← Book details Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 47

Sashe 14

Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Eh Mana shine, Wai Daman Kasan Ya Mahmud din ne?"
"So sai kuwa farin sani, muna haduwa da a kwantagora a unguwa Daya ma kuwa, ai kakarsa ta wurin Babansa 'yar can ce Nima kakata 'yar can ce Ummar mu kadai ta Haifa a Rimin sumaila Aurenta ya mutu ta koma gida, duk 'yan uwan Umma suna can kwantagoran na Niger state da Abuja, kinsa meya daure min Kai kuwa?"
Girgiza Masa Kai tayi alamar A'a.
"Cewa fa akayi ita zahrar an aura Mata Almajirin wani malami da yake a unguwarsu saboda duk Wanda yazo ze aureta sai an fasa Auren"

"Nima naji kadan daga labarinta gurin ya Sameer to ga dai mijinta Nan sauran bayanin Kuma ban San yanda akayi ya faru ba, tunda ya Sameer ba fada mana zeyi ba".

A parlour suka Sami mommy da kannan Rukayya Mata Bilkisu da Husna sai karamar yarinya 'yar Auntyn su Sameer Afra.

Tunda suka shigo zahra ke sadda Kai kasa da gaske nauyin mommy take ji, gaisuwar yaran suka ringa amsawa da gudu Afta ta nufo zahra tana Fadin "welcome Aunty" ta shige jikinta tana tattabata.
Hannunta zahra ta riqe suka karasa gurin da mommy ke zaune yayin da su Husna suka koma dayan parlourn.
A kasa Kan carpet suka zauna, a tare suka gaishe da mommy din, ta yiwa Mahmud sannu da dawowa sannan ta Dora da godiya, hidima da akeyi da Sameer. Zahra ta kalla ganin sai sadda Kai tajeyi yasa tace.
" 'ya ta ko jikin ne Naga bakya walwala sosai?".
Yana ji yayi fuska Bai tankaba ba dai iya shegen da tayi ba kenan jiyan saita magantu da bakinta.
Bata yarda sun hada Ido ba tace.
"A'a ba komai mommy lafiya ta kalau".
"To Masha Allah haka nake son ji, kina jina ki saki jikinki Dani ki daina Jin nauyi na kinji, ni uwace idan kina da damuwa duk da bama fatan hakan ki sameni ki fada min ki daina yanke hukunci da kanki".
"To in Sha Allah bazan qara ba na gode". Ta fada tana Wasa kitson Afra kanana Yar dasu.
Tashi mommy tayi tana fadin "Bari na fadawa Alhaji kunzo sai ku shuga ki gaisa yaga 'yar tasa wadda bai sani ba".
Ta nufi nufi wani corridor dake hannun dama.
Bata dade ba ta dawo tana fad'in "Mahmud kuje Yana parlourn kasa". Saida aka yiwa Afra wayo da chocolates sannan ta yards tabi mommy dakinta ita Kuma zahra suka nufi bangaren Abban su Sameer din.
A Nan suka same shi a parlourn Wanda yaji kayan more rayuwa dai-dai da shekarunsa, babban mutum mai cikar Kamala, fari sosai kamar irin buzayen nan, a Nan zahra ta gano inda Aunty Rukayya ta samo farin ta dan mommy dai irin wankan tarwada din nan ce shi yasa tayi mamakin Jin Rukayya kanwarsa ce uwa Daya uba Daya.
Da madaukakiyar fara'a ta taresu Yana fadin "Masha Allah sannunku da zuwa, ka kyauta Mahmud daka kawo min yarinyar nan kaga na Riga Alhaji Muhammad ganinta ko? masha Allah ku zauna".
Ya fada Yana nuna musu seat din Zama, basu zauna ba a kasa suka zauna suna gaishe shi, ya amsa cikin sakin fuska, da gani shi mutun ne Mai yawan fara'a.
