← Book details Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 46

Sashe 7

Ban Saketa Ba Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Washe gari da wuri suka tashi kasancewa sunada lucture ďin safe, suduka gayu suka ďauka na birgewa, dan 'yan matan akwai kala, kowa ta iya ďaukar wanka na birgewa, a tsaitsaye sukasha shayi suka fito.
'Yar tafiya kaďan takaisu aji (class), amma dayake akwai sauran lokaci saisuka samu k'ark'ashin wata bishiya suka zauna suna jiran lokaci yacika.
Kamar wadda aka zirkuďawa allura tafara waige2, xoxo da Reefat suka bita da kallon mamaki, ta mik'e zumbur tana fidda numfashi da sauri da sauri tamkar wadda tayi gudun fanfalak'e a sahara.
Inda tadasawa idanu ko k'yaftawa batayi suma su Reefat suke kallo, wani matashine fari atsaye jikin mota, dogone sosai da 'yar k'iba, saidai ba'a kirashi k'yak'yk'yawa sosai ba, amma babu laifi yanada nasadaidai k'yawun.
Hannayensa aharďe kan k'irjinsa, hakama k'afafunsa suna harďe dajuna, idanunsa k'ur akan iman daketa rawar jiki kamar taga mala'ikan mutuwa.
Murya k'asa2 xoxo ta ce, "da Reefat inagafa wanan iman takema wanan ruďin, ki lura da k'yau yana kama da musayeef.
Reefat ta ce, "gskyar ki xoxo, toko shine Dr Isma'il ďin?......
Kafin Reefat ta rufe baki iman tabar wajen cikin sauri da da sassarfa gamida rawar jiki, binta yayi da wani mayen kallo tamkar zai cinyeta, dayawan ďalibai kallonsu sukeyi suma.
Saida ta 6acema ganinsa sanan yaja ajiyar zuciya tareda ďan matse ido wasu k'ananan hawaye suka zubo kaďan a idonsa , hankacif ďin hannunsa yasa ya gige yanaďan murmushi k'arfin hali.
Ahankali yafurta My SAUDAT yaushe zaki dawo gareni?, yaushe zaki yarda BAN SAKEKI BA!!.
wlhy BAN SAKEKI BA, ki yarda dani, karki bari ciwon haukan sonki yacigaba damin illah, na tabbata babu wani likita dazai iya shawo kan matsalata saike kaďai.
"Kece cikon farincikina."
"Kice uwar ďana."
Akanki kawai nake tanadin rayuwata, miyasa zakimin haka?, waye yay min wanan kullin?.
waye!?.
Waye!!?.
Waye!!!......?.
dasauri yafaďa motar danjin juwa zata juyeshi ak'asa, ya kwantar da kujerara motar da sauri ya kwanta, sai fidda numfashi yake sama2....
Cikin k'ank'anin lokaci yafara fita hayyacinsa, dauriya da jarumta tabashi damar jawo wayarsa, batareda yasan wayake kiraba ya kara akunne.
Murya a sark'e ya ce, plz waye?.
Cikin rikicewa nacan ya ce, "Isma'il kana cikin k'oshin lafiya kuwa??.
Da k'yar ya iya faďin Nabil kazo katafi dani.
Arikice Nabil ďin ya ce, "kana inane?..
Ina makarantar su Iman!.
Hazbinallahu wani'imal wakil, Nabil yaketa ambata, yayinda tuni Dr Isma'il yasaki wayar k'asa dan numfashinsa yafara gagarar fita yanda yadace.
Su xoxo dai suna tsaye suna shawarar zuwa inda motar doctor Isma'il yake, dan sunga kamar amawuyacin hali yashiga motar.
Har ciki mai mashin yashigo da Nabil, yazaro ďari biyar yamik'ama mai mashin ďin, batareda yajira canjinba yay gaba.
Tundaga nesa yashaida motar Dr Isma'il, yak'arasa da sauri yabuďe motar akuma daidai wanan lokacin su Reefat suka iso wajen.
Tuni Dr Isma'il yafita hayyacinsa da alama ma numfashinsa shirin ďaukewa yake gaba ďaya.
Nabil yay k'ok'arin matsar dashi kujerar gefen direba, ya maye gurbin inda Dr Isma'il yake da.
Xoxo tayi k'arfin halin faďin lafiya kuwa?.
Nabil ya kalleta arikice dadai sauk'i 'yammata, baijira amsartaba yatada motar yafice daga makarantar aguje.
Kowadai kallon mamaki yabi motar dashi, wasuma har suna faďin mahaukaci.
Jiki a sanyaye xoxo da Reefat suka k'arasa aji, saikuma suka tarar da iman zaune tanata rusar kuka, kamar zata k'arar da kwallar idonta.
Tsakiya suka sakata suna lallashi, Reefat ta ce, "iman wai waye wannan mutumin??.
Kasa magana iman tayi saima wani sabon kuka daya taho mata.....
Shigowar malamin tahanasu cigaba da neman ba'asi.
Itama iman tashiga hidimar share hawayen idonta dan fiskantar malamin.

