Sashe 42
Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ammi najin fitar Aishat ta fito daga toilet din ta dauki wayar ta Kira number data karba a gurin zahra, Bata so Kira a irin wannan lokacin na safiya ba amma dole tasa hakan.
Lokacin Ammah na kitchen Musaddiq ya kawo Mata wayar yace kiranta akeyi, tana wanke hannunta wani Kiran ya shigo Saida ta goge hannunta ta karbi wayar, bakuwar number ce.
Dauka tayi tana amsa sallamar tana ficewa daga kitchen din ta barwa Alawiyya aikin, gaisawa sukayi da Ammi kafin Ammin tace.
"Ko Hajiya Asma'u ce maman Fateemah Zahra?".
Sai Ammah taji gabanta ya Fadi ana ambatar sunan zahra.
"Eh nice, Allah yasa lafiya?".
Dan murmushin da Bata shirya ba ya kwacewa Ammi.
"Lafiya kalau sai Alkhairi,sunan Hajiya zainab daga Nan sokoto mahaifiyarsa Mahmud mijin Fateemah".
Cikin nuna jin Dadi da tsantsar fari ciki Ammah ta Fara fadin.
"Masha Allah! Hajiya ya gida ya akaji da jama'a ai jiya ta fada min suna Nan naso na karbi number ki mu gaisa sai tace min wai bazata iya tambayar mi ba, to yau naso na karba a gurin shi mijin nata mu gaisa".
"Kai haba babu komai muya Kamata mu tako muzo muyi godiya yanzu ma bamu fasa ba wata dai Alfarma nake nema akan 'yata yau komai dare suna Nan bisa hanya zasuzo tare da 'yan uwa na sai anzo daga Nan an daukar min ita an kaita dakinta kamar kowace Amarya ba Wai a wayi gari a ganta a matsayin matarsa ba bana son ayi Mata wani duba na daban kinsan Yana yin kowa ne family da irin nasu matsalolin,duban irin kalubalen da aka fuskanta a Nan din kafin barinsa gida, naso ace wani nawa yayi Miki wannan bayanin to basa kusa kiyi hakuri nayi rashin kunya akan Dan Fara".
Ta fada tana 'yar dariya irin gentle din Nan.
Itama Ammar yin tata tayi, tana fadin.
"Na fashimta kina dai son kankarowa diyar taki mutunci ne ko?"
"Gaskiya dai Kam Allah dai ya saka Miki da Alkhairi kinyi abinda duk uwa ta gari zata yiwa yarinya mace Hussein ya fada min komai, mun gode da Karamancin ku garemu kin dauki yarinya kamar wannan kin bashi ba tare da kunsan asalinsa ba, sai nazo har gida nayi godiya in Sha Allah".
Sukayi sallama kasake Ammah tayi tana lissafo maganganun su da mahaifiyarsa Mahmud daga ji ba wata Babbar bace sosai sai dai tasan kanta da alamar Allah ya karbi Addu'oin ta Wanda take ba dare ba Rana akan Zahra na neman dace da kwanciyar hankali a gidan Aure, sai Kuma tayi murmushi wannan sirikar ta Zahra za'a da ita tasan ta Kan duniya wato sai ansan yayi aure ba Wai yazo da Matar ba kamar Auren bariki.
Part din Abban ta nufa na bangaren ta, tana shiga Yana aje wayarsa da ya gama. Ganin fuskarsa da wani irin annuri yasa ta fasa fada Masa abinda tazo dashi gara ta Fara Jin nasa tukunna.
"Wane irin albishir akayi maka haka Mai Dadi Daya saka Zuciyarka a irin wannan Nishadin haka?".
"Zoki zauna yanzu muka Gama waya da sirikin uwata Wai ashe yaron Nan mahmud Dan wajen General Muhammad Dange ne, Saida ya kirani yanzu na gano inda nasan fuskarsa Kullum na kalleshi sai Naga nasan fuskarsa ko a wani gurin ne daban Ashe fuskar mahaifiyarsa nake gani a tasa fuskar, kinsan kuwa waye General Dange? To babu abinda zewa Ubangiji sai godiya ya sakawa uwata da abinda hankali da tunanin mu Bai taba kawowa ba mijinta fa shine Dan general din Wanda ake hasashen Yana Daya daga Cikin matasan masu kudin Africa sahun farko duk fa yanda family dinsu sukayi popular a kasar nan ta fuskar arziki yaron yayi musu wata irin tazara, Abu Daya yake bani mamaki yanda ya iya jure rayuwa irin ta Cikin Almajirai ba kyamata ko kadan Abu Daya ne dai kawai ya ringa sani a tunani yanda tun bayan samun lafiyar yaron komai na makarantar ya canza akace NGOs sun shigo suna wannan mahaukatan ayyukan Wanda ba'a yinsu a sauran makarantu Dan ma daga baya sun canza salo sun shigo da wasu makarantu harma Dana Karkara".
Jinnina Kai kawai Ammah takeyi tasan wannan ba tsuminta ba ba Kuma dabararta ba Rahamar Allah ce ga bawa kawai da yake yinta ga wanda yaso a lokacin da yaso, lallai sun kunshi takaici da yawa a baya Amma Cikin Rahamaniyya ta Ubangiji sai gashi abun ya zamo wani haske daga karshe abinda babu Wanda ya zata Koda kuwa a Cikin mafarki ne.
"Abban Yara Nima abinda ya shigo Dani kenan na fada maka munyi communicating da mamansa yanzu".
