← Book details Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 47

Sashe 31

Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Har Abbas suka sauko Yana inda suka barshi,.bayan Abbas yaci abinci ya dawo kusa da mahmud ya zauna.
"Wai me yake damunka ne ko baka da lafiya mu wuce asibiti? Ko Kuma malantar ce tasa ka zama haka? Kasan ku alarammomin nan da izza kuke".
Ya fada Yana dariya, shima mahmud din dariyar yayi.
"Kai Amma Aishat kin kware gurin kinibibi yanzu har kin fada masa wannan maganar gaskiya min Dena sirri dake tinda yanzu babu Aminci a tsakaninmu kina da naki ma'amincin".
Itama dariyar tayi tana nufar corridor din dakin Zahra, tana tunanin wayon yarinyar da gani akwai abinda suke boyewa su duka Dan da alama horo ne take Masa a Cikin ruwan sanyi Dan ko rantsuwa tayi bazatayi kaffara ba da wata a kasa.
Cikin ikon Allah tana kokarin knocking taga Zahra ta bude kofar tana sabe da Yar gidanta Wanda ta tashi daga barci.
"Sannu Aunty, gata ta tashi tun dazu batayi dai kuka ba na Bata fresh milk dai sai Naga gara Tasha natural nata dai".
Ta fada tana Mika Mata Afnan din, abun mamaki sai yarinyar taki zuwa gurin uwar.
"Huta roro Nima na huta da tsotsa, amma kuzo muje ki gaisa da sweet heart ya dawo shine ma yake tambayar Afnan din tunda yau Abulkhairi baya Nan yaje week end gidan Dr Suraj abokin Daddynsa".
"Allah sarki shi yasa banganshi ba Ashe baya gidan".
Bata bukatar komai Dan ta yafa wani veil Amma karamine ta saka abaya Dubai maroon Mai adon stones kanana saita haskata sosai yarintarta ta Kara fitowa da wani sirrin kyau Dan asali ga kanshin turarenta da Kuma irin Wanda Hajiya Amina ta hada Mata masu janyo Hankalin oga duk irin kamewarsa kuwa.
Tare suka Jero suna magana wadda tasa Zahra yin wani tsadedden murmushi sai akayi dace duk su biyun suna facing din hanyar.
"Tabarakallahu ahasanil kaliqin".
Abbas ya fada.
Shi Kuma Dan gogan ya kasa dauke idanunsa daga kanta sai yaga murmushin kamar da gayya take yinsa.
Cikin takunsu na matan da suka San takan gayu suka karaso parlourn, sallama Zahra tayi.
Abbas ne ya samu zarafin amsawa shi kuwa mahmud tamkar an rufe Masa Baki, ai shi Abbas Bai zaci haka zahrar take ba yanda sweetie ke bashi labarin ta Sai yaga ai Sam Bata iya fasalta mutum ba.
Afnan na ganin Daddy ta shiga irin rawar murnar kaga abinda kake so din nan da Yara sukeyi tana zillo gurinsa zahrar ta nufa da nufin ta kaita.
Ita da duk saura ba Wanda yaga lokacin da mahmud ya diro gabanta Dan ja da baya tayi da sauri tana fad'in.
"Subhanallahi! Lafiya meye faru?".
Baiyi wata wata ba ya rungumosu ita da Afnan din dake hannunta.
Kici kicin kwacewa take Dan Bata taba tunanin zeyi irin wannan danyan aikin ba.
"Na shiga uku! Aunty ku taimaka min Dan Allah ku janye shi inaga bashi da lafiya kada yayi Mana illah Ni da yarinyar nan".
Ta fada tana kuka.
"Wallahi bazaki sakamin ciwon zuciya ba kin hanani sakat tun safe kin Hana ko fuskarki na gani,kinki yarda muje asibiti, me nayi Miki Mai zafi haka har kike ikirarin Wai mijinki ya Hana kije Asibiti, waye mijin naki bayan ni? Fada mini!!!..????"
Ya fada Yana hargagi abinda Bata taba gani ba kenan a iya zamanta dashi,kuka Afnan ta kwallah saboda yanda ya matsesu ga Kuma hayaniya da yake musu.
Da sauri Abbas ya taso yaga mahmud din kamar baya cikin nutsuwarsa.
Hannunsa Daya ya kamo sai yaji jikin nasa na tsuma.
Daidai kunnensa Abbas yayi magana.
"Pls sakarta kaga ka saka yarinya kuka, ka nutsu ta fada maka me yasa tayi hakan kowa ai yasan taka ce Ina ga da abinda kayi Mata Mai ciwo".
Da kyar ya yarda ya saketa ita da yarinyar. Zaunar dashi Abbas yayi ai Zahra na Dora yarinyar a cinyar uwarta lokacin Abbas na can Yana bashi Baki ta fice.
Tana shiga tayi locking din door tana sauke numfashi tare da goge 'yan hawayenta na karya data kakarosu.
"Wallahi saina rama zakayi bayani da bakinka guy ni zaka yiwa cin fuskar da ze Zubar min da daraja da kimata sai zuciyarta da Bakinka sun Fadi gaskiyar da kake boyewa, Kuma Wallahil Azim addu'ar tsamiya yanzu na Fara har FAHAZAMUHUM BI'IZIMILLAHI YA WADUDU YA JAMI'U MALIKIN NASI MALIKI YAUMIDDIN zanta zabga maka sai ka Raina kanka kasan Dan an baka kyautar zahra ba Yana nufi Zan Zama matar shige ba, sai duniya ta shaida zahrar Zahra ce, tayi kwafa ko yanzu na rage tension ko ya yake tunda kaima kaji a jikina ka Kuma karyata maganar daka fadawa 'yar uwarka jiya, Wai bakaga wadda tayi maka ba, sai kasan bayanin da zakayi musu Kuma tunda magana zarar bunu ce bata komawa.