Acan kuwa Nabil ya isa da Dr Isma'il asibitine arikice, taimakon gaggawa suka shiga bashi shida abokan aikinsa, dan shima Nabil ďin likitane, da taimakon oksajin Dr Isma'il yafara fidda numfashi.
A6angare ďaya kuma an manna masa k'arin ruwa da aka juye alurai har biyar aciki.
Bayan lafawar komai Dr Nabil yakira yayansa yasanar masa.
Cikin rikicewa yaya mansur ya ce, "Nabil badai ciwonsa bane ko??, ya akayima haka tafaru?.
Wlhy yaya bansan Isma'il yatafi makarantar su iman ba, na barsa agida dan ya ce min zaiyi barci, nikuma nanufi wani uzuri daya ďan tasomin.
Inama awajen yakirani ya ce, "nazo nafi dashi yana makarantar su iman.
Yaya yaja wani gwauron numfashi, to yanzu yajikinsa.?.
Da sauk'ima aii, yana barcine.
To Alhmdllh.
Dr Nabil yafaďi hakane kawai dan kar hankalin yaya yatashi, amma duk wanda yakalli Isma'il yasan yana cikin mawuyacin hali.........
Yaya yakatsema Dr Nabil tunani dafaďi, to yaga iman ďin?.
Wlhy yaya ban saniba, dan lokacin danajedai bata wajen, kodayake bawani saninta nayiba sosai.
ALLAH yak'yauta yaya yafaďa cikin sauke numfashi.
Amin dai".
Amma yaya bama saikazoba insha ALLAHU zuwa anjima komai zai dai2ta.
To shikenan Nabil, kaima ALLAH yasaka maka da alkairi kaji, samun aboki irinka sai antona.
Babu komai yaya aii yiwa kaine, nida Isma'il munzama ďaya.
To mungode saina kira anjima.
To yaya agaishemin dasu deexerh.
Zasuji insha ALLAHU.

Dr Nabil ya yanke wayar tareda maida kallonsa akan Isma'il.
Cikin lokaci k'ank'ane harya zabge, sai wani haske daya k'ara.
Yana tausayama abokinsa, saboda yanda soyayya take masa juyin waina, ALLAH ka warware mana wanan kulli dake tsakanin abokina da matarsa.
ya ALLAH ka bayyana gskyar lamari, kakuma maidasu amatsayin ma'aurata indai sunada rabon sake zama tare.
(Na ce, "ameen Dr Nabeel).

