← Book details Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 47

Sashe 25

Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin abinda Bai wuce minti talatin ba suka shiga Asibitin office din doctor suka nufa tunda ya bukaci ganin mahmud saboda ze cike wasu forms ze Kuma yi signing a takardun da za'ayi aikin.
Basu Dade ba suka Gama da office din doctor suka nufi dakin da Baba Malam din yake.
Suna tafiya kawai Habib kallon mahmud yake ya rikide ya juye daga mahmud din Baba Malam ya koma wani na daban Mai wani irin kwarjini da cikar Kamala ko Zama sukayi Hira irin ta da yanzu sai Habib yaji baze iyaba sai fa mahmud ya matsa Masa sannan yake Dan sakewa, ga Abubakar wanda shine babban guard dinsa Amma sukayi basaja ba Wanda ya gane, ga wani Karin abin mamakin Wai Bilyaminu ma yaran mahmud ne.
Har suka karasa dakin yana ta faman tunanin abun.
Masha Allah ba karamin Dadi sukaji ba da ganin yanda jikin Baban yake.
Sallamar su ya amsa Yana sakin murmushi tamkar ba Mai lalura ba, gani ma sukayi har wani haske ya Karayi duk da Daman farin mutum ne Shi, Yana kwance sandam da sauri mahmud ya Karasa kusa dashi Yana fadin.
"Masha Allah! Baba jiki ya Fara kyau Alhamdulillahi, ya kaje jin jikin naka?".
"Alhamdulillahi Mahmud jiki ya Fara kyau ko yanda nakeji da banbanci akan kwana ukun baya, sannunku da kokari Allah yayi Albarka yasa afi haka".
"Allahumma Amin".
Suka amsa su duka, Abubakar da Habib ne suka matso suna gaishe da shi da tambayar ya jikin nasa.
Ya amsa musu da sauki suma yayi musu godiyar dawainiyar da suketa faman yi dashi.
A Nan suka zauna har dare suna dauke Masa kewa mahmud ya cika Alkawari ya kirawo Bilyaminu video call yace ya Kaiwa iya Abu zasuyi magana da Malam, taji dadin yanda taga jikin nasa Dan sun Jima suna Hira har su mahmud sukaje suka Kara dubo Alhajin su Faisal.
Sai wurin goman dare na agogon kasar suka wuce daga asibitin, ba gida suka nufa ba, Abubakar ke driving sai Habib dake zaune a gefensa sai Kuma oga kwata-kwata dake baya yana ta cinkunar wayarsa.
"Sir ina zamu Fara zuwa?"
Abubakar ya tambaya cikin ladabi.
Saida ya Gama duba results din club dinsa real Madrid, sunyi Wasa lokacin suna Asibiti shine yanzu yake duba results din wasan.
"Wuce Africa Avenue kawai na gama ganawa dasu sai mu shiga Taj idan lokacin be Qure ba".
"Ok sir Leela palace kenan?".
"Eh a can nace musu zamu zauna"

"Ok."
Akalar motar ya canza daga hanyar da yake bi, shi dai Habib nasa ido ne Dan fadan da yafi karfinka sai ka mayar dashi Wasa.
Ganawa ce mahmud din zeyi da managers na different companies dinsa ya Dade Basu hadu ba sai dai ta Internet kawai, shine yayi amfani da wannan damar ya tarasu duk da yaso sai Nan gaba to wata kura ce ke neman tasowa shine yayi musu Kiran gaggawa.

Habib yaso fita mahmud ya Hana shi, ba karamin abin al'jabi Habib ya gani ba yanda yaga manyan mutane daga different countries suna Masa aiki a Nan Indian shifa har tsoro ya Fara kamashi waye Mahmud ne Wai? Yanda yaji managers da Accountant suna bada lissafi saida jikinsa ya dauki tsuma, basu suka baro Leela palace ba sai kusan Daya da rabi na dare.
Suna shiga gidan Mahmud ya wuce bedroom, requesting coffee kawai daga gurin Mr Ajey.
Su Habib dai sunci Abinci sannan suka wuce, kowa ya shige nasa, tun jiya aka hada dayan dakin Habib ya koma ya barwa Abubakar wanda suka Fara sauka.