Nan ta fede Masa daga biri har wutsiyar yanda Sukayi da Ammin mahmud.
Dariya Abban yayi yana fadin "Nima ya fada min har Yana bani hakuri da halin Mata na bidi'a Wai ita uwar sai tayi bikin danta kowa yasan yayi aure"
Sun Dade sun tattaunawa na Suma dole su nuna Mata gata tunda inda Allah ya kaita ba gurin Wasa bane na take Abban ya turawa Ammi makudan kudi ayi abinda ya Kamata Dan ma da furnitures a aje Wanda Ummee suka turo ba'a sakaba saboda babu guri Kuma Kaya ne na garari.
******** Tunda su zahra suka Gama Break fast suka koma parlour na uku suka zauna suhailat ta kunna musu tv ana yin wani series na 'yan Lebanon, manyan jakunkuna taga masu aikin Ammi suna fita dasu daga dakin da aka aje kayan da suka zo dasu ba dadewa Kuma taji maganar mutane daga dayan parlourn, sai kuma taga suhailat ta tashi da sauri tana fadin.
"Kai su mummy Badi'a ne yanzu da safen Nan haka kamar Wanda suke daga wata unguwar"
Ta wuce ta nufi inda suke.
Da gudu suhailat ta fada Kan mummy Badi'a tana fadin.
"Sannunku da zuwa mummy keda Hajji zuwaira, ina kwanan ku Ya hanya? Amma zuwan Cikin dare kukayi ko? Naga duka yanzu Sha Daya fa".
Gaisuwar suka amsa sannan mummy Badi'ar tace "ko kadan dazu muka zo wurin karfe Tara da rabi ta baya muka shigo muna sama ne gurin Ammi itama yanzu zata sakko".
Aishat ce ta shigo daga wata kofa wadda zahra Bata San ko Ina bane, ranta a hade ta cewa Zahra ta taso suka nufi gurinsu su suhailat.
Suna shiga bakin suka fara fadin.
"Masha Allah, wannan ce Fateemar? Matso mu gaisa Hajja zuwaira na fadin "nice dai ta karfen keta katako ce" mummy Badi'a na tare mata, cikin Jin nauyi zahra ta tsuguna ta gaisheni su Cike kunya da girmamawa.
Aishat sai taji tana jin haushin maganar Hajja ita ana ga yaki tana ga k'ura, Ammi na maganar a mayar da Zahra gurin iyayenta a Basu hakuri ita Kuma tana maganar wani itace ta karfe. Ammi ce ta shigo rungume da wani Abu anyi rapping dinsa tazo ta zauna kusa da mummy Badi'ar tana fadin gara ku tashi komai ya Zama ready kada kuyi dare tunda tafiyar mota ce".
Tashi tayi tana fadin .
"Hasana kuje kofar baya gamu Nan zuwa".
"Taso sister muje"
Ta fada tana taba kafadar zahra.
Ita fa Bata gane ba an sakata a duhu Ina zata kuma taji ana fadin kada ayi dare to suwa zasuyi Daren? Ita Kuma meya hadata da bakin Ammin da taji kamar da ita zasu tafi.
Ita dai bin Aunty Aishar takeyi wadda taji kicin kicin da rai kamar ta fasa kuka.
Wata lafceciyar GLK Mercedes-Benz 2024 model Parke a kofar baya sai daukar Ido takeyi Baba Habu drivern Ammi na Amana Yana gefe Yana jiran Umarnin Ammi.
Da saurinsa ya matso Yana gaishe dasu zahra, fa sauri zahra ta Dan duqa ta fadin.
Lafiya kalau Baba"..
Su Ammi ne suka fito har inda su Zahra suke tsaye Ammi ta Karaso, ta Kamo hannun Zahra ta dankata a hannun Hajja zuwaira tana fad'in.
Gata Nan Hajja na Baku Amana ku damkata hannun mahaifiyarta Dan Allah, Allah ya tsare hanya".
Kunshin abinda ke hannunta da wani gidan sarka White gold Mai azabar kyau sarkar kudinta sun tasarwa milion hamsin ta mikawa Zahra tana fadin "Allah ya tsare hanya ki gaishe min da mamanki".
Ta bude motar ta sakata ta juya ta koma Bata Kara kallonsu ba saboda ji tayi kamar rabuawar kenan.
Wasu hawaye Aishat taji sun cika Mata ido da gudu tabi bayan Ammi tana fadin .
"Why! Why! Why! Ammai kin kashe min farin Cikin bros wallahi".
Mahmud ne ya fito daga part din Abbie yaji wannan kalaman daga bakin twin sister dinsa.
Yayin da a waje itama Zahra data Gama fuskantar inda aka dosa ta kifa kanta a gefen kafadar mummy Badi'a tana sakin wani marayan kuka tana ayyana shikenan ta faru ta Kare wata sabuwar matsalar kuma.
A Hankali zahra ta bude idanunta sharaf da hawaye Jin motar ta harba da wani irin speed ta nufi main gate, ta juya ta yiwa gidan kallon karshe gidan data kwana Daya Tak a cikinsa da sunan matar dansu wadda a yau kuma bata San wane suna zata Zama ba, wata Kika sunanta ya tashi ya koma bazawa kuma, Dan rashin 'yanci ko Jakarta ta hannu ba'a Bata dama ta shiga ta dauko ba.
[27/02, 11:13 am] Abu Saleh: * AUREN HUCE HAUSHI*
AISHAT ISAH MUSAH
Maman Fateemah
99061432330
Or
08056362975
Page 78