Lokacin da Abbas ya juyo da zummar yiwa Zahra magana yaga sai filin gurin kallon Ina take ya yiwa Aishat..
"Ta gudu Ina zata tsaya ya nakasa ta yayiwa mijinta asara,kuma saboda Allah sai ka kakume Matar mutane da yammacin gari yaushe ka Zama haka yarinya da aurenta da komai wannan kasan haramun ne basai an fada maka ba, Ina cewa gida Daya kuka zauna ba diyar malaminka bace me yasa kasan kana sonta kayi shiru har wani ya aura ni Naga kokarinsa Daya amince ka taho Masa da irin wannan diamond baby din wata uwa duniya baya tsoron sharri shaidan ya gitta tunda gashi a gaban mutane ka iya rungumeta yaya idan daga Kai sai ita ne ai labarin ba irin wannan bane ki.."
"Stop!!!..... Aisha, ni kike fadawa abunda yazo bakinki? to Zahra halaliyata ce matata ce ta sunna".
Ya fada a zafafe tashi yayi ze fice da sauri Abbas ya riko shi.
" Dawo magana zamuyi ta fashimta".
Baiyi gardama ba ya dawo ya zauna, ita dai Aisha rasa ta cewa tayi wai barawo a hannun Mata.
Very close dashi Abbas ya zauna ya riko hannun mahmud Yana fadin.
"Munji matarka ce amma yanda sweetie ta fada min kace matar ubangidanka ce me yasa ka boye mata Bata cancanci haka ba, kasan irin wahalar Dana Sha da ita lokacin da case din Nan ya taso? yanda kasan zata zautu wallahi Amma sai ka dawo Mata da wata fuskar daba taka ba duk rintsi bakwa rufewa junanku komai, kasan ta fada min cewar wallahi matarka ce Dan ta shaida bazaka taba yarda kayi tafiya da mace irin wannan da mace kamar wannan babu alaka Mai karfi a tsakaninku".
Mahmud ji yayi duk ruwa ya cinye shi yarinya karama ta dagula masa lissafin da tasa ya saki layi duk yanda yake shirya nasa planning din ta rusa a lokaci daya yayi amansa ya lashe.

"To tayi hakuri ni kaina bansan me yasa na kasa fada Mata ba Ina Jin nauyin yanda Zan tunkari Ammi da Abbie da wannan maganar ba wallahi, sai Naga nayi wani Abu Daya sabawa al'adar mu ta Malam bahaushe, Kuma ita na rasa abinda nayi mata lafiya kalau mukazo gidan Nan Amma ta sauya min na rasa abinda yake min dadi wallahi Ya Abbas yarinyar nan itace weakness dina a rayuwa ni kaina nasan hakan, itace fa wadda nake fada maka na gani da dadewa a jirgi ita da Abbanta ka tuna?".
"Off cause anyi haka,Amma how comes hakan ta faru?".
Furzar da iska yayi daga bakinsa.
"It's long story, idan ka huta zamu tattauna akai, yanzu dai ki tashi like kiyi min Biko tunda Naga alamar kina da masaniyar laifina".
Baki Aishat ta dafe da hannu Wallahil Azim ban sani ba, nifa duk abin Nan hasashe nake yi ban tabbatar ba sai yanzu, ni wannan aikin ba nawa bane Kai zaka gyaro kayanka da abinda kayi Mata tunda Naga Bata da kwaramniya Sam, Kuma ya zakayi da ita kenan? Zakaje kace ga matata nan tsaraba fushin da nayi ko Yaya za'a kayi?".
"Ki Bari kawai alkawarin da nakeso kuyi min mu rufe maganar nan a nan duk da Faruq ma ya sani amma nasan tunda na kada Masa warning bazeyi karambanin fadawa kowa ba, nina taro match dina Ni zanyi playing din kayana kawai kuyi min addu'ar samun nasara kada Ammah tayi min nak'i".
Ya fada Cikin raunin murya.
[19/02, 11:46 pm] Abu Saleh: *AUREN HUCE HAUSHI*

MAMAN FATEEMAH

09062432330

Or

O8055362975.

Page 72
Chapter 31 · 0% Book details