Sashe 9
Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
"Daga jama'ar Annabi, kinsan mu 'ya'yan malamai ko Ina muka sauka gida ne".
Shiru tayi ta zuba Masa abincin zata Zuba nata ya dauke plate din.
"Kin manta ai ba raba Abinci a tsakaninmu muci kawai".
Tare sukaci abincin suka Gama, tana Dan kallonsa lokaci-lokaci, da gaske yazo Mata da abubuwan mamaki da yawa Amma azarbabi ba nata bane. Dole tabi kamai a hankali saida ya tabbatar ta koshi sannan ya saurara mata, Nan cikin parlourn suka dawo suka zauna ya dorata a cinyarsa yasa hannunsa ya zagayo cikinta yana ta faman
amsa wayayoyi, sai ya amsa way kamar uku, sannan ya aje ya fuskance ta. Wasu irin wayoyine guda uku Wanda ita dai sai a T.V take ganinsu amma sai gasu a hannunsa kuma ya wani ci magani Dan kada ta Tama Fara masa wasu tambayoyi.
'
"Bani labari ya akayi ciwo Bai tashi kamaki ba Saida nayi Nissan Zango, naji doctor tace Wai rashin samun biyan bukata ne yake kawo miki yawan ciwon marar saboda sha'awarki tana motsawa Baki samun biyan bukata".
Waro Idanu tayi Baki bude tana Masa wani kallo.."Ni kuma? Wane irin magana ce wannan bayan fibroid din Kuma harda bita da kullin sharri? ta Nan Kuma ta bullo? To ai sai tazo ta ta cire min sha'awar tunda ita ta ganta, kawai ta Fadi gaskiya tanaso tayi amfani da aikinta ta cuceni,tunda da hadin bakinka Ashe ni aka mayar sakarya aka tasoni tunda daga kauyen mu aka kawoni gurin budurwaka ta dubani,ta ganeni ciki da bai kaga ko idan ta aureka bani da wata fuffuka da zanyi Mata, wata Kila da Allah baisa ta fito da maitarta fili ba da Allah kadai yasan illar da zatayi min.Da Jin saita cire min mahaifa gaba daya, ka fada Mata wallahi da gatana Ina da gatan da wallahi ta cutar da lafiyata Saida ta kare rayuwarta a life in prison, kuma indai Kaine nabar Mata taje ta hadiyeka kada wata ta Kara ganinka tace tana so, an fada Mata Ni Ina da damuwa ne da zata ringa wulakantani in dai saina Kara zuwa ta dubani ciwon yayi min abinda Zeyi min Kuma yau in Sha Allah gida Zan koma bazan iya Zama a Nan ba Ni duk kanon ma ta fice min daga Rai, ka mayar Dani inda nafi wayo".
Ta karasa fada tana juyar da fuskar ta gefe.
Kwanto da kansa yayi gefen wuyanta. "Cewa fa nayi ki bani labari ba cewa nayi meye damuwar ki ba, Ni meye laifina daga na turoki a duba min lafiyarki".
Ai fadar hakan saiya tunzurata nan da nan sai hawaye.
"Oh! My God!, Mena fada Kuma? pls tell me".
"Kwace Kanta ta shiga yi tana fadin.
Daman nasan ba Sona kakeyi ba tunda Ni matar shige ce Bata da daraja kuma wallahi duk Wanda ya Zama sanadin da wannan gararin rayuwar ya sameni ban yafe Masa ba, da qimata da mutuncina an mayar Dani wata shakatafi kowa saiya takani yanda yaso bani da wata qima".
Ta sunkuyar da kanta tana wani kuka Mai cin zuciya.
Iya dagula lissafi tayi Masa Dan kasa cewa komai yayi sai sakata da yayi a jikinsa ya kwantar da ita shi kadai yasan abinda yakeji, suna haka yaji wayar Daya Bari a kunne wadda yake amfanin yau da gobe ta dauki kida Mai Dadi.
A hankali ya Kai duba gurin wayar, Sameer ne.
Dauka yayi baice komai ba "Ina kofar part din Nan kana da bakuwa".
"Dude ka shigo sai muyi maganar".
Ya kashe ya aje wayar, Jin ya ambaci Sameer ya shigo yasa zahra yayi kokarin zare jikinta amma Dan bawan Allah nan kememe yaki sakinta saiya gyara Mata Zama kawai.
Dago Kai tayi da niyyar yi Masa magiyar ta saketa ta tashi dai dai lokacin Sameer ya karaso gurin, be taba tunanin tana jikinsa ba tunda shi kadai ake hangowa Saida ya kure musu yanda ba yanda za'ayi ya koma, tsaye yayi shi Bai Kona ba shi Kuma be karasa gurinsu ba ita kuma Zahra kunya kamar ta nutse wallahi Bata taba tunanin rashin ta idonsa ta Kai har haka ba.
"Have a seat, kazo ka tsaya Wai kuka take min na kawota an Mata wulakanci na Maida ta gida ita ko sunan Kano Bata sonji".
Sameer 'yar dariya yayi "Ni ba ruwana a ciki Dan aikene ni kasan Mata Dan Abu kadan saiya tada musu hankali, Daman bakuwar tata ce Hajiyar makwarari ce ta kirani bayan nabar Nan Ina gidan mommy na mayar da Rukayya saiga kiranta Wai lallai saina daukota tazo taga madam shine mommy tace na kawo ta indan ba haka ba zata iya rikita lissafin kasan halinta dai".
"Ok ba damuwa ku shigo tare ai Hajiyarmu ce ba inda bazata shiga ba".
"Ok sir".
Ya juya ya fice daga parlourn da sauri,mamakin Mahmud ne ya kamashi sosai ya rasa wane irin so yake yiwa yarinyar Nan ne haka? Yana tare da wannan mezeyci da wata Haseena ai saidai tayi hakuri da can Bata you tasiri ba gurinsa ba bare yanzu daya Sami abinda ya kwallafa rain a kansa.
Zahra Jin Sameer ya fice yasa ta dago da kanta daga kijinsa tana ajiyar zuciya, Dan just tayi kukan ta Kama nasa guri sai mamakin furucin oga Sameer daya cika Mata zuciya wai sir to me hakan ke nufi itafa kada su manna Mata Dan karamin hauka gaskiya.
Dan Allah ka barni na tashi kaji fa Hajiya ce yace fa
Zata shigo, Kuma Dan Allah bakaji kunya ba ka wani sakani a jikinta salon yace bani da tarbiyya".
Wani kallo ya watsa Mata "ai yau ko waye ze shigo gurin Nan a haka ze samemu gara asan Ina sonki tunda kina ganin ba sonki nake ba har kina kallona kina fadin Wai matar shige ce ke idan aka sameni rungume da kayana Ina lallashi kuwa koya saiya sheda ina son abuna, nine dai ba Sona ake ba anfi son wannan Mai jan kamar karas tunda saboda shi aka yarfeni da bakaken maganganu".
Har ta bude Baki zata bashi amasa taji rangada sallamar Hajiyar makwarari, ai ita kanta Bata San yanda akayi ba ta tsinci kanta a tsaye ballentana shi da ake zaune a jikinsa, shi dai Sameer Bai San lokacin da dariya ta kubce Masa ba ganin yanda Zahra tayi wani wuk'i-wuk'i da ita shima gogan dariyar yake Amma a ciki.