"Allah yayi muku Albarka ya kade fitina a tsakaninku naji Dadi kwarai daka kawo min ita, yarinya ayi hakuri da juna kinji, mijinki na jama'a ne Saida hakuri kiyi Masa biyayya gwargwadon iyawarki, Kai Kuma ka kula da lamarin ta kada ka yarda wani ya wulakanta maka ita amana ce suka baka, a yanda kaje musu ba kowa ne ze dauki yarinya kamar wannan ya baka ba, to ka kula da ita sosai ka Bata dukkan farin ciki tayi rawar gani, daga karshe Ina rokonka abinda ban taba saka Baki a cikin duk kwaramniyar da akayi a baya ba sai yau, kayi hakuri ka koma gida ba girmanka da mutuncinka bane haka ai ba'a fushi da iyaye duk rintsi albarkarsu ake nema kome ka Zama indai kana da iyaye yaro ne Kai, nasan an bata maka Amma idan ka duba ko tukwicin wannan yarinyar da Allah yayi Maka ai sai ka huce ka nuna godiyarka ga Allah Daya baka ita, Kai ba karamin mutum bane a kasar Nan Koda kuwa a shekaru kake da karancin girma, kaje gida ka hada hankalin ka guri daya, Allah yayi Albarka ya Kara daukaka numa ganin sakonni mun gode kwarai da gaske, idan Kuma naji Shiru baka koma ba da kaina zanyi abinda baka so ayi din, Dan ko shekaranjiya Saida Hajiya Inna Tasha kukanta a dakin Nan Ina amfanin irin haka ai musulmin kwarai da yafiya aka San Shi kaji Mahmud ayi hakuri ayi afuwa Allah yasa son masu yafiya".
Tunda Alhajin ya Fara magana jikin Mahmud yayi sanyi da gaske duk badak'alar da akayi ko uffan Bai tofa ba sai yanzu Kuma yasan baya raba Daya biyu damuwar da yaga hajiya Inna a ciki ta Dame shi.
Cikin ladabi Mahmud ya Fara magana. "Nagode Abba in Sha Allah Zan koma, Nima nayi wannan tunanin ba fushi nayi dasu ba sune dai sukayi fushi dani, Ina son su huce ne tukunna kada na koma a maido hannun agogo baya".
"Kai haba wannan maganar ai babu ita to ai itama zahara'u ta zamar maka garkuwa, ki tashi ku tafi dare ya Farayi ga yanayin sanyi Allah yayi Albarka ayi kokari ayi yanda nace".
"In Sha Allah Abba".
'yar karamar Leda Fara Alhajin ya mikowa Mahmud Yana fadin "ungo rikewa 'yata".
Godiya sukayi Masa Sosai suka nufi kofa Yana saka musu Albarka.
Lokacin da suka fito Rukayya ta shigo suna tare da mommy.
"Aunty Rukayya har Ya Abban ya tafi?". Zahrar ta fada tana nufar inda Rukayyar take.
"Eh ya wuce tun dazu".
"Ok shikenan da sako Zan bashi gurin Ummah Amma na Kirata a waya".
Sallama sukayiwa Mommy Rukayya ta rakosu har gurin mota da ledar da mommy ta bawa zahra kyautar dangin turaren wuta dasu humra.
Da sukazo fita kudi masu yawa taga ya bawa Mai gadin gidan sannan suka wuce, tunda suka fito daga parlourn Alhaji Abban su Sameer Mahmud yayi dif da alamar anyi Masa famin wani Miki a zuciyarsa.
Ganin haka yasa zahra ta Kama kanta itama.
Titin gidan Bashir tofa suka fito gasu can sun fita gidan Buhari, sahad store taga ya shigo ya nemi guri yayi parking sannan ya bude Yana Fadi ki jirani ina zuwa ya wuce ciki.
Bai Dade da shiga ba wata mota tayi parking kusa da tasu, gurin akwai wadatar hasken da yasa kana iya ganin Wanda yake cikin mota.
Ba zato ba tsammani kawai idanun Zahra suka sarke Dana Musbahu Wanda ya fito daga gurin driver suna tare da wani Guy da alamar dayan irin ya'yan hutun Nan ne, da gani Suma sayyayar sukazo, da sauri ya nufo gurinta jikinsa har rawa yakeyi Yana fadin "Zahra!" dai-dai lokacin Kuma Mahmud ya fito tare da ma'aikatan gurin sun dauko Masa Kaya sun nufo motar, shi Kuma wannan gayen Yana ganin Mahmud yayi wata irin zabura ya nufeshi ya rungume shi jikinsa na wata irin tsuma Yana fadin "Ya Mahmud Ina ka shiga ka barmu".
[2/1, 6:08 PM] ASHMAR🤍: ✨✨✨

AUREN HUCE HAUSHI

MAMAN FATEEMAH.

Page 48.
Chapter 14 · 0% Book details