tana gamawa tajuyo zata Fita saifaman murmushi take Dan tasan daga yau imam tagama yawo.
Turus tatsaya baki bud'e tanabin Dr dake tsaye da kallo atsorace.
Takowa yayi cikin d'akin batareda yace komaiba, saida yaje gaban gadon sanan ya ce, "zoki cire abinda kikasamata agado.
Jikin raihansai rawa yake tazo tad'aga tacire layun data ajiye, ya ce, " nasan bayau kika fara saka mataba d'ebo sauran ma, da Sauri taduk'a k'ark'ashin gado saiga wani kasko da da tsokar nama an cacccaka k'ayoyi ajiki.
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Dr yaketa ambata, gaba d'aya zufa ta jik'e MASA jiki, waya ya d'auka yakira yayansa. Yaya kana kasuwane?.
A'a isma'il INA gida yanzu babu dad'ewa nashigo.
Yaya Dan ALLAH ka tattaro 'yan gidanan kuzo kuga abinda Nagani INA d'akin imam.
Kagani kuma, minenen kagani??.
Yaya saidai kunzo kawai. Raihan dai tana duk'e ak'asa da 'yan kayan surkullenta sai hawaye takeyi, shikenan aunty tak'ara sakata amatsala itakam tashiga uku, wlhy batason rasa Dr Isma'il Dan tana bala'in sonsa.
Babu dad'ewa saiga gayyar 'yan gidan duka, kowa yashigo saiya rik'e baki, iman ta ce, "na Shiga uku ni saudatu wanan kuma daga INA Doctor?.
Baiyi maganaba saidai nuna mata Raihan yayi.
Jikake tauuuuu deexerh ta d'auke Raihan da wani wawan mari, shima Marwan yabata d'aya a d'aya kuncin, dukanta zasu farayi Yaya hace karsu daketa, Dr isma'il ya ce, " Yaya wlhy kabarsu su zaneta aii ita tajama kanta, kuma nidai gsky Yaya ayau zan saki jahilar nan, wlhy bazan iya jurewaba, kije na sakeki saki uku!!!!.
Wani ihu ta buga tareda rik'e kafafun doctor tana kuka, Dan Girman ALLAH ya isma'il kamin rai narantse da ALLAH bazan sakeba, wlhy aunty CE tasakani.
Yaya yay murmushi itama aii bazata tsallakeba, kema kibita na sakeki saki uku kema, saikuma kuje wani gidan.
Wlhy kummin daidai 'ya'yana ALLAH yay muku albarka, zama da wad'annan yaran aii masifa CE, mamace mai wanan maganar.
Dr isma'il ya ce, "aii wlhy mama banda Abba dakansa yafad'a mana iyayen yarannan 'yan uwansane nikam danace suba jininmu bane, tsinannu gadon tsiya gadon jaraba, wlhy minti talatin nabaku kubar gidanan.
Raihan da aunty kuka suke suna rok'on ayi hak'uri wlhy bazasu sakeba sunyi nadama.
Deexer da marwan suka kalli juna suka shek'e da dariya suka fice.
d'akunan su Raihan sukaje suka ringa Watso musu kayansu waje, duk abinda sukasan na kud'ine sun d'aukeshi Dan iyayensu suka siya, daga aunty har Raihan babu wacce aka kawo dako kofi daga gidansu, duksu yayane sukai musu kayan d'aki.
Kafin su fito duk su dee.... Sungama Watson Musu kaya waje, haka suka Shiga tattarawa suna kuka, Yaya yabasu kud'i ga kud'in mota nan sai abi wani sarkin.
Har k'ofar gida su dee.... Suka rakosu 'yan unguwar sai fitowa suke kallonsu, wasu sai tsine musu suke wasukam suna shima su Yaya albarka, Dan Ansan mugun halin su auntyn a unguwar.
Kowa baya jin tausayinsu bare goyen baya.
*_(ni bilyn Abdul na ce, "tsuntsun dayaja ruwa shi ruwa kan doka Raihan da aunty)_*...............

*luv u oll my fan's*
*(((S)))......2017*
[8/6, 6:03 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_*

*_NA Bilyn Abdul_*

_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*

https://mrsbilkisa.blogspot.com

*miya kamata nayi?.*
_duk matakan tsaro dazaka sakama family naka saboda kasancewarka fasik'i bazai hana ALLAH kuntata makaba kaima, Dan ALLAH ba ayi MASA wayau_.
_yanzu mud'auki waya k'aramar alhaki, anyi ittifak'i aduniya babu abinda bature yayi aduniya yakar6u kamar waya._
_zakaga duk talaucin mutum ya mallaki waya, waya tashiga hannun babba da yaro, mace da namiji, talaka da amai kud'i, waya tazama babbar fitina ga rayuwarmu, Dan 6arnarta tafi amfanin yawa, wlhy yanzu 'yarka tana cikin gida saita fad'a tarkon fasik'anci ta dalilin waya_.
_Yarinya tanada waya, zata iya Shiga duk Inda takeso hankali kwance, dama tanada sha'awar yin wani Abu Mara k'yau to amma bata samu hanyaba, saikuma ga waya ta mallaka, zakaga tana chart da k'awarta ta makaranta ko wata 'yar uwarta, 'yar uwarnan tata zata kaita group Wanda babu wata 6arna acikinsa._
_to matsalar da ake fuskanta a group bakowane nagariba, akwai gur6atattu Wanda suna 6oye kansune, to idan tsautsayi yafad'a akan 'yarka sai gur6atattunnan su d'auki No. d'inta sukai wani group nasu, (tunda dama haka sukeyi Idan suka kaika group d'insu inkai irinsune saika zauna idan ba irinsu bane kafita)......._
_kuyi hak'uri mu had'u a page na gaba._
*ALLAH yasa mugane*