A gajiye mahmud ya shiga bedroom dinsa wayar da eyeglass din ya aje a Kan bedside ya wuce toilet.
Lokacin Daya fito Mr Ajey ya kawo masa coffee dinsa.
Saida ya saka pyjamas dinsa milk colour mai haske sannan ya zauna Yana sipping din coffee a hankali yana Jin dadin yanda yake ratsa Masa makogwaro Yana gangarawa.
Kira ne ya shigo wayarsa yasan ba previous bace har ze share sai ya dauka ya duba Sameer ya gani.
"Sameer" ya ambaci sunan a fili sannan ya daga Kiran.
Daga can Sameer din ya Fara magana.
"Sir Naga sakonka, wallahi da kyar na samu visar madam yau Amma sai Monday zata taho in Sha Allah gara nima dai na huta".
Ya fada Yana dariya.
"Au dariya ma kakeyi ko? wallahi idan tace na mayar dakai China da Zama Allah saika koma can,Kuma Banda madam zaka tafi, sai bayan wata shida zaka ringa zuwa Kuna gaisawa shima sai ta amince, idan Bata amince ba sai dai once in year".
"Tuba nakeyi gani nayi ka kasa hakurin rashinta a kusa da Kai tun yanzu to Yaya idan labarin yasha banban"?".
Ya fada Yana dariya irin ta shakakikan friends.
"Allah ya shiryeka badai abinda zakaji Dan saka Ido kawai, ka aje komai jibi ka wuce Nigeria Kai da kanka zaka kawota min ita Kano".
"Ok. In Sha Allah".
Sukayi sallama,wayar ya aje yana tunanin ko ya kirata ko Kuma ya kwanta ya huta.

** *** **

Barci sosai Zahra tayi Bata tashi ba sai kusan la'asar toilet ta shiga ta sake gyara jikinta.
Alhamdulillahi Abun ya Fara sauki sosai, amma dai ha lrokacin Yana Zuba over, Saida ta shirya ta nufo parlour tana rike da wayarta, ba kowa a ciki sai kamshin turaren daki da tureren wuta.
A hankali ta ratsa ta nufi dining Abinci ta gani kala biyu coconut rice ce sai danbun shinkafa da yaji vegetable a ciki, dambun ta Zuba kadan taci kadan ta tashi ta dawo parlour ta zauna. Aunty Hasana ta kiya har sau biyu ba'a dauka ba saita tura mata text, Aunty Safiya ta Kirawo lokacin suna makaranta dalibai na Exams, dauka tayi tana amsa sallamar zahra tana fadin.
"Kaga Mrs Dange, ya kanon?".
'yar dariya zahra tayi.
"Kaji dai Aunty Safiya, to Ina Azare Kuma kusa dake ma".
"Ahhh haba Dan Allah....!"
"Wallahi Ina layi na biyu bayan layinku".
Dan Jim Aunty Safiyar tayi tana tuna wani gida data gani lokacin da taje barka layin Wanda "yan layin suke ce masa gidan Dan America, masu aikin ginin ne da wani ya tqmbayesu gidan waye sukace Mai gidan Yana America shikenan suka sakawa Masa gidan Dan America.
"Kamar nasan gidan naje barkar haihuwa kwanaki baya Naga wani sabon gida akace mai shi baya kasar Ina shine gamu Nan zamu shigo da Amatu in Sha Allah".
"A'a kice na tashi na shirya abin tarba, Ina jira, Dan Allah kuzo da wuri".

Aunty zilai ce ta shigo fadin.
"Wallahi daga na Dan kwanta na huta barci ya daukeni".
"Ai Rai dangin goro ne hutu yakeso, Ina laifinki sannu kema ai jiyan yanke Miki barci akayi shi Kuma ba'a cin bashinsa sai an biya"
"Haka ne Kam ai anyi ta barka dai tunda na rabu da wannan kaddararren ciwon cikin gaskiya duniya da magani waye ze taba kawo masoro zeyi irin wanna aikin?".
"Gaskiya dai Kam".
Zahra ta fada.
"Amma dai uwar dakina kin Kira Hajiyar makwarari kiyi Mata albishir ko?".
Kai zahra ta girgiza alamar bazata kirata ba.
"A'a ba'a haka,ki kirata ki gaisheta ki fada Mata magani yayi aiki kiyi Mata godiya ai zataji dadi'.
"To shikenan na kirata anjima saina fada mata, yanzu me za'a Karayi Mai sauri zanyi Baki ne abokan aikina da muka zauna a Inda nayi service".