Itamadai iman zaune kawai take tana sauraren malamin, amma bata fahimtar abinda yake faďa; gaba ďaya tunaninta nakan Dr Isma'il SANYIN IDANIYAR TA.
Yau tsawon shekara huďu bata gansaba, ashe akwai lokacin dazaizo suga juna, taga yak'ara k'yau da girma, gawata kamala da nutsuwa sun sake riskarsa, uwa uba kwarjinin data hango a fuskarsa da annuri na musamman.
Ta share hawayen dasuka gangaro mata tareda ďan jan hancinta, lallai tayi dana sanin zuwan wanan rana.
Yau Doctor yatada mata tsohon ciwon dake cin ZUCIYARTA tsawon shekara huďu.
Tabbas da amafarki wanana ranar tazo mata da idan tatashi bazata sake komawa barcinba.
Haka tayita sak'e2, har malamin yafice batareda tasaniba, bare tayi ik'irarin fahimtar abinda yakoyar dasu.
Haryanzu hawayenta sun kasa tsayawa, dan haka k'awayenta sukaja hannunta domin fita susha iska, amma saita kakare dan bataso tafita waje tak'ara tozali da mugun mutuminnan mayaudari.
Murya asark'e ta ce, "kubarni anan kawai."
Saboda mi xoxo? tafaďa aďan raunane;.
Iman tayi murmushi k'arfin hali, babu komai banason fitane kawai.
Shikenan muma saimu zauna aii.
Reefat ta ce, "iman wai waye wanan mutumin naďazu?.
Iman ta cije le6enta na k'asa, muryarta da karsashi ta ce, "Isma'il!!.
Xoxo da Reefat suka kalli juna, wai Doctor kike nufi?.
"Kai kawai taďaga musu batareda ta iya maganaba.
Suma shiru sukayi, kowa yana sak'e2n abin aransa, da mamakin abinda yaraba iman da doctor Isma'il, domin alamomi sun nuna suduka suna matuk'ar son junansu, da begen kasancewa a fada ďaya.
Amma saigashi sun kasanance amabanbanta gurare, kuma cikin matuk'ar ruďani da nuna damuwa.
"Komiye dalili!!!!!!!!???"..........✍🏻

💕💚💕

Page.........8⃣.

................Har suka gama kar6ar luctures nasu duka iman bata cikin walwala, zata iya kuma rantsewa yau bata tsinci komaiba a darissan da aka koyar dasu.
Sukansu k'awayennata sun kasa gane kanta.
Tak'i ci tak'i sha bare walwala".
Ahaka suka dawo ďaki tanata basarwa, suna kuma zuwa ta kwanta batareda tasake shiga harkar kowaba.
Suma k'awayennata saisuka ďaga mata k'afa domin bata hutu na wucin gadi, tasamu damar cuďaya jiyanta da yau.
/^/
To shimadai a 6angaren doctor hakane, sai wajen gab da la'asar numfashinsa ya daidaita, zuwa wani kuma k'ank'anin lokaci yafarka.
Dr Nabeel dake gefensa yafara yimasa sannu.
Ya amsa cikin ďaga kai domin bakinsa yay masa nauyin dabazai iya maganaba.
Da hannu yay masa nuni da ruwa alamar abashi.
Dr Nabeel yamik'e da sauri yaďaukko gorar ruwa ya 6alle murfin ya tsiyaya akofi.
Ya taimakama Dr Isma'il yatashi zaune ya jingina da gado, sanan ya kafa masa kofin ruwan abaki.
Saida yasha kusan rabi sanan ya janye bakinsa alamar ya k'oshi.
Dr Nabeel ya ajiye kofin yana k'ara yimasa sananu, ya haďa masa shayi mai kauri wanda yasan sai sunyi dagama kafin yashashi, dan bayason cin abinci yanzu sosai.
Aii ko dak'yar yasha shayinnan, sanan yasha maganinsa yakoma ya kwanta.
Har tsawon kwana uku Dr Isma'il yana jinyar jiki data zuciya, sosai yay jinya akwana ukunnan.
Hakama gimbiyar tasa iman dukda bata kwanta ta ce, "batada lafiyaba jikinta da ayyukanta suna nuna alamar ciwo, danma tanada k'arfin hali da k'ok'arin 6oye damuwa, shiyyasa bakowane yake saurin gane matsalartaba kai tsaye.
Amma k'awayenta suna kula da ita suna kuma tayata addu'ar samun sauk'i a al'amuranta na jiya dayau, da gobenta.

Dr Nabeel yanason tanbayarsa miya faru amma yanajin tsoron dawo da hannun agogo baya dan haka saiya share kawai.
Bayan kamar minti talatain Dr Isma'il ya ce, "zaiyi sallah.
Abokina kabari zuwa anjima mana lokacin kak'ara samun k'arfin jikinka.
Zan iya Nabeel kaidai kaini bayi kawai.
Da taimakon Dr Nabeel yay alwala tareda rama dukkan sallolin da'ake binsa tundaga azuhur.
Chapter 7 · 0% Book details