*(page 37 & 38)*
Dr yatsaya kaida fata iman bazata Shiga d'akintaba wai ko akwai wani Abu dasu Raihan suka 6oye.
Iman ta langwa6e kai tana kallonsa, daddyn Musayeef ka kwantar da hankalimka, insha ALLAHU babu abinda zai faru, nad'azuma ba wayonmu yasa ka ganiba.
Hakane my life amma aii hanyar lafiya Abita da shekara ko.
Babu yanda zatayi dole tahakura suka Shiga d'akinsa akan da safe za'a bincike d'akin NATA.
Kayansa yacire yashiga wanka, itakuma tana zaune abakin gadon.
Musayeef yashigo d'akin yana d'ingishi, da Sauri ta ce, "kai kuma lfy kake d'ingishi?.
Gabanta yak'araso fuska ayamutse yana yarfe hannu, ya Nuna mata babban yatsan k'afarsa dayake jini.
Ya salam a ina kaje kaji ciwo?.
Aunty maa afalo nabige da kujela.
Ta sauke ajiyar zuciya tana d'aukarshi, saman cinyarta ta d'orashi takama k'afar zata duba doctor yafito daga bayi.
K'arasowa yayi Inda suke yazauna Kusada iman yana tambayar lfy?.
Kafar musaueef tanuna masa batareda tayi maganaba.
Woow! Shugaban hidima a INA kaji ciwo?.
Daddy a falo, yafad'a zaiyi kuka.
Kaga yi shirunka karkayi kuka, kaida zaka zama soja wanan d'an ciwon zakama kuka, ina zuwa..
Iman ta ce, " lallai su soja manya.
Dr Isma'il yazauna yana fad'in baki yardaba kenan??.
A'a nikam miye nawa ALLAH yakaimu lokacin.
Haka nikeson ji kawai.
Yagyarama musayeef wajen, ciwonma baida yawa amma sai jini.
Musayeef ya ce, "aunty maa yunwa nakeji.
Yunwa kuma musayeef?, ita saima yanzu tatuna babu Wanda yaci abincin rana agidan, Dr Isma'il dake bayansu yana saka kaya, ya ce, " badole yaji yunwaba inagama tun break d'in safe, wad'an nan shaid'anun sun mantar damu yunwar cikinmu.
Iman dai batace komaiba ta sauke musayeef daga cinyarta.
Kaga bari nafara maka wanka sanan saimuje kaci abincin.
Ya nok'e kafad'a alamar bayaso.
Ta harareshi kainifa banason ta6ara kamije namaka wanka.
Guduwa yayi Inda Dr yake, yarungume k'afafunsa yana fad'in daddy 6oyeni nifa bana son wankan.
Dr yarik'eshi yana murmushi, haba big boy rashin wankafa k'azantane, ko kanaso aringa cemaka k'azami.
A'a daddy.
Yauwa to jeka amaka wankan.
Nidai daddy saina fara cin abinci za'amin wankan.
Dr yad'ago yana kallon imam, aunty maa Dan ALLAH amana hak'uri muci abincin munajin yuwafa sosai.
Itama fuska ta marairaice Dan ALLAH karka biye masa, kallifa kayan jikinsa, ni bammasan inda yaje yay wannan dattinba.
d'aukar musayeef yayi yana fad'in mudai mun tafi saikin taho.
Rakasu da ido iman kawai tayi, yazatayi da uba da d'an.

Wanka itama tashiga, bayan tafito ganin lokacin sallar la'asar yayi tayo alwala, kayanta da Dr yad'ebo daga d'akinta yasaka a durowarsa taduba tad'akko zani da hijjab.
Tana cikin yin sallah, tayi raka'a ta farko tana ta biyu Dr yashigo d'akin tamkar anjehoshi, tsayawa yayi cak yana kallonta tamkar yau ya fara ganinta.
Ya ce, "hummm dama manya suna k'arya?.
Iman dai sallarta takeyi, saima yanzu ta tuna da shirinta, saurin kauda tunanin tayi tacigaba da sallah anutse.
Dr yafito daga bayi da Alama alwala ya d'auro, ya fice yana wata 'Yar dariya wadda iman batasan fassarartaba.
Koda ta idar da sallar duk jikinta yayi sanyi, tamanta wlhy har tayi saken da Dr yakamata, tagama shafa mai tayi 'Yar kwalliya, sanan tanufi 6angaren mama Dan taci abinci.
Musayeef yana ganinta yagudu cinyar mama, iman ta ce, " haba yaro zan kamakane aii.
Mama da deexerh sukayi dariya, mama ta ce, "mi mai gidana yayine?.
Mama wankafa zanma yaron nan shine yabiyo daddynsa suka fito wai yunwa yakeji, maimakon yaci abincin yadawo namasa wankan shine Yakama wata tashar.
Mama ta shafa kan musayeef asheni mijin nawa k'azamine ban saniba.
Deexerh ta ce, " a'a mama yanzu zamu cakire abinmu, musayeef zomuje ni nayimaka kaji.
Babu musu yabi deexerh.
Chapter 38 · 0% Book details