"Akwai samosa da nayi dazu na saka a fridge sai a soya Musa tunda da abinci da drinks ina ga ai ya Isa ko?".
"Eh hakan yayi".
Kitchen Aunty zilan ta koma ita Kuma zahra tabi lafiyar kujerar.
Aunty Rukayya ta kirawo.

Bata kusa sai mommy ta dauka cikin ladabi zahra ta gaisheta mommyn ce tace Mata. "Ai kuwa Rukayya na gidan Hajiyar makwarari dazu ta tafi ta manta wayar a gida garin sauri".
"To mommy Baki na Kira da layin Hajiyar na gode".
"To nagode Allah yayi Albarka, ya wajen Mai jikin Kuma Sameer yace sun wuce indai ko".
"Eh suna can da sauki".
"Allah ya bashi lafiya yasa ayi aikin a sa'a".
"Allahumma Amin nagode".
Sukayi sallama.
Akalar Kiran ta juya ga Hajiyar makwarari cikin sa'a wayar na hannunta ta Gama amsa wani Dan uwanta Malam na Dala Kiran zahra ya shigo.
Dauka tayi tana fadin,
"Salamu Alaikum, waye yake Kira?".
"W/slm, Hajiya nice zahra".
Dan Jim tayi tana tuna Ina tasan muryar Nan.
"Zahra wace ce kenan? Ko Zahara,un Hajiya Fateen lalloki?".
"A'a ba ita bace".
Sai zahra ta rasa me zata ce Mata ne, tace zahrar mahmud abokon Sameer, sai taji da nauyi ta fada Mata haka.
Rukayya ce ta shigo da cup din kunun tsamiya data damawa Hajiyar a hannunta.
"Wa Kika Sami haka naji kina ambatar zahrar lalloki".
"Ungo kiji ko wacece tayi shiru batayi min bayani ba ke kiji ko zata fada Miki".
Wayar Rukayya ta karba tana mikawa Hajiyar kunun a cup.
"Aunty Rukayya".
Zahra ta Kira sunanta.
Take ta dauki muryar zahrar.
"Au kice min amaryar big bro ce ai bayani Zaki yiwa Hajjaju, kince zahra Ina zata gane".
"Hajiya matar Ya Mahmud ce mutuniyar ki da Kika Gama maganarta dazu to gata 'yar halak ta kiraki".
"Ga Hajiyar ku Gama gaisawa Dan ba barina zatayi muyi hirar kirki ba idan Baku gaisa ba tunda nazo take you min zancenki".
Wayar ta mayar Mata ta nemi guri ta zauna.
" 'yar Nan Daman kece ki kak'i yi min bayani dan Ashatta".
Gaishe da Hajiyar tayi tana fadin.
"Cewa nake Zaki ganeni fa, Daman kiranki nayi na gaisheki Kuma na fada Miki ciwon Nan na cikina ya narke yanzu babu shi".
Wata zabura Hajiya tayi kamar yarinya tana fadin. "Kai Masha Allah kice nayo shiri na taho Azare na kawo Mik wani maganin saboda bibiko da Kuma aasske- sassake saboda sanyin dake Hana Yara haihuwa kinsan yanzu kuma sai a Fara shirye-shiyen haihuwa Kwana kadan ai sai laulayi, Dan ma naji labari mijin naki ya Kara yin halin nasa ya fice daga kasar wallahi sai kin jajirce kin zamar masa karfen kafa sannan zakiji dadin aure, Amma Kika zauna sanyin Nan sai kinyi tsa-tsa a banza Naga shi matan ma basa gabansa ta Neman kudinsa kawai yake, Kullum mutum na sama kamar tsuntsu to kinji dai na fada Miki".
Baki bude Rukayya ke kallon Hajiyar.
[2/7, 11:32 PM] +234 906 821 6318: * AUREN HUCE HAUSHI*
Chapter 25 · 0% Book details